Free chapter · Read without an account

8:The Man behind the badge

by Hauwa Jibrin Sulaiman · FADIANA

Karfe bakwai da rabi na safe, Rameez ya riga ya kasance a ofishinsa


Duk da cewa sauran ma’aikatan da ke sashen nasa ba su gama shigowa ba, shi ya har ya Riga da ya zauna a kujerarsa, laptop ɗinsa a buɗe, wasu files kuma a shimfiɗe a gabansa. Akwai cup ɗin coffee a gefen teburinsa, amma tun shigowarsa bai taɓa shi ba. Hankalinsa yana kan hotunan da ke gabansa


Rameez ba irin jami’an tsaro ba ne da suke son a san suna aiki. Ba ya yawan magana game da aikinsa, kuma ba ya jin daɗin bayyana bayanan investigations ɗinsa ga mutanen da ba su da alaƙa da su. A wajensa, aikin SSS ba kawai kama masu laifi ba ne, yana buƙatar haƙuri, lura da ƙananan bayanai, da iya haɗa abubuwan da wasu suke ganin ba su da alaƙa


Ya ɗauki wani takarda daga cikin file ɗin da ke gabansa, ya sake karanta rubutun da ke jiki


“Interesting” ya furta a hankali


A gabansa akwai bayanai kan wani tsohon case da aka buɗe shekaru da suka wuce, amma ba a taɓa samun cikakken bayani a kansa ba. Case ɗin ya shafi wasu kuɗaɗen kamfani da suka ɓace, wasu takardun da ba a samu ba, da mutuwar wani mutum da aka rubuta a matsayin abin da ya faru ba zato ba tsammani


A lokacin da aka fara binciken, an yi ta samun bayanai masu saɓani. Wasu shaidu sun sauya maganarsu, wasu takardu kuma sun ɓace daga inda ya kamata a same su


Daga ƙarshe, an dakatar da binciken saboda rashin isassun hujjoji


Amma Rameez bai yarda da duk abin da aka rubuta a ƙarshen report ɗin ba


Ya sake kallon wani tsohon hoton da aka haɗa da file ɗin. Mutumin da ke hoton yana sanye da suit, fuskarsa babu murmushi. A gefensa akwai wani mutum da aka yi masa alamar cewa yana cikin masu hulɗa da kamfanin a lokacin


Rameez ya matso kusa da screen ɗinsa, ya zuƙo hoton, akwai wani abu da bai masa ba


Ba lallai hoton kansa ne matsalar ba. Matsalar ita ce ranar da aka rubuta a ƙarƙashinsa ba ta yi daidai da bayanin da ke cikin report ɗin ba


Ya buɗe wani document, ya duba dates ɗin, sannan ya koma hoton “Someone got the dates wrong,” ya faɗa a hankali


Ya rubuta abin da ya lura da shi a notebook ɗinsa, ya yi alama a gefen takardar


Ba zai yi saurin yanke hukunci ba. Aikin investigation ba ya tafiya da zato kawai. Kuskuren rubutu na iya zama kuskure, amma idan akwai wasu abubuwan da ba su dace ba, dole ne a bincika


Ya ɗauki wayarsa, ya kira wani jami’i da ke aiki tare da shi


“Good morning! Ina son ka duba min wani abu a tsohon archive. Zan turo maka case reference ɗin yanzu”


Ya yi shiru yana sauraro


“Eh, na shekarun baya ne. Ina buƙatar original record ɗin, ba copy ba. Ka duba ko akwai wani amendment da aka yi bayan an rubuta final report”


Ya katse wayar, ya tura bayanan da yake buƙata


A wannan lokacin ne wani ma’aikaci ya shigo office din “Good morning, sir”


Rameez ya ɗaga kansa “Morning. Ka gama report ɗin da na ba ka jiya?”


“Almost sir. Ina gyara wasu details ne”


“Don’t almost it, complete it! Ka tabbatar dates, names da references sun yi daidai kafin ka kawo min”


“Yes, sir”


Ma’aikacin ya fita, Rameez ya koma aikinsa


Ba wai yana son ya wahalar da mutane ba ne, amma ya san ƙaramin kuskure na iya jawo babbar matsala. A irin aikinsu, ba a ɗaukar wani abu da sauƙi saboda kawai yana kama da ƙaramin abu


Bayan ɗan lokaci, aka kawo masa wani sabon report, ya karanta shi a hankali, yana yi wa wasu layuka alama. Akwai bayanan wani mutum da ake zargi da bayar da bayanan sirri ga wasu mutane, amma duk lokacin da aka nemi hujja, sai a samu saɓani


Rameez ya ɗora report ɗin a kan teburinsa

“Too many loose ends” ya faɗa


Ya san cewa akwai lokutan da gaskiya take ɓuya a bayan abubuwan da suke bayyana a fili. Kuma wani lokacin, wanda ya fi nuna kansa a matsayin wanda ba shi da laifi shi ne yake buƙatar a fi lura da shi


Sai dai ba zai bari zato ya rinjayi aikin da yake yi ba


Ya ci gaba da karatu, yana tattara bayanai, yana rubuta tambayoyin da yake son a amsa. Tsohon case ɗin bai bayyana masa cikakken labari ba tukuna, amma abu ɗaya ya fara fitowa fili, akwai wani ɓangare na binciken da ba a taɓa yin cikakken bayani a kansa ba


Kuma Rameez ba ya son barin tambaya ba tare da ya nemi amsarta ba


Da misalin ƙarfe goma na safe, Rayyan ya kira Rameez a wdaya “Where are you?”


Rameez ya kalli agogonsa kafin ya amsa

“Office mana, where else would I be at this time?”


Rayyan ya ce “Daddy asked if you’ll be home for dinner akwai small party”


“Toh zan kwokarta, I’ve got some work to finish”


“Don’t say you’ll try and then show up at midnight”


“Wannan daga bakinka ya fito? Kai da kake iya zama a office har dare?”


Rayyan ya yi shiru na ɗan lokaci “Ohh, toh ai bani nake ma Daddy alkawari ba”


Rameez ya yi murmushi  “Toh ka gayya masa I’ll come if I can”


“Tell him yourself” Daga haka Rayyan ya katse wayar


Rameez ya girgiza kai, ya mayar da hankalinsa kan files ɗinsa, ya san bro dinsa ya san shi sosai, duk da bambancin halayensu, akwai mutunta juna a tsakaninsu


A lokacin da suke yara, Rameez shi ne wanda yake yawan shiga matsala saboda barkwancinsa, Rayyan kuma sai dai ya tsaya yana kallonsa kamar yana tambayar kansa dalilin da ya sa ya zaɓi irin wannan rayuwar, haka suke har kawo girmansu


Ya koma ga tsohon case ɗin, ya rubuta wata tambaya a gefen takardar


‘Who benefited from the missing documents?’ Ya zagaye tambayar, sannan ya rufe file ɗin


Ba zai yi magana game da wannan binciken da kowa ba tukuna. Ba sai ya samu wani abu tabbatacce ba, a aikinsa, haƙuri ya fi saurin magana amfani


Meanwhile, Rahama safiyar ta fara ne kamar sauran ranaku


Mammy tana cikin kitchen tana duba abincin da masu aiki ke shiryawa, yayin da Baba yake zaune a parlour da wasu takardu a hannunsa


Sai dai tun bayan wayar da Baba ya yi da safe, yanayinsa ya sauya, ya karanta wani saƙo a wayarsa, ya kalli hanyar kitchen, sannan ya mayar da wayar aljihunsa


Mammy ta lura da hakan bayan ta fito “Me ya faru?”


Baba ya ɗaga kansa “Nothing”


Ta tsaya tana kallonsa “Dear na san ka, idan ka ce nothing da wannan yanayin, to akwai abin da ke damunka”


Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ajiye takardun da ke hannunsa “An sake turo min da wani saƙo ne game da wani tsohon al’amari, ban ga dalilin da zai sa mu daga hankalinmu ba”


Mammy ta matso kusa da shi “Wane tsohon al’amari?”


Baba ya kalle ta, sannan ya kawar da idanunsa “Ba komai ne ya kamata mu tattauna a yanzu ba”


Ta yi shiru ba ta son matsa masa idan bai shirya magana ba, amma ita ma ta san cewa akwai wasu abubuwan da suka yi nisa a rayuwarsu da ba za su iya mantawa da su kawai ba


Kafin ta sake tambayarsa, sai ga muryar Rahama daga saman bene “Mammy! Ina kika ajiye handbag ɗina?”


Mammy ta lumshe idanunta na ɗan lokaci “Rahama, ki duba inda kika ajiye shi jiya mana!”


“Na duba! Apparently, my bag has decided to disappear” 


Baba ya yi murmushi, amma bai ce komai ba

Rahama ta sauko da sauri, tana kallon kujerun parlour kamar handbag ɗin zai fito daga cikinsu


Da ta ga iyayenta suna zaune cikin shiru, sai ta dakata “Baba, Mammy, lafiya kuwa?”


Baba ya ɗaga kansa “Lafiya lau, me ya sa kika tambaya?”


Rahama ta kalle su duka “Because you both look like you’re attending a very serious meeting without inviting me”


Mammy ta yi murmushi “Babu wani abu Rahama muna magana ne kawai”


Rahama ta matsa kusa da ita “Mammy, are you sure?”


“Eh my daughter, ki je ki shirya”


Rahama ta tsaya tana nazarin fuskarta, kamar tana son ta gano abin da ake ɓoyewa. Amma kafin ta iya tambayar wani abu, wayar Baba ta yi ƙara 


Ya ɗauka, ya saurara na ɗan lokaci “Okay na ji, zan duba” Ya katse wayar, ya miƙe “Zan fita na ɗan lokaci”


Mammy ta kalle shi “Hope zaka dawo da wuri?”


“Eh dear”


Rahama ta bi shi da kallo har ya fita, sannan ta juya ga Mammy “Something is wrong”


Mammy ta ɗauki plate ɗin da ke gabanta, tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta “Ba komai ba ne, Rahama”


“Then why are you both acting strange?”


Mammy ta yi murmushi, ta shafa kumatunta

“Wani lokaci manya ma suna da abubuwan da suke tunani a kansu, ba komai ne ya shafi ki ba”


Rahama ta yi shiru, ta yarda cewa ba komai ne ya shafe ta ba, amma ta san iyayenta sosai. Idan akwai wani abu da yake damun su, ba kasafai suke iya ɓoye shi gare ta ba


Ta rungume Mammy  “Okay Mammy, I won’t ask again but if you need me, I’m here”


Mammy ta riƙe hannunta, ta sumbace shi “Na sani, sweetheart”


Rahama ta yi murmushi, ta koma neman handbag ɗinta


Bayan ta fita, Mammy ta zauna a kujerar da ke kusa da kitchen, ta ɗauki wayarta, ta duba wani tsohon hoto da ta ajiye a cikin wani folder na musamman, ta kalle shi na ɗan lokaci, sannan ta kashe wayar


Da rana Uncle Fahad ya zo gidan kamar yadda ya saba


Ya shigo da murmushi a fuskarsa, yana amsa gaisuwar da ma’aikatan gidan suke masa kafin ya nufi parlourn, ganin Mammy yasa ya zauna suka gaisa, ya ce “Yaya fah”?


“Ya fita amma ba zai jima ba”


Uncle Fahad ya gyada kai “Na kira shi da safe, amma bai ɗauka ba”


Mama Rahama ta kalle shi “Maybe yana busy ne”


“Probably” Ya amsa, sai kuma ya nuna jakkan hannunsa “Na kawo wa Rahama wasu snacks, na san tana son irin waɗannan, before ta ce Uncle baya sonta”


Mammy ta yi murmushi “Ikon Allah, toh Madallah”


Uncle Fahad ya yi dariya “Yes ai dole na”


Sai ga Rahama ta shigo parlour, tana riƙe da handbag ɗinta, ganinsa ya sa ta ce “Uncle Fahad!”


Ta ƙarasa wajensa, ta rungume shi “Finally! Someone who understands my needs”


Uncle Fahad ya kalle ta cike da fara’a “Me kuma kike buƙata yanzu?”


Rahama ta nuna jakar da ke hannunsa “What’s in there?”


“Abin da na kawo miki”


Ta zauna kusa da shi, ta fara duba abubuwan da ya kawo, ganin kayan ciki yasa ta ce “Uncle, you are officially my favourite person today”


“Today only?”


“Depends on what else you bring next time”


Uncle Fahad ya girgiza kai yana murmushi “Ke dai ba kya gajiya, zanga ranan da zaki canza”


Rahama ta ɗauki ɗaya daga cikin snacks ɗin, ta buɗe “Life is short Uncle, we must enjoy it”


Uncle Fahad ya yi murmushi, amma idanunsa sun tsaya a kan wayarsa da ta yi ƙara a aljihunsa


Ya cire ta, ya kalli sunan da ya bayyana a screen, murmushin da ke fuskarsa ya ɗan tsaya na secs sai ya kashe volume na wayar, ya mayar da ita aljihunsa


Mammy data lura da yadda Uncle Fahad ya yi shiru bayan ya kalli wayar, ido ta zuba masa amma daya dago yaga kallonsa take sai ya fara Murmushi ya ce “Rahama kin shirya tafiya Lagos din?”


“I’m working on it Uncle, although I still don’t understand why Baba is suddenly interested in connecting me with someone”


Uncle Fahad ya ɗaga idanunsa “Ya hada ki da wani kuma?”


Rahama ta gyada kai “Eh. Ya ce akwai wani mutum da yake tunanin haɗa ni da shi kuma bai fada min waye bane”


Uncle Fahad ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya yi murmushi “Maybe someone who can help you with the workshop arrangements, ki bari ya yi miki bayani”


“That’s what I’m hoping” Ta ci gaba da cin snacks ɗin


Da misalin ƙarfe huɗu na yamma, Hajiya tana zaune a parlour gidan su Rahama, tana kallon Rahama da ke ta shirye-shiryen kayan da ba wanda ya fahimci muhimmancinsa sai ita


“Rahama me kike yi yanzu?” Hajiya ta tambaya


Rahama ta ɗaga kanta daga inda take gyara abubuwan a kan tebur “Ina ƙoƙarin shirya abubuwan da zan buƙata, I have a system Hajiya”


Hajiya ta kalle ta daga sama har ƙasa “System ɗinki ne ya sa kika ajiye takalma a tsakiyar parlour?”


Rahama ta bi inda ta nuna da kallo, sannan ta ɗauki takalman da sauri “That’s temporary arrangement”


“Temporary arrangement ɗinki zai sa wani ya faɗi kuwa”


Rahama ta yi murmushi, ta kai takalman gefe “Okay Hajiya, na gyara”


Ta juya ta nufi wani side na parlour, Hajiya ta bi ta da kallo


Yadda take tafiya ya sa zuciyarta ta tsaya na ɗan lokaci, ba tafiyar kawai ba ce akwai wani salo a yadda Rahama take kawai Wanda duk sanda ta ganta sai ta tsinci kanta cikin damuwa


Ba ta yi magana ba, ta jira Rahama ta dawo ta zauna kusa da ita “Rahama zo nan”


Rahama ta ƙarasa, ta zauna a gefenta “Na’am Hajiya?”


Hajiya ta kalli fuskarta sosai, Idanunta sun fi komai jan hankalinta


“Yaushe kika gama karatunki?”


Rahama ta yi murmushi “Kin manta ne? Na gaya miki kwanakin baya ai”


“Na sani, Ina son in ji daga gare ki again”


Rahama ta fara ba ta labarin yadda ta ji bayan ta gama karatu, abubuwan da take son cimmawa, da yadda take fatan samun damar yin aiki a babban wuri, Hajiya tana sauraron ta, tana kallon yadda take magana


Ta sauke ajiyar zuciya “Allah ya ba ki sa’a Rahama” ta faɗa a ƙarshe


“Amin Hajiya! Ki yi min addu’a na aure mai kud’i kuma na fara aiki a babban waje”


“In shaa Allah”


Rahama ta ɗora kanta a kafaɗarta, sai shirme take mata Hajiya ta girgiza kai tana murmushi “Ke dai ba kya girma”


“Growing up is overrated Hajiya”


“Allah ya kyauta”


Rahama ta yi dariya, ta miƙe ta je ta ɗauko mata ruwa


Hajiya ta bi ta da kallo, amma wannan karon babu murmushi a fuskanta, Idanunta sun koma kan ƙofar parlour, inda Rahama ta shike zuwa kitchen


‘There is something I need to understand’ ta yi wa kanta wannan alkawarin a hankali


Da yamma ta yi, direban Hajiya ya iso gidan su Rahama domin ya ɗauke ta, Hajiya ta yi sallama da Mammy, ta rungume Rahama, sannan ta ce sai na sake dawowa


Rahama ta raka ta har ƙofar gida “Hajiya ki dawo da wuri, bcos gidan nan nasan zai yi shiru ba tare da ke ba”


Hajiya ta kalle ta da mamaki “Shiru? Ke kina cikin gidan nan, wane shiru za a samu?”


Rahama ta yi murmushi “Exactly, that’s why you need to come back and supervise me”


Hajiya ta girgiza kai, ta shafa kanta “Ki kula da kanki”


“In Sha Allah”


Hajiya ta shiga motar, direban ya rufe ƙofa, kafin motar ta tafi, ta sake kallon Rahama da ta tsaya tana daga mata hannu, murmushi tayi mata kafin suka fita….


Bayan motar ta isa gidansu Daddy, Hajiya ta sauka, aka tarbe ta da girmamawa. Ma’aikatan gidan suka sauke mata da kayanta, sannan ta nufi cikin gidan


Muhammad, mahaifin Rayyan da Rameez Wanda suke Kira da Daddy yana zaune a parlour lokacin da ta shigo, ya miƙe ya tarbe ta 


“Barka da zuwa Hajiya”


“Yauwa, Muhammad”


Ya taimaka mata ta zauna, Sannan ya sauka kasa ya zauna ya gaishe ta, har mamakin mahaifiyarsa yake yi, yadda take son abokinsa da iyalensa, dawowarta kasar bayan long time amma gidan ta sauka


Hajiya ta kalli ƙofar parlour “Abubakar (Baban Rahama) yana nan gidan wai?”


“Eh Hajiya, yana can library ne yana wasu research”


“Ka je ka sanar da shi cewa ina son mu tattauna wani abu”


Daddy ya gyada kai, ya miƙe


Bayan ɗan lokaci, sai gashi tare da Baba sun shigo parlour, ya gaishe da Hajiya, sannan ya zauna kusa da Daddy


Hajiya ta kalli su , ta san wannan ne right time daya kamata suyi wannan tattaunawar data daɗe tana jiran lokaci


“Abubakar, Muhammadu” ta fara cikin nutsuwa “ina ganin lokaci ya yi da za mu dawo kan alkawarin da muka ɗauka shekaru da suka wuce”


Su biyun suka kalli juna a taƙaice, Daddy ya gyara zamansa “Wane alkawari kike nufi, Hajiya?”


Hajiya ta ɗan ɗaga gira “kar ka gwada min cewa ka manta ne? Ah lalle yanzu kuwa ya kamata a dawo da maganar dan lokaci yayi”


Baba ya numfasa a hankali “Ba mu manta ba, Hajiya”


Daddy ya gyada kai “Ba mu manta ba, amma kamar yanzu bai yi sauri ba?”


Hajiya ta mayar da hankalinta ga Baba “Rahama shekarunta nawa yanzu?”


Baba ya ce “23 yrs zata cika”


Hajiya ta juya ga Daddy “Rayyan fa?”


“Yanzu haka yana da shekaru 32”


Hajiya ta yi shiru na ɗan lokaci, kamar tana auna abin da za ta faɗa na gaba “Lokaci ya yi da za a dawo da maganar. Ba na ganin akwai dalilin da zai sa mu ci gaba da jinkirta abin da muka daɗe mun yanke shawara a kansa, dukkansu babu wanda bai kai aure a cikinsu ba”


Daddy ya kalli Baba, sannan ya koma ga Hajiya “Toh Hajiya duk yadda kika ce ai dole akai zamu zauna”


Baba ya gyada kai “Hakan ma ya yi”


Hajiya ta jingina da kujerarta “Alhamdulillah. Allah ya sa alheri” duk amsawa suka yi da Ameen 


Hajiya ta kalli su biyun a ƙarshe“Abin da ya rage shi ne mu yi komai cikin hikima. Ba na son a yi gaggawa ta hanyar da za ta kawo matsala”


Baba ya gyada kai “Mun fahimta”


Daddy ya amsa cikin nutsuwa “Za mu yi yadda ya kamata”….


Da misalin takwas na dare, Rayyan ya dawo gida bayan ya gama aikinsa


Ya yi wanka, ya canza kaya, sannan ya zauna a ɗakin karatu na ɗan lokaci yana duba wasu takardu da ya kamata ya gama kafin gobe, haka Rayyan yake ba ya son barin aiki a baya idan yana da damar kammala shi toh kawai yayi ne


Bayan ya gama, ya rufe littafinsa, ya ɗauki wayarsa


Ya ga saƙon Daddy yana tambayarsa ko zai samu lokaci ya je gidan Uncle dinsa Abubakar


Rayyan ya amsa a taƙaice cewa zai je


Bai yi wani shiri na musamman ba. Ya ɗauki makullin motarsa, ya fita daga gidan


A hanyarsa yana tunanin cewa ya daɗe bai je gidan ba balle ya kira Mammy ko a waya ya gaishe ta, tuna hakan yasa yaji kunya matuka, wanda wajen kusan shekaru biyu kenan tun bayan tafiyarsa zuwa ƙasar waje domin wani aiki da ya ɗauki tsawon lokaci, though ya kasance cikin wani project da ya buƙaci ya zauna a can har sai an kammala wasu muhimman ayyuka


Bayan ya dawo, aiki ya ci gaba da ɗaukar lokacinsa as usual dai, saboda haka, duk yadda yake da Mammy da Baba, bai samu damar zuwa gaisawa da su kamar yadda ya saba a baya ba


Da ya isa gidan, aka buɗe masa ƙofa, ya shiga cikin parlour, inda ya tarar da Baba da Mammy suna zaune


“Assalamu alaikum” ya faɗa


“Waalaikumus salam” Baba ya amsa cikin farin ciki jin muryansa “Rayyan!”


Rayyan ya karasa ciki ya zauna yana murmusgi ya gaishe da shi, sannan ya gaishe da Mammy cikin girmamawa


“Ya karfin jiki?”


“Alhamdulillah” Mammy ta amsa “Kai fa? Yaushe ka dawo? Kasan ka ki mu yanzu”


“Haba Mammy ai ban Isa ba, aiki ne kawai ya yi yawa”


Baba ya yi murmushi “Nasan nature din aikin but at least kana rike zumunci Rayyan”


Rayyan ya gyada kai “In Sha Allah. Zan riƙa zuwa”


Mammy ta kalli fuskarsa da murmushi “Yaron nan ya girma sosai, rabona da ganinka har na manta yadda kake a baya”


Rayyan ya yi Murmushi kawai, Baba ya ce “Kanwarka ma ai tana nan, ta gama karatun”


“Allah sarki, Anya zan gane ta kuwa? Tun tana karama fah rabo na da ita”


Mammy ta ce “Shame on you”


Duk dariya suka yi, Baba ya jingina a kujerarsa

“Rayyan, akwai wani abu da nake son in yi magana da kai a kai”


Rayyan ya kalle shi “Na’am, Baba”


“Tunda Rahama ta gama karatu, kuma ina son in fara saka ta a system ɗin aiki, Ina ganin ya kamata ta fara samun ƙwarewa a wajen da zai taimaka mata ta gina future ɗinta, don Yau mune gobe ba mu ba”


Rayyan ya saurara ba tare da ya katse shi ba


Baba ya ci gaba “Za ta je wani workshop a Lagos, Ina tunanin idan za ku je, zan iya haɗa ku domin ka taimaka mata da wasu arrangements, ka san wasu mutane a can, kuma kana da masaniya kan yadda ake gudanar da irin waɗannan abubuwa”


Rayyan ya ɗan yi shiru “Which workshop Baba?”


Baba ya yi masa bayani a taƙaice game da workshop ɗin, tsawon kwanakin da zai ɗauka, da irin abubuwan da Rahama za ta koya a ciki


Rayyan ya saurara, sannan ya gyada kai “Okay If I can help, I will”


“Na gode. Ina so ta fara samun damar shiga tsarin aiki da wuri, ba na son ta gama service ta zauna a gida ne”


Mammy ta yi murmushi “Rahama tana da burin da take son cimmawa. In Sha Allah, Allah zai ba ta sa’a musamman yadda take maida hankali kan abubuwa”


“Amin” Baba ya amsa


Rayyan ya kalli agogon hannunsa, sannan ya sake mayar da hankalinsa ga hirar


Bayan sun yi wasu ’yan maganganu game da tafiyar, Mammy ta tambaye shi ko zai ci wani abu kafin ya tafi. Ya amsa cewa ba ya buƙatar komai, amma ta dage aka kawo masa abin sha da ɗan abinci


Meanwhile Rahama tana ɗakinta tana bacci, ta shafe yini tana shirye-shiryen tafiyarta, har ta gaji sosai, hakan yasa ta kwanta da wuri


Bayan ɗan lokaci, Rayyan ya miƙe

“Zan tafi yanzu Baba”


Baba ya miƙe shi ma “Allah ya tsare hanya, idan ka isa gida sai kayi magana da Daddynka”


“In Sha Allah”


Mammy ta raka shi zuwa ƙofar parlour “Ka gaishe mana da Mommynka da Hajiya pls”


“Zasu ji Mammy”


Rayyan ya fita, ya shiga motarsa, sannan ya nufi gida

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol