Free chapter · Read without an account
Chapter 24
Na shiga gidan a hankali, ina riƙe da ledar a hannuna. Da na shiga tsakar gida, sai na tarar da Baba da sauran mutanen gidan duk suna zaune a wurin, kamar suna jiran ganin abin da ke cikin ledar.
Na ji gabana ya faɗi. Na sunkuyar da kaina, na ƙarasa inda Baba yake zaune, sannan na ajiye ledar a gabansa. Ban iya ɗaga idona na kalli kowa ba, domin na lura da yadda suka mayar da hankalinsu a kaina da ledar.
Baba ya ɗaga kansa, ya kalli ledar, sannan ya ɗago idonsa ya kalle ni.
“Menene wannan, Rammu?” ya tambaya.
Na haɗiye yawu, na sunkuyar da kaina, sannan na ce a hankali:
“Wanda ya zo ne, shi ya ba ni.”
Baba ya sake kallon ledar, sannan ya tambaye ni:
“Wane ne sunansa? Kuma me ya sa ya ba ki wannan?”
Na yi shiru, ban san abin da zan ce ba. Kafin na iya buɗe baki, Kuluwa ta yi saurin cewa:
“Baba, saurayinta ne. Ɗan gidan kansila ne, yana sonta.”
Baba ya ɗago kai da sauri ya kalli Kuluwa, sannan ya ce cikin kaushi:
“Ke! Na tambaye ki ne?”
Kuluwa ta yi shiru, ta sunkuyar da kanta.
Baba ya sake kallona, sannan ya ce:
“Idan da gaske yake son ki, ya turo manyansa. Ba na son irin wannan shige da ficen. Ana zundena a gari, ku kuma kowa yana yin yadda ya ga dama a gidana!”
Na sunkuyar da kaina, ban ce komai ba.
“Tashi, ki wuce!” Baba ya ce.
Na juya zan wuce, na bar ledar a gabansa. Sai ya sake kirana:
“Ke! Dawo ki ɗauki ledarki.”
Na dawo a hankali, na sunkuya na ɗauki ledar, sannan na nufi ɗakinmu, ina jin kallon mutanen gidan a bayana.
Kuluwa ta biyo ni. Muka zauna, sannan muka buɗe ledar. A ciki muka tarar da turare da sabulai iri-iri masu kyau na zamani. Kuluwa ta ɗauki ɗaya daga cikin turaren tana kallo, ni kuma ina duba sauran kayan.
Muna cikin dubawa sai ga Aisha ta shigo. Da ta hango kayan, sai ta sauya fuska.
“Wai duk waɗannan kayan Farouk ne ya ba ki?” ta tambaya, tana kallon kayan da wani irin yanayi.
Na ɗan yi murmushi, na ce, “Eh.”
Ta ɗauki wani sabulu tana dubawa, sannan ta mayar da shi cikin ledar. Daga nan ta juya ta fita.
Da ta fita, sai na juya ga Kuluwa na ce:
“Kuluwa, ɗauki abin da kike so. Ki zaɓi wanda ya yi miki.”
Kuluwa ta ɗauki wani turare daga cikin kayan, ta buɗe shi ta ɗan ji ƙamshinsa.
“Wannan na zaɓa,” ta ce tana murmushi.
Na yi murmushi, na ce, “To, ki riƙe shi, naki ne.”
Na ware sabulu ɗaya na ce:
“Wannan na Mama ne, wannan kuma na Gwaggo. Baba kuwa ba zan ware masa komai ba, tunda ya ce in ɗauki kayana. Kuma na san Baba ba ya damuwa da duk abin da aka shigo da shi gidan nan.”
Kuluwa ta kalle ni, sannan ta ce:
“To, ai kin san halinsa.”
Na ware wa kowa abin da zan ba shi, na kai wa kowanne nasa.
A can kuwa, Aisha ta shiga ɗakin Gwaggo, ta same ta zaune. Ta fara ba ta labarin abin da ta gani.
“Gwaggo, kin ga mutumin da ya zo wajen Rammu? Mama, wallahi kin ga yadda yake? Ɗan gayu, ɗan birni. Ni dai ban san me ya gani a jikinta ba har yake kawo mata kaya.”
Gwaggo ta yi tsaki, ta ciji yatsanta, sannan ta ce:
“Bar yar banza! Ai indai ina da rai, babu wadda za ta fi ’yata sa’a a gidan nan.”
Aisha ta ce:
“Mama, ni fa ina son in auri mai kuɗi. Wallahi ni ce ta fi dacewa da irin waɗannan samarin, ba ita ba.”
Mama ta ce, “Insha Allah, in dai ina da rai, sai kun auri masu kuɗi. Ba zan yarda ku auri matalauta irin ubanku ba.”*****
Washe gari, na tashi na yi aikina. Mun gama komai, sannan muka fita.*****
A wani ƙauye, a gaban wani boka, wata mata ce zaune.