Free chapter · Read without an account

009

by SultyWrites · NI DA YA NABIL

_ NI DA YAYA NABEEL _


  _YOUNG WRITER✍️



* 009 *




Saida suka zauna sannan ya fara neman number Jumaymah, kusan missed call uku yayi mata bata daga ba, tsaki yaja ya ajje wayar sai gata ta biyo kiran, amsawa yayi ya kara a kunne ba tare da yayi magana ba, cikin kuka ta shiga faɗin, "Da gaske yanzu ka iya daukan wata kayi tafiya Babe? Ban taba tunanin hakan daga gareka ba. Ashe ba za'a yi wahalar miye gurbi na a wajen ka ba?". Shuru yayi yana sauraron ta can dai yaga abun nata bana ƙare bane sai kawai yace, "Barin kashe in kin gama kukan sai na kira" .

 Da sauri ta tsaida kukan nata kamar yana gabanta tace, "Na daina, na daina whl karka kashe". Numfashi ya furzar yana jin wani sabon tausayin ta na ratsa shi, cikin tausasawa ya shiga lallashin ta da kwantar mata da hankali, wanda a bangaren Asum ta kasa musu uzuri take kallon hakan a matsayin cin fuska, shiyasa ta cika tayi fam ji take kamar ta fice ta koma gida har wani tiriri take ji yana taso mata, ga wani jiri² da ta fara ji, bata san yaushe zuciyarta ta fara son sa ba da har take kishin sa ba har haka, dan ta san kanta tana daga cikin mata masu tsananin kishin abinda suke so, dan ko qawace in dai ta kwallafa mata rai to bata kaunar ganin wata kawar ta shiga jikinta, an dinga faɗa da ita kenan ballantana kuma miji, wayyo ni Asum na shiga uku ya zanyi da rayuwata ne, gashi wata ta yi min wuff da miji, wai meysa su Baffah zasu min haka ne, idan har sunsan a lokacin baza su miqani ga mijina ba meysa zasu daura auren ma, "Innalillahi wa Inna ilaihir raju'un, allahumma ajirni fi musibati". Haka ta shiga kamo duk addu'ar da tazo bakinta ko zataji saukin abinda ke nuqurqusar ta. Shi kuwa Nabeel duk wanna abun da ake bai sani ba yana can yana lallashin Jumaymah har saida aka fara sanarwa jirgi zai tashi sannan sukayi sallama ya kashe.

 Saida jirgin su ya daidai ta a sararin samaniya sannan ya juya wurin Asum data runtse idanunta tana murza goshin ta da hannun, hannun sa ya daura kan goshin nata, jin zafi yasa shi faɗin, "Har yanzun baki warware ba ne?".

Girgiza masa Kai tayi alamar ah ah dan it's better tayi shurun saboda yadda take ji in ta bude baki baza ta iya saita kanta wurin yi masa magana yadda ya dace ba  .

"Ke wai miye damuwarki ne?". Nan ma Kai ta girgiza masa alamar bakomai. Cikin ƙoƙarin control ɗin kansa yace, "Wai bana ce miki bana son Ina Magana ayi min shuru bane? ni fa bana san irin wannan girgije ² ki bude baki ki mun magana kawai". Bude idanunta tayi ta zuba masa su, shi ma idon ya zuba mata kafin daga bisani ya janye ya koma jikin kujerar ya kwantar da kansa yayi shuru. Can ma'aikaciyar cikin jirgin tazo tambayar abinda za'a kawo musu, coffee kawai yace ta kawo masa, ta juya wurin Asum tana tambayarta amma ko kallon ta batayi ba, haƙura tayi zata tafi yace, "Ki kawo mata duk abinda ya samu".

"Ohk sir". Ta amsa tana barin wurin. Ta kasan Ido yake sake kare mata kallo, ta  kifa kanta tsakanin cinyoyin ta. A haka har ma'aikaciyar ta dawo ta ajje masa abinda ya buqata da kuma abinda ta ga kamar Asum ɗin zata so. Tana barin wurin Asum ta ɗauki robar ruwan sanyin ta bude ta kafa kai, sai da ta sha kusan rabi sannan ta cire tana sauke numfashi. Zuba mata Ido yayi kamar wawa ganin ta maida robar ruwan bakinta ta karasa shanyewa sannan ragowar ta juye shi a fuskar ta yasa shi kiran sunan ta a hankali, "Assumi". Ba tare data kalleshi ba tace, "Na'am".

"Juyo nan ki kalleni". Ba musu tayi kamar yadda yace ɗin, kallon juna suka shiga yi na tsawon wasu secs kafin yace, "Meke damunki? Karki ce min babu cox definitely na san akwai wani abu".  Murmushin yaqe tayi tare da fadin, "Ba komai fa ya Nabeel, ciwon kan jiya ne yake neman dawo min amma nasan zai daina in sha allah". Tana gama fadin haka ta maida kanta jikin kujerar ta lumshe idanu. Ɗan tabe baki yayi dan bai yarda da ita ba cox dazu ai cewa tayi ba komai, ɗage kafaɗun sa yayi, daga nan bai kara cewa komai ba.

Bacci ne ya ɗauke ta, ba kuma ita ta farka ba saida jirgin su ya sauka, nan ma sojojin Germany ne suka zo taryensu,  magana yayiwa daya daga cikin sojojin da suka taho tare sannan ya kalleta yace, "Kuje zanzo in sameki".

Bata ce komai ba ta wuce. Wani tamfatsetsen hotel suka je inda aka kaita wani ɗaki me ciki da falo, bayan an gama shigo musu da kayan su ta kulle kofar tana mita ita kadai ni da ina da yadda zanyi ai bazan zabi auran soja ba, haba da Allah, haka kawai a kawo Ka garin da baka san kowa ba a ajje, wanna wani irin rayuwa ne. 

A nan falon ta kare surutanta saida ta gaji sannan ta tashi ta shige ɗakin, toilet ta wuce tayi wanka ta ɗauro alwala ta fito ta rama sallolin da sukayi missing a hanya, jin ana knocking ya sata tashi taje ta duba, ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel din ne tazo tambayar ta ko da akwai abinda take bukata, tace da ita bakomai tare da mai da kofar ta rufe .

Ɗakin ta koma ta faɗa kan gadon ta fashe da kukan da take ta faman riqewa tun a jirgi, cikin kuka ta shiga fadin Baffah da Abbah whl kunyi kuskure dan bazan iya rayuwa da mai mata ba bazan iya jura ba, ina da zafin kishi kan abinda nake so Kar zuciya ta kaini ga aikata aikin dana sani wanda zai zo ya shafeku duka, Abbah dan Allah ni dai kazo Ka dauken ni, a raba wannan auren qalubalen, wayyo Umma na Zuciyata zata fashe.

 Juyi kawai take a gadon tana kuka haɗi da sambatu kamar wata zararriya har bata san lokacin da Nabeel ɗin ya shigo ba, baice da ita komai ba ya rage kayan jikin sa ya wuce bathroom.

Lokacin da ya fito har bacci ya ɗauke ta ga busassun hawaye nan a kan fuskarta, girgiza Kai yayi kawai ya shirya sannan ya karasa ya gyara mata kwanciya saboda kar wuyanta yayi ciwo, zama yayi ya zubawa pretty innocent face ɗinta Ido, ya ɗau kusan 5 minutes yana kallon ta kafin ya tashi ya fiddo system ɗinsa da wasu takardu ya fita falo, zama yayi yana yatsina fuska tare da jujjuya hannayen sa da wuyan sa sukayi qara, aiki ya fara kamar ba gobe, yana cikin aikin ne aka kawo masa coffee da ya bukata, saida ya zubawa Wanda ya kawo ɗin ya sha kafin ya bashi umarnin tafiya  .

Ya dade yana aiki kafin ya tashi ya shige ɗakin, kallo daya ya mata ya fahimci ta tashi, ajje abubuwan dake hannun sa yayi a ma'ajjin su sannan yace, "Ki tashi ki nemi abinci kici kar yunwa ta miki illa ki janyowa kanki wahala, dan in kika janyowa kanki wani ciwon ni dai ba zan zauna jinyar ki ba, aikin dana zo yi zanyi, sannan ki tabbatar wanda ya kawo abincin ya dandana kafin kici". Yana gama fadin haka ya juya ya fice. 

Saida ta tabbatar da fitarsa kafin ta bude idanunta ta raka shi da harara, tashi tayi ta dauki after dress ta daura Kan kayan jikinta ta yafa mayafin ta fice a maimakon ta sa a kawo mata abincin kamar yadda ya faɗa.

 Hanyar data gani ta fara bi har ta gano elevator, shiga tayi ta sauka kasa. A reception ta tsaya ta saka order abinda zata iyaci sannan ta wuce Inda aka tanada dan cin abincin ta zauna, har aka kawo mata abubuwan data buqata aka jere, ɗaukan spoon tayi ta fara ci tare da faɗin, "Ni na fika aljanun kai ai, in taqamarka bishiyar kuka ni iccen tsamiya ce. Ace shikenan mutum sai tsirfa iri², wai ki tabbatar wanda ya kawo abincin ya dandana kafin kici". Ta ƙarashe tana me kwaikwayon maganar tasa hadi da murguda baki kamar yana gabanta ta cigaba da cin abincin ta hankali kwance.

 Wata yar budurwa ce tayi mata sallama kana kallon ta zaka san yar nigeria ce cikakkiya, daga bayan ta kuma wani matashin saurayi ne biye da ita, kujeru suka ja suka zauna saurayin yace, "Barka da hutawa kyakyawa, sorry mun zauna ba tare da izinin ki ba". Bata dago ba ba kuma ta Kara magana ba bayan sallamar data ansa, shi ma saboda sanin mahimmancin ta ne yasa ta amsa ɗin. Cigaba yayi da magana, "Haba mana big girl, ya za'ayi ki zauna a nan ke kadai, ai ba girman ki bane, kamata yayi ace akwai me miki firfita haɗi da baki labarai masu daɗi a gefe".

Sai a lokacin kuma matar ta yi Magana, "To ni dai da bazan ce komai ba amma Firstly dai yanzu ina wuni Aunty na". Dan tabe baki mutumiyar taku tayi a zuciyar ta tana faɗin gandandan dake ko kunya bakiji ba ki kalle ni yar firit dani kice min aunty. A fili kuwa amsawa tayi da, "Lpy kalau alhamdulillah".

"To ni dai sunana Fauza, yayana kuwa Fawwaz, tunda yaga fitowar ki ya dameni wai sai na rakoshi dan shi ya samu matar aure, to shi ne fa nace daga ganin sarkin power sai miya tayi zaqi".

"I'm Sorry, amma ni matar aure ce and kuna iya barin wajen nan tun kafin mijina ya ganku ya kuma san dalilin zaman naku cox za'a iya samun matsala". Da sauri saurayin yace, "Whattt? Matar aure fa kika ce? Haba mana an mata munsan irinku fa in bakwasan mutum saiku fake da fadin ku matan aure ne saboda ku samu sillibewa".

"Kai Malam ba wasa nake ma ba, ni matar aure ce matar field Marshal Nabeel H.A ...". Ai kafin ta rufe bakin ta saurayin ya bar wurin da sauri, tashi Ita ma matar tayi har bakinta na rawa wurin fadin, "Ya hakuri ma'am rashin sani ne whl, dan Allah kiyi haƙuri". Bata kara cewa komai ba har suka bar wurin sannan ta tashi ta koma daki.

Sosai tsoro ya kamata ganin dare ya raba amma har lokacin Nabeel bai dawo ba, takurewa tayi a karshen gado kamar kace kyat ta zuba a guje. Sai wajen 4am ya shigo, da mamaki yake kallon ta tana zaune can karshen gadon ta tura Kanta tsakanin cinyoyin ta, shi duk zaton sa ai ta jima da yin bacci amma motsin da yaga tanayi ya tabbatar masa da ba baccin take ba, bai ce da ita komai ba ya wuce bathroom.

Wanka yayi ya fito, tana nan a yanda take saidai zuwa lokacin bacci yayi nasarar sace ta. Saida ya gama duk abinda zaiyi kafin ya haye gadon, ganin a yadda baccin ya ɗauke ta sai yaji ta bashi tausayi sosai, da yasan zata zauna jiransa ai da yace tayi baccin ta kawai bazai samu dawowa da wuri ba, saboda Jumaymah ta riga ta saba masa in dai yayi irin wannan dadewar baccin ta takeyi abunta. Ƙokarin kwantar da ita yayi sai kuwa ta bude Ido tare da fasa ihu a firgice. Da sauri yace, "Shiiiiiiii firgitacciya, ni ne to". Da sauri ta shige jikinsa ta kankameshi tana me sakar masa kukan shagwaba, "Ni meysa zaka kawoni garin da ban san kowa ba kuma kayi tafiyar ka ka barni, kasan kuma ba iya bacci zanyi ba idan banga Ka dawo lpy ba".

Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke kafin yace, "Yanzu dai ba gani na dawo ba". Ya fada yana tattare mata gashin kanta daya kunce. "Ina kaje to?". Ta tambaya tana cuno baki.

"Abun daya kawoni naje yi mana". Bata fuska tayi amma bata sake cewa komai ba, jan karar hancinta yayi yana kallon face ɗinta a cikin dan guntun haske dake dakin kafin ya gyara musu kwanciya ya jawo duvet din ya lullube su. Fiqi fiqi Asum tayi tana Kallon sa, yayin da shi kuma ya tsurawa pop ido da alama tunanin wani abu yake can kuma ya juyo sukayi facing juna kasa² yace, "Wannan firgicin fa? Ba gani ba". 

Runtse idanunta tayi gam² tana me kankame jikinta kamar taga wani abun tsoro, dariya ta bashi amma ya maze ya ɗan murmusa kawai tare da riqo fuskarta yayi kissing din saman idanunta wanda hakan yasa ta waro su da sauri tana kallonsa, cikin wani irin salo ya kashe mata Ido ɗaya, da sauri ta janye idanun nata tana jin wani abu me kama da nauyinsa na tsirga mata, gefe guda kuma mamakinsa take dan ta rasa wani bangare zata ajje shi, gabaɗaya upside down yake sai ta fara gane masa sai ya sake juyewa. "Ki daina tunani na tunda gani gabanki". Sakin baki tayi cikin mamaki yadda akayi yasan tunanin sa take, iskar bakin sa me ɗauke da kamshi mint ya hura mata cikin ɗan bakin nata, da sauri ta jawo duvet din ta rufe kanta, yar dariya yayi ya sa hannu da niyyar janye duvet ɗin sai kuma ta riqe gam, jinjina kansa yayi tare da sakar mata ya zame ya shige cikin shi ma.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol