Free chapter · Read without an account
Page 18
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 18
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Cikin tsananin bugawar zuciya ya sunkuya kasa ya Kara riko fuskar yarinyar cikin rudani, itama Mimi manyan idonta irin nasa sak ta sake ware wa tana budewa kamar yadda yake da nasa a duk lokacin da wani Abu ya basa mamaki, "Subhanallah" ya fada yana shafa fuskar ta.
Cikin sauri na matso gurin gabana yana faduwa na finciko Mimi nace "zo mu tafi"
Cikin shagwaba tace "Maaa to ai uncle din nan ne ya bige ni kamar ya karyan kafa ma"
Na bude baki xanyi magana naji muryar sa data fara shakewa yace "zo beauty muga kafar ko na karya din"
Ganin ya biye mata yasa ta cire hannun ta daga cikin nawa ta tafi gunsa tana turo baki, murmushi ya saki Wanda ya bayyana hakoran sa farare ya riko hannun ta.
Kara sunkuyar da kansa yai gun kafar sa cikin faduwar gaba yake kallon kafar ta shape din kafar sa ce sak banbancin kawai wannan ta Yara ce, lumshe idon sa yai yana ambaton sunan Allah a zuciyar sa.
Hannu Mimi ta dora a kansa cike da shagwaba tace "Uncle baka duba kafar ba har ynxu na gaji"
Saita kansa yai kafin ya duba kafar Tata duk da yasan ba wani abinda ya Sami kafar kawai ragonci take, dagowa yai yace "uhm beauty ashe raguwa ce keh haka ba kiji ciwo ba"
Washe baki tai tace "toh Masha Allah, Uncle kaima a school din nan kake MAA dita ma anan take da kyar ta yadda tazo dani sai da na dinga birgima a kasa ina ihu"
Gajeriyar dariya Azlan yai yace "ni teacher dinsu ne, mai yasa bata so tazo dake?"
Daga kafada Mimi tai tana ware hannu alamun itama bata sani ba
Jan kumatun ta yai yana rike Mata hannu yace "muje toh class din yanzu su Maa din taki zan koyar"
Da sauri na tari gabansu cikin tsiwa nace "Sir ka sakar min yarinya ta zan shiga da ita"
Bin ta da kallo yai tundaga Sama har kasa wai yarinyar ta lallai yarinyar nan ta raina Sama tabe baki kawai yai ya zagaye ta ya nufi hall din
Kamar zan kuka na bi bayan su GA Mimi ina hango ta sai zuba take masa.
Muna shiga Hall dn gaba daya ido ya dawo kanmu bama Mimi dake rike da Azlan, ganin idon mutane yasa nayi gurin Asma'u wacce itama idon ta zuba mana na Kai tsakiyar hall din Mimi ta daga murya tace "Maa ki tsaya ni toh"
Ido na lumshe ina dana sanin zuwa da Mimi da nai, banza nai mata kawai don haushin ta nake ji na zauna gefen Asma'u.
Kallon sa Mimi tai ta dago ta kalle ni harara na watsa mata sai ta juya gunsa tace “Uncle Maa haushi na take ji zata min fada bara naje gun ta”
Daga Mata kai kawai yai ta juya tana tafiya har ta iso gurina, a kan cinyata ta zauna tana murza idonta wai don kar na Mata magana, banza nai Mata na maida hankalina kansa.
Jikinsa duk wani iri yake jinsa sbd arba da wannan Yarinyar da yai kamar sa da ita har ta baci har yanayin dimple dinsa irn nata ne komai nata irin nasa ne bai wani tsawaita ba don baya cikin mood Mai dadi ko assignment bai bayar ba.
Gurin da muke zaune ya taho idonsa akaina, murguda baki nai na juyar da kaina gefe gabana yana faduwa, tsayawa yai a gaban sit din da muke ya miko wa Mimi hannu, ban wani damu ba don nasan Mimi bata da saurin sakewa da mutane amma ga mamakina sai Naga cikin sauri ta Mika masa hannu ta sauka daga jikina.
Juyawa sukai zasu fita haka yasa na mike nima da sauri na mara musu baya, muna fita daga hall din na kalle sa nace "Sir ina zaka kaimin yarinya ta"
Kallona yai yace "siyar da ita zanyi"
Wata harara na watsa masa kafin na dauke kaina na maida shi gun Mimi da ta sake rike hannun sa sosai tana wasa da zoben dake yatsar sa.
Kamar zan yi kuka nace "sir don Allah Ka sakar min yarinya mu koma kaga muna da lecture ynxu Kar lecturen ya shiga"
Daga kafadar sa yai yana tabe baki yace "ina ruwana ki koma mana"
Da sauri nace "Mimin fa"
Kallona yai yana kankance idonsa yace "in kun gama komai zaki iya samun mu a office dina"
Zaro ido nai nace "da Mimi zaka tafi office din naka wallahi baxan yadda ba yadda duniya take ba gaski....." Ban karasa ba saboda yadda ya juyo a fuskace yana kallona idonsa har ya soma kadawa zuwa jaa.
Da sauri na sa hannu na toshe bakina cikin tsananin tsoro don ni ban taba ganin sa cikin wannan yanayin ba, kuma Allah ya sani bansan na fadi abinda na fada ba.
Juyawa yai kawai da Mimi suka tafi ina tsaye har suka wuce hawaye ke kokarin zubo min gashi ba halin binsu don test muke da shi ynxu dole na koma hall kamar na fashe da kuka ina mitar baxan sake zuwa da Mimi ba.
Mimi kuwa suna tafiya tana masa hira yana biye mata har suka karasa office dinsa duk inda suka wuce sai an bisu da kallo don yadda suka jeru dinnan haka ya Kara fito da kamannin su da juna sosai.
Suna shiga office din Mimi ta kalle sa tana sakin hannun sa tace "Uncle nan ne office dinka"
Murmushi yai yace "eh kina sonsa"
Dariya tai tace "sosai ma yayi kyau kuma da akwai AC ina son Ac amma bamu da shi a gida".
Murmushi Azlan yai yace "kice wa Daddyn ki ya siya miki".
Turo baki tai tace "Banda Dad ni Maa tace Dad dina ya mutu baxai dawo ba."
Dan maida hankalin sa yai gun ta yace "wace Maa din taki?"
Murmushi tai cikin farin ciki tace "ai kaganta Uncle itace Maa dita muna zaune a gidan mu da Abba da Umma da Maa da Ya Aisha da Ya Kamal da Ya Khalil sai ni."
Sam shi bai gane mai take fada ba tace bata da Daddy kuma tace Abba da Umma, cikin son fahimtar maganan ta yace "kin ce baki da Daddy kuma kince Abba da Umma?"
Dariya tai tace "Abba baban Maa ne Umma ma Maman Maa ce ni kuma granny tace Ya Aisha Aunty nace Ya Khalil da Ya Kamal uncles dina ne” ta karashe tana washe baki.
Cikin Mamaki yace "ita MAA din taki wace ita?"
Turo baki tai tana Zama akan kujera tace "Maa ce fah Mamana toh Uncle".
Zaro ido yai yace "ita ce Maman ki?"
Daga masa kai tai tana juyi akan kujerar sa cikin nishadi, mamaki ne sosai ya rufe sa sai a lokacin ya tuna yadda take cewa ya ajiye mata yarta Ashe maman tace amma wannan Yarinyar har ya isa ta haifi kamar yarinyar nan.
Mikewa yai ya nufi gurin fridge dinsa, budewa yai ya dakko ice cream ya nufi gurin Mimi da shi, Zama yai shima akan kujera yace "zo musha Ice cream"
Washe baki tai ta matso kusa dashi ta zauna tace "Ina sonsa sosai Uncle"
Murmushi yai yace "what's ur name beauty?"
Debo ice cream dn tai a spoon tana kaiwa baki Saida ta shanye sannan tace "My name is Khadija B"
Kallon ta yai yace "meye ma'anar B din?"
Cikin rashin damuwa tace "sunan Maa ne Batul"
Cikin mamaki yace "me yasa baki sa sunan Daddy dinki ba?"
Tabe baki tai tana lasar lips dinta tace *Maa ce ta samin bansan sunan Daddy naba"
Shiru kawai yai don baya so ya takura yarinyar da tambaya ahakan ma yaga kokarin ta da alama tana da wayo sosai.
Shan ice cream din suka cigaba suna sha tana basa labarin school dinsu da friends dinta, biye mata yai sosai yake Jin kaunar yarinya tana ratsa shi, shi sam baya Wasa da yara ko zama a kusa da su bayayi a cewar sa ciwon kai suke sashi sai gashi ya zauna yana hira da yarinya.
Sosai ta sake dashi don ta gama basa labarin kowa na gidan su hadda yadda Maa dinta take da cin abinci sosai, har labarin Hidaya sai da ta fada masa da maman ta.
Kallon ta yai yace "ynxu Maa din taki baxa ta siya miki wani babyn ba ki dinga wasa"
Marairaice fuska tai tana kalar tace haka tace "Uncle wai baxa ta siyo min ba ai maman hidaya ta siyo mana, kuma ni na fison ita ta siyo min mu dinga kwana tare dukkan mu"
Rike haba yai yace "gaskia MAA bata kyauta ba zan lallashe ta amma ta siyo miki wani babyn koh?"
Tsalle tai tace "thank you uncle"
Jan kumatun ta yai yace "ki daina cemin uncle ni Daddy dinki ne tunda kince baki da Daddy"
Ware manyan idonta tai tace "da gaske Uncle Ka zama daddy na?"
Daga mata kai yai yana karantar farin cikin dake dauke a fuskar ta
Murmushi tai tana tsalle tace "toh Daddy kazo school dinmu nima na nunawa friends dina kai nace musu ga Daddy na su daina cewa banda Daddy."
Mikewa yai yace "zanzo har school din naku Beatty nace musu nine daddyn ki"
Rungume sa tai tana murna rike Mata hannu yai suka fita don yasan ynxu haka sun fito daga lecture din duk da baya jin zai iya bata Mimi ynxu sam baya son rabuwa da yarinyar haka kurin yake Jin son kasancewa da ita, hakan yana sashi tsintar kansa cikin farin ciki.
Cafeteria suka nufa duk inda suka wuce binsu ake da kallo kawai bama ynxu da mutane sosai suka fito, ko a jikin sa da yadda ake kallon su don shi baya son shirme.
Kaita yai ta zabi abinda take so bayan ya jido Mata ice cream da chocolate a leda, sosai ta ci abincin da aka kawo mata don tana ganin kaza tace masa ita take so, fried rice da kaza ya karbo mata sai ruwa, zuba mata ido yai yana kallon ta tana cin abincin ta cikin nutsuwa.
Daukar wayar sa yai kawai ya shiga mata hoto sai style take masa tana turo baki suna yi suna dariya, duk students din da suke gurin kallon su suke suna mamakin dama Mr Azlan yana Wasa da dariya haka.....
**********
Hawayena na goge na kalli Asma'u nace "kina gani har ynxu yaki dawo min da yarinya ta fa Asma'u"
Dafa ni Asma'u tai tace "ki taso muje office din nasa toh mu duba mu gani, amma dama ya san kune?"
Girgiza kai nai cikin nadamar zuwa da Mimi nace "ina fa ya san mu kawai kalan dangi ne ni ban taba ganin Saba ma Sai a school dinnan"
Rike habar ta tai tace "amma wai baki ganin kamar Mimi da Mr Azlan kuwa?"
Hade rai nai nace "ki daina yada min yarinya da Mr Wicked fah Asma'u ba abinda ya hada su"
Dariya Asma'u tai ta mike tace "muje toh mu dubo su toh Maman Mimi"
Mikewa nai ina rataya jakata a kafada nace "yau Mai rabani da Mimi sai Allah wallahi tana ji fa ina mata magana amma tai min banxa ta bisa sbd ta raina ni ba"
Ita dai Asma'u bata ce komai ba sai murmushi da tai kawai, office dinsa muka nufa nan muka yita knocking amma a banxa ba a amsa mana ba, wani student ne dake zaune daga gefe yace "baya nan fah"
Da sauri nace "ina yaje don Allah?"
Sai da ya dan kalle mu na seconds Sannan yace "kamar cafeteria ya nufa shida wata yarinya"
Da sauri nace "mun gode"
Hannun Asma'u na janyo mukai gaba, muna shiga cafeteria kuwa idona ya sauka akan su ga Mimi da gabanta ke shake da plate tana cin kaza shi kuma yana daukar ta hoto a wayar sa sai dariya Mimi take shi kuma yana murmushi.
Raina naji ya Kara baci hakan yasa na karasa gurin su ina huci, Mimi da ta kai cinyar kaza bakinta tana murmushi dago idon ta tai muka hada ido da sauri ta ajiye kazar ta mike tsaye tana mar mar da ido alamun rashin gaskia............
***