Free chapter · Read without an account
BABI NA TALATIN DA BAKWAI
by Zainab · Zaren Rayuwar Mu
Zaren Rayuwar Mu
LOKACIN DAMANA ne ya fara wucewa. Lokacin agogo yana ɗan jimawa kafin ya wuce. Ƙasa ta fara bushewa leaves na itace busassu sun fara faɗowa. Ana iya jin sanyi-sanyi amma har yanzu be shigo sosai ba se de zafin da ake fama dashi da rana marar misaltawa.
Ahmad ya gama jami'ar Nigeria ta Nsukka daga department na Business Administration da second class upper. Yayi bautar ƙasa a Kano ya dawo Enugu. Anan ya fara cike-ciken neman aiki a waya. Duk wani abu na aiki kama daga federal government da state har na garinsu mahaifan shi Sokoto duk yana cikawa kuma yana tsammanin samu a kodayaushe.
Yana kwance a cikin ɗakin su yana danna wayar shi. Yanzu yayi wata biyar da gama bautar ƙasa yana jiran aiki. Duk da jiran da yake, yana zuwa yana aikin hannu yana samun yan kuɗaɗen shi yana wasu buƙatocin rayuwar shi. Notification ne ya shigo cikin wayar shi daga Gmail. Da sauri ya shiga Gmail ɗin shi. Saƙo ne daga ɗayan aikin da yake cikawa daga Abuja. Da sauri ya tashi daga kwancen da yake murmushi na kan fuskar shi. Cikin ranshi yace Alhamdulillah ya fito da sauri daga ɗakin su zuwa inda mahaifiyar shi ke aikin girki.
“Umma, an turo min saƙo daga Abuja ɗaya daga cikin ayyukan da na cika ina nema”
“Ah” Maryam ta faɗa dauke da murmushi tare da tashi tsaye ta rufe tukunyar miyar ta “Wai da gaske kake Ahmad? Kaii Alhamdulillah. Allah mun gode maka. Yanzu ka samu aikin Ahmad?”
“Ba zan ce ba amma zan tafi Abuja se munyi interview”
“Yanzu idan an gama interview ɗin se menene?”
“Se aga wanda suka ci a basu aikin”
“Allah yasa kana cikin su Ahmad. Allah ya baka sa'a da nasara a rayuwar ka. Kai Alhamdulillah Ahmad. Amma har Abuja? Yayi nisa dayawa”
“Umma kar ki damu tunda an samu abinda ake so”
“Hakane Ahmad. Tunda ga wasu nan shekara da shekaru an gama makaranta amma babu aiki. Mun godewa Allah”
Da murmushi akan fuskar shi yace “To kin gani Umma”
“Amma wani hanzari ba gudu ba, Ahmad. A ina zaka zauna? Kasan yadda Abuja take da tsadar rayuwa”
“In sha Allah Umma ba za'a rasa yadda za'a yi ba”
“To yanzu yaushe zaka tafi?” ta faɗa tare da haɗe hannuwanta wuri ɗaya
“Ranar Monday za'a interview. So zan ɗau hanya cikin ranakun sati”
“To yayi babu matsala Allah ya kai mu ya tsare ku. Idan Daddyn ku ya shigo se ka faɗa mishi”
“In sha Allah zan faɗa mishi”
Se bayan Maghrib mahaifin su ya dawo gida. Suna cin abinci Ahmad yake faɗa mishi labarin aikin.
“Kai ma sha Allah Allah yasa albarka Ahmad. Yanzu yaushe zaka tafi?”
“Cikin ranakun sati nake so. Assabar ko Lahadi”
“Yafi ka tafi ranar Assabar ka ƙara shiryawa chan”
Nodding kai yayi “To a Ina zaka zauna? Kasan de yadda tsadar rayuwa take a Abuja. Ga apartments ɗinnan su ma duk tsada ne dasu”
“Nima wallahi shi nake ta tunanin mishi. Kar kaje yan kuɗaɗen naka duk su tafi akan waɗannan abubuwan” Maryam tace
“Nima shi nake dubawa amma bari na kira wani daga cikinmu da yayi zama nan kafin ya koma Abuja“
“Dan Allah ka kira shi. Allah yasa a dace”
Ɗauko wayar shi yayi yayi kiran da yace. Cikin ikon Allah wanda yayi waya dashi yake faɗa mishi yana da boys quarters Ahmad ya taho duk lokacin da yake so kuma yayi spending time ɗin shi nan babu takurawa.
“To yanzu kaga haka yafi. Ze ga albashin nashi ya tsaya mishi”
“Eh gaskiya haka ne. Rayuwar yanzu tsada ne da ita ba ma ance Abuja ba. Allah ya bada Sa'a“ mahaifin su ya faɗa ya kalla Ahmad “Zan baka number shi se ku yi magana duk ranar da ka ɗauki hanya. Allah yasa a dace”
“Amin Daddy Nagode. Bari na tashi na shiga nayi waya da Baffa”
“Ah! Baka faɗa mishi ba?” mahaifiyyar su ta faɗi
“Yanzu zan faɗi mishi Allah yasa ba bacci yake ba”
“To Allah yasa”
“Amin Umma” Ahmad yace tare da tashi yayi hanyar ɗakin su yana kiran wayar Baffa.
Ɗauka Baffa yayi Ahmad ya zauna a gefen gado. “What's up bro?” Baffa yace
“All good o. How your side?”
“It's not fascinating here o but sha, we thank God”
“Alhamdulillah!”
“Yes, Alhamdulillah. So what's up?”
“You remember I dey look for job up and down for this Nigeria right? I have been invited to Abuja for an interview for the role of an Administrative Officer”
“You are not joking?!” Baffa yace da murna
“Not at all. You heard it right”
Dariya Baffa yayi yace “That's a nice step bro. Congratulations. Allah yasa albarka yasa a samu”
“Amin Amin Nagode Baffa”
“But how you go cope for Abuja now? You know how expensive it is to live in Abuja o”
“Dont worry about that. Daddy has talked to someone living there and I'm welcomed in his house”
Shiru Baffa yayi, chan yace “That's good. Daddy has tried”
“He really tried for me oo. Thank God”
“Na to just ping you say I want 50k for your side oo. Abuja and Abuja job no be small, guy”
Dariya suka yi su biyu “You have no problem, bro. 50k you ask, 100k you go get”
Wata dariya suka ƙara yi su biyu. Baffa yace “You should start looking for the woman you'll want to spend your life with”
“Guy, this is too early o. I go wait make myself comfortable before I keep woman o. I no wan stress myself or any man's daughter”
“Yes, no rush. No listen to these people that'll pressure you to have family just because you get job”
“You understand well well. Because why will I keep a woman I can't maintain? Make i no call wahala upon myself o. Make i jejely make myself comfortable so any woman that comes, no be wahala she go chop but a decent life we'll live”
“I like the way you think o. This one na beautiful mindset you get and you no talk lie o, na true you dey talk”
“I know guy. Make I hang up go pray. The Imam has started” Ahmad ya faɗa da sauri jin har an tadda Sallah Isha a Barrack ɗin su. Da sauri ya katse kiran ya fito.