Free chapter · Read without an account
23
by Asmy b Aliyu · OMRI HAYATII
by
Asmy b Aliyu
23....
da kansa ya bude mata kofar dakin,
ta shiga Sai Shima ya shigo Yana rufe kofar
tsayawa tayi cak!kirjinta na sama da kasa
me wannan guy din ke nufi?"
tambayar da tayiwa kanta kenan,
da mamaki ta juya tana kallonsa
takowa ya rikayi ya iso gabanta tana kallon girman tsayin da yake dashi tamkar mu'azzam dinta.sai dai a hakan mu'azzam
ya fisa tsayi sosai.........hannunsa ya xura ta bayanta ya matso daita gafdashi har kirjinsu na gogan na juna haka Suna
shakar numfashin junansu still hannayensa
na zagaye da bayanta Sai taga ya manneta a kirjinsa kafin yayi mata kyakkyawar runguma. tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da wani irin sauri
runtse ido tayi tana jin wani irin yanayi
na saukar mata.sai da ya gaji dan kansa
ya saketa Yana dan Jada baya kadan
ya juya ya nufi kujera wani farin envelope
ya dauko Kai tsaye ya nufeta ya riko
hannunta gamida ware tafin hannun
Yana saka mata farin envelope din
cikin idanunta yake kallo masu kashesa
Wanda zallar mamakinsa ne acikinsu.
thank you......!"da haka bai Kara kalma
ko daya ba ya juya ya nufi kofar fita
Yana fita ya rufe mata kofar a natse
batareda wata hayaniya ba.xubewa
tayi akan kujera tana Jan numfashi tana fitarwa duk a rikice take kallon farin envelope din kawai take Wanda kamshin
turarensa ya manne ajikinsa.tashi tayi da sauri ta shiga bedroom ta fara hada kayanta gamida jefa envelope din
acikin jakar kayanta batareda ta duba ko menene acikiba da haka ta fice daga hotel room din tana ta addu'ar Kar Allah
ya hadata da kowa har ma noory
a wannan lokacin bata bukatarta.
tana bukatar kebe kanta tana bukatar
jin shiru,saleem ya riga ya rikata
kwakwalwarta ya saka ta wata irin duniya
mai wuyar fita ko wane motsi da xatayi
tana jin hannayensa acikin jikinta.....
koda ta koma gidan maleeka, ko maleekar
bata nema ba dakinta kawai ta wuce
tana shiga ta murxawa kofar dakin key
anan ta zubar da kayan da ta shigo dasu
ta nufi kan bed,kwanciyya tayi gamida
manne fuskarta da pillow......
#######
#DANGEROUSE STEP
#THE MAFIA BOSS
Falon ya cigaba da kasancewa cikin wani irin shiru mai nauyi, wanda ko numfashin mutanen da ke zaune a wurin sai an nutsu sosai kafin a iya jinsa.
Dattijon yana zaune a tsakiyar falon, jikinsa sanye da fararen kaya masu tsada, fararen gemunsa sun sauko har ƙirjinsa. Wani irin farin rawani ne ya kewaye kansa, yana barin fuskarsa da gemunsa kaɗai a bayyane.
Mutane sama da goma ne suka kewaye shi, dukkansu sanye da baƙaƙen kaya. Babu wanda ya kuskura ya motsa, balle ya yi magana.
Sai kwatsam, dattijon ya dakatar da motsin bakinsa.
Ya buɗe idanunsa a hankali.
Wani irin kallon sanyi ya bi kan mutanen da ke gabansa, kafin ya ɗaga hannunsa na dama kaɗan.
Nan take, ɗaya daga cikin mutanen ya sunkuyar da kansa ƙasa.
“An same shi, maigida,” ya faɗa cikin wata murya mai cike da fargaba.
Dattijon bai amsa ba. ya runtse idonsa a hankali Yana Karanto wasu kalaman tsafi.
wani irin shiru mai ban tsoro ya Kara ratsa falon a Karo na biyu.
yafi minti goma a haka kafin ya daga Kai
ta saitin da saleem yake ya zuba masa
ido alamar shi yake saurare.
a hankali ya saka hannunsa cikin jikinsa
sai ga pant din mata ya bayyana a hannunsa.har gaban shugaban nasa
ya dora pant din kan wani farin kyalle
dake zagaye da wurin.a hankali dattijon
ya Kara dafa pant din ya runtse ido
falon ya Kara daukar wani irin shiru
nan take duk abunda ke falon ya fara
wata irin girgiza kofofin falon da windows suka fara bude kansu Suna rufewa
da wani irin sauti da wata irin Kara
mai ban tsoro.........Yafi minti biyar a haka
kafin komai ya lafa.a hankali ya bude
idanunsa.
Abu mafi ban tsoro game da dattijon shi ne idanunsa. Idanu ne masu wani irin yanayi na daban, masu kama da na mage, waɗanda ke da siririn baƙin ɗalibi a tsakiyar wata irin kalar rawaya mai ɗan haske. Idan ya ɗago su ya kafa wa mutum, za ka rantse babu wani abu da zai iya ɓoyuwa daga gare shi.
Ko da yake ya tsufa, idanunsa ba su nuna raunin tsufa ba. Akasin haka, suna ɗauke da wani irin kaifi da sanyin kallon da ke sa duk wanda ya haɗa ido da shi ya ji kamar an tona asirinsa.
A hankali yake buɗe idanun nasa, amma duk lokacin da ya yi hakan, sai falon ya ƙara shiga wani irin yanayi na tsoro. Babu wanda ya isa ya daɗe yana kallon idanunsa, domin kallon nasa kaɗai yana iya sa mutum ya manta abin da ya zo faɗa.
Waɗannan ba idanun dattijo kawai ba ne; idanun wani mutum ne da ya kwashe shekaru yana mulkin daular Mafia, har tsoro ya zama wani ɓangare na sunansa.
wata irin dariya ya fashe daita Wanda
yasa falon ya fara wani irin jijjiga.
"Madalla da samun jarumi kamar ka, mai basira da ƙarfin zuciya irin naka. Da izinin Mai Iko, kai ne za ka gaji wannan kujerar"
Dattijon ya ƙarasa maganar cikin wani irin farin ciki da ba kasafai ake ganin sa a fuskarsa ba. Muryarsa cike take da alfahari, yayin da yake kallon matashin da yake zaune a gabansa.
Ya ɗan dakata, sannan ya ɗaga hannunsa a hankali yana nuna kujerar da ke bayansa.
“Na shafe shekaru masu yawa ina riƙe da wannan daula. Na ga masu ƙarfin hali, na ga masu wayo, na kuma ga waɗanda suka ɗauka cewa za su iya zama a matsayina. Amma babu wanda ya taɓa sa na yarda da shi kamar yadda na yarda da kai.”
Ya sake kallon matashin, wannan karon murmushi ya bayyana a fuskarsa.
“Ba wai don kai ne mafi ƙarami a cikinsu ba. A'a! Na zaɓe ka ne saboda abin da na gani a tare da kai. Kai ne mutumin da nake da tabbacin zai iya ɗaukar nauyin wannan daula bayan na bar wannan kujera.”
Da jin waɗannan kalamai, falon ya shiga wani irin shiru. Wasu daga cikin mutanen suka yi musayar kallo, yayin da wasu suka sunkuyar da kawunansu.
Amma matashin da ake magana a kansa bai nuna wani irin farin ciki ko mamaki ba. Ya zauna cikin nutsuwarsa, fuskarsa babu alamun motsin rai.
Sai a hankali ya ɗago kansa, ya kafa wa dattijon idanunsa.
“Idan wannan shi ne burinka, Maigida, to ina fatan ka shirya ganin abin da zai biyo baya.”
Ya faɗi hakan cikin wata murya mai sanyi, sannan ya mayar da kansa baya.
