Free chapter · Read without an account

Chapter 23

by Salis M Reza · MIJIN AMAL


TALLA
Domin samun Data mai sauki da inganci zaku iya tuntuɓar wannan number. Data na kowanne network kuke so ***

(HIV Research)

*Chapter 23*
Har likitan ya zauna kan Amal a sunkuye yake tana tsoron kallonsa, sai addu'a take yi a ranta. Yaya dai ya kafe shi da ido ganin fuskar tasa kawai ta bada labarin zuciyarsa. Bayan ya zauna ya sauke ajiyar zuciya mai tsayi ya ce "I'm sorry to say har yanzu tana tare da wannan cutar. But mun samu nasarar kaiwa matakin Undetectable wato bayanin da nayi muku a baya wancen lokacin. Hakan na nufin zata iya rayuwa kamar kowa kuma..." Tun kafin ya ƙarasa Amal ta fashe da wani irin kuka mai karya zuciya jin dai bata warke ba. Yaya ya ce "Likita kenan har yanzu tana da cutar kake nufi ko kuma ya?" Likitan ya kalli Amal ganin irin kukan da take yi, ya girgiza kai alamar tausayi ya ce "Eh tana da shi, dama wannan gwajin shine na karshe wanda zai tabbatar mana. Kaman yadda nace muku a baya. Sauyawa mutun mai hiv jini baya sa a ranu da cutar saboda ba a iya jini take zama ba. Tana shiga cikin ɓargo da kwakwalwar mutum, wanda idan aka sauya jinin zai iya ɓata wancen ma. To amma yanzu ina so ki daina kukan nan ki saurare ni domin ko a yanzu anyi nasara saboda wannan matakin da kike kai a yanzu, da ke da wanda bashi da ita banbancin kawai ke kina da ita ne, kuma ta taɓa shiga jikinji, amma bayan haka komai zaki iya yi. Kuma ba zaki iya gogawa wani ba, koda kuwa ta hanyar saduwa ne idan kina da aure". Yaya ya ce "Kamar yaya ba zata iya gogawa wani ba, kuma koda tana da aure? Kayi mana ƙarin bayani dan Allah?". Ya kalli Amal ya ce "Kina tare dani?" Tayi shiru kamar ba zatai magana ba, sai kuma ta kawar da kai tana share hawaye. Ta ce "Na fahimta, kawai ba sai ka sake cewa komai, na gane komai". Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi. Ya ce "Har yanzu baki fahimci irin nasarar da kika samu ba. Kuma har yanzu a tsorace kike. Amma bani minti ɗaya kacal yanzu zaki fahimci abun da nake nufi. Ya tashi ya dauko wata takarda ƙatuwa ya buɗe ta a kan tebur ɗin gabansa. Sai ya fara bayani yana zana komai suna kallonsa daki-daki.

Ya ce "Wannan matakin da kike kai yanzu shine abin da ake kira U-U undetectable Untransmittable. Wato matakin da ba a iya ganin cutar a gwajin farko dana biyu sai a na uku, to ba za ki iya yaɗawa ga kowa ba. Ga yadda yake a sauƙaƙe". Yayi wani dogon layi ya ɗora da "Lokacin da mutum ya kamu da HIV da farko, ƙwayar tana da yawa sosai a jini, tana da ƙarfi, kuma zaka iya yaɗawa kowa cikin sauƙi. Amma daga lokacin da ka fara shan maganin (ART) kullum, to wannan maganin yana kashe ƙwayar cutar a hankali har sai ta ragu, har sai na'urar gwaji (viral load test) ta kasa ganinta a karon farko. A wannan lokacin likitoci sukan ce mutum ya kai matakin undetectable. Kamar kuma ke da cutar batayi nisa ba, kuma har aka yi aiki, kuma kike shan magani akai-akai. To yanzu kina wannan matsayin ne. Kuma ba wai yana nufin cutar ta ɓace ɓat daga jikin mutum bane, a'a tana nan a ɓoye ne a cikin ɓargo wanda bata da girman da zata iya shiga jikin wani ko cutar da kai mai ita. Kaman dai haka... Ba za ta iya cutar da kai ba. Ba za ka iya gogawa kowa ba, ko da ta hanyar mu'amalar aure ne, ko da ba tare da abun kariya ba (wato kwaroron roba) ko da zakuyi shekara 10 tare ne. An yi bincike a kan ma'aurata ɗaruruwa a duniya wanda ɗaya na da HIV, ɗaya kuma ba shi da shi, kuma suka rayu har na tsawon shekaru, kuma suka yi mu'amular aure  dubbai ba tare da roba ba, kuma mara cutar bai kamu ba. Amma a kullum idan mutum yaje gwajin gano cutar, wato test, to zai ci gaba da nuna POSITIVE ne kullum. Domin jikin ya taɓa haɗuwa da cutar kuma yana da alamarta. Wannan ba zai taɓa komawa negative ba.

Gwajin auna yawan cutar (Viral Load test) Wannan shi ne zai nuna undetectable ko target not detected. Wannan gwajin shi ne yake zai nuna kana da shi amma ba ta da karfi a jikinka. Yanzu ga sharudɗan U-U wanda zan baki... Dole ki riƙa shan magani kullum ba tare da fashi ba. Dole tunda kin kai undetectable kuma ki zauna a haka na akalla watanni shida. Dole ne ki je a auna miki viral load duk bayan watanni shida. Idan har kika yi haka, za ki rayu lafiya kamar kowa, kuma za ki iya aure da haihuwa ba tare da tsoron yaɗa cutar ba".

Yaya ya ce "Alhamdu, ashe dai anyi nasara hakan ma". Ya faɗa yana murmushi yana kallon Amal da har lokacin hawaye take yi. Bata ce komai ba, sai godiya da itama taiwa likitan jin kowa na masa godiya. Nana kuwa tun ɗazu ta koma gida akan yunwa take ji. Likitan ya haɗo mata magin da zata dinga sha da yake kyuta suke badawa, sannan ya faɗa mata lokacin da zata dinga zuwa gwaji da lokacin shan maganin. Suna shiga mota ta ce "Yaya gida zaka kaini". Anty zatayi magana ta ce "Dan Allah ku kaini gida na roƙeku". Mama ta ce "Ku wuce da ita gidan kawai, mun gode sosai da abubuwan da kuka mana. Allah ya saka muku da mafificin alkairi". Anty ta amsa da amin. Yaya ma haka, yana ta satar kallonta ya kasa gane mai kuma ya ɓata mata rai ita da ya dace tayi murna. Tun da ta shiga motar take kallon gefe ɗaya har suka iso gidan nasu. Ana tsayawa ta buɗe ta fito. Ta zagayo ta gaban direba. Ta ɗan saki fuska harda murmushin yaƙe. Ta ce "Babu abun da zan iya cewa da kai Yaya sai na gode, Allah ya saka da alkairi, anty kema haka na gode sosai". Tana cikin maganar hawaye ya ƙwace mata. Tayi saurin mayar da shi tayi gida da sauri. Anty na mata maganar tazo ta kwashi kayanta, amma ina. Haka dole ta sakko ta bita da kayan. Suka samu Nana ta gyara musu gidan da kuma ɗakin da Amal ɗin take. Abun yaso ya bawa Amal mamaki saboda ta yaya tasan zata dawo gidan. Amma ganin jakar kayan Nana ɗin a ɗakin ya wadatar da ita amsar tambayar tata. Tana shiga ɗakin ta faɗa kan takuraren gadon nasu ta fashe da kuka. Mama ta shigo ɗakin ta ce "Ban san kuma kukan mai kikeyi ba Amal, ai godewa Allah ya dace kiyi ba kuka ba, ko ba komai ai kin warke. Ko dai kewar Mijinki kikeyi?" Amal ta ɗago da sauri ta ce "Eh Mama, kukan da nake yi kenan da ya zama ta dadalin ɗan uwansa na samu wannan lafiyar, na rasa mai yasa na yarda tun farko, wallahi na tsani kaina gaba ɗaya". Mama ta ce "Ashe kukan dad'i kikeyi yarinya, ni yanzu ma batun komawa gidan nasa zaki fara yi tunda kin warke, kuma dai ko ba komai bai sake ki ba". Mama ta faɗa kanta tsaye, kuma da tabbacin hakan. Amal ta tsayar da kukan ta ce "Allah ya tsine masa, wallahi da dai na ƙara zama da shi gara na mutu banyi aure ba. Sannan ina gama wannan wata shida ɗin farkon da likita ya ce zan kai shi kotu a raba auren, idan kuwa ya ce zaiyi wata maganar na rante da girman Ubangiji zan faɗi duk abun da ya min abi min kadi". Mama ta ce "Wai shi Yasir ɗin ko? Ai kuwa dole ki koma masa matar Yasir tun da dai baiyi sakin ba. Kin manta lokacin da nake faɗa miki gaskiya sai kice min irinsu basu da yawa a duniya? Kice min ban san waye shi ba, ban san irin kulawar da yake baki ba, ko kin manta ne?" Mama ta karasa harda dariyar manya. Amal tayi shiru tana jin rasa abun faɗa. Tabbas da wata ce take tuno mata da waɗannan abubuwan da suka wuce, da wallahi sai ta tsinewa tun daga kan uwarta da ubants har kaka na biyar. Ganin haka Mama ta ce "Idan ma baki koma ba, ina tabbatar miki da cewar shi zai zo ya tafi da ke, ba dai yaji labarin kin warke ba. Kuma ko yazo babu ruwana saboda ba'a shiga tsakanin miji da mata". Tana kaiwa gurin Amal ta rushe da kuka wurjanjan kamr an mata mutuwa. Sosai take kuka har Nana na musu dariya daga waje. Da karfi itama ta ce "Sai dake matar Yasir, ɗan albarka, wanda yafi kowanne namiji a duniya". Ai kuwa ta ƙalƙalo wasu irin zagi irin na maguzawan farko ta watsowa mata. Dama cike take fan, tana neman fashewa. Ta tashi ta fito fuuu tana cigaba da zaginta har tana faɗin ta sake yin magana idan bata tattakata da cikin nata ba, daga karshe ta ce "Sannan idan kin aihu kije ki aure shi, tunda har ma kin tare a gidan nasa". Nana ta toshe dariyar ta. Har sai da ta tabbatar ta shige ta ce "Ko dai na bar gidan ne?" Ta faɗa yadda zata ji, amma ba zata san abun da tace ba". Haka dai suke neman mayar da ita mai almatsutsai sai tsoknarta suke yi. Tun abun na bata haushi har ya daina. Ta lura dai ta zama abar tsokana saboda yadda ta fifita shi abaya. Yanzu ga sakamako.

Sama da sati ɗaya kenan kullum mama maganar yaushe zata koma take. Farko ta ɗauka da wasa ms take yi, ashe ita fa da gaske take wallahi. Sai tace to meya amfanin zaman nata anan alhali tana da aure. Amal ta ce "Idan kina so na bar miki gida ne Mama ki fito fili ki faɗa min, amma dan Allah ki daina min maganar wannan mutumin, wallahi zuciyata zafi take min kamar zata soye". Mama ta sake faɗin "To ai na samu labarin ya dawo ne daga tafiyar tasa, shi yasa ma kika ga Nana ta dawo gida da zama, ashe wai korota yayi daga gidan naku da ya dawo ya sameta". Amal ta tsaya chak tana kallon Mama kamar wacce tayi suman wucin gadi. Ta kasa magana Mama ta bita da kallo wanda bata ma sani ba. "Baki san ya dawo ban..." Cikin tsawa ta ce "Wai meye haka ne Mama? Kina son zubar da girman ki da darajrki a gurinane, anya ma kuwa kece kika haife ni Mama? Mutumin da ya min irin wannan abun shi kike min maganar sa? Anya kuwa Mama, ko a gidan marayu kika ɗauko ni ban sani ba?". Ta ƙarasa tana kuka tana yarfe hannu, har wani shidewa ta keyi domin mama ta famo mata rauni a zuciyarta. Ita kanta Mama ɗin ta sha jinin jikinta da yadda take yi. Ta ce "Amal ni kike faɗawa haka ko ba ni na haife ki ba? Amal kin manta lokacin da nake son raba ki da yaron nan kike nuna min cewa ban san daɗin aure ba, ban san farincikin aure ba, har kina cewa bana sonki, kika nuna masa cewar ya fini mutunci a gurin ki, shine yanzu dan ina taya ki sonsa kike faɗa min haka?" Amal ta faɗa jikin Mama tana faɗin "Dan Allah kiyi hakuri Mama, a lokacin kuskure nayi da yarinta, Mama ki yafe min dan Allah na tuba ba zan sake ba, kuma dan Allah ki daina min maganar sa bana so dan Allah". Ta faɗa har tana hade hannu bibbiyu" Mama ta ɗagota tana faɗin ya wuce, amma idan yazo da kansa ba zan hana shi ya tagfida ke..." Amal ta toshe mata baki. Mama tayi murmushi ta ce "Yaran zamani kenan yan dad'i soyayya". Daga haka ta koma ɗaki tayi wanka.

Misalin ƙarfe takwas bayan ta sha magani tajiyo sallama daga tsakar gida, sai da bata gane muryar ba. Jin Mama na cewa a shigo tana ciki ne yasa ta tashi da sauri tasa hijjabi tana ƙoƙarin rufe Kofar yadda koma waye sai ta bada izini, amma kafin ta ga yin hakan har an buɗe an shigo. Ganin Hafsah yasa taja tsaki a fili tana faɗin 

"Dama kina gari?" 

Hafsah ta ce "Ina nan mana, kawai dai abubuwa ne suka sha min kai. To ya jikin?" 

"Jiki Alhamdu lillah, sai ina a daren nan?"

"Gurin ƙawata mana Amal" Ta amsa tana samun bakin gadon ta zauna. Zata yi magana Amal ta ce "Hafsah sanadin abun da kikayi yasa kowa yasan ina da wannan ciwon, kin kwaso min mutane sama da ashirin har wanda ma ban sani ba wai sun zo dubiya, wallahi abun ya bata min rai".

"To Amal ya zanyi, suna ta damuna a group wai kwana biyu basa jinki, shine nace baki da lafiya, suka ce sai anzo an duba ki, kuma wayar ki bata shiga, to ya kike so nayi". 

"Wannan dubiyar ta muna funci ce, domin wa aka taba zuwa dubawa sama da mutum ashirin, kawai dai sun samu labarin ne shine kowa yake so yazo yaga yadda na koma". 

Hafsah ta ce "Dan Allah kiyi hakuri, wannan ya wuce ban san ki da riƙo ba. Yanzu dai Albishirinki?" 

"Goro mai ya faru"?

"Yau naga Yasir, wai dama yana gari ne? Kinga yadda ya zama, yayi kyau abunsa kamar ba shi ba. Ni fa rabon da na ganshi an kusa shekara wallahi, ko number sa da nake da ita bata tafiya. Kuma wallahi..."Hafsa tashi ki fita mana daga gida". Ta faɗa tana miƙewa tsaye Kamar zata mareta. Itama Hafsa ta mike ta ce "Amal lafiya dai?" "Na ci ki tashi ki fita ko na fitar da ke, banza munafuka magulmaciya". "Amal ni ce munafika kuma?" "An faɗa miki ɗin, idan ba shi ya kawo ki ba meye na min maganrsa, kije cen kiyi ta ganinsa mana mai ya shafe ni da shi". Haka ta rakota har ƙofar gida. Mama na jinsu bata ce komai ba. Har ta dawo tana zaginta. Ranar haka tayi barci da zagin Hafsa, harda mafarkin ta mata shegen duka. 

Washegari ta tashi gabanta sai faɗuwa yake yi. Wanda har sai da ta je gaban madubi tana kallon yadda hawa da dauƙar saitin zuciyar tata keyi kamar talgen tuwo ya sha wuta. Misalin ƙarfe takwas kuwa mutane sukai ta shigowa ana mata barka wai sun samu labarin ta warke. Ita abun ma haushi yake bata, kuma tasan duk aikin mama ne. Kamar ƙarfe goma haka sai ga Anty Maryam ɗauke da ƙatuwar kula da kakar kayanta ta kawo mata, farfesu mai yawa na nama da kifi. Har ga Allah bata son suna shiga rayuwar ta kuma, idan son samu ne su rabu da ita ta huta. Shi yasa take kukan sake amincewa da tayi da su. A daidai lokacin take sake jin bugun zuciyarta na ƙarayuwa har anty ta tafi. Nana tana ƙofar ɗaki tana cik Farfesun suna hira da Mama da take wanki. Amal kuma na cikin ɗakin tana sauraron hirar tasu akan mijin Nana ɗin da har yanzu ba labarin sa. Kuma tana fama da faduwar gaban har lokacin. Kaman ta saka musu baki a hirar amma dai ta fasa tana ta sauraro. Daidai lokacin gaba ɗaya suka tsinkayayo sallama da muryar har karshen rayuwarta ba zata manta da ita ba. Take wani abu mai kama da zare ya fara mata yawo daga saman kanta har tafin ƙafa. Tana jin yadda Mama ke masa maraba kamar ma da farinciki a muryarta. Ta maƙale a tsayen da take ta kasa gaba ko baya. Gaba ɗaya yadda take ji kamar wata ce a tsaye a gurin ba ita ba. Zuciyarta na janta amma tana ƙoƙarin saita kanta. Bata san lokacin da ta ɗaga labulen ɗakin ba. Ai kuwa ta hango shi tsaye yana murmushi wanda tayi saurin sakin labulen tana dafe ƙirji. Take wata kalma da ya faɗa mata tayi saurin shigowa cikin tunainta. "To ki mutu ma mana, kar ma Allah yasa kisha maganin jikin waye". Take wani ƙwarin gwiwa yazo mata. Ta saita kanta sannan ta saka hijjabi harda niƙaf tayo waje a fusace...📝


Yau dai an haɗu bayan lokaci da yawa, ko mai zai faru tsakanin masoyan biyu?

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol