Free chapter · Read without an account

LOKACI CHAPTER 29

by Rabi'atu kabiru Fulani · LOKACI

***

⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳ 

RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI 

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA 

Under Team Yota's Amazing Pen's.

SADAUKARWA GAREKI KARYMAT BASHEER ❣️ 

FULANI ❣️ 
***

     PAGE 2️⃣9️⃣

Take mata baya ya yi, fuskarsa a kame take hakan yasa babu wanda ya yi gigin cewa zai gaishesa a cikin ma'aikatan, dan tun shigowar Zahra suka fara ƙananun maganganu, itama babu wanda yaga fuskar da zai mata magana, hakan ya sa suka fice salin alin.

Yana fitowa driver ya taso, hannu ya ɗaga masa, da kansa ya buɗe mata motar ta shiga, rufe ƙofar ya yi, sannan ya zagaya ya shiga driver seat, bismillah ya yi ya tayar da motar suka fita daga cikin building ɗin gaba ɗaya.

Tun da ta kife kanta a kan cinyarta bata ɗago da kanta ba, kuka take ƙasa_ƙasa, na baƙin ciki yanda ya yi mata faɗa kamar wata ƴarsa, abun ya ɓata mata rai sosai, ta rasa me yasa ya cika mata ido da yawa. Ya na jinta amman bai kulata ba, dan indai ta ce zata ci gaba da tafiya a haka tabbas ba za su shirya ba, duk yanda ya ke son lallaɓata kuwa.

Har suka zo ƙofar gidansu bata sani ba, parking ya yi, kansa ya jingina da kujera ya lumshe idonsa. Sun ɗau wajen 5minutes a haka, jin motar bata tafiya ne ya sa ta ɗago kanta, ganinta a ƙofar gida sai ta fara ƙoƙarin buɗe motar. 

Gyaran murya ya yi mata, bata juyo ba sai ci gaba da son buɗewa tafita da ta ci gaba da yi.

"Bayan magriba zaki baƙi na faɗa miki, idan kin shiga ki turo min Salmah" cike da bada umarni ya yi mata magana.

Wani baƙin cikin ne ya ƙara turniƙe ta. 

Unlock ya yi ta buɗe ta fita.

"Falmata" 

Juyowa ta yi ta zabga masa harara ta wuce gidan. Murmushi ya yi kawai ya girgiza kansa, ya na ganin shigarta ya ɗakko wayarsa ya kira Salmah dan yasan ba turo masa ita zata yi ba, magana suka yi ya kashe wayar ya ja motar ya tafi.

 Lokacin da ta shiga babu kowa a tsakar gidan hakan ya sa ta wuce ta zauna a gefen gado ta haɗe kanta da gwiwa, ita kanta batasan adadin lokacin da ta ɗauka a haka ba.

"Zahra! Zahra!!"

Kiran da Mahmah take mata ne ya sa ta ɗago kanta daga kan gwiwarta, a hankali ta juya tana kallonta, dan ta shigo ɗakin.

"Ina kika je tun ɗazu ba tare da kin sanar da kowa ba, da izinin wa kika fita? Har Salmah na tambaya amman ta ce ba ta san inda kika je ba"

Sauke idanunta ƙasa ta yi cikin sanyin murya ta ce "Restaurant ɗin mu na je" dan bata iya ƙarya ba sam a rayuwarta.

"Me ki ka je yi?"

Jin tambayar ta yi wani iri, har ba ta san ta ɗaga idonta ta kalleta ba, sake kawar da idonta ta yi daga kanta.

"Wajen Muhan na je"

Da mamaki Mahmah ta ce "waye haka?"

"Wanda kuka karɓi kuɗinsa" ta bata amsa.

"Muhammad za ki ce min, toh ya ku ka yi, ina fatan kun tattauna akan maganar bikin?"

Wani irin murmushi ta yi, sai dai cikin ƙanƙanin lokaci ya ɓace a kan fuskarta, hawaye ya maye gurbinsa a idonta.

"Mahmah.."

Ta kira sunan Mahmah cikin murya mai matuƙar rauni, bakinta ta buɗe za ta yi magana amman Mahmah ta katse ta.

"Na yi magana da wadda za ta fara yi miki gyaran jiki, sai kuma kiyi list na duk abin da kike buƙata, bamu da sauran lokaci sati biyu kamar kwana biyu ne"

Ɗago kanta ta yi gaba ɗaya ta kalli Mahmah, da idanunta da sukayi wata kala kamar ba na ta ba, ga hawaye kwance a cikinsu, amman ba su zubo ba, sannan ta fara magana cikin wata iriyar murya mai ɗauke da zafin da ta daɗe tana ɓoyewa.

"Mahmah daman burinki kawai na yi aure ko?" 

Ta jefa mata tambayar har lokacin idonta a kanta.

Kallonta Mahmah ta tsaya ta na yi sai kuma ta ce.

"Kamarya"

"Na gaji da faɗa miki bana son auren nan, amman kinyi shiru kamar ba ki fahimci abin da nake cewa ba, Mahmah auren da zan yi kawai kike gani ba ni ba, Mahmah me yasa baki damu da farin cikina ba? Ba ki damu da abin da nake ji a cikin zuciyata ba, damuwar ki kawai Mahmah na yi auren"

Hawayen da take riƙe wa ne suka fara zubo mata, saurin sharewa ta yi da bayan hannunta.

"Mahmah yaushe rabon da ki kalleni a matsayin ƴarki? Mahmah yaushe rabo ki tambayeni abin da na ke so ko kuma damuwata? Sai yanzu da maganar aure ta taso sannan kika fara kulani da abin da ya shafe ni?"

Shiru ta yi tana ƙoƙarin daidaita numfashinta, amman ta kasa.

"Mahmah wallahi ba zan miki ƙarya ba abin nan yana matuƙar yimin ciwo, ji nake kamar ba ki damu da ni ba, kinfi damuwa da auren nan da zanyi, haba Mahmah ni fa ƴar ki ce!"

Ta fara rasa control na kanta, saboda yanda abubuwan da Mahmah take mata suke dawo mata kamar a lokacin, har ba ta san ta ɗagawa mahaifiyar ta ta murya ba.

"Zan sake faɗa miki Mahmah, bana son wannan auren! Ba na son auren nan, kuma ba zan taɓa yin shi ba!"

Cikin kuka ta yi maganar, juya mata baya ta yi tana share hawayenta.

"Na gaji Mahmah! Na gaji! Wallahi na gaji!!!"

Wani irin shiru ne ya mamaye ɗakin.

Kallon tsantsar mamaki Mahmah ta ke bin ta da shi, ta kasa yarda da abin da taji Zahra ta ce, ji take ma kamar ba ta fahimci abin da take cewa ba.

"Zahra! Kin san abin da kike faɗa min kuwa?" 

Ta tambayeta tana nuna kanta, fuskarta ɗauke da mamakin da ya kasa barinta.

Share hawayen fuskarta ta yi, ta ɗago kanta ta kalleta, kanta ta gyaɗa mata alamun ta sani.

Mahmah girgiza kanta ta yi cikin rashin yarda 
"Saboda ina farin ciki zaki aure shi ne kike faɗa min haka? Ni Zahra?" 

"Ba haka ba ne Mahmah.."

"Toh ya ne ? So kike ki ci gaba da zama a gida? Duk da daman nasan bakya ƙaunar farin ciki na, shine dan kin ga yanzu ina farin ciki ki ke neman hanyar da zaki daƙile shi? Maganar auren nan wallahi babu fashi, ke ko gawarki ce sai an ɗaura da ita an kai ki, a can a kai ki kabarin ki, dan haka da ki so da kar ki so duk matsalar ki ce, Kuma kika sake saka ƙafarki ki ka fita sai na baki mamaki, gyaran jiki kuma za'a fara miki shi daga yau ɗin nan, ƴar baƙin ciki kawai sai dai ki mutu wallahi Zahra, amman aure babu fashi!"

Juyawa ta yi zata fita, sai dai kafin ta fita ta jefa mata tambaya.

"Mahmah kenan ni ba ni da wani zaɓi a rayuwata, sai abin da aka zaɓa min?"

Ba tare da ta juyo ba ta bata amsa.

"Kin gama tsufa a gida wane zaɓi gare ki Zahra? Kin wuce wannan *LOKACIN* ai" ta na kaiwa nan ta fice daga ɗakin cikin sauri.

Zubewa ta yi a gefen gadon, rufe fuskarta ta yi da tafukan hannayenta, wani irin kuka take wanda yake fitowa daga can ƙasan zuciyarta, abubuwa sunyi mata yawa, ta kuma yarda da maganar Mahmah na cewar bata da wani zaɓi a rayuwar ta ta, tun da gashi ko shi Muhan ɗin ai bai tambayeta ba, kawai ya yanke mata hukunci ne.

Salmah ce ta shigo ɗakin, ɗagota ta yi daga durƙushen da take, zaunar da ita ta yi a gefen gadon, itama ta zauna, kallonta take cike da tausayi, sun jima a haka ba tare da ta iya ce mata komai ba, sai kuma ta tashi ta ɗakko tissue ta fara share mata hawayen.

"Big sister dan Allah ki daina kukan nan haka"

Karɓar tissue ɗin ta yi, ta ci gaba da goge hawayen, sai dai tana gogewa wasu na sake zubowa.

"Baki san me nake ji ba Autah, tun da aka fara maganar auren nan babu wanda yake saurarata, har shi kan shi Muhan ɗin, Autah wai ni Muhan ya ɗaga wa murya, nifa Autah kamar wata sa'arsa ko kuma ƴarsa"

Ta faɗa mata ta na nuna kanta, tabbacin abin ya na ci mata rai sosai. Dariya ce ta kusa ƙwacewa Salmah, amman ta shanye abarta, saboda kar ta ƙara tunzurata, amman yanda tayi maganar kamar ta girme sa sosai.

"Gaskiya Muhan bai kyauta ba Big Sister, amman Big Sister kawai kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki ki nuna musu kin karɓi auren nan, kin ma fisu farin ciki da shi, ko dan Mahmah ban so ki ka yi mata magana a yanda kika yi mata ba, baki taɓa ba bai kamata ki fara ba a yanzu, ki ka ma yi haƙurin shekaru sai na yanzu ne ba zaki iya ba, ƙyale Mahmah da Muhan ɗin duk za su gane basu kyauta miki ba da kansu"

Kallonta Zahra ta yi sai kuma ta sauke ajiyar zuciya, shiru ta yi tana wasa da zoben hannunta. Salmah ta kula da abin da take yi, a hankali ta ce mata.

"Yanzu da kika je wajen Muhan ɗin ya kuka yi?"

"Autah sa'anki ne shi da kike faɗar sunansa kai tsaye haka?"

"Wai da na ga bakya sonsa, shi ya sa na ga basai na girmamasa ba, amman tun da kina son abinki dole na ce masa Yah Zay'd ai" cike da shaƙiyanci ta yi maganar.

Da sauri Zahra ta ɗago ta kalleta, sai kuma ta harareta.

"Autah ni yanda ya yi min magana ya ma fi ɓatan rai" 

Murmushi Salmah ta yi kawai, ba tare da ta ce mata komai ba, sai kuma can ta ce 

"Ƙannansa da amininsa za su zo anjima"

Kanta ta gyaɗa mata ta kwanta....


★★★

Ta na cikin Kitchen ɗin da ya zama mallakinta a gidan, Alhajinsu ne ya sa aka gina mata shi ta wajen get ɗin su, kafin ka shiga cikin gidan, saboda yanda lokaci ɗaya Allah ya sa ka mata albarka a harkar abincin nata, zuwar masa ta yi da maganar ta na son buɗe ƙaramin restaurant, ya ce a'a a cikin gida zai saka a yi mata, sannan ya bata mukullin mota ɗaya a cikin motocin sa, dan haka ita yanzu bata da wata matsala, har ma'aikata ta ke da su.

Order ta je ta kai da kanta, ta bar yaranta suna aiki, bayan ta kai ta shiga motar ta da niyyar komawa gida, cikin nutsuwa take tuƙin, hankalinta gaba ɗaya yana kan hanya, amman hankalinta ya na kan wata baƙar mota da ta kula ta na bin bayanta, da farko bata damu sai dai ganin ta bi wata hanyar, motar ma ta bi inda tayi, ji tayi tsoro ya na neman kamata, ƙara gudun motar ta yi, dan hanyar babu mutane sosai, kafin ta ƙara sanin abin da ya kamata tayi, ta ga motar ta wuce ta a guje, sai kuma ta sha gabanta.

A tsorace ta taka burki gabanta na tsananta faɗuwa, tsayawa ta yi ta na kallon motar cikin firgici, dan haka kawai ta ji a ranta masu ƙwace ne.

A hankali ƙofar motar ta buɗe, matashi ne ya fito da ga ciki, fuskarsa cike da nutsuwa da kamala, ya na sanye da farar shadda a jikinsa, hannunsa ɗauke da agogo, kusa da motar ya ƙaraso, knocking ya yi mata, sai ya sunkuyar da kansa yana neman izinin ta sauke gilashin motar.

Cikin shakka Khairiyya take kallonsa, a kammaninsa dai baiyi kala da mugu ba, sai dai shi mugu ba shi da kama, kamar ba za ta sauke ba, sai kuma ta sauke.

"Assalamu alaikum" ya yi mata sallama cikin muryarsa mai cike da nutsuwa.

"Wa'alaikumus salam bawan Allah lafiya?"

Murmushi ya yi kaɗan "lafiya lau, afuwan da yanda na tare ki dan Allah, daman magana nake son muyi please idan babu damuwa"

Kallon wajen ta yi ta ga sai jifa_jifa abin hawa yake wucewa. 

"Ina jinka"

"Sunana Faisal Abdallah, daman naganki ne a inda ki kai order, shine na tambayi abokina, wace ke ya faɗa min kina abinci na taro ko?" Ya ƙarasa da tambayarta, ganin duk yanda take a takure.

"Eh haka ne" ta basa amsa a taƙaice.

"Ma sha Allah daman ina neman wadda zata min abinci muna da taro na abokan kasuwancina, kuma naji suna yabon abincinki, toh idan babu damuwa ina son kiyi min Please"

Ajiyar zuciya ta sauke, sai ta buɗe jakarta ta ciro kati guda ɗaya wanda yake ɗauke da dukkanin bayaninta "gashi nan zaka iya tuntuɓata duk sanda ka shirya"

Karɓa ya yi da murmushi a fuskarsa ya ce "in sha Allah za ki ji ni, ki yi haƙuri da yanda na tare ki a hanya, ba na son na rasa ki ne"

Ɗan murmushi ta yi masa kaɗan "babu komai" daga haka tayi baya ta ja motar ta.

Bayan ya koma motarsa kallon katin dake hannunsa ya yi ya karanta sunanta a hankali.

"Khairiyya.." fuskarsa ɗauke da wani irin murmushi ya ajiye katin a kusa da shi ya ja motar shima ya bar wajen.

★

Ta na zaune ta na lissafi wayarta ta fara ringing , duba mai kiran nata ta yi, sai dai number babu suna, ɗagawa ta yi ta kai wayar kunnenta.

"Assalamu alaikum"

Daga ɗayan ɓangaren aka amsa mata.

Wa'alaikumus salam Khairi" ya taƙaita sunan nata.

Ɗan shiru ta yi ta ƙara duba wayar "ban gane me magana ba amman"

"Faisal ne, daman na kira ki ne akan maganar da mukayi ta abincin taro, na tattauna da abokan aikina, kuma sun amince"

Gyara zamanta ta yi ta buɗe littafin da take shigar da order, sai kuma ta ce ya yi mata cikakken bayanin taron. Cikin nutsuwa ya yi mata bayani da adadin mutanen da za su je, da kuma irin abincin da suke so. Ya na bayanin ta na rubutawa, bayan ya gama ta faɗa masa kuɗin da zai biyata, a take ya ce ta tura masa account, bayan ta katse ta tura masa ta ci gaba da abin da take. A ranta kuma ta na jin daɗin yadda Allah ke buɗe mata ƙofofin arziƙi ta hanyar da ba ta taɓa tsammani ba.

★

Bayan ya ajiye wayar ya kalli abokinsa da ke ta kallonsa.

"Yanzu da kace mata zaka yi taro yaushe ka shirya taron?" 

Murmushi ya yi "da na bar wajen kai tsaye soyayyarta naje nema, sai dai tayi min wani irin kwarjini da na kasa furta mata abin da yake raina, dan haka zan bi komai a hankali, taro kuma da ma'aikatana za muyi walima" 

"Ni ya kamata na kaiwa Mommy albishirin nan" 

"Ka bari komai ya tabbata ko Sadik?" Ya katse sa.

"Zai ma tabbata in sha Allah..."

FULANI
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol