Free chapter · Read without an account
Page 22
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 22
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Tsayawa Junaid yai cak ya juyo ya kalli Azlan yana mamakin abinda yake nufi da in ya taba ta sai ya karya sa, ya bude baki zai magana Baffa ya daga masa hannu dole yai shiru kawai yana kallon Azlan.
Ruwa Baffa ya umarci Mami data shafa mata a fuska, da sauri Aunty Sarah ta mika ma Mami ruwan shafa mata mami tai amma bata motsa ba cike da tsoro mami ta Kara shafa mata ruwan.
Wani ajiyar zuciya na sauke mai karfi ina jan numfashi na, a hankali na soma bude ido na hawaye ne Mai zafi ya sauko min, in har abinda na gani kuma naji ne gaskia knn Mr Wicked ne baban Mimi.
Lumshe idona nai ina fadin Innanillahi wa innanillaihir raji'un, Mami data zuba mata ido tana kallon ta a hankali ta dora hannun ta akaina tana shafawa, hakan dana ji kawai na fashe da kuka.
Zaro ido Azlan yai yana kallon ta, ta tabbata knn tana da aljanu yarinyar nn kallon baffa yai yace "tsoho ko Malam Sule za'a kirawo ne da alama kanta na motsi."
Harara Baffa ya jefa masa yace "Ka shiga hankalin kafa zaki"
Tabe baki yai yana daga kafadar sa yace "gani nai tana abun masu motsi a ka shine kawai na bada shawarar"
Girgiza kai Baffa yai kallon Aisha yai yace "ina ne gidan ku"
A hankali tace "Hausawa ne Baffa"
Gyada kai yai yace "bara na sa a maida ku gida kinji"
Abie da yake ta juya bracelet din yace "Aisha a ina kuka samu wannan abin hannun."
A tsorace ta dago ta kalle sa sai kuma ta juya ta kalli Batul da ke kwance har lokacin hawaye kawai take, ganin alamun tsoro a tare da ita yasa Baffa cewa "ki kwantar da hankalin ki kinji Aisha ba abinda zamu muku tambayar kawai zaki amsa"
Cikin rawar baki tace "na baban Mimi ne'
Da mamaki sosai Mami tace "baban Mimi kuma? Nidai a iya sanina wannan abin guda biyu ne iri daya na Junaid dana Azlan gashi kuma wannan ma iri daya ne sak alamun na Azlan ne kenn.."
Baffa ne yace "kar ku ruda ta zo kinji jikata'
Sai da ta kalle ni taga idona a rufe yake sannan ta juya ta kalli Mimi dake bacci jikin Azlan sannan ta nufi gurin Baffa tana juyo wa tana kallo na, dafa kanta Baffa yai yace “kamar ya na babban Mimi ba kunce ya rasu ba”
Girgiza kai tai tana hawaye tace "bamu San ko waye baban taba abinda muke dashi Wanda zai nuna mana baban ta wannan bracelet din ne kawai"
A ynxu kuwa kan kowa dake palourn ya rude, cikin bugawar zuciya Azlan yace "kee me kike nufi da baku san waye baban beauty ba"
Daga kai tai tana hawaye tace "bamu san waye baban taba wannan bracelet din ne kawai mallakin baban ta da yake hannun Ya Batul"
Mikewa Baffa yai ya kalli Abie yace "Muhammad zama bai ganmu ba a wannan gabar, gidan su yaran zamu je mu gana da iyayen su, don kaina ya rude kuma."
Shima Abie da ya gama rudewa Jin wannan maganar yace "Baffa muje toh," kallon Aisha yai yace "xamu samu baban ku a gida ynxu"
Daga masa kai tai tana share hawaye, Mika mata waya Baffa yai yace "samun number dinsa na kira sa tukun kar muje masa haka kawai"
Cikin rawar jiki ta karbi wayar tasa ma baffa numbern Abba, dialing numbern Abba yai ringing biyu ya dauka
Sallama Baffa yai cikin muryar sa mai cike da dattako
Daga can bangaren Abba ya amsa yana gaishe sa Jin muryar ta babban mutum.
Cikin dattako Baffa yace "muna tare da su Aisha ne da Batul in ba damuwa muna son zuwa mu hadu in zamu same Ka a gida"
Cikin dan fargaba Abba yace "suna lafia? Ko wani abun sukai"
Murmushi Baffa yai yace "ba abinda sukai magana ce dama muke so muyi akan Mimi"
Da mamaki Abba yace "Mimi kuma?"
