Free chapter · Read without an account

BABI NA TALATIN DA TAKWAS

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu 

RANAR LAHADI Ahmad ya wuce Abuja. Gidan da mahaifin su yayi magana ze sauka babban gida ne suna da boys quarters inda mazan gidan ke zama. Shima tun kafin ya iso aka gyara mishi ɗaki ɗaya anan ze zauna yayi duk abinda ya kawo shi Abuja kafin ya koma gida. 
Ranar Litinin da safe ya tafi maakaitar da ake nemansu har aka mishi interview. A wurin interview ɗin ne HR na wurin ke tambayar shi abinda yake tsammani a bashi na albashin shi. Shiru yayi kaɗan yana nazari kafin yace “Anything reasonable, I'll accept.” Ƙara tambayar shi tayi akan albashin da yake so amma Ahmad be faɗa ba duk da kuwa yasan idan ya fara aiki aka bashi albashin da be yi tsammani ba yayi ƙanƙanta ze aje musu aikin su ya koma Enugu. Bayan sun gama aka ce za'a neme su. Bayan ya koma gidan da yake zama mahaifin gidan ke tambayar shi ya suka yi se yake faɗa mishi tare da sanar dashi ze koma gida gobe kafin su neme su. Nan take yace mishi ai yanzu gida ne yazo ya bari har ya gama komai tukuna ya koma gida idan sun amshe shi ya shirya ya dawo gidan. Ahmad yayi ta godiya yana jin komai yazo mishi sauki most especially idan an ɗauke shi aikin kuma yana sa ran za'a ɗauke shi aikin. 

Sati ɗaya da interview ɗin su aka turo mishi interview na ɗaukar aiki. Yana gama karanta saƙon ya kira mahaifiyyar su yana faɗa mata. Babu abu na dad'i wanda Maryam bata ji ba lokacin da Ahmad yake faɗa mata an ɗauke shi aiki. Tayi murna sosai tana ta mishi addu'a. Da mahaifin shi ya shigo shima ya amsa wayar suna waya yana mishi addu'ar samun nasara a rayuwa.
Bayan ya gama waya dasu ne ya kira Baffa yana faɗa mishi. 
   “I get a bro wey go stay for Abuja! Congratulations!” Baffa ya faɗa cikin murna. Dariya Ahmad yayi yace “You should finish Law get this opportunity. Do your school of Law here in Abuja o”
  “No be to come Abuja. Can i afford to stay there?”
“Nawa for you ooo. You that'll be making big money for that Law you studied. You don commot from poverty oo”
Dariya Baffa yayi sosai jin abinda Ahmad yake faɗa “I for study corporate Law migrate to the States wey I go get big money”
   “You remember that girl? That Temi woman?”
         “I no fit forget Temi. That girl good”
  “Where she dey now?”
   “That one na rich pikin o. She dey stay for States”
  “Are you guys still in touch?”
“No, It has been long we greet each other”
 “You better look for her. Who knows she go help you go States?” Ahmad ya zolaye Baffa
Dariya Baffa yayi yace “You are crazy Ahmad”
Dariya shima Ahmad yayi yace “I'm kidding. Hope I'll see you home before I start this work for Abuja?”
   “Just tell me when you reach Enugu. I go come”
      “Okay, I'll let you know. Make I sleep guy”
       “Okay later or when you call me after reaching Enugu”

Cikin satin da akayi accepting Ahmad a aikin Federal government na Administrative Officer a Abuja, a satin ya dawo Enugu domin yayi ɗan shirye-shiryen da ze yi ya koma ya fara aiki. 
Washegari Baffa ya dawo gida daga hostel na University of Nigeria, Nsukka. Zama suka yi kamar yadda suke a da chan baya gabaɗayan su daga Daddy, Umma, Ahmad, Baffa har ƙanwar su Farida ana hira. Farida har take faɗa wa Ahmad tana so ya siya mata takalmi sneakers idan aka fara bashi albashi. 
Hirar su suke cikin jin daɗi da haɗin kai na nuclear family. Mahaifin su yace “Bana so na fara maganar aure amma dai kasan yanzu da ka samu aiki yarinya zaka nemo kayi auren ka da ƙananun shekarun ka”
Shiru Ahmad yayi, Baffa yace “Yace bashi da yarinyar da yake gani”
  “Se aje Sokoto a samo mishi yarinya ko yaya?” Mahaifiyyar su ta faɗi 
  “Auren haɗi? A'a zan nemo da kaina”
Dariya suka yi jin abinda Ahmad yace. Farida tace “Ku bari Yaya ya samo Abuja girl tunda yanzu chan ze fara aiki”
  “Kaga ƙanwar ka ta baka shawara” inji mahaifin su
Murmushi Ahmad yayi se anan yake fara tunanin idan ma aure ze yi, wace irin yarinya ze aura Kuma daga wane gari. 
  “No worry yourself. Make yourself comfortable before we start talking about marriage” inji Daddy 
   “Saboda ni se nayi kuɗi tukunna zanyi aure” Baffa ya faɗa 
   “Kuɗi? Wane irin kuɗi? Allah yasa ba kuɗin da se an tsufa ba kake magana, Baffa”
Dariya suka sa. Ahmad yace “Su ne fa yake magana Umma. Kinga ma ki cire rai daga ganin yaran Baffa”
  “Ai be isa ba yana gamawa ya samu aiki first albashin shi ma da shi ze yi aure” Dariya Daddy yayi da Farida jin abinda Mahaifiyyar su tace
   “Kin faɗa dai Umma. Dani da yarinyar wa za'a gane?”
Wata dariya suka ƙara yi suna masu cigaba da hirar su.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol