Free chapter · Read without an account

LOKACI CHAPTER 28

by Rabi'atu kabiru Fulani · LOKACI

***


⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳ 

RABI'ATU FULANI 

YOTA

Under Team Yota's Amazing Pen's.


      FULANI ❣️ 
***


WELCOME TO COOL EMPIRE 

Your Trusted Destination for Quality Products!

We deal in a wide range of products, including:

👗 All Kinds of Fabrics
🌸 Beautiful Laces
🧕 Luxury Abayas
🌺 Quality Atamfa
🌹 Musk and Fragrances
💊 Medicines and Healthcare Products
✨ And Many More!

Quality Products, Excellent Service, and Customer Satisfaction!

COOL EMPIRE — Your Satisfaction, Our Priority!

BARKA DA ZUWA COOL EMPIRE, INDA MU KE KAWO MUKU KAYA NA ZAMANI, DOMIN KAWATA ADONKU.
MU NA KAWO MUKU 
LACES
ATAMFOFI
RIGUNAN ABAYA
MAGUNGUNA DA SAURAN SU.

      PAGE 2️⃣ 8️⃣

Wani irin shiru ne ya ratsa tsakar gidan, an rasa wanda zai iya buɗe bakinsa ya furta ko wacce irin kalma, daga inda suke suna jin yanda Salmah take kuka, kamar wadda aka turo kuma ta dawo wajen, cameran wayarta ta shiga, cikin nutsuwa tayi wa jakar video, sannan ta fito da kuɗin, sosai videon ya yi kyau, ɗaki ta koma ta haɗa videon da hoton Aunty Zahra, a take tayi posting a watsapp, ta na daɗe wa batayi status ba, amman duk sanda ta yi sosai ake buɗewa dan tana da contact masu yawa, ganin waɗan da suka gani sun fara mata typing ne ya sa ta kashe datar ta ajiye wayar.

Ajiyar zuciya ta sauke dan tasan Big Sister na fushi da ita, sai dai ko abin da ya fi haka ne zata aikata, dan haka bata jin danasani akan abin da ta aikata, tana cikin ɗaki ta ji sunawa Mahmah sallama zasu tafi ɗan ƙaramin tsaki ta yi cike da jin haushinsu.

Kafin kace me zancen kuɗin auren Zahra ya je har inda ba'a yi tunani ba, a ranar maƙota suka fara shigowa, da sunan Allah ya sanya alkhairi sai dai ba haka bane a ransu, don son tabbatar da gaskiyar maganar ne, ita kuwa Salmah ta ajiye kujera a tsakar gidan ta zauna, duk wanda yazo, zai ga jakar kuɗin a gabanta, ƙarshe Mahmah ɗaki ta tafi, dan gani take kai tsaye duk abin da Salmah ta ke, saboda ita take yinsa...


★★★

Da ƙyar ya bar ƙofar gidan Inna,duk da cewa ya fita daga cikin gidan, amman haka ya ke ji kamar ya bar zuciyarsa a ciki, gangar jikinsa ce kawai a tare da shi, wani irin murmushi ne kwance a kan fuskarsa, wanda a da abu ne mai matuƙar wahala, amma yanzu baya masa wahala.

Bayan ya shiga cikin motarsa, jingina bayansa ya yi da kujera, lumshe idonsa ya yi, sannan ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya furta.

"Finally!"

Kunna motar ya yi, kai tsaye gidan Ammie ya nufa, dan ya san Sameer ya na can ya na jiransa, dan da shi aka kai kuɗin auren, yau baya buƙatar ya zauna shi kaɗai, yana da abubuwa da yawa, da yake so sun tattauna, mussamman ga shi da ya fi kowa sanin, tsawon lokacin da ya ɗauka ya na jiran wannan ranar, bayan an buɗe masa get, cikin gidan ya shiga ya yi parking, cikin nutsuwa ya fito ya nufi part ɗin sa.

"Assalamu alaikum Dude"

 Sameer ya gna zaune a falo yana danna wayarsa, jin sallamar Zay'd ne ya sa shi ɗago kansa.

"Wa alaikum salam, Mr groom" ya amsa masa cike da murmushi a fuskarsa.

Tsayawa ya yi ya na kallonsa, sai kuma ya yi dariya "kar mu fara haka da kai tun yanzu Sameer" miƙewa ya yi suka yi musabaha tare da ɗan rungumar juna.

"Once again congratulations Best friend ɗin Besty!"

Wani irin murmushi ne ya suɓuce masa.

"Muje part ɗin Ammie" ya ce ya na juyawa, can suka nufa suna magana.

Tana zaune a parlow ta na kallon shirin wasan hausa, ta na jin sallamarsu ta ɗago ta kallesu, fuskarta cike da wani irin farin ciki da ya kasa barin fuskar ta.

"Babban mutum"

Ƙarasawa ya yi wajenta, rage tsayinsa ya yi ya rungumeta sosai.

"Ammie!"

Bayansa ta shafa cikin farin ciki, kamar ba ta san murnar me ya ke ba ta ce "me ya saka ɗan Ammie farin ciki haka?"

Ɗago kansa ya yi ya na murmushi, idanuwansa cike da wani irin farin ciki.

"Ammie finally burina zai cika"

Baya ta ja kaɗan tana kallonsa.

"Wane buri?"

Hannayenta ya kamo duka biyun ya riƙo.

"Ammie na sameta, Ammie na jirata tsawon lokaci, Ammiee.. zan aureta zata zama matata Ammie"

Cikin mamaki ta buɗe bakinta tana kallonsa, bata taɓa tunanin Zay'd zai iya zama ya na mata wannan maganar ba.

"Ya rabb Zay'd"

Sake rungumar ƙafarta ya yi.

"Fatima Zahrah Ammie"

Shiru tayi, tana kallonsa, kamar ta na son tabbatar da abin da take zargi.

"Kenan ita kayiwa takwara da Princess"

Gyaɗa kansa ya yi cike da jin daɗi.

"Yes Ammie my besty!"

Sakin baki ta yi tana kallonsa, dan ta kasa ce masa komai, lissafin shekarun Teemah ta tafi, da kuma yanzu da aka saka ranar auren.

"Ammie bansan ta ya zan bayyana miki abin da nake ji ba"

"Ba sai ka bayyana min ba, fuskarka ta bayyana min komai, sannu Zay'd"

Dariya suka yi gaba ɗaya.

A dai-dai lokacin ne aka sake buɗe ƙofar parlown, Teemah ta shigo Ya khaleel a bayanta, magana suke cikin nishaɗi, suna ganin Zay'd suka tsaya.

"Wa nake gani kamar me girma ango?" Teemah ta faɗa tana nuna sa da yatsa. Dariya Khaleel ya yi "shiɗin ne da kansa, wanene idan ba shi ba"

Zay'd girgiza kansa ya yi yana murmushi.

Da gudu Teemah ta ƙaraso ta faɗa jikinsa. "Yah congratulations!" Shima Khaleel zuwa ya yi ta bayansa "Congratulations Oga, finally tuzurin Ammie zai yi aure.

"Thank you guy's"

Teemah zame jikinta ta yi, ta zauna tana kallonsa da wani irin murmushi a fuskarta ta ce " wayyo daɗi kasheni nima za'ayi biki a gidanmu" duk dariya suka yi saboda yanda ta yi maganar. Khaleel ma gyara zamansa ya yi ya ce.

"Ni dai babban yaya muna da roƙo dan Allah" ya yi maganar ya na haɗe hannayensa.

Kallonsa Zay'd ya yi ya ce "na me?"

Teemah ce ta yi saurin shiga maganar "dan Allah Yahh muna son ganin amaryarmu, ba zamu iya jira har ta zo nan ba pleaseee!"

Dariya ya yi cike da jin daɗin yanda ya ga ƙannan nasa suna farin ciki ya ce "really?"

"Yes Yahh, muna son ganin wadda ta yi nasarar mallake zuciyar babban yaya"

Khaleel kuma ya ce "we want to know the woman who finally managed to make our serious CEO smile like this"

Dariya Sameer ya fashe da ita "lallai yaran nan"

"Ayya Yah Sameer, nasan kai kasan matar ai, dan haka dole mu ma mu ganta"

"Ni ma ina tare da ita, muna son ganinta"

Zay'd ƙara jingina ya yi da jikin Ammie "shi kenan zaku ganta"

Cike da zaƙuwa Teemah ta ce "yaushe?"

"Soon" ya bata amsa.

"A'a Oga ba soon ba, ka bamu date kawai"

Ammie ce ta kallesu cike da wani irin farin ciki ganin, yanda farin ciki ya bayyana a fuskokin yaran nata.

"Ku bar min yaro haka, yanzu abin da ya kamata mu maida hankali shine shirin biki, dan babu lokaci duka 4weeks ne"

"Ammie ina son bikin nan ya zama na musamman" ya faɗa yana kwaɓe mata fuska.

"Baka da matsala Babban mutum"

Khaleel ya gyaɗa kansa "then we need a profer wedding committee" Sameer ne ya ɗaga hannunsa ya ce "i'm in"

Teemah ma hannunta ta ɗaga "Ni ma, amman gaskiya nafison ɓangaren amarya"

"Princess bana son a takura mata fa"  

Dariya suka fashe da ita, Sameer da Khaleel, ita dai Ammie mamakin irin son da ta fahimci ya na wa yarinyar ta ke, wadda itama a take ta ji tana sonta, dan ita mace ce me son duk abin da yaranta suke so, muddin bai kauce hanya ba.

A lokacin suka fara tattauna yadda zasu gudanar da bikin, ba ƙaramin biki suke shiryawa ba, sosai suka fara shirin cikin tsari, ga kuma event da suka shirya daban-daban, a take suka fara lissafin abubuwan da za'a yi, wuraren da za'ayi, gayyatar ƴan uwa da abokan arziƙi, da sauran shirye-shiryen da suka dace.

Sai da suka gama ta kalli Teemah "Princess muna buƙatar yin tafiya" 

Da sauri ta juyo wajenta "ina Ammie?"

"Dubai, zamu je haɗa kayan lefe"

Wani irin ihu murna tayi dan ta na son yawo "Dubai? Ammie wayyo Allah na can't wait"

Sameer ya yi dariya "Ammie da alama kin manta da ango, har kin tsayar da inda za'a haɗa lefe"

Kallonsa Ammie ta yi "Sameer ba mu da lokaci, dole muyi komai kafin lokaci ya ƙure mana"

Murmushi Zay'd ya yi "Ammie idan kuna buƙatar abu, just let me know"

Basu ta shi ba, har sai da suka gama shirya yanda tafiya Dubai zata kasance, sosai su ka gama tsara duk abin da ya ce.

Shi dai ya na zaune ya na kallonsu, wani irin nishaɗi na ratsa zuciyarsa, shekaru ashirin ya ɗauka ya na riƙe da buri a cikin zuciyarsa, yau kuma gashi ya na gab da cika, kansa ya ɗaga ya kalli sama a hankali ya furta.

"Alhamdullah"

★★★
*Bayan sati biyu*

Tsawon sati biyu kenan da saka lokacin aurensu, tun da ga wannan lokacin ta shiga cikin wata iriyar damuwa, kullum cikin tunani take, sosai take zama tayi zurfi a cikin tunanin da take ciki, a gefe ɗaya kuma, Mahmah da ƴaƴanta nata shirye shiryen biki cikin farin ciki, kowa da irin abin da yake son ayi, haka kuma kowa da irin shawarar da yake bayarwa, bata iya cewa komai koda sun sakota a ciki sai dai kallo.

Bata san adadin sau nawa ta furta bata son auren nan ba, amma kamar babu wanda ya ke fahimtar abin da take cewa, har ta gaji da faɗa ta koma yin shiru kawai.

Duk da irin damuwar da take ciki haka take wanke ƙafa taje Zay'd Signature, amman bata samunsa, sau uku tana zuwa, kuma basu haɗu ba, ƙarshe manager ya yi mata alƙawarin da zarar ya dawo zai kira ta.

Tana zaune a cikin ɗakinta ta rafka tagumi, sosai tayi nisa a cikin tunani kamar yanda ta saba, kamar daga sama taji wayarta na ringing, daga inda take ta saka hannu ta ɗakko tana duba me kiran, ganin Manager ne, ya sa ta ɗaga wa da sauri.

"Hello barka da yamma Sir"

"Barka Zahra, fatan kina lafiya"

"Alhamdullah"

"Ma sha Allah, daman oga yau ya shigo, zai iya fita a kowane lokaci, idan kina da lokaci ki shigo yanzu"

Da sauri ta tashi tsaye "Ganin zuwa yanzu" katse wayar ta yi, abaya baƙa ta ɗora akan kayan jikinta, sannan ta yi rolling da mayafinta, gaban mudubi ta tsaya, sosai fuskarta ta yi fayau, kamar ta mara lafiya, sai haske da ta ƙara, turare ta fesa a jikinta sannan ta fice ba tare da ta sanarwa da kowa ba, dan bata buƙatar tambaya, a jikinta kuma ta na jin wani irin dan wannan ce fitar ta ta farko ba tare da ta sanar da Mahmah ba.

Kai tsaye da ta je office ɗin manager ta nufa, ba tayi knocking, sai ƙofar da ta tura ta shiga da sallama a bakinta, gaba ɗaya idonta ya rufe hakan ya sa bata kula da mutumin da yake a tsaye ba ya bata baya, ba tare da ɓata lokaci ba ta jefa masa tambaya.

"Ya na ina Sir?"

Jin ya yi mata shiru har lokacin bai juyo ba, sai ta ƙara tambayarsa, jin shiru ne ya sa ta matsa kaɗan kusa da shi, ta na mamakin dalilin da ya sa ya yi mata shiru, ta na tafiya tana duba wayarta da take ta faman ringing, har ta matso daf da shi bata kula ba.

A lokacin ne ya juyo, jin takunta a dab da shi, itama a lokacin ta ɗago da ga kan wayarta, a take idanunta ya sauka a cikin nasa da ya zuba mata su baya ko ƙiftawa, kasa ɗauke idanunta ta yi akan fuskarsa, duk da yanda zuciyarta take bugawa da ƙarfi, ga mamaki ƙarara akan fuskarta.

Shi kam ya na tsaye ya na kallonta babu alamar mamaki akan fuskarsa, sai wani irin murmushi da ya ke jifanta da shi.

"Besty"

Ya kirata cikin wata iriyar sassanyar murya.

Buɗe bakinta ta yi amman ta kasa ce masa komai, ta yi tsammanin manager za ta tarar, ba shi ba, ta daɗe ta na shirya kalaman da za ta yi masa, ta maimaita su a zuciyarta bata san sau nawa ba, amman yanzu ga shi a gabanta, sai dai duk kalaman sun ɓace kamar basu taɓa wanzuwa ba.

Matsawa ya ƙarayi kusa da ita, baya ta ja jin jikinta ya haɗe da bangon yasa ta runtse idonta.

"Look at me Besty"

A hankali ta ɗago idanunta, suka sake haɗuwa da nasa, kwaɓe masa fuska ta yi.

Murmushi ya yi mata.

"Duk naji saƙonki, ba za ki auri yaro ba ko?"

Kai tsaye eh ta ke son ta furta masa amma kamar an rufe mata baki.

"Na yi kewarki Besty!"

Zuciyarta ce ta yi wani irin motsi, dan kai tsaye kalmar ta shige ta.

"Wallahi Besty i missed the the old day's, the old us, na yi kewar hirarki, dariyarki, murmushinki, yadda kike yawan ce Muhan ka dame ni ka rabu dani mana, har da yanda kike min shiru idan na ɓata miki rai"

Dariya ya yi wadda ta ƙawata fuskarsa.

"Wallahi har fushinki na yi kewarsa"

Ba ta san lokacin da murmushi ya bayyana a kam fuskarta ta ba, shima ya gani cikin farin cikin ganin murmushi a kan fuskarta ya ce.

"Wannan ita ce Falmata ta"

Da sauri ta dawo hayyacinta, ta ɗauke murmushin dake fuskarta, ta ce.

"Ba na so"

"Ni kuma ina so" ya bata amsa har lokacin da murmushi a fuskarsa.

"Na ji daɗin ganinki daman ina ta son mu tattauna maganar biki, me kike buƙata?"

Da ga jin abin da ya ce, idonta ya cika da hawaye.

"Muhan"

"Yes Besty"

Magana ta fara ƙoƙarin yi masa, muryarta ta fara rawa, ganin irin kallon da yake mata.

"Ka..san..dai.."

Murmushi ya yi ganin duk yanda ta daburce.

"Na san me?"

"Dan Allah ka soke auren nan, ba na sonka, ta ya za'a dinga nunaka ace kaine mijina, kowa haka zai ce na auri yaro fa, wataƙila ma na girme ka, wannan abin kunya ne fa, sannan..."

Shiru ta yi ta kasa ci gaba da maganar, ganin irin kallon da yake bin ta da shi, tazarar dake tsakaninsu ya ƙara ragewa, baifi taku biyu ya rage ya haɗe jikinsa da na ta ba ya dakata, a hankali jikinta ya fara rawa, saboda kusancin da suka samu ya yi yawa sosai, har ta na jin ɗumin numfashinsa a saman fuskarta, hannayenta ta cure waje ɗaya ta fara juya zoben hannunta da ƙarfi.

Kallon abin da take ya yi, sannan ya kalli duka tsayinta a gabansa, duk da ita ɗin doguwa ce, amman bata ƙarasa kaiwa ƙirjinsa ba, wannan shegen son girman da ta ke da shi, ita kaɗai take ganin abinta, amman duk wanda ya gansu, zai yi tunanin ya bata shekaru sosai da sosai, dan ita dai shekarunta a baki suke, ba'a jikinta ba.

"Me kika ce maimaita" 

Bakinta ne ya fara rawa, ta rasa ta inda zata fara, sun kuyowa ya yi daidai fuskarta, ya sa ka hannayensa ya saka ta a tsakiya, gaba ɗaya ya ware girman idonsa a kanta, da idonsa ya fara ladabtar da ita, ba ya son raini, ba kuma zai fara so a kanta ba, a hankali ya ƙara matsar da fuskarsa dab da tata.

"Ka yi haƙuri dan Allah" ta yi maganar kamar an fizgota daga bakinta, jikinta har lokacin rawa ya ke.

" Ya za ma na farko na ƙarshe, kada na ƙarajin magana makamanciyar wannan a bakinki, idan ba haka ba zan baki mamaki wallahi, kinji abin da nace miki"

Kanta ta gyaɗa masa, hawaye na zubo mata cike da takaicin yanda ta kasa taɓuka komai.

Hannayensa ya janye, sannan shima ya ja da baya.

"Kiyi list na duk abin da kike buƙata ki turamin, zaƙi baƙi yau da daddare, wuce na mayar da ke gida"

Babu musu ta yi gaba da sauri kamar mai jiran umarninsa....

FULANI
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol