Free chapter · Read without an account

A HEART TIRED OF HOLDING ON

by saddiqa.writes · NURI



"Ammi it's better if you just tell her the real reason behind their return. Let her discover that we're her family. She's not alone, she has us. Ammi, this little girl has been suffering all alone. Wallahi I pity her, I fell her pain especially considering her current state of mind. Can we just go back and tell her the truth? Her brother is there, waiting for her in Abuja."

Komai da Adda Safa tace gaskiya ne and it convince Ammi ta yadda. Kallonta Ammi tayi bayan dogon nazari tace "can you really understood that the girl lost trust in people.."

"But Ammi, we're talking about her only brother. If not for anything else, she'll at least want to go for Afif's sake. Zamu iya hadasu suyi magana ta waya maybe through a video call. She'll get to see him, and he'll get to see her too. Idan ya fada mata da kansa zata yarda Ammi"

Kai Ammi ta gyada sosai tana cewa "turn the car Safa. Let's go back." Babu wani bata lokaci Safa ta juya motar suka koma gidansu Nuri. Kamar dazu sallama suka yi suka tarar da Maman Nusaiba zaune tana tankade sannan bata amsa musu sallamarsu ba sai binsu da kallo kawai da tayi.

Dakinsu Nuri suka tsaya kamar dazu suka sakeyin sallama. Unlike dazu da Nuri ce ta amsa yanzu Inna ce Nuri is dealing with many thoughts a mind dinta.

Shiga suka yi kansu tsaye suna bin Nuri da bata dago sam ta kallesu ba da alama bama ta lura da zuwansu ba.

"Nuratu basu wajen su zauna.." no response!

"Nuratu." Inna ta kirata da dan qarfi tana dafata. A firgice ta dago tana kallon Inna idonta ya sauka kan su Ammi. Tunani ta tafi yi basu tafi ba dama ko kuwa. Ta bisu da wani kalar kallo kamin ta miqe ta basu waje.

Zama sukayi Ammi tayi qasa da kanta tana cewa Inna "Baba kuyi haquri mun sake dawowa."

Kai Inna ta girgiza tana cewa "ah haba babu komai ai."

Dan shiru Ammi tayi kamin ta fara da "ban san yadda zaku dauki abun bane... Amman dai .." sai ta kalli Nuri "Nuriyya Afif qaninki yana Abuja waiting for you!!!"

Da wani kalar sauri ta dago ta sauke idonta kan Ammi "wanne Afif din?"

Dafata Safa tayi tana cewa "Ammi let me take over.." Kai Ammi ta daga mata don Safa ta fita kaifin harshe sosai.

"Nuriyya."

Bata amsa ba ammn kallon da take mata ya tabbatar mata tana tare da ita.

"I don't know whether you'll believe us, but honestly, your brother, Afif, is in Abuja. Mu din 'yan uwanku ne ta hanyar mahaifiya,  Gidado Ardo family!"

Bata san sunan kakan Mami ba amman ta haddace sunan Abban mami kamar Abbanta, Gidado yes haka sunan yake..

Kasa magana tayi sai binsu da kallo da take yi ganin haka yasa Safa ta dauko wayarta tayi dialing number din Afif WhatsApp video call. Tana fara ringing ya dauka kamar yana jira haka Safa tayi sallama ya amsa yana gaida ita. Murmushi tayi masa tana cewa "guess what kiddo?"

Dan bata rai kadan yayi don already shi ya saba dasu "for Allah sake Adda Safa ki dena cemin kiddo. I'm in my twenties so I'm not a kid haba mana."

Dariya ta danyi tana cewa "ga Adda Nuri nan.. yau na ganta and guess what wallahi ta fika kyau da kake cewa na ganta sai naji kamar ba yar ahalinmu bace."

Nuri tunda taji muryar Afif ta gama yadda da zancen Safa. "Don Allāh bani ita na ganta.."

Miqa mata wayar tayi Nuri ta miqo hannunta dake rawa ta amsa tana kallon secreej din wayar. It was Afif, her one and only brother.

"Biyayye."

"Adda."

Hannu tasa ta toshe bakinta da kyau gudun kar tayi kuka don taji alamun yana zuwar mata.

"Adda, am.. how have you been? It's been days since you last called me, and you don't even have a standard phone number anymore."

