Free chapter · Read without an account

Chapter 42

by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI

***

***

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
Chapter 42.
Ceton Ubangiji da agajinsa suna zuwa ne asanda bawanshi me tawassali ya shiga cikin wani hali, amma bai manta da ambaton Ubangiji ba, nasan abin da ya faru da ni ceto ne daga Allah.
    Saura yunƙuri baifi ɗaya ba wuƙar tsafin Hafsa ta huda cikina, a lokacin komi ya tsaya, hatta da fitar numfashina ya tsaya a iyakar ƙirjina, sai azabar ciwon naƙuda da zubar jini danaci gaba da yi.
      Cikin juyi ɗaya Saminaka ya tsaya akan ƙafafuwan shi, bai jinkirtaba ya nufo wajenmu tare da ture Hafsa daga kaina ta koma gefe a kiɗime ganin ya tashi bayan tsafin da tayi ma shi. 
    Sam baya cikin hayyacinsa amma a haka ya ƙanƙame hannuwana a cikin na shi yana sambatun dake nuni da baya cikin hayyacinshi.
 
 A kiɗime Hafsa ta soma harhaɗa kayan tsafi zan kira abin ko bakanci ta wuce ciki bayan ta sake yayyafe shi da wasu ruwan wanda suka ƙarasa birkice tunanin shi.

     Har zuwa sannan fitar numfashina bata daidaita ba a fizge nike jan numfashin cikin azabar ziwo.
   Bazan iya gane awanni nawa na kwashe a wannan yanayin ba, kawai de na tsinci kaina ne a asibiti ina kwance, da farkowata kuma na tabbatar da babu komi a cikina saboda wani irin sakayau da nike jin kaina.
  Tambayar data fara faɗomin ita ce ta zaburar da ni na tashi a ɗimauce ina sakin siririyar ƙara marar sauti ban damu da raɗaɗin azabar dana ji daga ƙasan cikina ba, domin kuwa zuciyata ce ya saƙa min zargin kodai Hafsa ta farke cikina.
     Sautin muryoyi biyu na ji daga gefena wanda hakan ya sakani kai dubawa wajen a sukwane ƙirjina na ɗagawa da sauka.
    "Yah Allah sannu My Rimsha sannu kinji bara inkira Doctor infaɗa ma shi kin tashi."
   ya faɗa tare da kusanto ni da ɗayar muryar wacce ta kusa sumar da ni a zaune.
   Ba muryar kowa bace face muryar yarona, jinjiri wanda keta faman tsala uban ihu da zazzaƙar muryar shi irinta jarirai.
   Da dukanin zuciyata na saka hannayena da babu ƙwarin kirki na amshi yaron dana cire ran samuwar shi a doron ƙasa, saboda zalunci da son zuciya irin na kishiyata Hafsa wacce babu Allah a ranta.
    Gyara ma shi zama na yi a hannuna tare da saka yatsata manuniya na dinga zagaye bakin yaron dake ta rarumar yatsar alamar abincinsa ya ke nema.
    Sosai yanda ya yi ɗin ya wanke zuciyata, har wata dariya me sauti wacce ke cike da nishaɗi ta kubce min, na shiga yiwa yaron wasa hawayen godiya da farinciki na gangarowa daga fuskata.
    "Alhamdulillah gaskiya aiki ya yi kyau Mrs Saminaka tunda na iske ki zaune da kanki."
   Doctor  ɗin da ke dubani ya faɗa lokacin da suka shigo da fara'a a fuskar shi.

   "Ammadai ki kula kuma kiɗan gyara zaman saboda akwai yanka a jikin ki da aka yi miki SC."
Ya faɗa cikin ankarar da ni, sai a lokacin na gane ashe zugin yankan ne nike ji amma na kasa ganewa tun tuni, farinciki ganin kyakkyawan balaraben yarona wanda ya ɗauko kamanina zuryar na sake mamaye ni.
      Tsabar farinciki sai kawai na shiga hawaye ina kuma a dariya lokaci ɗaya.

    Haka Saminaka ya riƙe kafaɗuna shima yana hamdala gami da godiya ga Allah akan ni'imar da yayi ma shi ta samun ƙaruwa, nan yaci gaba da kulawa da mu kamar zai cinye mu tsabar so da ƙauna.
    Hakan ƴan uwa da abokan arziƙin shi suka cigaba da tururuwar zuwa suna taya shi murna samun ƙaruwa, kowa gazo ya kalli yaron sai ya ƙara wasuma dakyar suke aje yaron saboda tsiga rai da gare shi ga kyau iya kyau domin kuwa sak jinin larabawa haka ya ɗauko, hancin shi ne kawai irin na Saminaka dogo samɓalele irin na fulani.
   Sai da na tabbatar sa yaron nawa ne, na kuma ji ɗumin shi yanda ya kamata sannan na tambayi Muhammad ɗina dan bangan shi ba.
      "Ai Muhammad yana can wajen Hafsa." amsar da Saminaka ya bani kenan data kadamin gaba nan take har bansan lokacin da nace a razane ba.
   "Hafsa wace Hafsar kuma?." na tambaya da yaren larabci gumi na tsatsafo min.
     Ɗan kallona Saminaka ya yi na tsayin sakanni sannan ya ce.
    "Lafiya dai ko Rimsha?."
   Ya yi tambayar yana ƙure yanda zumi ke ɓarko min da kallo.
 Ban iya cewa komi ba sai komawa da nayi na jingina da gadon, memories ɗin abubuwan da suka faru na dawo min fes a cikin idona.
   Daga ranar tunanin Hafsa da wani irin zullumi basu sake barina ba, ga wata rashin nutsuwa da zaman Muhammad a wajenta data same ni, cikin kwana biyu na ƙara ramewa nabi na bushe saboda zullumi da fargabar komawa gida, bansan kuma dame Hafsa zata ɓullo ba wannan karon tunda na tsallake rijiya da baya a wancan karon.

      Du yanda banson komawa gida dole na haƙura muka tattare komi namu bayan na kwana shidda a asibiti, yarona na cikin ƙoshin lafiya, nima ta wasu fannin ina lafiya saide abin da ba'a rasa ba, amma zuciyata sam babu nutsuwa tsoro da firgici sun gama mamayeta.

   A ranar da aka sallamemu a ranar muka koma gida, farinciki cike da fuskar Saminaka shi dakanshi ya riƙe yaronmu da muka sakawa suna Muhammad Rizwan amma muna kiran shi da Junaid saboda sunan mahaifina ne.
     Daga ƙarshe dai na koma gida na kuma haɗu da Hafsa, Muhammad ya dawo gareni cike da kewata, babu abin da ya same shi kamar yanda na hasasa.
   Babban abin da yafi kashe ni da mamaki bai wuce yanda Hafsa ta shiga ta fita tai kane-kane a sashe na ba, ta dinga nuna kulawa agareni da kuma ɗana Junaid, wanda sau dubu zata ɗauke shi ta aje bana samun nutsuwa sai na ɗauke shi na dudduba inga babu abin da tayi ma shi.
    Sosai mutanen dake tausaya mata saboda ita bata haihuba ke bani mamaki, sai nan nan ake da ita ana mata sannu akan ɗawainiya da take yi, shi kanshi Saminaka ba ƙaramin nuna jin daɗi yake ba tare da yabonta akan yanda ta sauko aka zauna lafiya, ta kuma karɓeni hannu bibiyu ba.
   Sautari ina kallon shi ne amatsayin gawa wata rana domin kuwa yanda Allah ya nuna min Hafsa na ƙoƙarin kashe shi har lokacin hoton yanayin bai gushe a zuciya da idaniyata ba."

Sake share ruwan hawaye da majinar  da suka taru a fuskarta Rimsha ta yi, tare da kwantar da kanta a kafaɗar Maryam kuka me ƙarfi na sake kubce mata.
    Radaɗi da ƙunar irin baƙar wahalar rayuwar da tasha na sake dawo mata, kamar lokacin ne abin ke faruwa.

Maryam kuwa lumshe idanuwanta da suka kaɗa suka yi jazur ta yi....✍🏻

MARYAM STAR CE

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol