Free chapter · Read without an account

Chapter 42

by Sayyada barrister · BIYU A ƊAYA

BIYU A ƊAYA 
   (Don't judge a book by its cover)



Page 42
Sayyada barrister 
***
YOTA 13 
The five ink legends



Sit palourn ya yi, ba a jin motsin komai sai ƙarar AC da standard fridge da ke aiki, sai kuma standard fan dake kaɗawa. Ba ki ɗaya sun zuba wa Dr Waahab na mujiya cike da mamaki, yarinyar da yake so tana ƙasar Ghana!

A hankali Dr Waahab ya sauke numfashi ya ce 

"Eh a ƙasar Ghana take, ina me neman alfarmar man da ku nema min auranta"

Mamaki duk ya kashe su zaune, musamman Daddy jin ɗansa yana neman alfarmar a aje a nema masa auren...

"Kai ma wasa kake yi, waye ne zai bar abin da ya ke yi ya je har wata ƙasa nema maka  aure?"

Cewar Alhaji babba, jikin Dr Waahab ya soma rawa a hankali, gumi ya cika masa goshi, duk da sanyin da yake palourn, ya kasa ci gaba da magana, Abbie ya ce

"Haba Babangida yanzu duk cikin ƙannenka babu wacce ta yi maka sai wancan ta Ghana?"

DR Waahab ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya ɗago suka haɗa ido da Sa'eed, jinjina wa Dr Waahab kai ya yi alamun ya amsa da eh. Runtse idanunsa ya yi a hankali ya ce

"Ayi hakuri ita ce zaɓi na, na yi mata alkawarin zan koma gare ta"

"To hell with your promise, idan kai ba ka da hankali to mu muna da shi"

Cewar Daddy, Abban Ashfat ya ce

"Waseem abi abun a hankali, kai Babangida ya za ka kawo abin da ba zai yu ba, abu mafi sauƙi shi ne, muna sauraron ka, ka zaɓi koma wacece a cikin wannan Ahalin za a aura maka ita"

"Daddy ayi hakuri Angel ce zaɓi na"

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun"

Shi ne kalmar da ke fitowa daga bakin iyayensa, Alhaji ƙarami ya ce

"Ka ji wani suna sai ka ce na babyn roba, wai Angel, shi ne matsalan tafiye-tafiye"

"Aiko sai dai ya hakura da ita, don mu ba za mu amince ya auro wata wacce take ba ƴar wannan Ahalin ba, kai koda a wannan garin take"

Cewar Daddy, Abbie ya ce

"Mu bi abin a hankali, a ba shi lokaci ya je ya yi tunani"

"A'a ba za ayi haka ba, a nan za a yanke hukunci"

Cewar Alhaji ƙarami, Dr Waahab ƙirjinsa ya sananta bugu, tsoron sa ɗaya kada a sanya shi karya alkawarin da ya yi wa Bilqees, Alhaji babba ya ce

"Tun ɗazu abu ɗaya ku ke ta maimaita wa, maganar gaskiya ita ce, babu wanda zai fita wata ƙasa nema masa aure, batun ma ya yi mata alkawari bai taso ba, kawai babu shi babu auranta"

"Ya Hayya Ya Qayyum birahmatika astagees"

Shi ne abin da Dr Waahab yake karantawa cikin zuciyarsa, ji ya yi kamar ana binne sa cikin rami da ransa, ya zai yi? Ya rasa number Angel, kuma yanzu iyayensa su ce ba za su nema masa auren ta ba?...

"Na ji Mamie nka tana cewa za ku daidaita sakaninku da Ashfat, to ya abin yake?"

Cewar Daddynsa, ƙirjin Dr Waahab kamar ya tsage ya fito sabar tashin hankali da bugun da yake yi, musamman jin an ambaci sunan Ashfat, zai yi magana Alhaji babba ya ce

"Shi kenan, mun ɗaga masa ƙafa zuwa wani sati, su daidaita kansu kamin mu zauna mu saka ranan biki"

"Hakan ya yi Alhaji babba, Allah ya ci gaba da haɗa kan mu ba ki ɗaya"

Cewar Daddynsa suka amsa da 

"Amin"

Abban Ashfat ya ce

"Ah Waseem ka ce surki na ne ma?"

Sai raha suke yi, suna jinjina al'amarin, Dr Waahab kamar ya sanya kuka ya mik'e ya fito jiki a sanyaye, Sa'eed ya biyo shi a hankali ya daga ƙafaɗarsa tare da cewa 

"Aboki dakata mana"

Dr Waahab ya tsaya, sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya da ƙarfi, ya jingine da jikin garu, ya kurawa Sa'eed idanu bai ce komai ba...

"Please bro kada ka sanya wa kanka damuwa, ka nutsu ka yi tunani"

"Sa'eed ba komai, ni kuma irin tawa ƙaddarar kenan"

"A'a kada ka ce haka, ai ba a ɗaura maka aure ba, har yanzu kana da lokacin da za ka ci gaba da addu'a da neman zaɓin ubangiji"

"Haka ne na gode sosai, zan ƙarasa ɗakina"

Sa'eed ya yi masa rakiya har ɗakinsa sai da ya tabbatar Dr Waahab ya kwanta sannan ya fice. Runtse idanunsa ya yi yana jin komai ya fice masa a zuciya, musamman cewa da aka yi su daidaita kansu da Ashfat, shi ba wai ya tsane ta bane, kawai bata ra'ayin sa matsayin wacce zai yi rayuwa da ita, kalmar so guda ɗaya ce kuma babu ya furta ta wa Angel...

Yana ta zancen zuci bacci ya ɗauke shi, ya yi mafarkin Angel tana ta kiran sunan shi, a lokacin da ya farka ya haɗa gumi da ƙyar ya yi ta karanta addu'oin sannan ya samu ya koma bacci yana mamakin mafarki da rana, sai azahar ya tashi ya yi sallah bai iya ya fito ba sai bayan sallah la'asar ya yi wanka ya yi shirin zuwa wajen aiki yana zaune bakin bed yana ɗaura wrist watch nasa aka turo ƙofar ɗakinsa.

A hankali ya ɗan waigo yaga Mamie ce, ta ƙaraso tana cewa

"Ashe dai kana ciki? Shirun ya yi yawa"

Ta zauna ba kin side bed drower, ya ɗan ɗago tare da cewa 

"Ina wuni Mamie"

"Lafiya Babangida, in ce lafiya ka killace kan ka a ɗaki?"

Da ƙyar ya iya sauke numfashi ya ce

"Mamie bacci na yi wunin yau"

"Za ka tafi wajen aiki yanzu?"

"Eh night duty gare ni"

"To ya yi kyau Allah ya tsare"

"Amin Mamie"

"Daddyn ka ya zo min da albishir me daɗi, akan batun auren ka da Ashfat"

Kamar ya yi kuka amma ya daure ya ce

"Eh Mamie"

"To daman ni ma ita ce zaɓina, kaga yadda take kulawa da ni a lokacin da ka tafi ƙasar Ghana, yarinyar kirki ne kuma hakan zai sake haɗa kan mu dukkanin mu"

Sauke numfashi Dr Waahab ya yi, ya ce

"Mamie lokacin tafiya na aiki ya yi, ya jikin Mommie?"

"Da sauƙi, to sai da safe za ka shigo ko?"

"Eh in sha Allahu"

"Jikinta da sauƙi Jamila ta bata magunguna ta sha ta yi bacci ma"

Ya mik'e ya saɓa side bag nasa ya ɗauki wayar sa, Mamie ta fito, ya bi bayan kai tsaye ya iso parking space ya tadda Sa'eed zaune yana waya, yana ganinsa ya katse ya taso zuwa gare shi yana cewa

"Likita bokan Turai har an fito?"

"Sa'eed na fito sai kuma da safe"

"To ba damuwa mu haɗu gobe da safe a side"

"Okay"

Cewar Dr ya shige cikin motar sa kai tsaye sai hospital. Dr Waahab tun da ya iso office nasa ba abin da ya iya tabuka wa, har 10:00 pm yana zaune a office Dr Faisal ya shigo yana cewa 

"Special doctor evening"

"Dr Faisal barka dai ya aiki?"

"Alhamdulillah na samu maka number amma ban san na waye ba"

Cike da farin ciki Dr Waahab ya ce

"Bani"

Ya miƙa masa yawar ya ce

"Ka kwafe ta"

Ya kwafe sannan Dr Faisal ya fice daga office nasa, a take Dr Waahab ya kira layin a kashe ya hakura zuwa anjima zai kira, har cikin dare number baya shiga, gari yana wayewa ya dawo gida, duk jiki a sanyaye, ya yi parking ya fito ɗakinsa ya nufa, ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet ya watsa ruwa ya fito ya sanya jallabiya ya kwanta, cikin bacci ya ji ana nocking ya buɗe idanunsa ya tashi ya buɗe ƙofar Sa'eed ya gani, ya sauke numfashi ya dawo ya zauna bakin bed tare da cewa 

"Sa'eed ka ji ni shiru ko?"

Ƙarasowa ciki ya yi ya zauna kan stool ya ce

"Eh da fatan lafiya?"

"Bana jin daɗin jikina shi ne na kwanta"

"Look Waahab kada ka sanya wa kan ka damuwa, in dai Angel matar ka ce, babu me hanawa, in kuma ka ga ba ayi da ita ba daman ba matar ka bace"

Murmushi Dr Waahab ya yi, a hankali ya ce

"Haka ne, amma i really love her, i want her by my side, ta haɗu, irin matar da nake so na yi rayuwa da ita"

"Na fahimci yanayin da ka ke ciki bro, mu ci gaba da addu'a"

"In sha Allahu"

Sa'eed yana ta jan shi da hira har rana ta yi sosai suka koma side na shi, acen su ka yi breakfast...

*********

Ammie na ɗaka tana gyara bed, ta ji sallama a palour ta leƙo ganin Aunty Nazeefa ce ya sa ta ƙaraso ta zauna kan kujera tare da cewa 

"Nazeefa ke ce tafe?"

"Barka da rana, ai ban ga ta zama na na ce sai na zo na fesa miki"

"Ai ke kam ba ki rabo da labarai, to me ya faru?"

"Uhm wannan Yaron ɗan wajen Bilkisu, shi ne ya zo mana da bidi'a cikin gidan mu"

"Ikon Allah Dr Waahab?"

"Eh mana, ba ki ji abin da ya faru jiya ba?"

"A'a ban ji ba, me ya faru?"

"Hajjiya ina Abban Ashfat ya ba ki labari"

"Kin san halinsa ba kasafai yake sanar dani wasu abubuwa ba"

"To jiya a ɗakin taro duk matasan gidan nan sun zaɓi matan da za su aura a cikin kannensu amma Dr Waahab ya ce sam shi a waje ya samo ba ya son auren haɗin gida"

Sauke numfashi Ammie ta yi, taji babu daɗi a tunanin Ashfat zai zaɓa...

"UHM abin ya bani mamaki, kin ga fah ka ƙi jinin ka"

"To me kuma mazan suka ce?"

"Alhaji ƙarami ne yake sanar dani sun ce sam sai dai ya zaɓo a cikin Ahalin nan"

"To a ina ya samu wacce zai aura?"

"Ke wai a Ghana"

"Ghana kuma?"

"Eh a cen fa, a wannan tafiyar da ya yin ne ya haɗu da yarinya"

"To abin da mamaki kam, Allah shi kyauta"

"Amin"

Sai hira Aunty Nazeefa take yi mata, amma ita hankalinta yana wani wajen tausayin Ashfat ta ji yadda take son Waahab abin ma har haushi yake bata...

"Kin ga tafiya zan yi sai anjima"

"To Nazeefa na gode Allah huta gajiya"

"Amin"

Ta fice, Ammie ta rafka tagumi tana tunani...


********************

Abin ka da babban family nan da nan zance ya karaɗa ko'ina akan zaɓin Dr Waahab wasu su ce ko su sun tashi yin aure irin nasa za su yi, wasu kuma cewa suke bai dace ba, duk da haka babu wanda ya sake tunkarar sa da zancen.

Sai dai ya yi sanyi damuwa duk ta bayyana kan fuskarsa, ga shi yana kiran layin da Dr Faisal ya ba shi na wani ma'aikacin ALAJA SPECIAL RESTAURANT amma baya shiga.

Kwance yake a ɗakinsa ya zurfafa cikin tunanin, bai ma ji shigowar kowa ba sai dai ya ji murya akan sa

"Yanzu ka kyautawa kan ka?"

A hankali ya ɗan ɗago ganin Daddynsa ne ya sa ya tashi ya zauna, tare da cewa 

"Daddy ban ji shigowar ka ba"

"Ai ba za ka ji ba, hankalin yana cen Ghana"

A hankali ya sauke numfashi tare da cewa 

"A'a Daddy kawai ina hutawa ne"

"To na ji kuma na zo mu yi magana ne"

"To Daddy"

Ya zauna a bed side ya ce

"Mun yi magana da mahaifiyar ka, ta ce ita zaɓinta Ashfat ce, kuma ni ma haka ne, don haka ka ma cire wata cikin ranka"

Da ƙyar Dr Waahab ya iya sauke ajiyar zuciya, kamar ya yi hawaye amma ya jure ya ce

"To Daddy Allah ya yi mana zaɓi mafi alkhairi"

"Amin, bana so na sake jin wani abu daga baya"

"To Daddy"

Daddy ya fice, Dr Waahab da ƙyar ya tashi ya watsa ruwa ya fito zuwa side na Mommie, ya tadda duk suna zaune Jamila, Suhaima, Hauwa da Teemah suna hira, shigowar Dr Waahab yasa suka ɗan dakata suka gaishe shi ya amsa, hankalin yana kan Mommie cikin kulawa ya ce

"Sannu Mommie ya kike jin jikin ki"

"Alhamdulillah bana jin komai"

"To ya yi kyau haka ake so, ki ci gaba da shan magungunan ki"

"To Yarona, me ya same ka duk ka yi sanyi?"

Ya ɗan yi murmushi ya ce

"Ba komai Mommie bacci na yi bai jima ba na tashi"

"Ah hakan ma ya yi"

Ya yi mata sai anjima ya dawo side na Mamie tana zaune ta saka tv a gaba tana kallon labarai, ya yi sallama ta amsa ya zauna ta ce

"Ka gama fushin?"

Ya ɗan ƙwakulo murmushi ya ce

"Fushi kuma Mamie?"

"Eh mana kana so ka haɗa ni da ƴar'uwata, bayan an saka ran Ashfat ita ce matar ka shi ne za ka ce wai ka samo wata a cen Ghana"

Ya ɗan gyara zamansa a hankali ya ce

"Mamie babu soyayya a sakanina da Ashfat asali ma a matsayin ƙanwa na ɗauke ta, ban..

"Kai fita cikin ido na, bana son jin komai babu kai babu auran kowacce mace in ba Ashfat ba"

"To Mamie"

Ya mik'e tare da cewa 

"Na tafi"

"Allah ya bada sa'a"

"Amin"

Ya fice, kai tsaye zuwa ɗakin Sa'eed shi zaune yana cin abinci ya zauna cikin ɓoye damuwarsa ya ce

"Ka kammala cin abinci ka yi min rakiya"

"To Angon Angel"

Bai san sanda murmushi ya suɓuce masa ba, ya ce

"Tarihinta zai koma mafarki"

"Don't give up bro, har yanzu akwai lokaci"

"Haka ne, amma Mamie ta ce Ashfat ita ce zaɓinta"

"Ka yi hakuri bro komai zai wuce, Khairan in sha Allahu"

"Allah ya sa"

"Amin"

Yana kammala cin abinci suka fice shan iska...

*************

DR Waahab yana zaune a ɗakinsa, yana danne danne a system nasa, ya ɗauki wayar ya kira layin Ashfat ta ɗauka ya ce

"Ki zo ina ɗakina"

"Ok"

Ta faɗa ya katse kiran, babu jimawa ta shigo sanye da doguwar riga ta Abaya maroon color ta yi mata kyau, ta yi sallama ya amsa ba tare da ya daina abin da yake yi ba, ta zauna kan carpet tana kallon sa, a nutse yake komai, sai taga ya ƙara kyau, kayan dake jikinsa sun yi masa kyau.

Ya kashe system nasa ya juyo sosai yana kallon ta, ta sudda kai ƙasa, shiru ya ratsa a hankali ya kira sunanta 

"Ashfat"

Ta ɗago suna kallon juna, duk da ya yi mata kwarjini da yawa amma kuma ganin ya bata dukkanin hankalinsa yasa take sake kare masa kallo...

"Magana nake so mu yi ta fahimta"

"To"

Ta faɗa, ya ci gaba da cewa 

"A'isha ban taɓa jin tsanar ki ba, ko haushin ki, ko wani abu mara dad'i game dake, ni yayanki ne, kuma ina son farin cikin ki, zan iya tsayuwa a rayuwarki na inganta ta, ba zan bari wani abu ya cutar dake ba, that's my promise not only you, what i mean akan ku dukkanin ƙannena"

Ƙirjinta yana ya bugawa, ta sauke numfashi tare da sudda kanta ƙasa, ya ci gaba da cewa 

"Zan so ki aure namijin da yake burin mallakar ki, yake jin cewa ke farin cikin sa ne, ko da kuwa ba ki sonsa zai ba ki kulawa da ki aure namijin da baya jinki a matsayin matar da zai yi rayuwa da ita, za ki cutu, za ki ji da ba ki aure shi ba"

Hawaye suka gangaro mata, tana jin numfashinta ya fara sama² ya ci gaba da cewa 

"I'm on the stage as you are, apart of love, na san yadda ki ke ji, ni ma haka nake ji akan Bilqees, ina sonta, ina so ta zame uwar ƴaƴana, ina so mu kasance a inuwa ɗaya"

"Ashfat zan iya amincewa na aure ki, amma ba zan iya ba ki farin ciki ba, kallon ƙanwata nake yi miki"

Kuka ta fara, da ko da hali a lokacin za ta cire son da take masa tayi fatali da shi, wannan ai wulaƙanci ne ya sanyata gaba yana faɗa mata wata yake so ba ita ba...

"Me yasa kika goge number Bilqees?"

Da sauri ta ɗago jikinta ya soma rawa, ba kinta ma haka ta ce

"Ba ni ba ce"

"Ke ce, Ashfat ke ce kada ki yi min karya,

Ji ta yi ɗakin na juyawa da ita, kamar ta ƙwala ihu, ya ci gaba da cewa 

"Why?"

Ta sudda kanta ƙasa, tana ci gaba da hawaye, ya ce

"Me yasa za ki yi mata haka? Kada ki so kan ki da yawa...

Ai bata tsaya ya ƙarashe ba ta fice da gudu kai tsaye ɗakin Mommie ta shiga, inda nan ne ya koma wajen hiran su, Mamie Ammie da Aunty Nazeefa suna zaune daga gefe suna hira. Jamila na kwance, Suhaima, Hauwa da Teemah suna gefe su ma suna hira.

Kamar daga sama suka ga Ashfat ta faɗo musu bata ma ganin gabanta ta ƙwala ihu tana cewa

"Zan mutu, na shiga uku Ya Wahaab baya sona"

Kallon ta suke sai kuka take yi, Jamila ta ce

"Ke Ashfat mene ne haka? Ya za ki shigo ki tsinka mana zuciya?"

"Aunty Jamila ya Waahab ya furta baya sona"

"Ke ki rufe wa mutane ba ki, saboda ya ce baya son ki shi ne kika shiga uku"

Cewar Ammie, Aunty ta ce

"Dole ta ji babu daɗi, ɗan'uwanta ne fa, ya ce baya sonta"

"Ashfat daga ina kike?"

Cewar Mamie, ta share hawayenta ganin ashe iyayensu na ɗakin, ta ce

"Ɗakin ya Waahab"

"Uban me ya kai ki ɗakinsa shi da ya ce baya sonki?"

"Shi ya kira ni"

Mamie bata ji daɗin furucin Ammie ba, ta ce

"Haba Ammie bai da ce ki ce haka ba"

"Hajjiya Balkisu abin da ciwo, a ce ɗan'uwanka ya ƙi ka"

Cewar Aunty Nazeefa, ran Ammie ya sake ɓaci ta ce

"Ki tashi ki koma side namu ina zuwa"

Tari Mommie ta fara, hankalinsu ya koma kanta, da ƙyar numfashinta ya dawo dai-dai, Ammie ta ja ɗiyarta zuwa bangaren su, Aunty Nafeesah ta bi bayansu...

Ran Mamie a ɓace ta fice zuwa ɗakin Dr Waahab, yana ci gaba da aikinsa ta shigo rai a ɓace ta ce

"Ka kyauta ya yi maka kyau, tun da nema ka ke yi ka tado rigima"

Ya mik'e tare da cewa 

"Subhanallah Mamie me ya faru?"

"Au tambaya ta ma kake yi, me ka faɗa wa Ashfat take kuka?"

A hankali ya sauke numfashi, jikinsa ya yi sanyi ganin yau ran Mamie ya ɓaci ya ce

"Ƙanwata ce maganar fahimta mu ka yi da ita"

"Babangida na faɗa maka bana so na ji ko na gani, ka ɓata wa kowa rai akan wannan batu amma naga yanzu ka girma ka kai ka yanke wa kanka rayuwar da ta dace da kai"

A hankali ya rage tsawonsa ganin tana tsaye, ya ɗan ɗago ya ce

"Mamie ki fahimce ni...

"Ba zan fahimci komai ba, tun da haka ne, ka yi abin da ya dace wa rayuwar ka"

Tana gama faɗin haka ta fice, ya sauke numfashi kamar ya yi kuka, wayarsa ta yi ringing kusan sau uku sannan ya ta shi ya duba ganin sabuwar number ce ya sa Bai kira ba, ya kwanta ganin dare yayi, aka sake kiran wayar, a hankali ya ɗauka tare da cewa 

"Hello"

"Yallaɓai likita...










Ayi hakuri da typing errors.



Comments and share fisabilillah

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol