Free chapter · Read without an account

5-6

by Fauziyya Tasi'u Umar · GADON ZINA

Karɓe wayar yayi yace “Ke baki da hankali" cikin Masifa tace masa “eh mana Ni dama bani da hankali akan haƙƙina wlh ko dai a bani kuɗina ko kuma nayi tonon silili"  girgiza kai yayi ya matsa jikin loccar da yake aje kuɗi ya Zaro dubu biyar ya mika mata tace “Nawa ne wannan ɗin?" kwantar da murya yayi yace “5k ce Simah banida kuɗi zamu warware ai"  dukan table na gabanta tayi tace “Idan na karɓi 5k nayi ƙwai anan wajen kaga mal ka bani haƙƙina ko kuma nasa a karɓar min" sake Zaro wata 5k ɗin yayi ya ɗora mata yace “Na faɗa Miki banida kuɗi ki riƙe wannan ki jira anjima zan kiraki" karɓa tayi ta kirga ta zabga masa harara tace “Ga tsiya ga jaraba Aikuwa bazaka ƙara sha min nono ba shegiyar burar taka ce ma kamar magnet idan ana tunawa da ita Bazaa iya abin arziƙi ba" tana faɗin haka ta fice ta nufi wani shagon sai da Rufaida ta siya musu guda uku ta siya musu bread da suger ta nufi gida tana tafe cikin takunta na isa da ɗaukar hankali tana kaunar cingum kai da ganinta kasan tarbiyya dai babu ita a wannan waje, gida ta shiga da sallamarta ta ishe Mama ta dawo ta bankaɗa labulen ɗakin mama tana cewa “Mama wancan ɗan hau ɗin naje nayiwa hauka ya biyani haƙƙi....." maganar ce ta maƙale ganin maman nasu kwance ita da wani mutum a gado suna romance ɗin juna. Da sauri ta saki labulen ta juya baya tana wani irin haki saboda tsoro  duk da cewa ba yau ne karon farko da ta fara ishe Mama a wannan halin ba.
Sumsum ta shige ɗakinsu ta  aje kayan dake hannunta ta zauna daɓas a saman gadon suka kalli juna da Huda da take daddanna Wayarta tana shirin magana Huda ta tsayar da ita da cewa “Idan har ba zaki daina yiwa mama kutse ba to bazaki daina ganin abin da zai tashi hankalinki ba Simah Meyasa bazaki kiyayi shigar mata ɗaki ba" Ajiyar zuciya ta sauke tace “Amma Hudah wannan abin na Mama ya ƙazanta da yawa ina ganin cewa ko Abbanmu ne suke tare bai kamata su rinƙa irin wannan abin a inda hankalinmu zai kai ba hudah ai mun kai mata kuma mun kawo ƙarfin da bai kamata ace komai muna gani ba" taɓe baki Hudah tayi tace “To ita Bataga haka ba kuma Kema banda abinki har wata daidai kike nema a wajen mama matar da ta rantse da Allah bazata taɓa aikata daidai ba domin babu abinda daidai ta haifar mata sai tarin nadama" Kwanciya Simah tayi kanta na juyawa ita kam duk da iskancinta tana jin ciwo da baƙin cikin ganin mahaifiyarta a wannan hali saidai ko a fuska bata isa nunawa ba yanzu mama zata hau su da gorin da wannan sana'ar ta Karuwanci ta raine su tun basu kai mutane ba kuma da ita take ci gaba da rainon su har yanzu da suka isa mutane ubansu tunda ya gudu ya barta da cikin Simah bai ƙara waiwayarsu ba.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol