Free chapter · Read without an account
RAYUWAR SUBAI'AH Part 2
RAYUWAR SUBAI'AH
*Part 2*
*FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA*
*DASHEN ALLAH WRITES ASSOCIATION*
Cikin dariyar shi mai ƙarama fuskar shi tsananin kyawu, ya ce "Baƙin sun iso kenan? Sannun ku da zuwa."
Wani irin kallo Subai'ah ta bishi dashi, wanda har hakan yasa ta kasa amsa mai sannun da yake yi masu.
Dai-dai lokacin da H-karima ke shigowa falon, cikin dariyar ta ta ce "Dama ina jiran dawowar ka, kazo kaga ƴan uwan ka waɗanda ba ka sani ba."
Ta samu wuri ta zauna ta ce "To gadai sunan; da Baban ka da Baban su uwa ɗaya uba ɗaya
Ya ce "momy na sansu amma tun suna ƴan haka"
Ya nuna dai-dai adadin tsawonsu da hannun shi.
Kallon hannun nashi Subai'ah tayi, wani luf-luf dashi daganin fatarshi ta tabbatar cewa mutum ne wanda jin daɗi ya ratsa shi ta ko ina.
Yaci gaba da cewa "Amma dai sunyi saurin girma ne, sannun ku da zuwwa."
Suka amsa mai tare da gaishe shi cikin girmamawa, wuri ya samu ya zauna nan sukaci gaba da firarsu gaba ɗaya.
Bayan sun gama firar ya tashi zai tafi ɗakin shi, sai yake cewa
"Wata cikin ku tazo ta karɓar maku, nayi maku siyayya biyo ni mota ta amsa."
Subai'ah ce ta bishi, bakin motar shi, tafiya suke tana ƙara kallon shi.
Suna isa ya buɗe ya ɗauko, dai-dai lokacin da tasa hannu biyu ta karɓa, sai kayan suka zube a ƙafar ta, cikin sauri shi kuma ya riƙe hannun ta yanayi mata sannu.
"Aiya! Ba kiji dai ciwo ba ko? Sorry."
Ta ɗaga kai tare da faɗin "Banji ciwo ba ya dai bugarmin ƙafa sosai ne."
Ya tsugunna sosai yana shafa ƙafar tata, tare da faɗin barshi kawai zankai kayan."
Ta ce "Haba Auncle zan iya."
Haka ta ɗauko wasu shima ya ɗauko wasu suka shiga.
🌷🌷🌷Tana kwance bisa makeken gado, ita kađai tanata juyi, maganganun da ƙawarta Asiya ke yawan fađa mata sune suke dawo mata a wannan lokacin.
Subai'ah da Asiya sun kasance ma'abutan karatun littafan Hausa novel ne, to a duk lokacin da Subai'ah take karanta novel; ko bayan ta gama karantawa, takan ce "Ai wane na cikin littafi kaza yayi min, Allah ya bani muji irin shi. "
Asiya takance mata "Ki daina kamanta irin mujin da zaki Aura da mujin novel, domin kuwa ba bu su, suma kansu marutan da suke rubuta tsararren namiji irin shi, suna yine kawai don su ƙayata labarin su, su kuma ja hankalin mai karatu, amma badon akwai irin wannan namijin a duniya ba. Idan kikace ke irin mujin da kikejin labarin su a littafai zaki Aura, to zakita rainama maza wayau ne, don haka ki cire wannan tunanin a zuciyar ki, in kin karanta littafi ki barshi a inda kika ganshi. "
Subai'ah takance, Oho dai! ƴar baƙin ciki ke kika sani, nidai ai buri na in Auri kyakykyawan namiji, kuma saina auri irin mujin novel ko zaki mutu 😄."
Asiya takance "Mutuwa tame? Allah ya baki."
Subai'ah na gama wannan tunani ta đauko wayar ta cikin hanzari, ta fara duba lokaci, ƙarfe Tara da rabi, tasan lokacin Asiya batayi barci ba, ta lalubo number ta, ta danna mata kira.
Tana đagawa ta ce "Sannun ku mutanan Abuja kun shige AC ko kiran mu ba'ayi a sanar damu an sauka lafiya."
Subai'ah ta katseta da cewa "Ke shegiya dakata! Al-bishirinki! Ko da yakema ke ƴar baƙin ciki ce, gaddamarmiya, kikace babu kyakykyawan namiji, to yau na hađu dashi. "
Asiya ta tuntsire da dariya ta ce "kice daga zuwanki kinyi kamu, Allah ya ƙara donƙon soyayya. "
Subaiah ta ce "Andai Kama ni.........