Free chapter · Read without an account

24

by Asmy b Aliyu · OMRI HAYATII

OMRI HAYATII 

By
Asmy b Aliyu 

24......

wani irin bacci tayi wanda bata samu yinsa ba a daren jiya Sai bayan la'asar 
ta tashi.wannan karon duk ciwon
jikin da ta tashi dashi taji ya gama walwalewa a hankali.sai dai ga mamakinta har yanxu fuskar Saleem talba bata daina gilma mata ba yayi tsaye cak!a cikin ranta
lumshe idonta tayi tana tuna daren jiya
a yanayin da suka tsinci kansu acikinsa.
tana tuna komai nasa wani irin karfine
dashi tamkar doki.sai dai wani babban sirri a tattare dashi ya iya sarrafa macce
a gado sarrafawar da tafi Jan hankalinta 
a tattare dashi.komai ta tuna Sai Kuma
ta yamutse fuska tana jin haushin kanta
meyasa Zata wani damu da mutumin 
da sau daya ta taba ganinsa a rayuwarta.
Dan ma kaucewa tunaninsa yasa ta mike tsaye tana zare duk wani abu dake 
cikin jikinta tana jefar dashi nan tsakiyyar dakin Kai tsaye toilet ta shige
ta sakarwa kanta ruwa masu dumi........
koda ta fito daga wanka rigar marar
nauyi ta saka batareda ta shafa komai 
ajikinta ba.sai turarrukkanta masu 
sanyin kamshi da dadi da ta saka,
ta dauki wayarta da ta saka a silent 
taga kusan 20miss calls daga noor
2 misscall daga mu'azzam.babu Wanda 
ta kira acikinsu ta jefar da wayar akan 
soofa.batada karfin yin waya a yanxu
saboda yunwar da takeji,ta zura casuall 
slippers a Kafanta masu wani irin taushi 
masu dauke da tambarin sunan (Gucci)
ajikinsu.da haka ta fice daga dakin.
babu kowa acikin dinning area din
ganin ta karaso cikin dinning area 
yasa mai aiki tazo da sauri tana mata
sannu da fitowa.ta jamata kujera
ta zauna,nan take ta fara serving dinta
Sai da ta gabatar ma da komai Wanda
tasan xata iyaci a lokacin sa'annan tabar gurin a natse take cin abincinta batareda
da taji wani dandanonss a bakinta ba
still abunda ya faru tsakaninta da saleem Talba Yana gilma mata cikin idanunta,
akwai wani strange feeling da takeji
a kasan zuciyarta dangane dashi da zuciyarta ta kasa samun natsuwa akan hakan.bata jimaba ta zari tissue ta goge bakinta ta koma room dinta,Kai tsaye
bathroom ta nufa Sai da tayi brush ta fito
Kai tsaye wayarta ta dauka.ta fara dialling lambar noor,tamkar jira noor din take ta dauka."noor ta rika fada akan meyasa bazata daga wayarta tabi ta dagamata hankali.dan shiru malaak din tayi
kafin tace tayi hakuri kanta taji
Yana ciwo shiyasa ta dawo gida.sannu noor tayi mata cike da damuwa a muryarta.yar hira suka taba kafin suyi sallama, dialling lambar mu'azzam tayi
Sai dai a Kashe taji wayar.
Sai lokacin hankalinta ya koma kan envelope din da saleem ya damka a hannunta,haka kawai Kuma zuciyarta take ta son taga menene aciki.bag din da ta dawo daita ta dauko tana xaxxage kayan 
dake cikinta farar envelope din ta fado
daukar envelope din tayi tana duba bayan envelope din da aka rubuta sunan 
(Talba group of companies)wani irin
tsari mai daukar hankali ke tattare da rubutun,Bude envelope din tayi
cheque ne ya fara fitowa kafin card dinsa
Shima na talba's group da tarin digits dinsa har guda ukku..........cheque din 
ta dauka zuciyarta na dan sosuwa
tana jin har aranta baida kudin siyan 
jikinta.wannan ma kaddara ce 
Sai dai kudin da taga an rubuta akan cheque din taji Suna jijjiga duniyarta,
wani irin motsawa taji zuciyarta nayi
Kare bude idonta tayi akan cheque din
still 20millions take gani a rubuce.
da wani irin mugun sanyi jiki ta aje cheque din.dauriyya kawai take but tana jin ya'r rawa da jikinta keyi.mikewa tayi tsaye tana jin iskar dakin gabaki daya tana canja 
Mata.tunda take a rayuwarta babu namijin 
da ya taba bata 20millions ko mu'azzam 
bai taba bata ba,duk siyayyar da xai yimata bazata fi ta 10millions ba shi da wuya ya bata kudi yafi siya Mata abubuwa
masu daraja kamar diamond neckles
ko earrings.a hankali ta yaye dogayen 
curtains din window tana jin duk
sanyi AC dake aiki cikin room
din sanyi sa ya mata kadan iska take son
shaka daban.tafi minti goma a haka
kafin ta yanke shawarar nemansa 
Kai tsaye.wayarta ta dauka tana zuba
numbers dinsa,nan take tayi dialling lambarsa har tagama ring bai daga ba
ta Kara Kiran nan ma shiru Sai taji
ranta ya fara baci.kasa jiran Kiransa
tayi ta tura masa gajeran sako 
akan tana son su hadu ta basa kudinsa
bata bukata..........akan idonsa text dinta
ya shigo wayar na a silent daidai lokacin 
da suke meeting daya daga cikin companies dinsa dake garin Abuja.
Shima yau yanayinsa duk a sanyayen
yake bai taba kawowa ransa ko a mafarki
macce Zata shigo cikin lamarinsu
Dan ko kadan bai son duk wata alaka
da zata hadasa da matan.sai gashi
shugaba yasa shi abunda yakejin ya masa
wani irin nauyi a kirjinsa.ba malaak ce
farkon wacce ya fara nema ba kusan mata 3 Yana nema Sai dai duk wacce taurarinta 
basuyi daidai da nasa ba ,bata Kara kwana 
daya a duniya Sai dai gawarta.yadda malaak din take da class da kamewa
ya dauka ma virgin ce Sai da yakai
inda yakeso yakai yaga akasin haka.
haka wannan kaidarsa ne tunda ita ke rike da makullan empire dinsu a yanxu
babu namijin da Zata Kara hada gado 
dashi bayan shi.dan koshi kishinsa tsoro
yake basa.bayan Sun gama meeting
ya koma office dinsa mai dauke da wata irin duniya acikinta.ya dauki wayarsa
ya kira malaak din da bai gama rike 
sunanta ba yadai saka mata Suna
(goal)dan yanxu itace duk wani tushen
arzikinsu.har ta katse bata daga ba 
Kara Kiran wayar yayi Sai gashi ta dauka.
zan aiko a kawo maka cheque dinka
bana bukata ko amfada maka kudin 
ka Zasu girgizani na cigaba da mu'amala da kaine....tunaninka bai gayamaka gaskiyya ba Mr.Talba Ina jiran address 
yanzu zan turo driver.da zallar mamaki
yake sauraren tsiwar da take zuba 
masa ta cikin wayar.da alamar zatayi
zafin kai Amma komai zafin kanta
Ae bata Kai nasa ba jin yayi maganganunta
na wani irin tafasa masa zuciya
wani irin hayaki yaji Yana fita ta cikin kansa.ki jira zan aiko driver yanxu 
zaixo ya tafi dake ki kawo mun da kanki idan kin isa.....da haka ya sauke 
wayar Yana jin idonsa na juyewa lokaci daya,jikinsa ya dan fara jijjigar da yake
musamman idan Yana cikin fushi
Sai kokarin controlling din kansa
yake.yafi minti biyar a haka kafin 
ya sake dialling wata lambar.cikin bada umurni yake fadin."aje wuri 
kaza zaa zo masa da sako.haka kawai
yace ya katse Kiran drivernsa ne
ya kira Kuma yasan gidan yayar malaak din 
Dan Sai da yayi bincika akanta tun a safiyar da suka kasance da junansu....

######
gaba daya ranta a bace yake wuraren Karfe 7 na dare Sai ga lambar Saleem
din na kiranta.hararar wayar tayi batareda
ta daga ba har ta katse.shi Kuma bai Kara Kira ba gajeran sako ya tura mata akan ta fito kofar gida yanxun nan minti biyar 
ya bata.ta fito da cheque din ,idan ta Isa 
ta kawo da kanta.haushi da mugun
mamakin sa suka tarar mata ji yadda
yake bata umurni kamar wani ubanta
Riga da wando ne ajikinta wandon ma 
3quaters Sai shirt ta dauki budadiyyar doguwar riga black mai maballai ajikinta
ta saka Sai mayafinta ta dauki cheque din 
da card dinsa ta nufi kofa.tamkar Zata
tashi sama.a falo ta tarar da maleeka,
kallonta maleeka tayi kafin tace Sai Ina?"
yanxu zan dawo sako zan bayar.itama maleeka din bata damu ba dan rayuwarsu 
babu takura kowa rayuwarsa yake
yadda yakeso haka babu wani saka ido.
kalar motar da tagani a wurin yasa 
taji numfashinta na sama da kasa
bawai ba tasaba ganin manyyan motoci bane a duniya gidansu akwai gidan su mu'azzam dinta akwai.sai dai ta fara saka shakku aranta,da alamar Saleem din
gidan manyya ya fito.driver na hangota
ya fito daga motar ya bude mata
back seat ya sunkuyar da Kai cikin girmamawa wanda bai yadda ya kalleta ba.kawai ka Kai masa kiyi hakuri
madam Kar na rasa aikina yace na kawo ki 
da kanki ki basa.dan shiru malaak din 
tayi tana mamaki karfin halinsa,
babu wani tunani ta shige motar.
cike da girmamawa driver ya rufe motar 
ya shiga bangaren driver ya tada motar 
sukabar gurin......tafia mai nisa sukayi
har suka zo wata tsadaddiyyar unguwar
manyyan masu kudin da sukaci suka
tada Kai,suna zuwa daidai (Talba mantion)motar ta tsaya driver yayi horn
Mai gadi ya wangale get din,aka shige 
da motar ciki.driver nagama parking 
cikin parking lot da motoci basu wuce kwara biyar ba dukka Kuma manyyan
cars ne babu ta kasa da 100millions
driver ya fito ya bude mata kofar
motar.shiyayi mata jagora har zuwa entrance din shiga gidan.daga nan 
ya juya ya koma.tsaye tayi a wurin 
fuskarta a daure tana jiran a bude
kofar,a hankali kofar ta bude ta daga Kai tana kallon Wanda ya bude kofar
kusan zuciyarta bugawa tayi tana jin kafafunta na kasa daukarta.wani irin 
kallo yake binta dashi Wanda taji 
wata mugun kasala ta lullubeta 
duk balain da ta shirya xatayi masa
jin tayi komai ya bace bat cikin kanta bakin nata ma mutuwa yayi.........


#ASMY B ALIYU 
#malaak farook Rano 
#Saleem Talba
#mafia /money/Power
#Hotlove/Romance 
#Omri Hayatii 
#***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol