Free chapter · Read without an account
Chapter 44
BIYU A ƊAYA
( Don't judge a book by its cover)
Page 44
Sayyada barrister
***
YOTA 13
The five ink legends
Dr Waahab sabar farin ciki kamar ya tashi sama, Allah ya amshi addu'ar sa, a hankali ya sauke ajiyar zuciya, yana ƙara godewa ubangiji, shikenan komai ya zo ƙarshe zai mallaki Angel, burin sa zai cika, zai inganta mata rayuwa..
"Ka yi gaggawar yanke hukunci Alhaji, me yasa baka nemi shawarar mu ba?"
Cewar Alhaji babba, Abban Ashfat ya ce
"Ku yi hakuri wannan ne abin da ya dace, kada mu hana shi auran yarinyar da ransa yake so, auren yanzu ba kamar namu ba baya bane, haka ma ba za ku haɗa hankalin mu da basu ba, babanmu yana da hakuri da juriya, yana yi wa kowa biyayya, bai taɓa nuna gazawar sa ba, don haka mu ma lokaci ya yi da za mu faranta masa"
Shiru palourn ya ɗauka, ana auna maganganun Abban Ashfat, ko shi Daddyn Dr Waahab baya jin daɗin ganin sa cikin damuwa, kuma ya amsa zai auri Ashfat ne saboda ya faranta musu...
"To duk da haka sai mun zauna mun sake yin shawara, kana ji fa yarinyar da yake so tana cen Ghana ba fa ban Damaturu ko Bama ba, sai an shirya, sannan ma su waye za su je nemo masa auranta?"
Cewar Alhaji babba, Abban Ashfat ya ce
"Ko ni Kaɗai zan sako sa gaba mu tafi"
"Ni ma ina bayan wannan tafiyar"
Cewar Abbie, Alhaji babba ya sauke numfashi ya ce
"To shikenan kada mu yi hanzarin sanarwa mu ɗan dakata tukuna"
Dr Waahab dadi kamar ya kashe shi, kan sa a ƙasa yana wasa da zoben dake hannun, Daddyn sa ya ce
"Ai sai ka tashi ka tafi, ka wani sunkuyar da kai"
A hankali ya ce
"Na gode muku sosai"
Ya taso ya fito, kai tsaye ɗakin Sa'eed ya nufa, yana shiga ya ce
"An amince na auri Angel"
"Don't tell me bro"
"Da gaske Abban Ashfat ne ma ya fara amincewa"
"Ma sha Allah, kaga yadda kake dariya kuwa, sunan wata wai washa"
"Ya kai masa duka a baya ya ce
"Alhamdulillah"
Su ka yi dariya, Dr ya zauna tare da cewa
"Bacci ma nake ji"
"Ai muna cikin alkhairi bro ka je ka huta"
"Ok thanks"
"Zan so ganin wannan Angel ɗin da ta yi wa nata ƙafa"
Murmushi Dr Waahab ya yi ya ce
"Har da mai za a je ɗauko min mata ta"
"Iyeee ango mijin amarya"
Dr Waahab ya fice yana murmushi cikin farin ciki ya dawo ɗakinsa ya kwanta, nan da nan bacci ya ɗauke shi...
**********
Mamie ce zaune ta rafka uban tagumi, ranta a ɓace, bata ji daɗin yanke hukuncin da Abban Ashfat ya yi ba, da ya bari an yi auren. Ta mik'e tana safa da marwa ta dubi Daddyn Dr Waahab da shi ma abin bai yi masa daɗi ba, kawai ba yadda ya iya ne yasa ya yi shiru kuma ya san Abban Ashfat kawai kara ya yi...
"Gaskiya Alhaji Waseem ba a kyauta wa Ashfat ba, dubi fa har rashin lafiya ta yi da ta ji labarin Babangida wata ya zaɓa ba ita ba"
Sauke numfashi Daddyn Dr Waahab ya yi tare da cewa
"Ni ma ban san dalilin sa na yin haka ba, kuma fa muna zaune tare Dr Waahab ya sanar da mu a sanya ranar bikin sa da Ashfat"
"Ni kam na rasa da wanne ido zan kalli Ammie da Ashfat"
"To maybe zai yi musu bayani"
Dr Waahab ya turo ƙofa ya shigo, ya tadda iyayensa suna tattaunawa ya ƙarso tare da yin sallama, Daddy ya amsa tare da cewa
"Night duty ko?"
"Eh Daddy Mamie barka da yammaci?"
"Babangida ya yi maka kyau ka kyauta, na ce ka kyauta"
Ya sudda kai ƙasa, a hankali ya ce
"Ki yi hakuri Mamie, Abban Ashfat ne...
"Rufe min baki, Allah yasa ba zuwa ka yi ka canja masa tunani ba"
"A'a Mamie ba mu yi magana ba"
"To ni ban amince da wannan auren ba"
Bai ce komai ba, Daddyn sa ya ce
"Tashi ka tafi"
Ya mik'e ya fice, side nasu Ashfat ya shiga ya tadda wata rigimar Ammie da Ashfat suna yi wa Abban Ashfat bai kyauta ba
"Daddy me yasa za ka ce haka? Ka goyi bayan ya auri wata ba ni ba?"
"Ke ina wasa dake, har na yanke hukunci ki tsaya kina jayayya akai, Abdulwahab ba mijin ki bane, ki ma saka hakan a ranki"
"Haba Abban Ashfat bai da ce ka faɗi haka ba, baka ga yanayin da take ciki bane ka bita a sannu ...
"An ƙi bin ta a hankali, ta yi duk abin da za tayi, haba sai kace wacce za ta rasa mu, ke ba musulma ba ce, ki nemi zaɓin Allah mana, na gama magana Dr Waahab ni da kaina zan nema masa auren Bilkisu"
"Abba"
Su ka ji murya Dr Waahab, Ashfat ta zube a ƙasa tana kuka, Ammie ganin shi yasa ta shige ɗaka rai a ɓace, Abban Ashfat ya sauke numfashi tare da cewa
"Ka fito?"
"Eh Abba, ka ka yi mata faɗa bata da laifi, ni ne me kaifi"
"Laifin me ka yi? Ai kai ma baka da laifi, ka yi tafiyar kawai"
Dr Waahab babu yadda ya iya ya fice zuwa hospital.
*********
Duk ta rame a cikin kwanaki biyun nan, ta yi sanyi kamar ba ita ba, bata yawan magana Abbanta ya ki bata fuska, tana kwance a ɗakinsu Teemah zaune kusa da ita ta ce
"Aunty Ashfat ki yi hakuri, shi ne abin da nake ta faɗa miki, ki yi baya baya da son ya Waahab amma kin ki, dube yadda kika jefa kanki cikin damuwa"
A hankali ta ɗago ta kalli Teemah ta ce
"Ban taɓa tunanin zan rasa Ya Waahab ba, Teemah ni ma ban san na yi nesa a ƙaunar sa ba, idanuna sun rufe"
"Ki yi hakuri yanzu ki tashi ki ci abinci kin ji"
"Bana jin yunwa"
Ta faɗa, sallamar Dr Waahab su ka ji, da mamaki suke duban sa yana tsaye bakin kofa, sanye da ƙananan kaya sun yi masa kyau, ya dubi Teemah ya ce
"Ki ba mu waje za mu yi magana"
Ta tashi simi² ta fice, ya zauna kan carpet ya dube ta, ta ɗauke kanta gefe bata son ganinsa, ya sauke numfashi tare da cewa
"Ashfat ina me ba ki hakuri, ba...
"Na fahimci komai Abdulwahab, tun da ka gama samun zaɓinka me yasa za ka shigo in da nake"
Bai ji daɗin furucin ta ba, amma yasan tana cikin damuwa ne, ya sauke numfashi tare da cewa
"Ki karɓi ƙaddara da hannu biyu Ashfat, daman cen ke ba mata ta ba ce, da ban faɗa a soyayyar Bilqees ba ke ce wacce zan...
"Ka tashi ka fice min, bana son ganin...
Wasu saukan zafaffun mari ta ji sun sauƙa a ƙuncinta, a gigice ta ɗago, ganin Ammie yasa ta gimtse bakinta, Dr Waahab bai so ta mare ta ba, ba zai yi a dake ta kuma a hanata kuka ba...
"You are very stupid, ba ki san da waye kike magana bane, is he your mate?"
Dr Waahab ya ce
"Ammie ki yi hakuri kada ki yi mata faɗa"
"Ka kyale ta, me aka yi mata za ta sanya mutane a gaba tana rashin kunya"
Ita dai Ashfat sai kuka, Ammie ta fice, Dr Waahab ya gyara zamansa tare da cewa
"Ki yi hakuri Ashfat bana son ganin yanayin da kike ciki, har ga Allah bana son ganin kina cikin damuwa"
Ba ta ce komai ba har ya gama yi mata nasiha ya fice...
*******
Yana kwance a ɗakinsa da daddare ya kira layin ALAJA suka gaisa ya ce yana so ya yi magana da Angel, ta ce ya bata wasu mintina, ya bata babu jimawa ta kira ya katse sannan ya sake kiran layin, ta ɗauke tare da yin sallama, ya amsa ya ce
"Mon Ange ya kike?"
"Lafiya Mon amour, ya aiki?"
A hankali ya sauke numfashi ya lumshe idanunsa ya amsa da
"Sai godiya"
Suna hira, har suka kusan raba dare sannan su ka yi sallama....
***********
Tashin hankali aka yi a family saboda majority sun ce ba su amince da Dr Waahab ya auro mata daga waje ba, kaɗan ne suka yarda, duk da haka Abban Ashfat, Abbie da Alhaji babba basu karaya ba, suka tara meeting, aka haɗa manya manyan cikinsu aka zauna akan batun...
"Abin da ya sa na tara ku anan shi ne, kamar yadda kowa ya sani akan batun auren Babban Dr Waahab ne, to shi dai Allah ya yi matarsa a cikin Ahalin nan take ba, da farko mun ƙi yarda amma duba da wasu abubuwan yasa muka amince, don haka za aje Ghana nema masa auren Bilkisu"
Cewar Alhaji babba, nan aka fara cece ku ce, Alhaji ƙarami ya ce
"Yanzu fisabilillah haka za a tashi mutane akai su cen wata ƙasa neman aure, in ba abin Babangida ba ga mata nan a family sai ma wanda ya zaɓa amma ya ce sai ƴar Ghana"
Sauke numfashi Abban Ashfat ya yi ya ce
"Hakuri za mu yi, waɗan da za su je su yi magana sai mu yi bukin jirgi"
"To kai yanzu sanya rana za aje ko kuma ɗaurin aure?"
Cewar Alhaji ƙarami, Allah babba ya ce
"Duk yadda ta kama"
Sai magana ake yi, kowa cewa yake yi bai da lokacin tafiya cen, Alhaji babba ya ce
"Zan jagoranci tafiyar, sai waye?"
Abban Ashfat ya ce
"Sai ni"
"Ni ma zan je"
Cewar Abbie mahaifin Suhaima, sai Daddyn Waahab ma ya ce
"Shikenan ba damuwa ni ma zan je"
"To in dai haka ne, ni ma zan je"
Cewar Alhaji ƙarami, a takaice an samu manya, guda biyar, sai kuma Dr Waahab sai Sa'eed mutane bakwai kawai za su tafi. An jima ana tattaunawa sannan aka watse aka fara shirye-shiryen tafiya Ghana....
*************
Jamila ce ta fito tana hawaye, za ta koma garin ta in da take aure, Abbie da Suhaima su ka yi mata rakiya zuwa mota, a lokacin Dr wahaab ya fito zai wuce hospital, ya tsaya tare da cewa
"Jamila za ki tafi babu sallama"
Ta sauke numfashi ta share kwalla ta ce
"Abdulwahab na yi tunanin kana bacci ne"
"Ina da morning duty ai bana baccin safe"
"To ni kam zan wuce sai lokacin bikin ka na dawo"
"Allah ya kiyaye hanya, amma don Allah ki daina zuwa ganin gida by road please, a jirji za ki na zuwa"
"To Wahaab in sha Allahu"
"Nan gaba in za ki dawo ki yi min magana zan tura miki kuɗin jirji"
"Na gode"
Abbie ya ce
"To ga shi kai ma irin auranta za ka yi"
"Abbie barka da safiya"
"Barka dai likita zan kai ta airport"
"Ok Abbie sai ka dawo"
Suhaima ta ce
"Yaya ni ma za a tafi dani Ghana dauko maka amarya"
Ya ɗan dube ta ya ce
"Ke ma ai amarya ce"
Ta rufe fuska tana dariya, suka shige mota suka bar gidan. Shi ma ya shiga ya wuce wajen aiki sai yamma lis ya dawo...
Yana parking ya fito jiki duk gajiya a lokacin Ashfat ta yi parking ta fito hannunta riƙe da wayarta da jakarta, yana ƙoƙarin shigewa ciki ta ce
"Sannu da dawowa Ya Waahab"
Ya sauke numfashi ganin fuskar ta, ba yabo ba fallasa ya ce
"Yawwa ke ma sannu da dawowa"
"Ya aiki?"
"Sai godiya, ke ma ya aiki"
"Alhamdulillah, ka yi hakuri akan abin da nayi maka"
Da mamaki yake dubanta yau kuma kamar ba ita ba, ya ce
"Komai ya wuce"
"Thanks"
Ta shige ciki, ya bita da kallo, ya shigo side nasa ya watsa ruwa sannan ya fito ya yi abin da ya saba ya gaishe da Mommie sannan ya gaida Mamie ba laifi ta ɗan sauƙo kuma hakan ya yi masa daɗi....
**************
Kamar yadda aka saka ranar tafiya Ghana, haka ko aka yi lokaci ya yi, yau ce ranar tafiya, don haka kowa ya kammala shirinsa, Dr Waahab sai farin ciki yake yi, tun jiya ya sanar da Alaja zuwansu, ta yi farin ciki zai cika alkawarin da ya ɗaukarwa Malliman...
Dr Waahab ya shigo ɗakin Mommie tana zaune Suhaima ta haɗa mata ruwan zafi tana sha, ya zauna tare da cewa
"Mommie zan yi kewarki"
"To kwana nawa ne ma za ku yi, ai ba za ku jima ba, ina nan ina jiran isowarsa surkata"
Murmushi ya yi ya sosa keyarsa, ya ce
"Haka ne Mommie ba za mu jima ba"
"To Allah ya kai ku lafiya, a gaishe su"
"Za su ji in sha Allahu"
Ta yi masa addu'a ya fito zuwa side na Mamie ya tadda Daddyn sa zaune ta shirya masa kaya cikin luggage nasa, ya zauna tare da cewa
"Barka da safiya Mamie"
"Barka ango"
Ya sudda kai ƙasa yana murmushi, Daddy ya ce
"Ai ka kyauta da ka sanya muka bar duk abin da mu ke yi za mu je nema maka aure wata ƙasa"
"A'a Daddy ayi hakuri"
Daddy ya girgiza kai, Dr Waahab ya burge shi sosai duk da ake wannan abin bai taɓa musu da kowa, abu kaɗan sai bada hakuri.
Side na Ammie ya shige ya tadda Abban Ashfat da Ammie da ita Ashfat ɗin a zaune a palour suna hira yayi sallama suka amsa ya gaida Ammie ta amsa sannan ta ce
"Abdulwahab sai an dawo ko"
"Yawwa Ammie na gode"
"Ya Wahaab Allah ya kai ku lafiya"
"Amin Ashfat na gode"
Ya dawo side nasu, suka fito tare da Daddynsa aka saka musu kayan su a boot Alhaji babba ma sun iso parking space ya ce
"To! First in history zan tafi ƙasar Ghana"
Su ka yi dariya, motoci uku suka kai su airport, babu jimawa suka wuce Abuja, washegari suka wuce ƙasar Ghana....
________________
Ghana ta yi kira, ba zama an ɗaurawa kare aure😂
Ayi hakuri da typing errors
Comments and share fisabilillah