Free chapter · Read without an account
Chapter 45
by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI
***
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
Chapter 45
Amma kuma wani sashe a zuciyarsa na sake maimaita ma shi sunanta, asalinta, ɗabi'unta da kuma zubin halittarta daya gama tantancewa tun tana ganiyar yarinta, sannan wani wawaken fili da zallar ƙaunarta marar sirki ta share a zuciyar shi tayi zaman daɓaro, kuma a nan kurkusa baiga abin da zai fidda ita ba, shi kanshi yana mamaki irin zallar soyayyar da yake yiwa Zunaina, kuma daidai da rana ɗaya bai taɓa jin soyayyar ta ragu ba, bamatada niyyar fita daga zuciyar shi gaba ɗaya ko rayuwar shi zata samu salama....
Momma Zaune take akan sofa, fuskar nan fayau babu kwaliyya ko kaɗan, kamar ba Momma matar Daddy ƴar gayu ba, fuskar nan tata ta jeme ta rame damuwar da fargabar rashin dawowar ɗanta gida gaba ɗaya ta gama tsurar da ita.
Wayarta dake gefenta ce ta yi ƙara alamar shigowar kira, sai da ta yi kamar ta share ganin Hajiya Zainab ce, se kuma ta ɗaga tare da karawa a kunne ta yi shiru tana saurare.
"Hajiya Haleem?." ta kira sunanta kamar me son tabbatarwa.
"Na'am Hajiya Zeey barka da yamma."
"Au dama kina akan layi shi ne za ki tsit, ina nan shigowa zuwa anjima in sha Allah."
Kamar Momma zata dakatar da ita, saboda a yanzun bata buƙatar zuwanta, bama ita ba bata buƙatar zuwan kowa bayan ɗanta, bata buƙatar kowa ya zo a wannan yanayin sai ta yi nasar gyara alaƙarta da mijinta.
Tana nan zaune tana tunanin dazai kawo mata nafita, bata san ta ɗauki long time ba sai da ta ji rurin mota ta shigo gidan, amma sam bata kawo a ranta zuwan Hajiya Zainab ba a yanzun ta ɗauka sai zuwa anjima zata shigo.
Murɗa handle ɗin ƙofar aka yi ta waje, tare da buɗe ƙofar aka shigo, su biyu ne amma Hajiya Zainab kaɗai ta yi sallama wacce ta caɓa aɗo cikin wani rantsasten keshi ɗan ubansu wanda ya gaji da haɗuwa, daga gefenta kuma shalelenta ce tsuke cikin ƙananun kaya wanda suka fito da surarta tar, kamar a jikinta aka ƙera kayan.
Ƙarasa suka yi ciki Nazleey na ƙarewa parlorn daya hargitse kallo tana yamutse fuska.
"Hi Mom." ta faɗa tare da ɗagawa Momma hannu takai zaune kusa da uwarta akan sofa tana taunar chewing gum.
Murmushin yaƙe Mommah ta ƙaƙalo tare da sosa kanta ta ce. "Ah wai har kun ƙaraso, ashe kuna hanga dama, sannunku da zuwa bara a kawo muku ruwa."
Ta faɗa tana niyyar tashi.
"No Mom, kawaide a fara gyara wajen yayi darty da yawa." Cewar Nazleey tana ƙarewa ɗakin kallo a yatsine.
Sakato Momma ta yi tana ƙarewa Nazleey kallo, tana jin babu daɗi har ranta kamar cin fuska ne ta yi mata.
"Wai lafiyarki ƙalau kuwa Hajiya Halima dubi yanda kike a yamutse da alama ko wanka ma baki yi ba tun tashin ki barci ko?." Hajiya Zainab ta faɗa tana ƙarewa Momma kallo up and down.
Murmushin yaƙe Mommah ta yi, tana jin duta muzanta ta sosa kanta tare da faɗin.
"Wallahi dota bayi cleaning ba na tashi bana jin daɗi, kuzo muje Up stairs sai mu tattauna a can."
Tana gama faɗin hakan ta soma kwallawa ƴar aikinta sangartatta kira wacce sam bata san aikinta ba ta saka ta tayi shara, su kuma suka ɗunguma sukai sama su duka.
Tsaidasu ta yi tare da yin wanka ta kimtsa kanta, sannan ta zauna tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta suka gaisa sama-sama.
"Gajiya na yi da jin ki tsit, ga kuma yarinyar da muka rigada muka tasota tana tsakiyar karatunta, kullum zancenta ɗaya wai yaushe Mujaheed zai zo ita ta zaƙu ta ganshi tana missing ɗin shi."
Zama Mommah ta yi cike da damuwa tana ƙoƙarin maida hawayen idonta ta ce.
"Wallahi H.Zainab ina cikin tashin hankali, yau sati guda kenan banga koda ƙafar Mujaheed a gidan nan ba, wayoyin shi a kashe, du wani waje da kika san zan iya samun shi na je amma baya can, na rasa yanda zan yi ra daina."
"Yo ina Alhaji Ahmad ɗin da zaibarki kina neman yaro?."
Nan take gaban Mommah ya yanke ya faɗi, ta soma juya sunan Alhaji Ahmad a ranta, tunaninta na maimaita ata abin da ya faru a waccan ranar, kuma da ace ta nitsar da hankalinta waje ɗaya, data jima da gane tun ranar bata sake ganin shi ba a cikin gidan, kuma da ace ta nutsu data jima da gane baya garin domin kuwa da yana nan babu yanda za'a yi ya kwashe tsayin satu baizo ya duba koda Afnan ba.
Kallon Juna Nazleey da Hajiya Zainab suka yi kowanen su da alamun tambaya ganin yanda Momma ta faɗa duniyar tunani.
"Mommah zamu wuce zanje shopping and please idan Mu Mujaheed ya dawo ki sanar min koda ace shi bai zo ni zan zo saboda ina son ganin shi." Nazleey ta faɗa tare da saɓar jakarta ta yi gaba.
Haka suka tafi suka bar Mommah numfashinta na barazanar tsayawa saboda tashin hankali, mijinta da ɗanta sun tafi sunbarta ba tare da sun damu da yanayin da zata iya shiga ba, musamman Mujaheed bata taɓa tunanin zai iya gudunta ba, nan take zuciyarta ta ƙara tsanar Zunaina tana ganin ita ce sillar komi, ita ce ta tarwatsa mata gida, tun sanda ta saka ƙafa tabar gidan take ganin jaraba da tashin hankali sanka-sanka, babban abin da yafi damunta bai wuce abin Alhaji Ahmad ke ƙoƙarin aikatawa ba na kwashe dukiyar shi ya baiwa Zunaina.....
****.
JUNAID
Driving ya ke, yana yana ƙarewa gefen titin kallo, lokaci zuwa lokaci yana saki ƙaramin tsaki, tare da duba agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa.
Baya so lokacin tashin Abeey daya barci ya yi bai koma gida ba, kuma baya son komawa gida ba tare da yayi katarin ganin abin da ya hanashi zaman lafiya ba, tunanin da kuma tunanin halin da zata kasance ya hana shi sakat, a yanzun data dage da ƙarfin tsiya ta kutso cikin rayuwar shi, baya iya taɓukawa kan shi abin kirki dole sai tunaninta ya shigo a kan shi, tun yana ƙaryata kan shi, har yanzun ya amince tun yana dannewa da nunawa kan shi hakan ba komi bane yanzun ya gasgata.
Haka ya yita walagigi a titi shi kaɗai yana kaiwa da komowa, daga ƙarshe dai ya gaji ya haƙura ya juya yana sake kalle-kallen yana driving da saka ran ko me kama da ita ya gani, amma har ya isa titin unguwarsu bai ganta ba.
Horn ya yi security ya buɗe ma shi ya danna hancin motar.
Ko gama daidaita parking bai yi ba ya ya ɓalle murfin ya fita, direct cikin gida ya nufa a gajiye, farar fuskar nan tashi data iya shanye damuwa babu fara'a ko ɗigi, kai tsayi sashen Abeey ya nufa da sallama ɗauke a bakin shi ya shiba bayan ya tura ƙofar.
"Wa'alaika salam Son." Saminaka dake jingine akan bed ya amaa sallamar da muryar shi marar ƙarfin amo.
Wani sanyi ne ya lulluɓe Junaid da ya yi tozali da mahaifinci wanda ya samu lafiya.
Cikin tafiyar shi ta cikakkun lafiyayyun maza masu tashin ƙuruciya da naira ya ƙarasa yana saka hannuwanshi cikin aljihun wandon ƙananun kayan jikin shi.
"Abiy ya jikin naka?." ya tambaya ciko sauƙaƙiyar hausar shi wacce ke fita da tajweed.
Ɗan yunƙurowa Saminaka ya yi tare da janyo hannun Junaid ya sumbata, kafin ya amsa shi da yaren larabci.
Zama Junaid ya yu sukaɗan zanta kaɗan, kafin ya haɗawa Saminaka maganin shi ya bashi ya sha, ya sake gyara ma shi wajen ya taimaka ma shi yayi wanka, ya sauya tufafi marasa nauyi masu tambarin camponyn Saminaka, ya tabbatar da babu abin da zai buƙata sannan ya juya da niyyar fita sai aka turo ƙofar, Uncle ya shigo da sallama, yana ganin Junaid ya tuntsure da dariya lokaci ɗaya yana idasa shigowa ɗakin, muryarsa ba hayaniya ya ce.
"Ah harka dawo kenan?." Ya tambaya yana kallon gefe da gefen shi, sai kuma ya sake kwashewa da dariya sannan ya ce. "Ya banganta a gefenka ba, ko har ka kaita ɗakinka ne?."
Tsuke fuska Junaid ya yi tare da raɓawa da gefen Uncle ɗin ya wuce har yana bangaje kafaɗar Uncle ɗin.
"Ouch, Yaaya kana ganin wannan giant ɗin yaron naka zai ɓallan kafaɗa." Uncle ya faɗa yana yamutse fuska alamar yaji zafin buguwar.
Murmushi Saminaka ya yi sannan ya ce.
"Na lura kai ke tsokanar shi, kumadai sarai kasan hali, baya son haka, gashi ma sha Allah da babban jiki, aikai ka sani du randa ya gotaka ko sannu bazanyi maka ba."
"Haba Yaaya na lura kamar ka fi son wancan mugun da ni, tayaya zaka cw haka bayan shi ke cin zalina, yaro yabi ya raina ni dan kawai yaga ya kere ni a tsayi."
Murmushi Saminaka ya yi, tare sa gyara kwanciyar shi jin wani sabon barcin na shirin ɗaukar shi.
Harya gifta ƙofar ɗakin, sai kuma ya dawo, yakai mintuna biyu yana tunanin ya shigo koko ya ƙara bata time, sai kuma zuwa can ya yi knocking lokaci ɗaya ya kama handle ɗin ƙofar ya buɗe amma bai shiga ba, sai ya yi cikakkiyar sallama cikin balarabiyar muryarsa me cike da kamala....✍🏻
AMANAR BILYN ABDUL CE.