"Afif dagske kana Abuja.. dagaske you're waiting for me acan?"

Kai ya gyada mata shima yana qoqari kar yayi hawayen don already Nuri ta fara hawaye.

"Yes I'm here Adda. I'm waiting for you. I'm here to see you Adda."

"Zan zo afif zan ganka.. Afif wai su 'yan uwan Mami ne?"

Kai ya gyada mata yana cewa "yes Adda for now idan kinzo za muyi magana ki yadda ki biyosu kawai kinji Adda am."

Kai ta hau gyada masa tana share hawayenta ta dago ta kalli Ammi tana cewa "aunty na yadda zan biku can zanje naga biyayye am."

Inna da sai yanzu ta gama fahimtar asalin abinda ke faruwa ta miqa hannu ta karbi wayar and there he is, Afif Abdullahi.

Dan hade rai Afif yayi ganin Inna yana cewa "Adda wa kika bawa wayar ne?"

"Dalla Inna ce?"

"Ban santa ba don Allāh ni ki amshe wayar."

Babu musu Inna ta mayar da wayar wajen Nuri don tun da can Nuri tafi sauqin hali kan Afif. Afif hold grudges tun suna yara haka yake akwai riqo.

Miqawa Adda Safa wayarta tayi tana cewa "zan biku." Murmushi Safa tayi tana riqe hannunta tace "we're glad Abbu your grandfather yana can shima waiting ya hadu da Jikarsa Hasken Mami."

Qasa tayi da kanta tana share sabon hawayen daya zubo mata.

Haka kawai ta samu kanta da cewa "Mami fa?"

"Abbi is working on that. They'll go all the way to her husband's house, but you have to come with us first because you're the only one who knows where the house is. That's why Abbi wants you to come along. He has something very important to discuss with you."

Kai ta gyada mata tana dagowa ta kalli Ammi tace "na yadda Inna kin yadda?"

Kai Inna ta gyada, bata da abin cewa don mamaki da kunya ya gama kasheta awajen.

Dangin Mami ake magana, marar asalin da ta tsana ta takurawa ta tsangwama duka saboda rashin asali. And now it has turned out that the very relatives of the woman she had despised were the ones who paid for her surgery!!!

Duk shiru suka danyi for some moments kamin Ammi ta katse shirun da "jibi in Allāh ya kaimu zamu tafi sa muyi booking flights mu tafi ynzu mu barku anan kuyi sallama da mutane gobe in Allah ya kaimu sai mu tafi gidanmu ku kwana ko?"

Kai Nuri ta gyada tana jin dama za'a tafi yanzu kawai. Ta qagu taga biyayyenta. Haka nan badan taso ba ta rakasu har bakin motarsu tana binsu da kallo cike da mamakin nan daya kasa barin ranta wai su din 'yan uwansu ne.

Bayanta dawo ta tarar da Inna a inda ta barta bayan ta fita kana ganinta kaga wadda keda qatuwar damuwa. Bata kulata ba ta samu waje ta cigaba da aikin da take yi sai dai unlike dazu da take moody ynzu cike da wani farinciki take gyaran nata.

Inna ta saci kallonta, wani irin nauyin Nurin taji tana ji tun kamin azo kan Mami. Kawai the fact that the blood relatives of the woman she had despised were the ones who saved her, coupled with the fact that yanzu sunzo zasu tafi dasu, zasu dawo qarqashinsu da rayuwa maybe forever.

Bawai baqin ciki take ba, kawai akwai abinda mutum zaiyi ya rinqa jin kunyar abinda ya aikata, yaji dama za'a iya dawowa baya ya goge abinda ya aikata, irin haka Inna take ji. Ta tafi tuno kalar cin mutuncin da tayiwa Mami, kalar maganganun data rinqa jifanta dashi, there was a time data taba ce mata maybe ma bata da uba meaning she's born out of wedlock. Ynzu taya zata iya zama cikin danginta.

Hawaye kawai taji ya fara bin fuskarta daidai Nuri ta dago suka hada ido. Da kallo tabi Inna sai dai bata kulata ba sam, deep inside her tasan abinda ya saka Inna kuka. Ba zata rarrasheta ko ta bata baki ba. Zata barta tayi kukan son ranta sannan ta mugun jin dadin haka, taji dadi da Inna taga dangin Mami kamin ta mutu, wannan yana daya daga cikin burinta and is like a dream come true.

 FU'AD'S POV...

"When are you leaving? I mean, when are you going to Nigeria?"

Kallonsa kawai Fu'ad yayi sai ya girgiza masa kai yana maida idanunsa ya rufe. Yana kwance kan sofa yayi shigar baqin kaya daga kan designer trouser dinsa har rigar jikinsa including safar dake qafarsa baqa ce.

"I'll be leaving on Sunday In Sha Allah. I told you about that boy, our newly discovered cousin ko?"

Kai ya daga masa ba tare da ya bude ido ba "an gano sister dinsa..."

Wani iri yaji da ya sashi bude idanunsa da suka sauya duka kawai yau haka yake jinsa kamar baya da lafiya.

"So, I'm hoping to go and welcome her. The girl has been through so much. I never imagined that the kind of things we hear about or watch on TV could actually happen in real life, especially to someone so young. Wallahi, I already feel so sorry for her, even before meeting her..."

Miqewa Fu'ad yayi ya zauna yana maida kansa sama ba tare daya kula Fa'iz ba. Shima Fa'iz din bai damu ba, don ya gama sabawa da wannan new Fu'ad din.

"She's so young to face all this. She's truly brave."

Bude ido Fu'ad yayi yana kallon Fa'iz ba tare da yace dashuy komai ba.

"So, I think I'll be going back on Sunday, the same day they're taking her to Abuja..."

Da Kai Fu'ad ya amsawa Fa'iz ba tare da ya bashi amsar tambyar da yayi masa a farko ba na sanda zai tafi.

Da kallo Fa'iz ya bishi, baya son wannan halin sam amman ya gaji da tambyar Fu'ad mene damuwarsa yana ce masa babu komai bayan yasan akwai komai.

Haka suka cigaba da zama kamar kurame, yau duk surutu da takurar Fa'iz Fu'ad ya kaishi qarshe da yaji baya son yi masa maganar shima daga qarshe ma tashi yayi ya bashi wajen duka. Da kallo Fu'ad yabi bayan Fa'izz, irin deep kallon nan. He wished he could open up and tell Fa'iz what was bothering him, but he couldn't.

Ya bude baki ya tonawa Umminsa asiri, ya bude baki yace Umminsa ta rabashi da wadda yake so, ya bude baki yace Ummi ta tsine masa indai har zai cigaba da kula yarinyar nan.  Ba zai iya tonawa mahaifiyarsa asiri ba, gwara ya bar abin aransa yadda babu wanda ta fadawa dalilin sauyawar Fu'ad din haka shima babu wanda zai fadawa dalilin sauyawarsa. He will will keep on holding on to it, zai cigaba da riqewa har qarshen rayuwarsa. Duk da yana ji ajikinsa hakan ba qaramin cutar dashi zaiyi ba ko yace yama yi.  He's always on medication na takurawa zuciyarsa da yayi da damuwa, his heart was really affected. Ta fara gajiya da dukkan quncin da yake boyewa. A times yana jin haushin kansa na yadda yake da irin wannan riqon, riqon da yake shirin illata masa rayuwarsa.

Jiya bayan an tashi daga sallahr jumu'a ya fara jin wani irin uneasiness haka cikin qirjinsa da dama yana ji to amman na jiyan yafi damunsa. Ba wannan ba ya shiga bandaki zaiyi alwalar Asr ya danyi tari sai ga jini a tarin nasa. Hannunsa yabi da kallo kamin ya dauraye ya fita zuwa asibiti bayan an idar da sallar ba tare da buqatar rakiyar kowa ba.

After a series of examinations da diagnosis, the doctor confirmed that he was suffering from heart failure! He had burdened his heart with so much stress and emotional pain that it was beginning to give in. Baya buqatar likita ya fada masa damuwa ne ya jawo masa ya shi akaran kansa ya sani. He had already noticed the changes over the past few days. Sometimes, even while sitting still he could feel his heartbeat slowing down. Sannan ko work out yayi sai yaji numfashinsa kamar zai dauke abinda baiyi da.

Yanzun ma daya bi Fa'iz da kallo ji yayi dama Ammi ce ta haifeshi ba Ummi ba, he can't deny the fact that Ummi da take mahaifiyarsa ta jawo masa ciwon zuciya!!!

To be continued...

like, comment and share 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol