Free chapter · Read without an account
Riya Chap 9
by Quenneriya · Riya
Sakk ya tsaya ganin abinda ke faruwa..
Cikin bakin rai yace.. meye haka !!!!
Riya tayi firi firi da ido yayin da Sa’adatu je neman agajin da har yanzun idonta da yaji a ciki … sai lokacin Abban yayi hanzarin debo ruwa a cikin wani katon kwano ya kwarawa sa’adatu a fuskar … Saida yayi saw uku sanan ta fara ganin … Idon nan nayi jajirr.. gashi dama tanada ido sosai so sai ya kara futowa, ..
har lokacin Riya na tsaye zuciyar sai zafi take da kunci dan taso ta mata abinda yayi haka..
dama kwana biyu bata yi fada bah …
… .. Naja’atu ce ke fadawa Abban nasu duk abinda ya faru…Tana gamawa sa’adatu ta karbe da cewa ni ba hana mata tuwon nayi bah gani nayi ga yan uwanta nan suma yunwar suke ji shiyasa nace zan zuba baki daya…
Abba yace naji … kowa ya wace min sanan daga rana irin ta yau kar na kuma ganin kinyi kinyi fada da ita… yace yana kwallan Riya rai bace…
Riya ta kasa Jurewa kaway ta fashe da kuka irin mai tahowa tun daga kasan zuciya… ta huce dakinta….
tun daga wanan ranar kuwa Sa’adatu najin tsoran fada da Riya dan bayan yajin data wasa mata harda uban duka tasha sanan hannun Riya zafi ne dashi kar bah hanun mace bah …
Mallan abdul koh sai takurawa Riya yake dan da maganar soyeya tun tana kwacewa har itama tazo ta fara biye mishi…
Saboda yana kashe mata zuciya da kalamai masu sanyi and sai kuma yawan kyautata mata da yake ..
kwatata Riya yanzun bata fida kudi gurin sayan break a makaranta shi ke saya mata kumi…
wani lokaci har yayi mata sayayar kayan makulashe ta tafi dasu gida duk da bata don haka…
Duk abinda suka a cikin makarantar mallan baba bai sani bah … Saida aka samu wani
munafikin yaje ya laburtamishi
da fari be yarda bah saida
watarana …
Bayan an sawka daga makaranta Mallan baba na tsaye bakin banban office din makarantar dan so yake ya fara sa musu ido sosai duk da cewa yasan Abdul dan uwanshi ne ba zaiyi abinda be kamata…
cen ya hango su … Riya ce tsaya tana Rike da litatafen Abdul wanda yake gaya musu karatu dasu…. Tana murmushi cikin chawki tace..
yanzu ka korar min da kawayena da an tashi zasuyi tafiyar sun dena tsayamin mu tafi tare
Ya dan kwaleta yace toh bah gani bah har gida zan rakaki.. Ya karasa fadi cikin cool voice dinshi..
A’A nidai inda abban mu ya ganin wlh zai iya karyamin kafa da hanun … ungo litatafen nan Bari naje…
ta mika mishi litatafen zata huce yace….
zanyi missing nake Rie ..Tayi murmushi dan tana jin dadin sunan da yake kiranta dashi …
Tace insha’Allah sai ran Asabar dan alhamis da juma’a bah makaranta….
ya mara murmushi tayi gaba har ta huce aji buyu sai taji yace …
Rieeeeee ya dan ja sunan ..
ta juyo sanan ya kara mata murmuchi ya mata alamu da hanunshi zeyi missing nata , ya kuma mata bye bye da hanun .. sanan ya huce bangaran dakunan su!!!
Dik wanan abun daya faru akan idon Mallan baba yaji zuciyar shi ta motsa !!
cikin wani irin bacin rai yace !! ah makarantar nan ?? Kuma Abdul ???
Innalilahi ..
yasakawa ranshi cewa gobe insha’Allah zai kira Riya ya tambayeta dan yasan yarinyar bazatayi karya bah inda bah yanzu ta fara bah … because in yace ya tambayi Abdul zai batawa kanshi lokaci….
Riya na zuwa gida tayi wanka , Tayi sallah sanan sukaci abinci ita da kaninta da duk jimawa da zatayi kan hanya sai sun jirata sanan suce tare…
suna zawne cikin daki ita da kaninta suna karatu dan Boko dan next week za’su komai Makaranta kuma final months ne zasuyi karatun karshe na shekarar daganan sai bayan 3 month zasu dawo….
Ta sakawa ranta insha’Allah zatayi kokari ta huce ajin nan dan kar ta maimaita tunda ah fari ta saka wasa . Gashi kuma batada maki sosai..
duk ta damu ..
sai yanzun take dana sanin beyewa kawayan ta da sukayi ta shirme bayan dayawa daga cikin su suna karatu itace daii sai ah hankali..
da Juma’a tazo koh har ala ala take dare yayi gari ya waye, ta tafi makaranta taga sanyi ida niyanta …
ah lokacin Riya na fama da ciyon soyeya Irin First love ❤️ dinan na kuruciya ..
Mallan Abdul sawrayinta na fari kuma shine wanda ta fara jin soyeyar shi a ranta ..
da suka zo kwanciya sa’adatu tasu ja Riya suyi koda fadan baki be amma worning din da Roya ta mata sai ya fado mata ah rai tana tsoran suyi fada ta kuma ilatata da wa’annan yan iska hanun nata….
Washe gari tana zuwa makaranta koh shiga ajin su bata yiba taga wani dan sawrayi yace mata mallan baba na kiranta ah office dinshi
koh kadan Riya bata kawo wani abu a ranta bah akan maganar Abdul ce za’a mata !!
tana shiga office din tace …
ASSALLAMU ALAIKUM …
mallan ya Amsa Sallamarta yace zawna !!
Ta zawna akan kafet din dake malale ah office din ga sanyin AC ..
Ta kuma kara gaisheshi sana tayi shuru tana jiran abinda zai fada…
Mallan yadan nisa yace … Lariyatu ya kira ainahin sunanta, sanan tace na’am
yace… duk abinda zan tambayarki ki fadamin inda bah kaha bah kinji nace wallahi koh toh zan kira Abban ki na sanar dashi komi .
Riya ta dan tsorata hawaye tuni sun fara malalowa daga idon ta dan ta kware a kuka duk cewa ta fara gane bayanin mallan idan ya dosa
ya kuma kwallan yace …
meye tsakanin ki da Abdul…