Free chapter · Read without an account
BABI NA TALATIN DA HUƊU
by Zainab · Zaren Rayuwar Mu
Zaren Rayuwar Mu
TUN RANAR da nayi wannan outburst Zaid ya dena barin se na kira shi tukuna yake tahowa cin abinci. Yana zuwa da kanshi without me calling him or trying before he eats. Amma kuma magana bata ƙara haɗa mu ba tun ranar. Baya min magana nima bana mishi se de idan ya gama cin abinci yana cewa ‘Thank you.’ Kaina na sunkuye bana kallon shi a duk lokacin da yake godiyar shi. Ɗakin shi kuma na kan shiga na duba abinda be yi ba na mishi duk da shi kam komai yana iya yi da kanshi baya jira a mishi wani abu. Yaji sauƙi sosai amma har yanzu be fara zuwa offshore ba. Yaya Hauwa bata dawo gidanmu ba kuma ina tsammanin ta taho taga yadda Zaid yake a cikin gidanshi. Nasan idan taga akasarin yadda take tunani ita da kanta zata faɗa wa Abban su duk abinda ya faru a gidanmu wayasani ko su sa a sake ni.
Yau da safe Zaid ya fita ni kuma yau off nake bana fita aiki. Na jima ina bacci kafin na tashi. Haka kawai nake da ra'ayin yin masa da miyar taushe yau. Kasuwa na tafi na siyo fresh kayan miya da duk abinda nake buƙata.
Cikin blender ta nayi blending shinkafar masa na haɗa ta na aje domin ta tashi. Shinkafar bata tashi ba se wuraren ƙarfe huɗu ina ta tunanin dawowar Zaid kar ya dawo ba'a gama abinci ba.
Bayan na gama komai na haɗa masa nasa a food flask masu kyau ban ma taɓa amfani dasu ba nayi wanka nasa doguwar riga lace ɗinkin ta daidai da jikina ni bana so kaya su min yawa ko kaɗan nafi so a min daidai da jikina kuma ba irin wanda ya matse ni ba. Ɗankwali na na ɗaura na fidda sumar gashina abaya kamar yadda nake. Kwalli nasa a idanuna nasa janbakin nan me shining a lips. Ban shafa powder ba ina ganin yadda fuska ta ke shining na Vaseline nama fi son ta haka tayi min kyau yau. Siraran high heels ɗina na saka na ɗauko waya ta and I took a few pictures of myself ina ta kallon kaina.
Shigowar mota naji a cikin gida na tashi na leƙa ta window Zaid ne ya dawo. Ajiyar zuciya na sauke yau ni nake so nayi serving nashi.
Fitowa daga ɗakina nayi ina ta jiran shigowar shi se gashi ya shigo.
Cikin sanyin murya nace “Welcome home Zaid”
Kallona ya fara yi tukun ya amsa “Thank you”
Hannun shi na riƙe muka wuce ɗakin shi a tare har muka kai be cire ba.
“Bari na haɗa maka ruwan wanka” na faɗi mishi
Tsaye yayi na shiga banɗakin shi na haɗa mishi ruwan wanka. Bayan na gama na fito ya shiga na buɗe wardrobe ɗin shi na ɗauko mishi kayan da ze sa wa. Dama shi manyan kaya basu dame shi ba kuma yanzu dare yayi na ɗauko mishi three quarter da farin vest me short sleeves.
Ina nan ɗakin Zaid ya fito. Akan idanuna ya shirya. Bayan ya gama shiryawa ne nace mishi “Mu tafi dinning yau na dafa maka abinci me dad'i wanda ban taɓa dafawa ba, it's something different”
Zaid be ce komai ba muka fita. Ina jin silence dake tsakaninmu da kuma rashin jituwar da muke amma ina so wannan gap ya rufe gabaɗaya. Naga idan ban yi da kyau ba haka zamu dinga zama da Zaid kamar ba ma'aurata ba.
Nace ya zauna zanyi serving nashi, babu musu ya zauna.
Food flask na buɗe ƙamshin masa yana fitowa na buɗe flask na miya. Masa uku nasa mishi nasa miya a ƙaramin bowl. Homemade juice da nayi na zuba mishi a glass cup. Koda na ɗago idanuna Zaid has this amusing look yana kallon abincin da nayi serving mishi.
Folding hannuwan shi yayi a kirjin shi kallo ya dawo kaina.
“Menene?”
Murmushi yayi, tun lokacin da na faɗa mishi gaskiya ban ƙara ganin fuskar shi haka ba a tare dani se yau. Murmushi nima na mishi ina kallon shi wani iri.
“Ke kika yi da kanki?” Zaid ya tambaya yana kallona.
Gyaɗa mishi kai nayi ina kallon shi. Ajiyar zuciya ya sauke ya sake hannuwan shi da yayi folding a kirjin shi.
“Bana cin masa, Hadiza” ya faɗa min yana kallona se kuma ya kalla masa.
Cikin mamaki nace “Baka ci?”
Gyaɗa kai yayi. Shiru nayi for some seconds se nayi murmushi nace “Me zan sake dafa maka to?”
“A'a , ba se kinyi wani abinci ba. Kar ki wahalar da kanki”
“A'a ni nace zanyi, ai da ba zan iya ba, ba zan ce zanyi ba"
Girgiza kai yayi. “Zan sha tea na kwanta dare yayi”
“Bari na dafa maka ruwan to”
“Ba se kin wahalar da kanki ba”
Na fara tafiya zuwa kitchen nace “Waya ce wahalar da kaina zanyi?! Yanzu zan dafa maka ruwan”
A kitchen na ɗaura ruwa nasa Lipton da fresh ginger da cardamom da kunne ɗaya na yaji. Su na cikin dahuwa na fara gasa mishi bread. Bayan ruwan sun dahu na zuba a cikin ƙaramin flask nasa gasashshen bread a cikin plate na tangaran na dawowa Zaid dasu. A gaban shi na ajiye abincin da na kawo mishi naje zan haɗa mishi tea yace “Don't worry about that”
Kallon shi nayi se yayi saurin riƙe flask ɗin dole na zauna.
“Ya akayi baka cin masa? Na ɗauka nayi wani babban ƙoƙari yau”
Murmushi naga yayi “I ate it once and vomited”
“Shiyasa baka ci? Trauman har yanzu be fitar maka ba?”
Shrugging kafaɗa yayi yace “Masan yayi kyau. Thank you for making it”
Murmushi ne akan fuska ta ban ce komai ba na fara cin masar da nayi. Ni fa tunda baya ci wanda ya rage zan sa a cikin fridge ne na dinga microwaving har ta ƙare ba zan yi wasting abinci ba.
“Dama kina cin abinci da hannu?” naji yayi commenting, da kuma na kalle shi ba ni yake kallo ba
Wani murmushi na ƙara yi nace “Yes, of course. Baka taɓa gani ba?”
“Yes. Forgot to say thank you for this” ya nuna cup na tea da plate na toasted bread
Murmushi na Kan fuska ta be gushe ba. Da sauri na tashi na shiga kitchen na wanko hannuna na dawo kar ya tashi ya wucewar shi.
“Saurin me kike yi?” ya faɗa bayan na zauna.
Wata irin kunya naji saboda ban ɗauka hankalin shi na kaina ba.
“Babu komai” na amsa tare da saukar da idanuna a ƙasa kamar wata wacce tayi sabon saurayi yazo gidansu zance tana jin kunyar shi bata gama sabawa dashi ba.
Zaid yasa idanun shi sosai akan Hadiza. Eyelashes ɗinta sun kwanta akan ƙasan idanun ta. Fuskar ta na ɗauke da murmushi me birge duk me kallon ta. Hancin ta dogo ne bayi da girma sosai just medium. Her lips too, she has small lips that are beautifully carved. Fuskar ta se shining take daga gani ko powder bata shafa ba. Hadiza na da duhu kaɗan ba za'a ce tana da baƙi sosai ba. Za'a iya ajiye ta a gefen tsaka-tsaka na launin fata tana da haske amma kaɗan ba sosai ba ko kaɗan. Irin hutun da take ciki ne yasa skin ɗin ta yake da kyau barin ma idan aka kai hannuwan ta a gefen yatsu da maɗauri. Hadiza bata da ƙiba kuma ba za'a ce ta cika zama sirariya ba amma de bata da ƙiba. Her chest is not flat but also not so full se bayan auren nan nata ma chest ɗin ta ya zama half full. She's a beautiful woman, a pretty beautiful woman amma tunanin da Zaid yayi a cikin ranshi kuma ya haɗa da zuciyar ta bata da haske sosai akan irin cin amanar da ta mishi.
Cire idanun shi yayi akanta yana tunanin wani abu akanta. Duk irin wannan haɗuwar da tayi, da irin kyawunta, zuciyar ta bata da kyau kamar siffar ta. Yana tunanin da ace yadda ta gama haɗuwa haka zuciyar ta take a haɗe bata lalace ba, yasan ba wanda ze nuna mishi sa'ar mata.
“You know” Zaid ya fara magana, yasa na ɗago kaina ina kallon shi da son sanin abinda ze faɗa “Al'adar mu na bahaushe, yayi placing mace ta gari a woman that cooks and clean amma ni sam tunanina baya kan wannan abubuwan. Kin san addinin da muke yi be faɗa macen da take goge-goge ko dafa abinci ba, ya faɗa wacce idan ka kalle ta zaka samu natsuwa a cikin ranka. And God told us we're garments for each other. God told us He placed between spouses affection and mercy. A woman that you'll have serenity with, but Hadiza, you lacked all those things that makes a woman wife. Do you know?”
Na faɗa dama ba aikin ba, wanda nake yi domin shi yana appreciating ko ze yi appreciating? Ga abinda Zaid ke faɗa min yana kallona a cikin idanuna a cikin eyeblass ɗina.
“Haka kake gani, Zaid?”
“Hakane Hadiza. Ba haka nake gani ba”
“Yanzu kana nufin duk abubuwan nan da nake saboda na samu yardar ka, inayi a banza ne? Ba fa goge-goge da abinci kawai nake ba. Ina kulawa da kai Zaid. Tare muke yin breathing exercise naka. Meyasa ba zaka duba dalilin da yasa na chanja halaye na ba? Wane irin mutum ne kai Zaid? Wallahi ban sanka ba. Ban sanka ba Zaid. Wannan wane irin riƙo ne? Ina ta baka haƙuri na chanja halaye na wanda basu da kyau a wurin ka amma duk baka gani Zaid? Me kake so nayi? Ka faɗa min duk abinda kake so zan maka. I'm ready to be a garment for you idan kana da matsala kazo min da ita zan rufe ka Zaid. You have affection and mercy for me nima yanzu sune nake da a gare ka. Bana son wani abu ya same ka ina jin tausayin ka duk wani abu wanda ze wahalar da kai bana son shi, Zaid. Ina ƙaunar ka har cikin zuciyata. Yanzu na zama wacce zaka samu natsuwa a wurin ta kuma zan zama wacce kake kallo kaji sanyi a rayuwar ka idan wani abu ya dame ka, Zaid. Ka bani dama mana”
Na tsani kaina da duk irin maganganun da nayi wa Zaid. Kamata yayi nayi zuciya na faffasa komai dake wurin nan har shi na fasawa kai akan ɓacin ran da nake ciki amma kuma ban yi ba saboda ina son aure na, ba aurena kawai nake so ba. Aurena da Zaid nake so saboda nasan ba zan samu wani irin shi ba, kamar shi koda kwatankwacin irin shi ne. Shi na daban ne kuma ze cigaba da zama na daban a ciki mutane.
“Do you even love me anymore, Zaid?”
“I do, Hadiza” yace tare da tashi tsaye “I'll never stop loving you. I love you and it's going to be forever”
Hawayen da nake riƙewa suka samu damar zubowa a idanuna na fara kuka tare da rufe fuska ta da hannuwa na. Zaid tafiyar shi yayi be ce min komai ba be rarrashe ni ba. Wallahi Zaid irin mutanen nan ne masu haƙurin gaske amma idan suka dena haƙuri, mugaye suke zama because Zaid has basically turned into a Villain in my story.