Daga kai Baffa yai yace "eh ita shiyasa nace in ba damuwa zamu iya samun ka ynxu"
Abba da yake zaune a gefen Umma yace "in shaa Allah ina gida dama zan fita ne amma zan tsaya na Jira ku"
Murmushi Baffa yai yace "mun gode sosai sai mun iso"
********
Umma da tunda Abba ya fara waya take kallon sa da son Jin karin bayani duk da kuwa wayar a speaker take, kallon ta Abba yai bayan ya ajiye wayar yace "Umman Aisha bari naje na Kira yan uwana su zo kafin su iso duk da ban san me suke so suyi magana akai ba amma ina ji magana ce mai muhimmanci"
Daga kai Umma tai tace "Allah yasa muji alkhairi dai kawai amma ni duk gabana sai faduwa yake Abba"
Murmushi Abba yai yana Jan kumatun ta cike da kauna yace "yaushe Sadiyayye ta ta fara jin tsoro nidai nasan Sadiyayye ta jaruma ce"
Murmushi Umma tai tana juya idon ta tace "har ynxu baka tsufa jika ce fa dakai"
Murmushi yai ya dan dale mata baki yace "kul kika Kara cewa bana tsufa har ynxu jina nake garau, ko so kike na auro yar yarinya ce na tabbatar Miki da garau nake"
Harara Umma ta sakar masa tana turo baki, dariya Abba yai yace "Sadiyayye ta uwargida kuma amarya har abada Insha Allah, Allah yai miki albarka Matata"
Murmushi Umma tai tace "Ameen Mijinaa."
Sai da ya tabbatar hankalin ta ya kwanta sannan ya fita don zuwa tahowa da su kawu Nasiru
*********
Baffa ne yace “Muhammad sai mu tafi ko da Mustapha da Junaid sai Azlan ku matan ku zauna”
Mummy da take so ayi komai a gabanta tace “Baffa don Allah muma muje tare mana ayi komai muna gun”
Hade rai yai yace “banyi ra'a yi ba ku zauna mazan ne kawai zasu je” mikewa yai ya kalle ni da har ynxu nake kwance sai dai na dena hawayen amma idona a rufe yake.
A hankali cikin nutsuwa baffa yace "taso kinji jikata"
Ban masa musu ba na mike a hankali don dama na gaji na rasa yadda zanyi ne kawai.
Ko bangaren da Mimi take ban kalla ba na fita daga palourn motar Junaid muka shiga nida Aisha sai uncle Mustapha a gaba, Azlan kuma ya dauki Baffa da Abie sai Mimi dake kwance a jikin Baffa a back sit.
Tafiyar minti 30 ce ta kawo mu kofar gidan mu, muna zuwa na bude kofar na fita na shige gidan a soron gidan na hadu dasu Kawu Nasiru a gaggauce na gaishe su na shige cikin gidan, ban hadu da Umma ba haka yasa na shige dakin mu kawai na kwanta akan katifa ina rufe idona.....
Aisha ce data shigo ganin su Kawu Nasiru yasa ta fada musu bakin suna jiran su a waje, fitowa sukai sai dai Suma tozali da sukai da su Junaid ba karamin daga musu hankali yai ba musamman ganin mimi kwance a jikin Azlan.
Khalil da yazo wuce wa Abba yasa shi shiga da Mimi cikin gidan gabansa yana faduwa da alama magana ce mai muhimmanci za'a yi yau dinnan.
Babban gida suka nufa gaba daya don gidan Abba ba gurin da za'a sauke su, a Palourn baki suka zauna bayan an gaisa Baffa yai gyaran murya yace "abinda yasa muka zo nan sbd wani Abu daya shige mana dubu gaba dayan mu, na farko kamannin da Mimi take kama da jikokina kamar an tsaga Kara na biyu kuma abin hannun jikana da ya bata kusan shekara biyar knn sai gashi yau a jakar Batul, sannan kuma Aisha tace abin hannun na baban Mimi ne toh abin ya daure mana kai sosai shiyasa nake son sanin shin waye *baban Mimi?*"
Sunkuyar da kai Abba yai hawaye na taruwa a idonsa, Kawu Nasiru ne ya gyara zama yace "gaskia ba'a san waye baban ta ba don fyade akai ma Yarinyar mu ta haife ta"
Salati Baffa yai yace "subhanallah amma naga karamar yarinya ce Batul din har yaushe ta haifi Mimi"
Azlan kuwa sunkuyar da kansa kawai yai gaban sa yana faduwa jin ta hanyar da aka samu Yarinyar sa lallai da zaiyi ido hudu da ko waye sai yaci ubansaa
Murmushi wanda yafi kuka ciwo Abba yai yace *"BA BATUL BACE MAHAIFIYAR MIMI"*
***