Free chapter · Read without an account

Page 5

by Nana Disoo · GUGUWAR RAYUWA

GUGUWAR RAYUWA 🌪️
(...kowa da inda ta kaɗa shi!)

​NA NANA DISO

​PAGE 5

​"Wanda ya yi ƙoƙarin gaya mini saboda ba ni da wani amfani a idonku, ko? To karatu ne dai... wallahi yaro sai dai ya zama ɗan iska, amma ba dai ya zama wani abin alfahari ba!"
​Muryar Kaka Fulani ce ke dukan tsakar gidan a zafafe yayin da take ƙarasowa ciki, tana banka labule tana huci.
​Umar ya ɗago kansa a sanyaye ya zuba mata idanu. Shi dama can mutum ne marar son hayaniya ko kaɗan; wanda ke ɗan taka mata birki ya riga ya tafi Landan, yanzu kuma ga shi ta dawo za ta addabi mahaifiyarsu. Cikin daurewa da girmamawa ya ce
"Ina yini, Kaka?"
​"Munafuki! Ai har da kai a cikin muguntar! Na ga makarantar Islamiyyar da kake koyarwa nan-nan take kusa da gidana ko? Amma saboda kun tsotsi baƙin hali irin na uwarku, ba ka san ka shiga ka gaishe ni ba! Na ma ji daɗi da fitsararren yaron nan Ahmadu ne ya tafi. To wannan yaron ma zai iya yin wani karatu? Kai, ba lallai ba! To in ba munafurci irin na Yahaya ba, ta yaya zai samar wa ɗansa gurbin karatu a waje amma ya kasa samar wa Habuna?!" Ta ƙara zuba wa Umar mugun kallo tana harara: "Wai kai Umaru, ba da kai nake magana ba? Ina fitsararren ya tafi wannan karatun ne da har kuke wani ɓoye-ɓoye?"
​Umar ya rasa ma me zai ce mata; ya kamata a ce tsohuwar nan ta sauke waɗannan ɗabi'un nata domin shekaru ba ƙaramin ja suke yi ba, amma abin nata kullum gaba yake yi.
"Wai Umaru, ba za ka yi mini magana ba ne sai ka yi mini shiru?!"
Ya sauke numfashi a hankali ya ce
"Landan (London) ya tafi karatu."
​"Oh ni Fulani! Birnin Landan?! Yanzu Yahaya yana da uban kuɗin da zai kai yaron nan Landan amma ya kasa gyara mini inda nake kwana?! Tabbas wannan aikin asiri ne! Kawai ya ɗauki lasisin rashin mutunci da karuwanci ya damƙa wa yaro a hannu!"
​Mama dai na gefe tana kici-kicin harkokinta, ko kallon inda Kaka Fulani take ba ta yi ba don ba ta da lokacin zubar da mutuncinta a kanta.
​Kaka Fulani ta juyo kan Mama tana huci:
"Asma'u, don girman Allah wanene malamin naki? Ki taimaka ki gaya mini shi mana, don na san wannan aikin asirinsu ne! To in ba aikin asiri ba, ta yaya Yahaya zai kashe wannan uban kuɗin? Na san ma gonarsa ta gado ya sayar! Tabbijan... to kai Umaru, miliyan nawa aka kashe a wannan haukan?"
​Umar ya dube ta a sanyaye ya ce
"Kaka, ki samu Baba ki tambaye shi, ina ga shi ne zai ba ki amsar da za ki fi gamsu da ita."
​Mama ma daga baya miƙewa ta yi ta bar mata tsakar gidan ba tare da ta ce uffan ba. Ta ƙarasa ayyukanta, sannan ta leƙa zaure ta kira wani almajiri ta ba shi kuɗi ya siyo mata waken alala kwano uku. Tana ƙoƙarin ɗaukar ledar naman da Umar ya shigo da shi, Kaka Fulani ta yi wani wawan zafin nama ta fizge ledar a fusace
"Ina da tabbacin ɗana ya kawo ko jikana! Don haka wallahi ba za ki ci ba!"
​Tana gama faɗar haka ta banka ƙofa ta fice da naman.
​Wani zazzafan hawaye ne ya wanke wa Mama fuska. Abubuwan da wannan matar ke mata Allah ne kaɗai Ya san iyakar ciwonsu; ta gaji... ta gaji da wannan wulaƙancin na Kaka Fulani!
​Umar ya matso kusa da ita, ransa a jagule yana lallashinta
"Don Allah Mama ki daina damuwa da halin Kaka... wata rana sai labari. Kuma naman ma ta daɗe ba ta ci ba, in sha Allahu yanzu idan na fita zan siyo miki ko balangu ne mu ci."
"Don Allah ka daina barnar kuɗinka haka Umaru. Komai ka samu ƙoƙari kake yi ka kashe mana shi a gida..."
"To Mama, meye amfanin kuɗin idan ban faranta muku rai da su ba?"
​Murmushin ƙauna da tausayi Mama ta yi, domin ta san halin Umar sarai da rashin son kai. Can kuma sai kewar Ahmad ta taso mata, a hankali ta ce
"Allah Ya kiyaye mini kai Ahmadu... Ya tsare ka, Ya yi muku albarka baki ɗaya."
​Bayan an idar da sallar Isha'i, Baba ya biya gidan Kaka Fulani domin duba lafiyarta. Yana shiga ko zama bai yi ba, ta ɓarke da faɗa da masifa:
"Wato tunda ba ni na haife ka ba, ban isa ka sanar da ni ka sayar da gonarka ba ko?!"
​Baba ya zuba mata idanu cike da mamaki
"Ban gane ba... wace gona kuma?"
"Gonar da ka sayar ka biya wa yaronka makaranta a Landan mana!" ta faɗa tana murguɗa baki.
​Wani guntun murmushi ya kufce wa Baba saboda yadda ta fira sunan garin, ya girgiza kai:
"Ni ban sayar da wani abu nawa ba, Hajiya. Yaron nan fa kyauta wani bawan Allah ya samar masa da wannan karatun. Ba ni da hannu a ciki, ko sisi ba na tunanin akwai nawa a ciki."
"To amma ba za ka gaya wa Alhajin kana da ƙani Habu ba sai ka ɓoye?! Saboda baƙin ciki da son kai ko?!"
​Baba ya san dama za a rina, don haka ya ce:
"Shi Ahmadun ne ya samu da kansa, ni kaina ban ma san Alhajin ba."
"Wallahi Yahaya ka ji tsoron Allah! Ka daina munafurci da baƙin ciki, zuciyarka gaba ɗaya ba ta da alheri! To na dai gaya maka, yadda ka samar wa ɗanka, ka gaggauta samar wa nawa ɗan shi ma!"
​Baba bai ƙara cewa ƙala ba; ya yi mata sallama a sanyaye ya juya ya fice daga gidan.
​"Malam, kana saurare na kuwa? Na ji ka yi shiru! Anya kuwa ba shafar aljanu ce ta samu Surayya ba? Domin na ƙara bincike jiya, an tabbatar mini ba a gida ta kwana ba! Ni a ganina ma kawai a ɗaura mana aure da ita, idan yaso sai ta tare a gidanmu..."
​Tsafi gaskiyar mai shi! Kafin Ustaz Auwal ya rufe baki, sai ga Malam ya hau shi da zazzafan faɗa da zaro idanu
"Wai me yarinyar nan ta tare maka ne kake kafa mata idanu haka?! Ko da gaske so kake ka yi mata fyaɗen da ta faɗa?!"
​Dasss!
​Wani irin matsanancin shock ne ya ziyarci zuciyar Ustaz Auwal! Ya ɗago kansa yana kallon Malam da idanu cike da kaduwa:
"Malam... ta yaya zaka yi mini wannan baƙar shaidar?! Don na..."
"Kada ka ƙarasa maganar nan!" Malam ya daka masa tsawa. "Na gaya maka ɗiyata ba ɗiyar banza ba ce! Ka fita daga sabgarta gaba ɗaya, wannan shi ne gargaɗina na ƙarshe a gare ka!"
​Gaba ɗaya kan Ustaz ya gama ɗurewa. Ya yi tsit yana bin tafiyar dattijon da idanu cike da jimamin yadda asiri ya gama rufe masa idanu.
​A gida kuwa, Kausar lamarin yayar tata ya gama dukan ƙirjinta. Abin da ya fi ba ta takaici shi ne yadda iyayensu suka zuba mata idanu ba sa iya ce mata uffan; wani sa'in idan takaici ya ishi Inna har kuka take yi a ɓoye, amma ba za ta iya tsawatar wa Surayyar ba!
​"Alhaji... gaskiya ba sha ka yi iya na kuɗinka ba! Yanzu tunda an gama ginin sabon gidan, so nake in gwada hawa wannan motar taka mu fita."
​Wata zabura Alhajin ya yi cike da sha'awa
"Taki motar ma ta kusa ƙarasowa baby girl! Ni dai babban burina ki kwana a nan har zuwa gobe sai ki tafi."
"Hahaha! Kai Alhaji... duk irin jijiyoyin jikinka da na gama warwarewa har sai an ƙara wani daren kuma? To nawa zaka ƙara mini?"
"Zan haɗa miki da gida na kanki!"
​Wata zabura Surayya ta yi tana kallonsa da idanu masu cike da zallar kwadayi, domin ta san da gaske yake yi! Ta miƙe caraf ta nufe shi, ta dāne jikinsa tana wani lankwasa murya... Daga nan suka ci gaba da aikata baƙar alfasharsu.
​Washegari da sassafe, Alhajin ya miƙa mata mukullin wata sabuwar mota ƙirar zamani, ya haɗa mata da wata tsadaddiyar waya ta zamani. Daga nan Surayya ta kama hanya, kai-tsaye unguwarsu ta nufa.
​Tun a bakin titi mutane suka shiga zuba mata idanu cike da matsanancin mamaki har ta ƙaraso daidai ƙofar gidansu. Ta daɗe a tsaye a wajen motar tana jin wani irin ƙyanƙyamin ƙauyancin unguwar yana kamata.
Yanzu ace wai kamar ni Surry Baby nan ne gidanmu?!
​Malam na ganinta ya washe baki cikin sanyin rai:
"Sannu da zuwa Surayya... kin zo lafiya?"
Ta dube shi a wulaƙance ta ce:
"Malam, ɗauko mini ledar nan daga mota."
​Jikin Malam na ɓari ya ɗauki ledar ya shigo da ita gida! Mutanen da ke zaune a ƙofar gida duk sun rikice; anya Surayya ce kuwa? A'a ba ita ba ce! Haka kowa ya bar zancen domin a saninsu Surayya dogon hijabi take sakawa, amma wannan da suka gani shigar banza ce a jikinta.
​Kausar na zaune a tsakar gida ta ji ƙas-ƙas ɗin takalmin yayar tata. Inna ta tarbe ta tana mata sannu da zuwa. Surayya ta wuce ta zauna kusa da Kausar, tana ƙare wa tsohon ginin gidan kallo daga sama har ƙasa cikin gundura
"Malam, ka shirya kawai... za mu bar wannan tsohon gidan!"
​Inna ta zabura cike da ɗoki
"To... to ina za mu koma kuma?"
​Wani irin zazzafan zafi ne ya turniƙe zuciyar Kausar, ƙirjinta na neman fashewa saboda ɓacin rai! Ta miƙe tsaye tana kallon Malam da Inna a fusace
"Babu inda za mu je Wallahi babu inda za mu je a gidan nan! Surayya, ki je can ki ci kuɗin karuwancinki ke kaɗai, amma iyayena ba za su ci ba! Ku kuma kuna kallonta ta fi kwanaki biyar ba ta gida amma kun kasa tambayarta inda ta je
​Tas
​Surayya ta juyo da zafin nama ta kifa wa Kausar wani zazzafan mari! Ta nuna ta da yatsa tana huci
"Idan ina nan kika ƙara yi mini wannan haushin, sai na yi miki abin da ya ninka wannan marin sau goma!"
​Ta juya ta shige ɗaki tana jan tsaki da ƙarfi
"Ana muku gata kuna nuna jahilci! Ina son in fidda ku daga wannan baƙin talaucin amma kun tsaya kuna wasu maganganun banza!"
​A birnin Landan kuwa, yau kwanaki biyu kenan da fara zuwan Ahmad makaranta. Sosai yake jin daɗin karatu, kuma kuɗin alawus ɗin da Alhaji ya ba shi ko taɓa su bai yi ba har yanzu, domin nisan da ke tsakanin jami'ar da gidansu bai wuce a take shi a ƙafa ba.
​A hanyarsa ta zuwa makaranta, ya hango wani ƙasaitaccen garejin gyaran motoci. Ya shiga ya samu manajan wurin, ya tambaye shi ko zai iya samun aikin ɗan koyo a gefe bayan ya taso daga karatu. Manajan ya amince masa. Burin Ahmad yau idan ya koma gida ya fara aikin, domin ya samu ƙaramar waya ko zai riƙa jin lafiyar iyayensa a gida.
​A kan hanyarsa ta dawowa, ya tsaya a wani babban kanti ya sayi 'yan kayan abinci domin ya lura da tsadar abincin waje, don haka ya yanke shawarar zai riƙa dafa abincinsa da kansa.
​Yana tura ƙofar falon gidan nasu, ya ci karo da wani abin da ya kusan sarƙe masa numfashi!
​Falon ya cika maƙil da samari da 'yanmata kuma kusan duk fuskokin Hausawa ne! Ga wani uban kiɗa yana tashi, hayakin shisha da giya sun turniƙe falon.
​Wani irin zazzafan fushi ya rufe Ahmad! Ya taka a fusace ya fincike wayar da ke kunna kiɗan, ya kashe shi ƙaf! Ya juya yana huci, idanunsa sun kaɗa sun yi jajur:
"Wallahi-tallahi, wannan ita ce ranar ƙarshe da za ku ƙara cika mana gida da mata kuna aikata shaiɗanci da alfasha! Idan ba haka ba, sai na nuna muku ainihin kalar rashin mutuncina a garin nan!"
​Kafin ya rufe baki, wata budurwa ta tako a yangace tana wani ƙas-ƙas da takalmi. Jikinta sanye yake da wata 'yar ƙaramar rigar ƙirji (half vest) da wando kalar ruwan ƙasa (brown pant) wanda ya gama fitar da surar jikinta a waje.
​Tana ƙarasowa gabansa, ta saki wani shegen murmushi, ta rungume Ahmad ƙam a ƙirjinta tana shafa kansa cikin wata lallausar murya mai cike da sihiri...

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol