Free chapter 路 Read without an account
Chapter 43
by MARYAM STAR 路 茒AURIN ZUCI
***
***
饾樋饾樇饾檺饾檷饾檮饾檳 饾檿饾檺饾樉饾檮馃攼
Chapter 43.
Tana jin yanda wani abu me kaifi ya soma huda zuciyarta, hannu tasaka ta zagaye Rimsha a jikinta tana jin tsananin tausayin matar na lullu蓳e, a fili cikin 茩aramin sauti ta furta.
"Ya Allah, ashe dama haka mutanen suke azzalumai ne basu da imani? ashe ba 茩aramin gata na samu ba daban rayu nayi cu蓷anya da su ba, Alhamdulillahi ya Rab. " Maryam ta fa蓷a a sarari kuka na kwace mata, yayinda wasu memories tsakaninta da kakaninta ya dinga dawo mata, mussaman a wata rana da tayiwa Kaka Abu wata tambaya.
****
Maryam "Kaka Abu zan iya tambayarka game da aikinka?."
Kaka Abu "Ih mana Noor ki tambaye ni akan komi zan amsa ma ki."
" Mutanen waje suna da da蓷in zama ko?."
Kallonta ya yi a lokacin, cikin aon gane abin da takr nufi ya ce da ita.
"Sam wasu daga cikinsu basu da da蓷in sha'ani, wasu kuma mugaye ne marasa tsoron Allah, wasu kuma salahan bayi, wannan fara'a da dariyar da kike ganin mutanen waje na yi, ba gaskiya bace dayawansu akwai wata manufa a cikin fara'arsu, a yanzu dai a duniyar nan banga abu me wuyar sha'ani ba irin mutane, kedai kici gaba da maida hankali akan abin da ke gabanki, kar ki tsaya biyewa mutane da 蓷abi'unsu, domin kuwa wata rana zasu iya jefa rayuwarki cikin tasku."
"To amma Kaka miyasa ni bana zama cikin mutanen, ina yawan ganin wasu suna shiga gidansu wasu, nifa ko aikena baka yi sai an da蓷e sosai, kuma idan na fita ina jin da蓷in yanda mutane ke sabgoginsu."
****
Muryar Rimsha ce ta dawo da ita duniyar zahiri daga tunanin data afka.
" Nasan za ki yi tunanin Hafsa ita ka蓷aice 茩alubalena ko, a'a ba ita ka蓷ai bace, kawaide ta zama sanadin bu蓷e 茩ofofin soma afkuwar 蓷addarorina, wansa suka cigaba da gara rayuwata matakai daban-daban har suka sada ni da wata rayuwar wacce bansata ba, bankuma san yanda zan fitar da kaina daga cikinta, ki sake gyara zama Maryam domin kuwa yanzune za ki ji asalin labarin zalunci da muguntar da aka aikata min."
"A'a dan Allah karki sake karya min zuciya iya hakama ya ishe ni, zuciyata tayi rauni."Maryam ta fa蓷a idanuwanta na cika tab da ruwan hawaye."
Kama hannayenta Rimsha ta yi tana girgiza kanta a raunane ta ce.
"A'a please kibarni insanar da ke abin da ke soso zuciyata zanji sau茩i idan na amayar da abin da ke cikina, kin kuwa san tsayin shekarun dana 蓷auka ban yi magana da wani 蓷an adam ba, kinsan lokacin dana kwashe ina addu'ar Allah ya kawo wanda zan tattauna matsalolina da shi, wata茩ila zan samu sau茩in abin da nike ji yana min ciwo a zuciyata."
"Shiru Maryam ta yi alamar tana sauraren Rimsha.
Sai Rimsha taci gaba.
****
"A hankali naci gaba da rainon Junaid da Muhammad yara da suka taso tamkar 拼an biyu kuma cike da 茩aunar junansu.
Hafsa bata sake yin wani abu dazan zargeta ba, saide akwai wata fara'a da take yawan yi min wacce ke tsorata ni, bana son wannan shiru 蓷in nata domin nasan ba lallai na alkairi bane, bana son pritending 蓷in ta dake yawan yi tana nuna kamar tana sona, nafi son muci gaba a yanda muka fara, ta zage ni a gaban kowa ta kuma taangwame ni.
Tsakanina da Saminaka kuwa 茩auna da kulawa sai abin da yayi gaba, domin kuwa haihuwar Junaid da nayi kamar an sake sabunta ma shi soyayyata, a 蓳angaren kasuwancin shi ma sai sam barka domin kuwa bu蓷i tako ina sai 茩ara gaba-gaba yake.
Muna cikin shekara ta uku da aure ya sabunta mana sabon gini na zamani, irin ginin da babu kalar shi a area 蓷inda muke, ya kuma bamu jarin da zamu gina kasuwanci.
Sosai naji da蓷in wannan jarin domin kuwa kasuwancina na ha蓳aka naci gaba, na 茩ara tattara ribata na zuba hannun jari a wani 茩aramin kamfani da aka bu蓷e na siyar da azurfa da gorl, cikin shekara 蓷aya nima na ginu na kuma tsayu da 茩afafuwana, na zama babbar bacen da ake damawa da ita a fanin kasuwanci, ban kuma yarda kasuwancina na baya ba, ina siyo abubuwa da yawa daga Dubai in siyar a Nigeria in kuma kai musu wanda ke sau茩i a nan can kuma babu su sosai.
Sosai 茩ofofin arzi茩i suka bu蓷e min, rayuwata ta sauya, na daina damuwa da Hafsa da iskar data laukota, dan bana ma wuni gida nafi zama shaguna na ina duba yanayin kasuwancina, yarana kuma Muhammad da Junaid suna samun cikakkiyar kulawa, tunda na rula Junaid ya fara magana na daina kiran Muhammad da sunan shi kai tsaye sai de ince Baffa ko kuma Uncle, da haka shima Junaid ya saba da kiran shi Uncle kamar yanda na sabar ma shi.
Sai da Junaid ya cika shekaru uku cif, sannan ciki ya bayyana a jikin Hafsa, sosai nataya ta murna, kuma nayi mamaki da sam bata wani laulayi bata fasa hidimominta na yau da kullum ba komi tana iya yi hankali kwance, sa蓳anin ni da kusan kullum a asibiti nike wuni ina jinya saboda abin da tayi min.
Saminaka ma yayi murna sosai da cikin jikinta, kuma ya bata kulawa sosai kamar yanda nima ya bani daga farko kafin ya juya min baya.
Cikin ikon Allah ta haife cikinta lafiya inda ta samu 茩aruwar yaro Namiji, sosai nayi farinciki da Allah ya wadatamu da samub 茩aruwar yara maza, haka shima ta 蓳angaren Saminaka ga 茩aninshi 茩arami da har ya fidda rai da samun 茩ane Allah ya bashi, ga kuma mazan da muka haifa ma shi.
Sosai na hidimta mata da ku蓷a蓷ena, bandai shige mata ba kamar yanda ita tayi min, amma ina zuwa ina gaida ita da baby kullum safe sa dare.
Rayuwa ta mi茩a arzi茩in Saminaka sai bun茩asa yake, har sunanshi ya fito cikin manyan 拼an kasuwa da ake damawa dasu a wannan lokacin.
Tun a lokacin yana ganiyar tashen 拼an siyasa ke rububin shi amma yana kauce musu kasancewar shi matashi me son dogaro da kai.
Bayan rayuwa ta sauya mana sai ya zamana a sabon gidanmu bana iya sanin abin da Hafsa ke ciki, kamar yansa itama bata iya sanin halin da nike ciki saboda wawaka-wawakan 蓳abgarori aka gina mana kowa da nashi, yayinda na Saminaka ke tsakiyarmu.
Kwatsam wasu ranaku na soma gane Hafsa na shigowa da maza cikin gidan, kuma kamar ba mutum 蓷aya ba dan nasha ganinsu sun shigo ko zasu fita, ban bari naja zargin da nisa ba na 蓳aras saboda bai shafeni ba, amma mi, bayan wani lokaci sai na lura abin yana yawa, bayan shigo da su da take kamar akwai abin da sukw aikatawa da ba daidai ba, itadai ba aiki ko kasuwanci take ba bare ace abokan aikinta ne, wata rana da rana, lokacin banfita shago ba saboda bana jin da蓷in jikina, Muhammad da Junaid kuma sun tafi makaranta, haka kawai na gaji da zaman sashena sai naji ina son sashenta in 蓷auko yaronta Fahad yazo ya 蓷ebe min kewa da zaman ka蓷aici, domin kuwa ko 拼ar aiki bani da ita tun abin da Ma'a tayi min ban sake yarda da kowa ba, nafi ganewa 拼an aiki maza ko kuma ni inyi da kaina.
Saye nike cikin shiga irinta larabawa domin kuwa itace shigata ban fiye saka kayan hausawa ba duda Saminaka yana son haka nafi sakewa cikin shigata ta al'ada.
Lokacin hutu da kwanciyar hankali sun mamaye ni, na da蓷a yin kyau fiye da baya na zama cikakkiyar matar aure me cike da wadata tako ina, har 蓷aukar ido zubin halitta da kyawuna ke yi tsabar hutun dana samu.
Wani irin dokawa kaina ya yi da 茩arfi, gabana ya yanke ya fa蓷i, na soma 茩o茩arin jada baya domin in gudu, saide kash kaddarar data zaunar da ni gida domin qanzuwa a ranar ta rigada ta gabato.
Wani ti茩e茩en ba茩i 茩irin 蓷in mutumi sangameme barar kyawun siffa zaune shi da wasu maza su biyu, gabansu kuwa wani 茩aton kasko ne dake fitar da ba茩in haya茩i, yanayin yanda suturar jikinsu take kawai abin zargi ne.
Bansan yanda aka yi ba sai gani nayi mutumin ya mi茩a hannu, nan take na isa gaban shi ba shiri.
茦ur ya 茩ure ni da kallo kamar maye da munana jajayen idanuwansa da babu alamar tsoron Allah ko imani a cikinsu.
"Wannan zinaren fa? "
Mutumin ya fa蓷a yana kallon Hafsa.
"Ranka ya da蓷e abin koyi wannan ba茩ar ce data warware min aiki."
Hafaa ta fa蓷a ciki tsantar ladabi kamar ba ita ba.
Ku kashe ni da like and comment my 拼an amana.
MARYAM STAR AMANAR BILYN ABDUL.