A wannan lokacin ne dattijon ya ƙara faɗaɗa murmushinsa, domin wannan ne ainihin dalilin da ya sa ya zaɓi wannan matashi a matsayin magajinsa.
wani irin nauyi kirjinsa yayi baisan Kuma
wace irin kaddara ta Zata shigo da malaak farook Rano acikin rayuwarsu ta mafia ba.
“Taurarinku sun yi daidai da na wannan yarinyar. Haɗuwarta da wannan daula za ta ƙara mata ƙarfi da ɗaukaka. Da zuwanta ne wannan daula za ta kai matsayin da muka daɗe muna fata. A ƙarshe, mun samu irin macen da muka kwashe shekaru muna jiran zuwanta.”
Ya ɗan dakata, sannan fuskarsa ta sauya, kamar ya tuna da wani abu mai muhimmanci.
“Amma fa akwai wani sirri a tattare da ita. Wannan yarinyar tana da wanda take so a gefe. Wannan na iya zama babbar matsala a cikin aikimmu. Kaima wannan na iya zama matsala a gareka, musamman idan aka yi la'akari da irin tsananin kishin da kake da shi. Ba ka taɓa yarda ka raba abin da kake so da wani ba.”
Dattijon ya karkatar da kansa, yana kallon matashin da idanunsa masu kama da na mage.
“Duk da haka, za mu ci gaba da shirye-shiryenmu. Aurenta da wannan saurayin tamkar yana cikin ƙaddararta ne. Za mu bar auren ya gudana, amma akwai wani shiri da muka tanada a ɓoye.”
Ya ɗan rage muryarsa, sannan ya ci gaba da fadin.
“Zamu tabbatar cewa wannan auren ba zai ba saurayin damar more rayuwar aure da ita ba. Kai ne za ka riƙa amfani da kusancinka da ita wajen tabbatar da cewa burinmu ya cika, a duk lokacin da ka ga dama. Amma ka tuna, kada wani ya fahimci ainihin manufarmu.”
Dattijon ya yi murmushi mai cike da sirri.
“Taurarinka da nata ne za su ci gaba da riƙe mana wannan daula. Kuma idan komai ya tafi yadda muka tsara, babu wanda zai iya hana mu cimma burinmu.”gyada Kai yayi alamar ya fahimta Sai dai can a kasan kirjinsa wani irin nauyi ne ke danne dashi.
bayan ya Kammala wannan bayanin
daya bayan daya ya rika karbar korafin
yaran nasa.sai kusan 3 na dare taron ya watse.......
##SALEEM TALBA
(The Devil's Heir of Mafia)
Babu wani motsi da ake iya ji a koina. Komai yayi tsit, alamar cewa dare ya riga ya gama rabawa da duniya ya barta cikin wani irin natsuwa mai ban mamaki.
A wannan lokacin ne wata baƙar mota ta shigo cikin harabar wani katafaren gida, duplex home, wanda aka zuba dukiya wajen gina shi da kawata shi. Tun daga ƙofar shiga har zuwa cikin harabar gidan, komai yana nuna irin arziƙin wanda ya mallake shi.
Saleem Talba ya fito daga motarsa, bai tsaya ko’ina ba. Kai tsaye ya nufi babban part dinsa dake cikin gidan Wanda yafi
kowane part girma da tsaruwa.
Yana shiga, sai ya cire baƙaƙen kayan da ke jikinsa, ya ajiye su a gefe. Daga nan ya nufi wata babban wandrobe da aka aza a bangon dakin hannu yasa ya turata
Sai ga wata kofa ta bayyana.
Ya sanya hannunsa a kan wata na’ura, sannan ya shigar da wasu lambobi. Bada daɗewa ba, sai aka ji wani ƙaramin ƙara, ƙofar ta buɗe a hankali.
Amma abin da ke ciki ba kayan ado ko kuɗi ba ne.
Wata ɓoyayyar ƙofa ce da ta buɗe zuwa wani ɗaki na musamman, wanda ba kowa ne ya san da wanzuwarsa ba. A cikin ɗakin ne dukkan sirrinsa da abubuwan da suka shafi rayuwarsa ta Mafia suke ajiye. Har ma da wani wuri na musamman da yake amfani da shi wajen tattaunawa da babban shugaban Mafia idan bukatar hakan ta taso.
A taƙaice, wannan ɗakin shi ne ofishinsa na sirri a cikin gidansa—wurin da babu wanda zai yi tunanin yana nan, ko da kuwa ya shafe shekaru yana zuwa gidan.
Saleem ya shiga, ya duba wasu daga cikin kayansa, sannan ya mayar da duk abin da ya ɗauko cikin wata jaka. Bayan ya gama, ya fito ya rufe ƙofar a hankali, ya mayar da komai yadda yake.
idan xaka kalli bangon xaka iya rantsewa babu wata ƙofa da aka taɓa sakawa a wurin.
Kai tsaye ya nufi bathroom
Ya cire kayan da ke jikinsa, ya kunna ruwan shower. Ruwan ya fara sauka a kansa, yana ratsawa ta cikin baƙin sumar kansa zuwa fuskar da ta saba kasancewa cikin tsauri.
Amma a wannan lokacin, Saleem bai yi kama da mutumin da ya sa wasu ke tsoron sunansa ba.
Ya rufe idanunsa.
Wani irin zafi ya turnuke ƙirjinsa, yayin da tunanin abubuwan da suka faru a rayuwarsa ya fara dawowa masa ɗaya bayan ɗaya.
Ya tuna da yarintarsa.
Ya tuna da lokacin da ya kasance yaro marar wani iko, yaron da aka zalunta a cikin gidan da ya kamata ya kasance mafakarsa.
Ya tuna da fuskar kishiyar mahaifiyarsa—matar da ta mayar da rayuwarsa tamkar wani irin hukunci, har ta kai shi ga shiga wata rayuwa da bai taɓa mafarkin kasancewa cikinta ba.
A hankali ya buɗe idanunsa.
Kallon da ya yi wa madubin da ke gabansa ya nuna masa mutumin da ya zama a yau. Amma a bayan wannan fuska mai tsauri, a
Lebɓansa suka motsa kaɗan, ya furta wata magana cikin sanyin murya
“Kin yi kuskure ɗaya ne a rayuwarki…”
Ya dakata, yana kallon fuskarsa a cikin madubi.
“Kin ɗauka cewa abin da kika yi mini zai ƙare dani."
Sai ya yi wani irin murmushi mai sanyi.
Na zama abunda kikeso na xama din
kudi kikeso nayi kota wace hanya
ko ba hanya mai kyau bace
ko haramtacciyyar hanya ce
wani murmushin da babu farin ciki ko digo ya sauke acikin fuskarsa.nayi kudi
nayi kudin da na baki farin ciki da natsuwa
nayi kudin da kika fara nuna mun soyayya
kika bani farin cikin da koda Ina yaro
ban samesa ba.burinki ya cika duniya
ta sanni Hajjaaah duniya tasan karfin iko da power da kudin talba's group
duk ta haramtacciyyar hanya
a haka farin ciki kikeyi?"ya fada Yana Kara kallon mirror idonsa na juyewa a hankali zuwa wata kalar.yana komawa asalin
fuskar the Devil's hair dinsa na mafia
A daren Saleem Talba bai manta da abin da ya faru a baya ba.
Domin duk da cewa duniya ta san shi a matsayin wani matashi maiji da kudi da kurciyya
a bangaren dayan rayuwarsa .Yana jiran lokacin da duniya Xata sansa a matsayin cikakken dan mafia.
#ASMY B ALIYU
#Saleem Talba(the Devil's hair
#malaak farook Rano
#mafia /love/money
#love/fate
#Omrihayatii
#***...