Free chapter · Read without an account
THE NEWS WE NEVER EXPECTED
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER FORTY-EIGHT: 48
THE NEWS WE NEVER EXPECTED
JIDDAAH BARKUM
———
Bayan sun ɗan huta a ɗakin Inteesar na kusan awa guda, suka tashi suka yi freshen up gaba ɗayansu, Farida ta yi wanka ta canza zuwa wata doguwar rigar cotton mai launin sky blue, yayin da Inteesar ta saka wata kyakkyawar peach-coloured home gown, da suka gama shiryawa, suka sauko ƙasa tare, tun kafin su isa dining area, ƙamshin abinci ya bugi hancin Farida, ta tsaya cak, “Subhanallah!” Inteesar ta juya tana kallonta, “Me kuma?” Farida ta dafa cikinta, “Wallahi yunwa nake ji kamar ban ci abinci ba tun shekara ɗaya,” nan take Inteesar ta fashe da dariya, “Kin zo tun safe, ba ki ci abinci ba, kin tsaya surutu,” ta faɗa cikin raha, Farida ta harare ta tana dariya, suka shiga dining area, an riga an shirya musu abinci, jollof rice, grilled chicken, salad da chilled juice, Farida ta zauna tana kallon abincin, “Wannan gidan naku ba ya son baƙi su rame, abincin mu biyu kamar na mutum goma ne!” Inteesar ta yi dariya tana zama, “Ki fara ci tukuna,” ba tare da ɓata lokaci ba, Farida ta ɗauki spoon, “Bismillah,” suka fara cin abincin cikin natsuwa, sun ɗauki wasu mintuna suna cin abincin ba tare da wata magana mai yawa ba, sai bayan sun ɗan ci ne Farida ta ajiye spoon ɗinta, ta juya tana kallon Inteesar, wani murmushin tsokana ya bayyana a fuskarta, Inteesar ta gane irin kallon nan, nan take ta ɗaga gira, “Meye?” Ta tambaya tana zaro wa Farida ido, Farida ta yi dariya, “Ban ce komai ba,” “Na san abin da za ki faɗa,” Farida ta jingina da kujera, “Toh yanzu dai…” Ta ɗan matsa gaba, “Ki ba ni labarin Aliyu,” Inteesar ta lumshe ido tana murmushi, “Wanne labari zan ba ki?” Farida ta girgiza kai, “Yau ba za ki tsira ba,” Inteesar ta ɗauki glass ɗin juice ta sha, “Me kike son ji?” “Komai,” “Komai kuma?” “Daga farko har ƙarshe,” Inteesar ta yi murmushi, “Tun daga farko?” “Tun daga ranar farko,” Farida ta haɗe hannayenta, “Ina sauraro,” Inteesar ta sauke numfashi, sai wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskarta, ta fara ba ta labarin yadda suka fara haɗuwa, yadda suka fara magana, da yadda komai ya fara a hankali, Farida kuwa tana sauraro kamar wadda ake ba wa labarin wani film mai ban sha’awa, lokaci-lokaci tana zaro ido, wani lokaci kuma ta fashe da dariya, da Inteesar ta gama ba ta wani ɓangare na labarin, Farida ta dafa ƙirjinta, “Kaiii!” Inteesar ta kalle ta, “Me?” Farida ta nuna ta da spoon, “Lalle, Intee, haka kika faɗa soyayya sosai?” Nan take Inteesar ta zaro ido, “A’a!” “Wallahi kin faɗa, ji fa yadda kika saki jiki kina zuba mini labarin Aliyu!” “Ban faɗa ba,” Farida ta fashe da dariya, “Toh waye yake murmushi idan sunansa ya bayyana a waya?” Inteesar ta buɗe baki za ta yi magana, a dai-dai lokacin ne wayarta da ke kan table ta fara ringing, dukansu suka waiga, sunan da ya bayyana a screen ya sa Farida ta saki dariya, Mi Amor ❤️ “Inteeeee!” Farida ta faɗa tana dariya, Inteesar ta kai hannu za ta ɗauki wayar, amma kafin ta kai gare ta, Farida ta fisge ta, “Farida!” “Ki bari, ki ba ni wayata!” “A’a wallahi, ba zan ba ki ba sai na ɗaga,” ta miƙe da sauri daga kujerarta tana gudu kaɗan, Inteesar ta biyo bayanta, “Farida!” Farida tana dariya ta danna receive, ta ɗaga wayar kafin Inteesar ta kai gare ta, “Assalamu alaikum,” a ɗaya ɓangaren Aliyu ya ɗan yi shiru, bai gane muryar ba, amma a background ya ji muryar Inteesar, “Farida, wallahi ki ba ni wayata!” Nan take ya ɗan yi murmushi, “Humaira?” Farida ta fashe da dariya, “No,” Aliyu ya ɗan yi shiru, “Toh, wa kenan?” “Farida ce,” “Oooh…” Nan take ya tuna, “Farida… Yaya Adam, right? From Lagos?” Farida ta sake dariya, “Lallai an yi maka bayani na da kyau,” Aliyu ya yi murmushi, “Of course,” duk suka yi dariya, “Toh, ya hanya?” ya tambaya cikin mutunci, “Kin zo lafiya?” Farida ta kashe wa Inteesar ido ɗaya kafin ta amsa, “Alhamdulillah,” “Madallah,” sai ta ɗan gyara zamanta, “Angonmu…” Aliyu ya yi dariya a hankali, “Na’am?” “Mungode da kulawa fa,” Inteesar ta zaro ido, “Farida!” Farida ta yi kamar ba ta ji ba, ta ci gaba, “Na ga auntie ɗina har ta fara hasken amarci,” nan take Inteesar ta dafe goshinta, “Ya Salam!” Aliyu kuwa murmushi ya mamaye fuskarsa, ya jingina da kujerarsa, “Ni ma ai tana kula da ni dai,” Farida ta yi dariya, “Toh, Allah Ya sanya alkhairi,” “Ameen,” “Ya kawo ’yan biyu sau biyu,” Aliyu ya fashe da dariya, “Ameen ya Rabb,” “Ba guda ba?” “A’a,” “Twins guda biyu” duk suka yi dariya, Farida ta miƙa wa Inteesar wayar, “Ga angonki nan,” ta karɓa tana harararta, Farida kuwa ta koma kan kujerarta tana dariya, “Ni dai na gama aikina,” “Farida, please!” Inteesar ta faɗa kamar za ta yi kuka, Aliyu kuma yana dariya a ɗaya ɓangaren layin, Farida ta ɗaga hannayenta sama kamar wadda ba ta yi komai ba, “Ai gaskiya na faɗa,” Inteesar ta dubi wayar kafin ta kai ta kunnenta, sai ta koma ta zauna a kujerar dining ɗin, “Assalamu alaikum,” a ɗaya ɓangaren Aliyu ya yi murmushi, “Wa alaikumus salam, Babygirl,” nan take ta ji kunya saboda har yanzu kalaman Farida suna yawo a kanta, “Ya gida?” “Alhamdulillah,” “Ya aiki?” “Alhamdulillah, komai lafiya,” sai ya tambaya cikin kulawa, “Ke kuma, ya yau ta kasance? Na san kina da babbar baƙuwa, all the way from Lagos,” Inteesar ta sauke numfashi, “Alhamdulillah, gata nan duk ta dame ni,” ta faɗa tana murguda wa Farida baki, Farida kawai ta yi dariya tana girgiza kai, Aliyu ya yi murmushi, “At least, she will cheer you up ai,” “Uhmm,” kafin ya sake cewa, “School fa?” “Daidai,” “Kin dawo yanzu?” “Eh,” sai ta ɗan yi shiru kafin ta ce, “Don’t mind Farida,” Aliyu ya yi dariya, “Me ta yi?” Ta turo baki, “Ka sani,” Aliyu ya ƙara dariya, “Ai gaskiya ta faɗa,” Inteesar ta rufe idanunta, “Mi Amor…” “Na’am?” “Kada ka biye mata,” Aliyu ya jingina da kujerarsa yana murmushi, “A’a, gaskiya zan biye mata mana,” “Me?” Ta zaro ido kamar tana ganinsa, sai ya yi kamar yana tunani, “Toh, Babygirl…” “Uhmm?” “Da gaske za ki haifa mini ’yan biyu sau biyu?” Nan take Inteesar ta rufe idanunta, wani irin kunya mai daɗi ya mamaye ta, har ta kasa magana, a gefen dining table ɗin kuma, Farida tana kallonta tana dariya, tuni ta gane abin da ake faɗa, sai ta fara girgiza kai, Inteesar ta juya ta harare ta, Farida ta ƙara dariya, Aliyu kuwa yana ta murmushi yana jiran amsa, da ya ga ta yi shiru, sai murmushinsa ya ƙara faɗaɗa, “Babygirl?” Ta yi shiru kawai tana wasa da fingers ɗinta, “Uhmm?” Sai ya yi murmushi, “Answer me,” Inteesar ta dafe goshinta, “Ya Salam!” Aliyu ya yi dariya, “Toh, ina sauraronki, what about the double twins?” Ta kasa cewa komai, sai murmushi kawai take, Farida kuwa ta rungume pillow tana kallon Inteesar da wata irin dariyar tsokana, Inteesar ta harare ta, Farida ta yi gwalo tana dariya, sai Inteesar ta juya baya kamar ba ta gan ta ba, Aliyu ya ji shirun, “Farida tana wajen ko?” “Eh,” “Still watching you?” Inteesar ta yi dariya, “How did you know?” “Because I know sisters like her,” ta yi murmushi, “Bye, Mi Amor, I will call you later,” “Alright, my love, take care,” ta kashe wayar, Farida ta miƙe da gudu tana dariya, “Twins! Twins!” “Faridaaa!” Inteesar ta yi tsalle daga kujerarta ta nufi inda take, Farida ta ruga zuwa falo, Inteesar na bayanta, “Wallahi zan kama ki!” Farida tana gudu tana dariya, “Babygirl, answer me!” Ta kwaikwayi muryar Aliyu, nan take Inteesar ta ƙara sauri, “Ki tsaya!” Duk falon ya cika da dariyarsu, Farida na zagaye sofa, Inteesar na binta, “Twins sau biyu!” “Farida!” “Twins sau biyu!” Daga sama zuwa ƙasa, falon ya kaure da dariya, ba wanda zai kalle su ya ce ɗayansu auntie ce, ɗaya kuma niece, sun fi kama da sisters da suka taso tare, kuma a wannan lokacin, farin ciki ne kaɗai ya mamaye gidan, bayan sun ɗan yi gudu, Farida ta zauna tana haki, Inteesar ma ta zauna kusa da ita tana ƙoƙarin maido da numfashinta, ta ɗaga kai ta tarar Farida tana kallonta, murmushi ɗauke a fuskarta, Inteesar ta zaro ido, “Mene ne?” Farida ta lumshe ido, “Ya Allah!” “Me?” “Wannan ba soyayya ba ce,” Inteesar ta harare ta, Farida ta girgiza kai, “A’a, wannan ya wuce soyayya,” “Farida, me haka?” “A’a, ki saurare ni,” ta matsa kusa da ita, “Wallahi ban taɓa jin ki na magana da wani namiji haka ba,” Inteesar ta yi murmushi ba tare da ta shirya ba, “Really?” “Sure, you know it,” Farida ta kalleta sosai, “Kina son shi sosai, your face says it all, kina samun nutsuwa tare da shi ko?” Tambayar ta fito cikin tausasawa, ba tsokana ba, Inteesar ta yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan ta gyada kai a hankali, “Eh,” Farida ta yi murmushi, “Na gani,” “Me kika gani?” “Yadda idanunki suke haskawa idan kina maganarsa, yadda kike manta da kanki da kowa idan kina tare da shi,” Inteesar ta sauke kai tana murmushi, sai Farida ta rungume ta a gefe, “But don’t take things too much to heart, Inteesar, ki bi komai a hankali, kada ki dinga zafafa abubuwa da yawa, ki tuna, don’t love too much, don’t hate too much, because that too much can hurt you so much, okay?” A hankali Inteesar ta gyada kai, sai Farida ta yi murmushi ta sake rungumarta, “Allah Ya sanya alkhairi,” “Ameen,” “Ya sanya farin ciki da fahimta a tsakaninku,” “Ameen,” “Ya sa ki zama the happiest wife,” Inteesar ta yi dariya, “Ameen,” suna zaune a falo suna hira ne Nana ta sauko daga sama, sanye take da wata doguwar riga mai launin sky blue ta atamfa, ta ɗaura dankwalin kayan wanda ya zauna sosai a kanta, fuskarta cike da annuri, “Yaya Nana!” Inteesar ta kira ta, Nana ta yi murmushi, “Ku dai kun fara cin abinci ba ku kira ni ba, ku biyu idan kuka haɗu sai ku manta da kowa,” dukansu suka yi dariya, “Wa ya isa ya manta da ke? Mun zata ko kina sama kina cin abinci da Uncle ne fa,” in ji Farida, Nana ta yi murmushi kafin ta ce, “Gaskiya na ji daɗin zuwanki,” Farida ta yi murmushi, “Ni ma na ji daɗin ganinku sosai,” “Dama sai yanzu kika tuna da mu?” Inteesar ta tambaya, Farida ta harare ta, “Kamar ke da kike busy da Mi Amor,” nan take Inteesar ta kai hannu za ta bugi Farida, duk suka fashe da dariya, Nana ma tana dariya tana kallonsu, “Ku dai ku ƙyale Intee, duk kun sa mata ido,” Farida ta ɗaga gira, “Yaya Nana, ke ma kina goyon bayanta?” “Tabbas,” Inteesar ta yi murmushi cikin nasara, “Kin gani?” Farida za ta sake magana kenan, sai Nana ta ɗan yi shiru tana murɗe fuska, kalaman suka tsaya a bakinta, ta kai hannu ta ɗauki ruwa, ta sha kaɗan, Inteesar ta lura, “Yaya Nana, lafiya?” Nana ta girgiza kai, “Lafiya lau,” amma ko ita kanta ta ji jikinta ya ɗan canza, tun safe take jin wani irin kasala, sai dai ta ɗauka gajiyar aiki ce, Farida ta ce, “Ki ci abinci mana,” Nana ta ɗan yi murmushi, “Zan ci,” Farida ta miƙe ta debo mata abinci ta kawo mata, “Thank you,” ta faɗa a hankali, sai ta ɗauki cokali ta kai abincin bakinta, amma da ta haɗiye, sai ta ji wani irin tashin zuciya, gabanta ya faɗi, ta ajiye cokalin nan take, Inteesar ta sake kallonta, “Yaya Nana?” Nana ta miƙe tsaye da sauri, “Excuse me,” ba tare da ta ƙara magana ba, ta juya da sauri ta nufi toilet, Inteesar ta dafe goshinta, “Me ya same ta?” Farida ta miƙe, “Kinga yadda fuskarta ta canza?” Kafin su ƙarasa magana, sai suka ji sautin amai daga toilet, nan take suka kalli juna, “Yaya Nana!” Inteesar ta ruga ta nufi toilet ɗin, Farida na biye da ita, suna isa bakin toilet ɗin, sai suka tarar da Nana tana jingine da sink tana amai, Inteesar ta shiga a firgice, “Subhanallah!” Ta matsa kusa da ita, “Yaya Nana, me ya same ki?” Nana ta girgiza kai, “Ban sani ba,” a dai-dai lokacin ne suka ji buɗewar ƙofa, Yaya Umar ne ya sauko, da alama ya ji abin da ya faru, yana fitowa daga sashensa, da ya hango Farida tsaye a bakin toilet, gabansa ya faɗi, “What happened?” Ya tambaya cikin sauri, kafin su ba shi amsa, sai ya hango Nana, nan take ya ƙarasa gare ta, “Sweetheart!” Muryarsa ta canza gaba ɗaya, ya tsaya kusa da ita, ya kai hannu ya riƙe kafaɗarta, “What’s wrong?” Nana ta yi ƙoƙarin murmushi, “Babe, I’m okay,” “No,” ya amsa nan take, “You are not okay,” ya kai hannu ya taɓa goshinta, “Kina jin zazzabi?” “A’a,” “Dizziness?” “A’a,” “Headache?” Nana ta yi ɗan dariya, “Babe…” Amma Umar bai yi dariyar ba, fuskarshi ta nuna alamun damuwa sosai, Inteesar da Farida suka kalli juna, Farida ta raɗa mata a hankali, “Yana sonta sosai,” Inteesar ta yi murmushi, ko makaho zai gane, Umar ya sake kallon Nana, “Since when?” “Yanzu kawai na ji tashin zuciya,” “Kin ci wani abu a waje?” “A’a,” “Are you sure?” “Yes,” ya yi shiru, sai ya riƙe hannunta, “We’re going to the hospital,” Nana ta girgiza kai, “A’a, Babe,” “No,” ya katse ta, “No, sweetheart,” ya matso kusa da ita, “Wife, we’re going,” Nana ta ɗan yi dariya, “Ka cika damuwa, Babe, it’s not something big to worry about,” “Maybe, but we are going now, wife, we are still seeing a doctor, and don’t argue again,” ya faɗa yana tsare ta da ido, Nana ta ga daga fuskarsa cewa ba zai sauya shawara ba, sai ta sauke numfashi, “Okay, sir,” ta faɗa tana murmushi, nan take ya ji sanyi a ransa, “Good,” ya amsa, Farida ta murmusa, Inteesar ma ta kasa ɓoye nata murmushin, amma Umar bai damu da su ba, duk hankalinsa yana kan Nana, ya juya yana riƙe da hannunta, “Let’s go,” suka fito, Inteesar da Farida na biye da su a baya, Umar ya taimaka wa Nana ta zauna a kan sofa, sannan ya haura sama ya ɗauko mata hijab, su ma Inteesar da Farida suka ɗauko nasu hijab ɗin, suka shirya, daga nan suka rankaya gaba ɗayansu zuwa asibiti.
Bayan kusan awa guda, suna zaune a waiting area na asibitin, Nana tana gefen Umar, Inteesar da Farida kuma suna zaune a ɗaya gefen, sai yanzu ne hankalin kowa ya ɗan kwanta, banda na Umar, tun mintuna goma da suka gabata, sau uku ya tambayi receptionist ko result ɗin ya fito, har Farida ta fara dariya, “Uncle,” Umar ya kalleta, “Yes?” “Patient ɗin kai ne ko Yaya Nana?” Inteesar ta yi dariya, har Nana ma ta yi dariya, amma Umar ya girgiza kai, “We are talking about my wife’s sickness, Farida,” duk suka sake dariya, Nana ta jingina da kujera, “Babe,” “Uhmm?” “Relax,” ya kalleta, “I am relaxed,” nan take ta ce, “No, you’re not,” duk suka fashe da dariya, kafin Umar ya ba da amsa, ƙofar office ɗin doctor ta buɗe, likitar ta fito tana murmushi, “Mrs. Umar?” Nan take kowa ya yi shiru, Nana ta miƙe tsaye, “Yes,” likitar ta kalli file ɗin hannunta, sai murmushinta ya ƙara faɗi, “Congratulations,” duk suka tsaya cak na wasu daƙiƙu, kamar babu wanda ya fahimci abin da ta faɗa, Nana ta lumshe ido, “Sorry?” Likitar ta sake murmushi, “Congratulations,” sai ta dubi file ɗin, “You are pregnant,” duk suka yi shiru, wani irin shiru ne ya mamaye wajen, Nana ta tsaya cak, “Me?” Likitar ta yi dariya, “You are approximately eight weeks pregnant, which means about two months,” nan take idanun Nana suka cika da hawaye, ta dafe bakinta da hannayenta biyu, kamar ta kasa numfashi, “Babe…” Ta furta cikin rawar murya, Umar ya tsaya yana kallonta, shi ma kamar bai ji da kyau ba, “Two months?” Likitar ta gyada kai, “Yes, everything looks fine,” Nana ta juya ta kalli Umar, hawaye na farin ciki suka fara zubo mata, “Babe…” A wannan karon, Umar ma ya kasa ɓoye yadda idanunsa suka canza, ya matso kusa da ita, ya kama hannunta da ƙarfi, kamar yana tabbatar wa kansa cewa gaskiya ne, “Sweetheart…” Muryarsa ta yi ƙasa, “Alhamdulillah,” Nana ta fashe da kuka, kukan farin ciki, shekaru bakwai, cikakku, na jira, na addu’a, na fata, na haƙuri, yau Allah Ya amsa, Umar ya rungume ta a hankali, ya manna goshinsa da nata, “Alhamdulillah,” ya sake furtawa, “Alhamdulillah,” Inteesar kuwa ta tsaya tana murmushi, murmushin da ya cika fuskarta gaba ɗaya, Farida ta kama hannunta, dukansu suna kallon ma’auratan, zuciyoyinsu cike da farin ciki, a karo na farko cikin shekaru bakwai, Umar da Nana suna dawowa gida da labarin da suka daɗe suna jira, labarin da zai sauya rayuwarsu har abada.