Free chapter · Read without an account
Chapter 9: The Unwanted Companion
Washegari da safe, hada hada ake a gidan, masu aiki na ta fama da girkin da Mammy ta ce su girka wanda zasu kai ma Hajiya, while Rahama tana can tana fama ita ma
Da yamma ne jirginsu zai tashi zuwa Lagos, shine zasu gidan da safe bcos su gaida Hajiya and Daddy ma yana son ya tattauna da Rahama da Rayyan game da workshop ɗin da za su halarta da kuma yadda za su yi aiki tare a harkar kasuwanci idan suka je can
“Rahama kin gama shirya komai?” Mammy ta tambaya tana kallon ɗiyarta da ta fito daga ɗakinta da handbag a hannu
“Eh Mammy, komai ya kammalu, sai dai idan akwai wani abu da kika ɓoye min a cikin kayana shine kawai zan manta”
Mammy ta yi murmushi “Wane abu kuma zan ɓoye miki?”
“Ban sani ba fa, amma sai dai idan ba Mammy na ba, don komai ma kina iya yi” Rahama ta amsa da ɗan murmushi
“Ya salam, pls ki daina wannan shirmen naki, ki je ki duba ko kin ɗauki duk abin da kike buƙata”
“Toh Mammy”
Ta juya ta koma ɗakinta, ta sake duba jakar da ta shirya, sannan ta fito, Baba ya riga ya shirya, yana jiran su a falo
“Kun gama ne?” ya tambaya
“Mun gama Baba” Rahama ta amsa
Bayan sun tabbatar da cewa an ɗauki kayan da za su tafi da shi suka shiga mota, masu aikin Mammy suka Kai warmers din cikin booth
Bayan da suka isa gidan, aka karɓe su cikin fara’a, ma’aikatan gidan suka taimaka wajen sauke abincin da suka zo da shi, yayin da aka yi musu jagora zuwa falo
Daddy da Mommy sosai suka ji dadin zuwansu, sosai aka gaggaisa kamar an jima ba’a ga juna ba, Hajiya tana cikin ɗakinta da ta ji zuwansu ne, sai ta fito
Rahama ta miƙe tsaye da ta gan ta “Hajiya ta”
“Rahama ta” Hajiya ta amsa cikin fara’a
Ta rungume ta a hankali, sannan ta zaunar da ita kusa da ita “Ya hanya? Ya gida?”
“Alhamdulillah Hajiya, komai lafiya”
“Ma shaa Allah, Allah kuma ya sa a yi tafiya lafiya
“Aminn Hajiya ta”
Sai sannan Mammy da Baba suka samu damar gaisheta, nan masu aiki suka kawo musu abin sha, yayin da ake tattaunawa kan tafiyar da workshop ɗin da za su halarta
Daddy ya kalli Rahama
“Pls Rahama, ina so ki maida hankali sosai a wannan workshop ɗin, wannan dama ce mai kyau a gare ki, musamman yanzu da kika gama karatu. Ina so ki koyi abubuwan da za su taimaka miki wajen gina kanki a fannin aiki da kasuwanci”
Rahama ta gyara zama “Toh Daddy, In sha Allah zan maida hankali”
“Good! Ina so ki fahimci cewa workshop ɗin nan ba tafiya ce ta yawon buɗe ido kawai ba, za ku haɗu da mutane daban-daban, ku koyi abubuwa, ku fahimci yadda ake gudanar da business, kuma ku samu damar gina kyakkyawar alaƙar aiki da sauran mutane”
“In sha Allah, Daddy”
Daddy ya juya ya kalli Baba “Na san ka fahimci abin da nake nufi, Ina so Rahama ta fara samun irin wannan exposure tun yanzu. Ta gama karatu, kuma lokaci ya yi da za ta fara fahimtar yadda professional world ɗin yake”
Baba ya gyada kai “Sosai ma, ai shi ya sa na ga wannan workshop ɗin zai amfane ta sosai”
“Exactly. Kuma ina ganin idan ta samu damar yin aiki tare da Rayyan a wasu daga cikin abubuwan da za a tattauna, zai fi mata sauƙi, Rayyan ya daɗe yana cikin wannan fanni, don haka zai iya taimaka mata ta fahimci abubuwan da ba za ta iya koya daga littattafai kaɗai ba”
Rahama dai tayi shiru tana jinsu cikin nutsuwa, tana ƙoƙarin fahimtar irin aikin da ake sa ran za ta yi
Baba ya ɗaga kai yana kallon ƙofar falon, sannan ya sake kallon Daddy
“By the way, ina Rayyan ɗin yake?”
Daddy ya ce “I thought zan haɗa su tun yanzu in yi musu highlighting na abubuwan da suke buƙatar sani kafin su tafi”
Baba ya kalli agogonsa “Kana nufin har yanzu bai fito ba? Dalilin zuwan knn sbd kayi masu bayani”
Daddy ya ɗauki wayarsa “Na aika masa da saƙo tun ɗazu, na gaya masa ina son ganinsa, shi da Rameez, sbd duk suna gida yau, I want us to go through some important things before they leave”
Yana gama magana, sai ga sounds nasu a waje
Bayan ɗan lokaci, Rayyan da Rameez suka shigo
Rahama tana zaune kusa da Mammy, amma tun lokacin da ta ji motsin shigowarsu, ta ɗaga kanta tana kallon ƙofar bcos maganar cousin take tunawa
Rayyan yana shigowa idonsa ya faɗa cikin na Rahama dake kallonsa, wani irin shocked ne dukkansu ya Kama su
Rahama ta buɗe idanunta sosai, tana kallonsa kamar ba ta yarda da abin da take gani ba. A take hoton mutumin da ya ɓata mata rai a airport ya dawo mata a fili. Fuskar da ta yi ƙoƙarin mantawa da ita, muryarsa da ta ji tana mata magana cikin fushi, da waccan rigar fara da ta lalace sbd abincin da ta zubar masa
Dukansu sun dawo mata lokaci guda…. No way! Wannan shi ne mutumin da za ta yi tafiya tare da shi?
Zuciyarta ta fara bugawa da sauri, ta kasa kawar da idanunta daga kansa, tana kallonsa kamar idanunta za su faɗo
Rayyan ma ya gane ta nan take, sai dai shi ba ya yawan nuna abin da yake ji a fuskarsa, ya ɗan tsaya, ya kalleta na wasu sakanni, sannan ya ɗauke idanunsa daga kanta kamar bai taɓa ganin ta ba
Though abin da ke faruwa a zuciyarsa ya sha bamban da yanayin fuskarsa… Her again?
Rameez kuwa ya bi kallon Rayyan, sannan ya lura da yadda Rahama take kallonsa, ya ɗan daure fuska yana ƙoƙarin fahimtar abin da ke faruwa, amma bai ce komai ba
Rayyan ya ƙarasa shiga falon, ya gaishe da mutanen da ke ciki da ladabi
Rameez ma ya gaishe da su, sannan suka zauna
Mammy ta kalli Rayyan da murmushi
“Fatan ka gama shiri ko Rayyan? Domin ga Rahama nan har da box ɗinta ta zo”
Rahama ta juya da sauri tana kallon Mammy, Rahama? Box?
Sai a lokacin ta fahimci cewa ba kawai za su halarci workshop ɗaya ba ne, chap wannan mutumin ne za su yi tafiya tare da shi tun daga nan Abuja har zuwa Lagos
Ta sake kallon Rayyan, wanda ya zauna yana kallon Daddy kamar babu wani abu da ya faru
A ranta ta ce, Tabdijam! Dama wannan ne Rayyan ɗin?
Mammy ta lura da yanayinta “Yaya dai?”
Rahama ta juyo gare ta, ta ɗan matso kusa da ita kamar tana son ta faɗa mata cikin sirri
“Mammy wlh ni ba na son sa, ba zan tafi da shi ba”
Maganar ta fito da ƙarfi fiye da yadda ta yi niyya, kowa ya juya ya kalleta
Rayyan ya ɗaga kansa a hankali ya watsa mata wani dirty look, sannan ya kawar da fuskarsa
Daddy ya ɗan daure fuska “Me ya faru, daughter?”
Rahama ta nuna Rayyan da yatsa
“Daddy, wannan mutumin mugu ne! Mun haɗu ranar da na dawo gari, ya zage ni kamar ba gobe, ya kira ni da dabba, har da cewa zai cire min ido. Yanzu kuma wai shi ne zan yi tafiya tare da shi?”
Da sauri Rameez ya juya ya kalli Rayyan
Rayyan yaki cewa komai
Daddy ya kalli ɗansa da mamaki
“Rayyan yaushe ka zama haka? What is this behaviour?”
Rayyan ya ɗaga kansa “Daddy, ni ban ma taɓa ganin ta ba”
“Laaa!” Rahama ta yi saurin magana “Wai dama manya ma suna karya?”
Ta kalli mutanen da ke falon, sannan ta sake kallon Rayyan “Ni fa ba zan manta ba wlh mutum ya zage ni a airport, har ya ce zai cire min ido, sannan yau ya ce bai taɓa ganina ba.. Kai, Allah ya kyauta toh!”
Kusan kowa ya kasa riƙe dariya bcos yadda tayi sounding
Rameez kuwa ya sunkuyar da kansa, yana ƙoƙarin danne dariyar da ta taso masa, amma da ya sake kallon fuskar Rahama, sai ya fashe da dariya
“Sorry, sorry” ya faɗa yana ƙoƙarin nutsuwa
Rahama ta juya ta kalle shi “Baka yarda bane? Kai ma kana cikin masu irin wannan halin ne Yaya?”
Rameez ya girgiza kansa “Ba komai, sorry”
Although ynx ya fara fahimtar abin da ya faru. Wannan ita ce yarinyar da Rayyan ya ba shi lbrnta bayan sun dawo daga airport, ya tuna yadda ƙaninsa ya yi ta korafi a kan wata yarinya da ta ɓata masa rai, da yadda ya ce da ba don ita mace ba ce daya dake ta
Yanzu ga yarinyar a gabansa, tana ba da nata labarin cikin yadda ya sa ya kasa riƙe dariya
Rayyan ya jefa masa wani kallo “Rameez”
“Okay okay” Rameez ya amsa, yana share hawaye a gefen idonsa saboda dariya
Daddy ya sake kallon Rayyan “Please it’s okay. Shame on you, Rayyan! Ka je kana faɗa da ƙanwarka sbd rashin zumuncinka? Ace ba ka san ƙanwarka ba?”
Rayyan ya ɗan buɗe baki, amma bai samu damar magana ba
Baba ya shafa gemunsa yana kallon Rayyan
“Ai fah kuwa,saboda rashin zumunci irin nasu, ace sun haɗu amma ba su san juna ba”
Mom ta kalli Rahama “Rahama ki kwantar da hankalinki. Ba za ki yi tafiya da shi ne a matsayin maƙiyinki ba ynx kunsan cewa ku blood ne, babu wata matsala in shaa Allah”
Rahama ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ɗan turo baki “Ni dai na faɗa, na san shi tun farko, kuma ban san shi da alkheri ba”
Rayyan ya juya ya kalleta “Who asked you?”
Rahama ta buɗe baki “You see ai na faɗa haka halinka yake”
“Rahama” Mammy ta kira sunanta cikin gargaɗi
Rahama ta rufe bakinta, amma ta ci gaba da kallon Rayyan cike fushi
Hajiya, wadda take kallon yadda yaran biyu suke ta musayar magana, ta yi murmushi a hankali “Idan kun so kar ku nutsu kuyi abun dake gabanku, ku tsaya ku ce zaku fara gardama tun anan”
“Ni ban fara ba Hajiya” Rahama ta faɗa da sauri “Shi ne yake farawa”
Rayyan ya yi kamar bai ji ta ba, Rameez ya sake yin murmushi “Daddy I think this workshop is going to be interesting”
“Rameez” Rayyan ya faɗa a hankali, yana kallonsa
“Me? Ban ce komai ba fa”
Daddy ya girgiza kansa, sannan ya koma kan abin da ya kira su domin tattaunawa
“Okay, enough! Yanzu ku saurara, Ina so ku fahimci cewa workshop ɗin nan yana da muhimmanci. Rahama za ki yi amfani da wannan damar wajen koyon yadda ake gudanar da harkokin kasuwanci da yadda ake mu’amala da mutanen da za ku haɗu da su”
Rahama ta gyara zama “Toh Daddy”
“Rayyan ina so ka taimaka mata ta fahimci abubuwan da suka shafi business ɗin. Ka nuna mata yadda ake tafiyar da wasu daga cikin ayyukan da za ku tattauna. Ba wai ina nufin ka yi mata komai ba, amma ka taimaka mata ta saba da professional environment”
Rayyan ya gyada kai “Ok Daddy”
“Good! Kuma ina so ku yi aiki cikin fahimta. Duk abin da za ku yi, ku tuna cewa kun je ne domin aiki da koyon abubuwa, ba don yin gardama ba”
“Daddy ai ni ba na gardama” Rahama ta faɗa
Rameez ya ɗaga gira “Really?”
Rahama ta juya ta kalle shi “Eh mana Yaya!”
“Okay” ya amsa, yana murmushi
Rayyan ya jingina da kujerarsa, yana kallon Daddy bai ƙara cewa komai ba, a ganinsa, idan ya yi shiru zai fi sauƙi, domin ya riga ya fahimci cewa yarinyar tana da shegen surutu kamar ba Mace ba, uwa uba ba kamun kai
Bayan sun gama tattaunawa, aka shirya musu abin da za su ci kafin tafiya Rahama ta zauna kusa da Mammy, tana ta yi mata magana a hankali game da Rayyan, duk da cewa tana ƙoƙarin kada kowa ya ji
“Wlh Mammy, ban san me ya sa zan yi tafiya tare da shi ba, daga cikin mutane duka, sai shi?”
Mammy ta kalleta “Rahama ki daina, ba yau kika fara haɗuwa da mutane masu halaye daban-daban ba, ki yi haƙuri, ki maida hankali kan abin da ya kai ku”
“Na ji Mammy” ta amsa, amma daga yanayin fuskarta, a bayyane yake cewa ba ta gamsu ba
Rameez ya zauna kusa da Rayyan, a hankali ya matso ya yi magana cikin ƙaramar murya “So, this is the girl?”
Rayyan bai kalle shi ba ya ce “Which girl?”
Rameez ya kalli Rahama, sannan ya dawo da kallonsa gare shi “The airport girl”
Rayyan ya juyo a hankali “Rameez, I swear if you start…”
“Okay I won’t say anything” Rameez ya katse shi, yana ɗaga hannayensa “But this is funny”
Rayyan ya ɗauke kansa “It’s not funny”
“To you”
Rayyan ya yi shiru
Rameez ya ɗan jingina da kujerarsa, yana jin daɗin yadda lamarin ya kasance, wai yau Rayyan ne ya rasa kalmomin da zai yi amfani da su? Though yau sbd Rahama, ya ga wani sabon yanayinsa
Can kuwa sai Baba ya duba agogonsa
“Lokaci yana tafiya, ya kamata ku fara shirin tafiya airport”
Daddy ya gyada kai “Eh haka ne. Rameez ka kai su airport ynx tunda ƙarfe biyu tayi, Ina so su isa da wuri kafin boarding”
“No problem Daddy” Rameez ya amsa
Rahama ta kalli Mammy, sannan ta ɗaga jakarta “Na tafi kenan?”
“Eh, ki ɗauki kayanki” Mammy ta amsa
Bayan sun yi sallama da Hajiya da sauran mutanen gidan, Rameez ya taimaka wajen ɗaukar jakunkunansu zuwa motarsa. Rayyan ma ya ɗauki nasa kayan, yana tafiya a bayansu
Rahama ta da gan shi, sai ta juya ta kalli Mammy “Mammy shikenan dai”
Mammy ta kalleta da mamaki “Rahama!”
“Toh Mammy, me na ce kuma?”
“Ki wuce ki shiga mota”
Rahama ta yi shiru ta shiga motar ya zauna a baya, ganin haka yasa Rameez yayi sauri ya zauna a kujerar me zaman banza yasa driver yazo zai Kai su
Rayyan ya shigo baya shima, ya zauna ba tare da ya kalleta ba
Da ta lura da haka, sai ta ɗan matsa jikinta zuwa gefen ƙofar, tana ba shi space kamar yana da wata cuta da za ta iya kamuwa da ita
Rayyan ko kallo bata ishesa ba
Rameez ya sauka ya fitar da driver yayi maza ya shiga kujerar direba, ya kunna mota, sannan suka bar gidan
Bayan sun hau titi Rameez ya yi ƙoƙarin fara hira domin kada tafiyar ta kasance cikin shiru ya ce
“Rahama, ya ya kika ji da workshop ɗin? Kin taɓa halartar irin wannan taro a baya?”
“Eh, na taɓa” ta amsa
“Good! To za ki ji daɗin wannan ma, in sha Allah”
“In sha Allah”
Rayyan yana zaune yana kallon wajen ta window, kamar hirar ba ta shafe shi ba infact damunsa ma suka fara
Rameez ya duba madubin mota, ya ga yadda Rahama ta ɗan kalli Rayyan, sannan ta juya da sauri, ya yi murmushi
“Rayyan, kana da wani abu da kake son ka gaya wa Rahama game da workshop ɗin?”
“No”
Rahama ta juya ta kalle shi
“Allah ya kiyaye ai da ka ce kana da abin da za ka gaya min, zance ka barsa kawai”
Rameez ya fashe da dariya, Rayyan ya juyo ya kalleta “Keee can you keep quiet for once?”
Rahama ta buɗe baki “Ni nayi da Kai ne toh? Though ai Kai ka fara”
Wani kallo ya watsa mata
“Toh, me ya sa ka kalle ni? Ai hakan nr yasa na yi magana”
“Ke baki san yin shiru bane? Are you sure you’re okay?”
“You see! Wannan shi ne halinka tun ranar da muka fara haɗuwa”
Rameez ya girgiza kansa yana dariya
“Please you two, we haven’t even reached the airport”
“Ka gaya masa” Rahama ta faɗa
Rayyan ya koma kallon taga, ya rasa me zai mata Wanda zai ji dadi
Rahama ta yi saurin juyowa ta kallesa
Rameez ya ci gaba da tuƙi, yana jin daɗin hirar da ke faruwa a bayansa. Tafiyar da ya yi tsammanin za ta kasance cikin shiru ta zama kamar yana ɗauke da comedians ne
Da suka isa airport, Rameez ya tsaya a inda ya dace, sannan ya fita ya taimaka musu da kayansu
“Ku tabbatar kun duba komai kafin ku shiga” ya faɗa
Rahama ta gyada kai “Na duba komai tun a gida”
Rayyan ya ɗauki jakarsa “Good for you”
Ta juya ta kalle shi “Do you ever get tired of being rude?”
Ya kalleta na ɗan lokaci “Do you ever get tired of talking?”
Rahama ta buɗe baki, amma Rameez ya katse ta “Enough! Me haka ne?”
Rahama ta yi murmushi “Ni kam ba ni da matsala, zan iya samun wani jirgin dabam”
Rayyan ba tare daya kalleta ya ce “Please do”
Ta ɗaga gira “Ka ji fa! Yana son in bar shi, ai wannan ba zai yiwu ba wlh”
Rameez ya sake yin dariya “Kut wannan halin naku sai ku, Rahama Yayanki ne ki daina masa magana anyhow”
Da sauri ya juyar da kanta
Suka shiga cikin airport tare da kayansu, suka bi hanyoyin da ake bi wajen checking da boarding. Rahama tana tafiya da sauri, tana son ta gama komai kafin Rayyan ya sake ɓata mata rai. Shi kuma Rayyan yana tafiya cikin nutsuwa, ba tare da ya damu da saurin da take yi ba
Da suka isa inda ake duba ticket da kayansu, Rahama ta miƙa nata, sannan ta tsaya gefe tana jiran a kammala
Rayyan ya tsaya a ɗan nesa da ita, da ta lura yana ƙoƙarin nisanta kansa, sai ta yi murmushi a ranta “Good! At least we agree on something’
Bayan an kammala dukkan abubuwan da suka dace, suka jira lokacin boarding
Rahama ta zauna tana duba wayarta. Rayyan ya zauna a wani wuri dabam, ya fitar da wayarsa ya fara dannawa
Da aka sanar da boarding, Rahama ta miƙe ta ɗauki kayanta, ta bi sauran fasinjoji. Rayyan ma ya tashi ya bi bayanta, amma ya tabbatar da cewa yana da ɗan tazara tsakaninsu
Sai dai da suka shiga jirgin, aka sake jefa su cikin irin matsalar da ta faru a tafiyarsu ta farko
Rahama ta duba lambar kujerarta, ta kalli layin kujerun, sannan ta tsaya
A hankali ta sake duba boarding pass ɗinta, ta ɗaga kai
Rayyan yana tsaye kusa da ita, yana duba nasa boarding pass
Rahama ta kalli kujerar, sannan ta kalli fuskarsa “No way” ta furta a hankali
Rayyan ya yi kamar be san wani yana existing a wajen ba
Rahama ta ja numfashi a hankali, ta ajiye jakarta, ta zauna, sannan ta juya kanta zuwa window
Rayyan ya zauna a kujerarsa, ya ɗaura belt, sannan ya fitar da wayarsa
Bayan ɗan lokaci, Rahama ta juya ta kalle shi, yana kallon wayarsa, fuskarsa babu alamun damuwa.
Ta yi tsaki a hankali, Rayyan ya ɗaga kai “What?”
“Nothing.”
“Then stop looking at me”
Rahama ta buɗe baki cikin mamaki “Who is looking at you?”
“You were”
“Please don’t flatter yourself. I was looking at the seat”
“Then look at the seat” Rayyan ya fada babu alamar wasa a muryansa
Ta juya kanta da sauri, tana jin kamar za ta fashe da kuka, amma ta tuna da maganar Mammy cewa ta yi haƙuri, ta maida hankali kan tafiyarsu
Jirgin ya fara shirin tashi. An sanar da fasinjoji su tabbatar da cewa an ɗaure belts ɗinsu, sannan ma’aikatan jirgin suka bi ta cikin layukan kujeru suna tabbatar da cewa kowa ya shirya
Rahama ta gyara zamanta, ta ɗaure belt ɗinta, sannan ta kalli window
Da jirgin ya fara motsawa, Rahama ta ɗan matse hannunta a kan armrest. Ba wai tana tsoron tafiya ba ne, amma duk wannan haɗuwar da ta yi da Rayyan tun safe ta sa ta gaji da komai
kar a manta a danna follow, hilis follow me😭