Free chapter · Read without an account
Page 4
by Nana Disoo · GUGUWAR RAYUWA
GUGUWAR RAYUWA 🌪️
(...kowa da inda ta kaÉ—a shi!)
​NA NANA DISO
​PAGE 4
​"Na zo na ja maka kunne ne kawai! Rayuwata daban, taka daban Billahillazi, idan ka ƙara samun Babana da zancen cewa ba na zuwa makaranta, sai na ce wa kowa fyaɗe kake so ka yi mini a ofis ɗin nan, shi ya sa kake ta bibiyata"
​Wani irin zazzafan gumi ne ya karyo wa Ustaz Auwal lokaci guda, ya wanke masa fuska har cikin riga.
​Numfashinsa ya sarƙe cak! Mafarki yake yi ko kuwa gizo kunnuwansa ke masa? Ya dafe ƙirjinsa da ke bugawa da ƙarfi, laɓɓansa na rawa
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Surayya! Surayya, don girman Allah ki ce mini mafarki nake yi... Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yaa Hayyu yaa Qayyum!"
​Wani shu'umin murmushi Surayya ta saki, ta ɗaga gira sama tana watsa masa kallon raini
"Ka duba nan Ustaz ɗan mai tuwo da miya! Wannan shi ne gargaɗi na ƙarshe da zan yi maka a kan rayuwata! Kuma maganar wani aure tsakanina da kai, to daga yau ta mutu murus! Ka je can ka janye zancen, don na gama wuce ajin ɗan mai tuwo da miya, matsiyaci jinin tsiya!"
​Tana gama furta hakan, ta juya ta turo ƙofar ofishin da ƙarfi, ta fice tana wani nannayan tsaki mai ɗaci.
​Ustaz Auwal ya yi mutuwar tsaye a wurin, launi da kwarjinin fuskarsa suka sauya gaba ɗaya zuwa wata kalar firgici, idanunsa suka rine suka yi jajur.
Anya ba shafar aljanu ce ta samu Surayya ba? Kai, subhanallah! Wallahi wannan ba Surayyar da aka sani ba ce! Tabbas ba ita ba ce... To ko jinnu ne suka jirkita mata tunani? Ta yaya hakan za ta faru? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Wace irin baƙar rana ce wannan? Wane irin ruɗin zuciya ne wannan yarinyar ta faɗa ciki? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel!
​Yarinyar da ko tafiya ba ta yi da kanta a ɗage, yarinyar da ita ce amirar ɗalibai a wannan makarantar, yarinyar da ya ɗauka babu mai kamun kai da hazakarta... Tabbas, ba zai ƙyale wannan maganar ba, yana tashi ɗalibai kai-tsaye zai nufi gidan Malam!
​A can birnin Landan (London), tun da jirginsu ya sauka a filin jirgi, bakin Ahmad ya kasa rufuwa saboda tsananin ɗoki da annashuwa.
​Zuwa aka yi aka tarbe su, sannan aka ɗunguma da su zuwa wata unguwa mai ban sha'awa. Unguwa ce mai kyawawan gidaje masu tsari, kodayake ba su da wani girma sosai. Wani bature ne ya buɗe musu wani gida mai kyau yace musu nan ne masaukinsu ba a cikin ɗakunan makaranta ba.
​Baturen ya juya ga wasu samari biyu da ke ciki, Mubarak da Mukhtar, ya nuna Ahmad yace
"Wannan shi ne sabon abokin zamanku, Ahmad."
​Saurayin biyun suka tsaya suna ƙare masa kallo tun daga sama har ƙasa. Yaro ne dogo, kyakkyawa na gaske, kodayake ba fari tas ba ne, amma fatarsa mai haske ce wadda wahalar rayuwa ta ɗan sauya mata launi. A kallo ɗaya zaka fahimci ba zai wuce sa'anninsu ba, sai dai shi yana da ƙirar manyan maza masu cikar ƙasusuwa da kwarjini; ga manyan idanu da siririn hanci mashaaAllah, tare da wata 'yar siririyar wushirya da ta ƙara fito da zallar kyan jinin Fulani ko Shuwa a tare da shi.
​Ahmad ya miƙa musu hannu cikin fara'a yana sauke numfashin girmamawa:
"Barkanmu da saduwa."
​Sun ji daɗin yadda ya sauke kansa ya gaishe su cikin girmamawa, domin sun zaci ko irin masu ji-da-kan nan ne. Suka shiga cikin gidan; ɗakuna biyu ne cif a ciki, sai kicin a falon, bandaki biyu, da kuma wani ɗan fili na gida mai kyawun gani.
​Suna tura ƙofar falon, suka ci karo da wani matashin da shima ba zai wuce sa'arsu ba, yana zaune dirshan a kan kujera ya baje ƙafafu, yana zugar shisha hayaki na fita ta baki da hanci!
​Dumm!
​Take zuciyar Ahmad ta yi wani wawan bugu, gabansa ya faɗi, ransa ya ɓaci ƙololuwa! Wani irin ɗaci ya tokare masa maƙogwaro, har ya ji gaba ɗaya shauƙin karatun ya fita daga kansa. Yana shirin buɗe baki ya yi magana, sai kalaman yayansa Umar suka daki dodon kunnensa a can ƙasan zuciyarsa
“Ahmad, a can za ka ga abubuwan mamaki da firgici masu yawa. Za ka haɗu da mutane daban-daban, masu ɗabi'u da tarbiyya kala-kala, har da addinai masu sauyin yanayi. Wani za ka gan shi da sunan musulmi amma yana aikata dukkan manyan laifuka (kaba'ira). Idan ka zuba idanu kana kallon irin waɗannan mutanen, ba za ka taɓa samun nasara a rayuwarka ba! Amma idan ka zuba ido a kan mutanen kirki, to tabbas za ka cimma manyan nasarori. Ba kowa ake gyara wa kuskurensa a lokaci guda ba, wasu da yawa ba su san ba daidai suke yi ba, wasu kuma sun kasa jure jarrabawar rayuwarsu ce. Ahmad, ka hango mutanen kirki a rayuwarka, ka hango waɗanda suka bar kyakkyawan tarihi, sai ka samu babban rabo a rayuwarka!”
​Kalaman Umar suka sanyaya masa jiki lakwas.
​Mukhtar da Mubarak suka kalli wanda ke zugar shishar suka kwashe da dariya:
"Kai abokinmu, ashe har ka sauka da zafinka haka?!"
​Matashin ya ɗago kansa daga zugar hayakin yana sheƙeƙe
"Ai ku nake ta dakon gani maza!"
​Mubarak ya yi wata shegiyar dariya yana tafa hannu
"Ni fa dama jira nake yi in samu wannan tallafin in shigo Landan in zuba tsiyata! Fitina da nishaÉ—i sai wadda na ga dama a garin nan!"
​Mukhtar ya amshe zancen da zafi-zafi
"Kai mutanena, ai ni dama jira nake in bar su Old Man a can gida in taho nan in je gidan giya, in shana da mata in tsula tsiya ta son rai! Wallahi Babana har da wani kuka a filin jirgi wai don Allah in sa masa farin ciki... hahaha!"
​Ali ya ajiye robar shishar da ke hannunsa, hayaki na fita ta hancinsa, ya ce
"Su Old Man an sha kuka yadda ya kamata kam! Ni kunsan fa da ƙyar Mamana ta samo mini wannan admission ɗin, har da wani sharɗin wai idan nazo in riƙa aiki bayan karatu. Na ce mata zanyi mana a baki! Yanzu dai ku hanzarta ku watsa ruwa ku huta, anjima mu wuce club mu doke daren nan!"
​Ali ya juya idanunsa da suka kaɗa ya kalli Ahmad
"Abokina, ya naga ka yi tsit ba ka ce komai ba?"
​Ahmad da jikinsa ya gama yin sanyi lakwas, ya bi su da wani kallo mai cike da jimami ba tare da ya furta ko kalma ɗaya ba. Ya ɗauki jakar kayansa ya shige ɗaki, ya shiga jerawa a sanyaye. Ya shiga banɗaki ya watsa ruwa, ya ɗauro alwala ya zo ya kabbara sallar da ke kansa.
​Wani irin ciwon duniya da tsananin kewar gida suka tokare masa ƙirji.
Allah sarki iyaye... yanzu duk irin sadaukarwa da kukan da iyayen yaran nan suka yi a kansu, wannan ita ce sakayyar da za su nuna musu kenan?
​"Allah Ya shirya mana ku..." Ahmad ya faɗa a sarari yana sauke numfashi cike da damuwa, sannan ya kwanta a kan gado.
​Ko alamar sallah sam bai ga ɗayansu yana shirin yi ba; sai ma wani uban kiɗa na zamani da suka kure ƙararsa a falon yana amsa amo a cikin gidan gaba ɗaya.
​A can gida kuwa, tun bayan da Umar ya fara karatun jami'a, rayuwarsa ta zama ba shi da wani isasshen lokaci ko kaɗan. Daga makaranta kai-tsaye garejin aikin makanikancinsa yake wucewa, ba ya komawa gida sai can cikin dare.
​Yau ma kamar kullum, ya shigo gidan da sallama, hannunsa ɗauke da baƙar leda mai ɗauke da kifin miya, nama, da kayan miya.
​"Sannu da zuwa, Umaru." Muryar Mama ta daki kunnensa.
​Umar ya ƙarasa cikin ɗakin yana goge gumin goshinsa da bayan hannu:
"Sannu da gida Mama. Ya na ga yau babu alamar ƙullun alala a kusa da ke?"
​Mama ta yi shiru na wasu daƙiƙu, kafin ta ɗago kanta a sanyaye tace
"Jiki da jini Umaru... na ce bari in É—an huta ne yau."
​Jin wannan amsar ya sa Umar gane komai a take; ya san kuɗin da Mama ta tara na jarin alalar ne ta ɗauka ta bai wa Baba domin ya ƙara a jarin sana'arsa.
​Ba tare da ɓata lokaci ba, Umar ya zura hannu a cikin aljihun wandonsa, ya ciro damin kuɗi 'yan dubu-dubu ya miƙa wa Mama a hannu:
"Mama, ga wannan dubu goma ne a ciki. Ki ƙara a jarin alalar taki. Dama na yi niyyar zan sayi ƙarin kayan aiki ne a shagon makanika, amma a yanzu buƙatarki ta fi tawa muhimmanci."
​Mama ta kalli kuɗin, wani irin zazzafan tausayinsa ya cika mata ido har ƙwalla ta fara taruwa:
"Umaru... Allah Ya yi muku albarka, Allah Ya haskaka..."
​Bata ƙarasa addu'ar ba, aka turo kyauren gidan da wani irin mugun ƙarfi har sai da ƙofar ta daki gini! Wata muryar masifa da bala'i ta cika tsakar gidan a hasale
​"Ina kike tsinanniya mara asali An asirce mini ɗa, an mayar da shi wani soko Yanzu har jikana ya tafi amma babu ko..."