Free chapter · Read without an account

Chapter 43

by Sayyada barrister · BIYU A ƊAYA

BIYU A ƊAYA 
     ( Don't judge a book by its cover)



Page 43
Sayyada barrister 
YOTA 13 
The five ink legends 



A hankali ya lumshe idanunsa jin muryar ta yaya yi har cikin ransa, yana ji tana ta kiran shi da sunayen da take kiran su da shi...

"Yallaɓai likita! Uncle! Mon amour"

Ya sauke numfashi ya amsa da

"Mon Ange"

Yana ji ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce

"Barka da dare?"

"Mon Ange barka dai, kina lafiya?"

"Lafiya kalau, ina kiran ka da kayina ba ya shiga"

Ta ba shi tausayi, a hankali ya ce 

"Wannan layin waye ne?"

"Na ALAJA"

"Ok hope everything goes well"

"Yeah!"

"Kin kyauta da kika kira ni, ina Mama?"

"Tana nan, ina side na ALAJA ne"

Ya sauke numfashi yana jin daɗi, ji yake kamar an ba shi ita, baya so ya faɗa mata ya rasa number ne...

"Uncle"

"Na'am Mon Ange"

"Baka da lafiya ne?"

 "Ba na jin daɗin jikina shi yasa ki ka ji murya haka"

"Sannu Uncle Allah ya baka lafiya"

Ya yi murmushi tare da cewa 

"Amin"

Sun ɗan yi hira, ta ƙatse, ya koma ya kwanta, yana jin ƙaunar ta na shiga duk wani ƙofa dake jikinsa, a haka bacci ya ɗauke sa...


WASHE GARI 

Ya tashi da ƙarfinsa, ya watsa ruwa ya shirya cikin riga da wando na yadi ruwan ƙasa, ya kafa hula da white eyes glass, ya ɗauko white coat nasa da side ba, da wayarsa ya nufo ɗakin Mommie, ya turo ƙofa ya yi sallama suka amsa masa, tare da gaishe shi ya amsa ya zauna ya kalli Mommie da ta zuba masa ido tun shigowar sa ta ce

"Barka da safiya Mommie"

"Barka dai Yarona, an fito za a je wajen aiki"

"Eh Mommie ya jikin?"

"Alhamdulillah da sauƙi"

"Sannu Mommie ki din ga cin abinci kina shan magungunan ki"

"To Yarona zan yi, ka samu matar aure, a ina take?"

Ya sauke numfashi tare da cewa 

"Ashfat ce"

"A'a Hajjiya Balkisu ta ce min ba ita ka zaɓa ba"

Ya ɗago a hankali ya dube ta, ya jinjina mata kai alaman eh, ta ce

"Wacece?"

"Sunanta Bilqees amma ana kiranta da Angel, a ƙasar Ghana take"

Ya faɗa ya sudda kai ƙasa, don ya san ita ma ranta zai ɓaci, a ce ya ƙi auran ƴar'uwar sa...

"Na sani yarinyar ta chanchanci ka so ta shi ya sa ka zaɓe ta, na san yarona ba zai zaɓi abin da zai zame mishi damuwa ba, amma tana sonka?"

"Eh har mun yi magana da iyayenta sun ce na turo iyayena"

"Ina bayan wannan zaɓin"

Jamila da Suhaima suka kalli Mamansu da mamaki, ita da bata son auren bare yau kuma take cewa tana goyon bayan Dr Waahab, cike da farin ciki ya ce

"Na gode Mommie, amma Mamie bata so, Ashfat take so"

"Na yi magana da ita, kuma zan yi magana da Abbie"

"Na gode Mommie Allah ya ba ki lafiya"

"Amin"

Ta ce, ya tashi ya fito zuwa ɗakin Mamie ya da sallama ya shigo ta amsa fuska ba a sake ba, ya zauna jiki a sanyaye ya ce

"Barka da safiya Mamie"

"Alhamdulillah ka fito?"

"Eh Mamie"

Shiru ba ta ce komai ba, ya dubi fuskar ta a hankali ya ce

"Mamie fushi kike yi da ni?"

Ba ta ce komai ba, ya numfasa ya ci gaba da magana 

"Zan iya jure komai amma ban da fushin ki, ki yi hakuri na ɓata miki ba zan sake ba"

"Ba fushi nake yi da kai ba, bana so matsala ta taso sakanina da ƴan'uwana musamman mahaifinka ka san yadda suke shi da Abban Ashfat"

"Mamie in dai auran Ashfat a gare ni shi ne farin cikin ki na amince"

Ta sauke numfashi ta ce

"Ta shi ka tafi kada ka makara"

"To Mamie ba ki yi min addu'a ba"

"Allah ya tsare ya bada sa'a"

"Amin na gode Mamie"

Ya tashi ya fito jiki a sanyaye, ya ci karo da Ammie tana ƙoƙarin shigewa kitchen ya gaishe 

"Ammie barka da safiya"

Yadda ta amsa bai yi masa daɗi ba, ta shige kitchen ba tare da ta tsaya sun gaisa kamar yadda su ke yi ba. Ya wuce side na Daddyn sa ya tadda duk suna zaune suna shan shayi, ya yi sallama ba laifi sun amsa amma Abbie ne kaɗai ya ba shi fuskar, jikinsa ya yi sanyi, ya kalli Abban Ashfat da duk yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa, sai kuma Daddynsa da ko kallon sa bai yi ba.

Ya sauke ajiyar zuciya, ba tare da ya yi dogon tunani ba, ya ce

"Ina me baku hakuri akan rashin kin amincewa da Ashfat da na yi a matsayin wacce zan aura, ku yi hakuri na yi laifi ku yafe min, na amince zan aure ta, a sanya ranar bikin da sauran ƴan'uwana"

Da mamakin Dr Waahab sai ga shi sun sake masa fuska, Daddyn sa ya ce

"To ko kai fa, ni lokacin da na auri mahaifiyar ka, babu wani gadda ba a ma nemi shawarata ba, mahaifin mu me sunanka kenan ya aura min ita, ga shi kuma mun zauna yanzu babu wacce nake so irinta"

Dr Waahab kansa a ƙasa, Daddyn Ashfat ya ce

"Dukkanin mu haka aka yi mana, koma ga shi mun ƙulla zumunci, duk muna cikin farin ciki"

Alhaji babba ya ce

"Alhamdulillah hakan ya yi, Allah ya sanya alkhairi, za mu zauna mu tattauna a sakaninmu sai mu ga abin da ya dace"

Abbie ya fahimci yanayin Dr Waahab shi yasa bai ce komai ba, har ya mik'e ya yi musu sai anjima ya fice, kai tsaye parking space ya iso ya tadda Sa'eed yana ƙoƙarin ficewa ya ɗaga masa hannu ya fice. Dr Waahab ya shige mota ya wuce hospital


***********

Sai da yamma ya dawo, ya watsa ruwa ya fito ya duba Mommie sannan ya duba Mamie ba laifi ta sakar masa fuska, tare da cewa 

"Babangida Ashfat fa bata da lafiya, an sayo drip ma za a saka mata Aunty Nazeefa bata nan"

"Subhanallah bari na saka mata"

"Yawwa ka saka mata"

Ya fito ya shigo bangaren su Ashfat, a palour ya tadda Ammie cike da girmamawa ya gaishe ta

"Barka da yammaci?"

Ta ɗan ɗago ta amsa da 

"Abdulwahab sannu ka dawo?"

"Eh Ammie ya jikin Ashfat?"

"Da sauƙi"

"Tana ina?"

"Ɗaki"

Ta nuna masa da yatsa, don ita takaici ya ishe ta, ya tashi ya shigo ya tadda tana duƙunƙune duk jikinta a rufe, ya ɗauko drip da ya gani, ya fiddo da hannunta yana ƙoƙarin makala mata ta buɗe idanunta ta sauke su kan kyakkyawar fuskarsa, a hankali ta sauke ajiyar zuciya, ya ɗago ya kalle bai ce komai ba, ya maƙala mata, ya ce

"In ya kusa ƙarewa sai ki sanar da ni ta waya"

"Me ya sa ka ceci rayuwata? Me ya sa ba ka bari na mutu ba? Why Ya Waahab? Me ya sa baka sona?"

Kamar ba zai ce komai ba, ya ɗan tsaya na wani lokaci sannan ya juyo ya dawo bakin gadon ya tsaya, ya sauke numfashi tare da cewa 

"Ni likita ne, aikina shi ne ceto rayuwa kan al'umma, sannan don na ceci rayuwar ƙanwata ai ba laifi bane"

"Me ya sa ba ka sona?" Wasu dabi'u ne nake da su da ya saka ba za ka amshe ni a matsayin matar ka ba?"

"Ko ɗaya ba ki da wata mummunar ɗabi'a, asali ma na fi yabon ki duk cikin ƙannena, kuma ni ban ce bana son ki ba, ban tsane ki ba"

Abban Ashfat ya sauke numfashi, yana tsaye tun shigowar Dr Waahab ya shigo ya duba jikinta Ammie ta ce yana ciki, ya ƙaraso zai shigo shi ne ya ji suna magana, ya tsaya yana sauraro...

"Amma a gaban iyayena ka ce ba za ka amshe ni a matsayin matar da za ka aura ba"

"Ashfat na zaɓi Bilqees ne saboda wasu dalilai, tana buƙata na cikin rayuwarta"

A hankali ta saki kuka, ai ita ma tana buƙatar sa cikin rayuwarta...

"Bilqees marainiya ce, bata da uba, sai mahaifiya, amma ke fa, kima da Abba kina da Ammie kina da mu kina rayuwar farin ciki kin samu duk wani abin da ɗan Adam yake buƙatar samu, ina so na auri Bilqees na kawo ta cikin Ahalin mu ta samu farin ciki amma kuma hakan ba zai yi ba saboda ke"

A hankali ta ɗan tashi ta zauna, ta ce

"Ya Waahab ba zan iya auran kowa ba in ba kai ba, in kuma ba haka ba na hakura da auran"

"A'a Ashfat ki bar wannan maganar har ki samu sauƙi kin ji?"

Kai ta gyaɗa masa alamun to, ya sauke numfashi ya fito Abba ya gani yana ƙoƙarin shigowa ya tsaya tare da matsawa gefe ya ce

"Barka da yammaci Abba?"

"Likita sannu ashe kana ciki?"

"Eh Abba jikin nata ma da sauƙi"

"To ma sha Allah"

Dr Waahab ya fice, Abban Ashfat ya shigo ya tadda ta zaune, ya zauna ba kin bed tare da cewa 

"Ashfat ya jikin?"

"Da sauƙi Abba"

"Sannu ko"

"To Abba"

Ya yi niyyar ya sanar da ita, albishir da ya shigo da shi ba amincewar auranta da Dr Waahab ya yi, sai dai jin tattaunawar da da su ka yi ya sa ya canza ra'ayinsa. Ya numfasa ya ce

"Ashfat ban ji daɗin ganin ki a irin wannan yanayin ba, da hankalin ki da wayon ki bari damuwa ta cutar da ke"

"Abba ba laifi na bane"

"Na sani amma ki sanya wa zuciyar ki hakuri"

"To Abba"

Ya yi ta yi mata nasiha sannan ya fice, Suhaima, Hauwa da Teemah suka shigo sai bata baki suke yi, sun jima a wajenta sannan suka koma side nasu....

********

Dr Waahab ya yi shirin kwanciya, ya haura bed ya danna wa number da Angel ta kira shi da shi jiya bugu biyu aka ɗauka ya ji muryar ALAJA tana cewa

"Who's on the line?"

"Yallaɓai likita from Nigeria"

"Oh you! Ya ya kake?"

"Alhamdulillah ina so na yi magana da Angel"

"Ok let me inform her, Mamanta akwai problem bari na kira ta side nawa"

Bai ce komai ba ta katse har bacci ya fara satan shi wayar ta yi ringing, ya duba ganin number ne ya sa ya katse kiran ya kira ya ji murya tana cewa 

"Uncle"

"Na'am Mon Ange"

"Barka da dare?"

"Yawwa barka dai kina lafiya?"

"Alhamdulillah Uncle"

"Uncle kuma?"

"Mon amour"

"Yawwa Mon Ange, da fatan ba damuwa ko?"

"Ba komai Mon amour"

"Ki ci gaba da yi min addu'a kin ji?"

"To in sha Allahu"

"Ki koma ki kwanta kin ji?"

"To"

"Take care"

Ya katse kiran, bai jima ba bacci ya yi awun gaba da shi...


************

Ya shirya kamar kullum zai tafi wajen aiki ya fito side na Mommie ya fara shiga suka gaisa sannan ya shiga ɗakin Mamie tana zaune hannunta riƙe da casbi, ya zauna cikin kulawa ya ce

"Mamie an tashi lafiya?"

"Alhamdulillah Babangida, an fito?"

"Eh Mamie"

"To ya yi kyau Allah ya tsare ya bada sa'a"

"Amin Mamie, na sanar da su Daddy ma an sanya ranar bikin da Ashfat"

"To ma sha Allah, hakan ma ya yi, ka shiga ka sake duba jikinta"

"To Mamie"

Ya mik'e ya fito ya iso side na Ammie, ya tadda tana zaune a palour hannunta riƙe da wayarta, ya gaishe ta, ta amsa ya tambayi jikin Ashfat ta ce

"Jiki da sauƙi amma tun jiya ta ƙi cin abinci"

"Subhanallah bari na duba ta"

Ya shiga, a lokacin ta mik'e tsaye, sanye da doguwar riga mara nauyi, jiki ba kwari ya iso ya isa suna kallon juna, ya sauke numfashi tare da cewa 

"Me ya hana ki cin abinci?"

Ta ɗan ɗauke kanta ta ce

"Bana jin yunwa"

"Zauna"

Ta zauna, ya ajiye side bag nasa da white coat ya rage tsawonsa ya zuba mata jollof ba Arish wanda ya ji kifi da nama, sannan ya haɗa mata tea ya ajiye kan carpet ya ɗago ya kalleta ta zuba masa ido sai kallon sa take yi ya ce

"Sauƙo"

Ta sauƙo ta zauna kamar yadda ya ce, ya tura mata gabanta ya ce

"Ki ci"

Ta sinci kanta da son ci ko don Ya Waahab ne ya zuba mata, ta fara ci ta ce

"Kai ba za ka ci ba?"

"A ƙoshe nake"

Bata ce komai ba tana ci, sai da ta ɗanci sannan ta ce ya ishe ta, ya bata magungunanta ta sha, sannan ya ce

"Ki koma ki kwanta zan wuce wajen aiki"

Ya ɗauko kayansa ta ce

"Na gode"

Kallon ta kawai ya yi sannan ya fice, da mamaki ta fito palour da ƙarfin jiki, Ammie ta bita da kallo tare da taɓe baki, murmushi kawai ta yi, ta wuce ɗakin su, ta tadda suna cin abinci ta zauna Teemah ta ce

"Bismillah ki taho mu ci"

"A'a Alhamdulillah Ya Waahab ya bani na ce"

Da mamaki suke dubanta, Hauwa ta ce

"Iye lovers"

Ta yi dariya suna ta sokanarta. Haka da ya dawo da yamma ma ya sanya ta a gaba sai da ta ci abinci ta sha magani sannan ya dawo ɗakinsa.

Washegari da safe ma haka, bayan ya shirya ya fito ya shiga ɗakin Mommie suka gaisa sannan ya wuce ɗakin Mamie bayan ya gaishe ta, ta yi mai addu'oi sannan ya fito ya dawo side na Ashfat ya tadda ta yi shirin zuwa wajen aiki, sanye da black suit riga da wando sai kuma farar rigar ciki ta yi rolling sannan ta sanya after dressing akai.

"Ya Waahab barka da safiya"

Ya sauke numfashi tare da cewa 

"Barka ya jikin?"

"Da sauƙi"

"Za ki je wajen aiki kenan?"

"Eh"

"Abdulwahab"

"Na'am Ammie barka da safiya"

"Barka har an fito?"

"Eh Ammie zan wuce"

"To a dawo lafiya"

Ya fito Ashfat tana biye da shi, ya buɗe motar sa ita ma ta buɗe ta zauna a mazaunin gaba bai ce komai ba, ya zauna a driver seat ya tada motar sai da ya kaita wajen nata aikin sannan ya wuce hospital...


**************

Zaune suke a palour kasancewar Dr Waahab night duty gare shi, shi kaɗai sai iyayensa, kan sa a ƙasa, tun da yaga kiran Alhaji Babba ya san da magana. Yana sauraron su suna tattaunawa akan wani abu da bai fahimta ba, sai da suka gama, sannan Alhaji Babba ya ce

"To Alhaji ka ce mu zo akwai abin da za ka sanar da mu, muna sauraron ka"

Abban Ashfat ya sauke numfashi a hankali ya ce

"Baban mu"

Ya kira sunan Dr Waahab saboda takwaran mahaifinsu ne, shi yasa ake kiran sa da Babangida, Dr Waahab ya ce

"Na'am Abba"

"Ya sunan yarinyar da take Ghana? Ina nufin wacce ka ke so"

Da ƙyar ya sauke numfashi zuciyar sa na bugawa ya ce

"Bilkisu"

"To ma sha Allah, waye mahaifinta"

A hankali Dr Waahab ya ɗago yana bin su da kallo, Abbie ya ce

"Ka amsa masa mana"

"Bata da mahaifi"

"Ban gane ba, daga sama ta faɗo?"

Cewar Alhaji babba, sannan ya ɗaura da cewa 

"Wai duk wannan na menen"

Dr Waahab ya ce

"Marainiya ce, mahaifinta ya rasu, amma tana tare da mahaifiyarta"

Abban Ashfat ya ce

"Allah sarki, na janye baka Ashfat ka auri Bilkisu"

A tsorace Dr Waahab ya ɗago yana kallon Abban Ashfat, da mamaki ɗauke kan fuskar, ji yake yi tamkar a mafarki, Alhaji babba ya ce

"Ya da haka? Me kake nufi?"

"Na amince ya auri Bilkisu"

To ai mu ke gaba da kai, mun gama magana Ashfat zai aura.

Cewar Alhaji babba, Daddyn Dr Waahab ya ce

"Ba dai ranka bane ya ɓaci? Ai shi da kansa ya amince da auran shi da Ashfat"

"Ko ɗaya raina bai ɓaci ba, ya auro marainiyar ya inganta mata rayuwa"....





Ayi hakuri da typing errors 



Comments and share fisabilillah

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol