Free chapter · Read without an account
Chapter 45
BIYU A ƊAYA
( Don't judge a book by its cover)
Page 45
Sayyada barrister
***
YOTA 13
The five ink legends
GHANA INTERNATIONAL HOTEL
Suna isowa airport kai tsaye hotel suka nufa, kasancewar zaman da Dr Waahab ya yi a hotel na tsawon watanni uku ya sa ya saba da manajan, kama wa bai ba shi wahala ba, sai dai wannan karon bangaren ya bambanta da na wancen lokacin ɗakuna shida suka kama, iyayensu kowa da ɗakinsa Dr Waahab kuma da Sa'eed ɗaki ɗaya. Sun huta gajiya kowannen su ya watsa ruwa ya samu nutsuwa sun ci abinci, sannan ya kira ALAJA ya sanar da ita sun iso amma sai washegari iyayensa za su haɗu da Malliman.
Da daddare suna zaune Sa'eed ya kira Suhaima a waya suna hira, Dr Waahab ya kira layin ALAJA ya ce ta haɗa shi da Angel, haka ko aka yi, tana kwance ita da Mamanta duk da ba hira suke ba amma bacci ya gagare ta, shigowar ALAJA ya sa ta tashi ta zauna, tare da cewa
"Sannu da zuwa Maa"
"Mamanki ta yi bacci ne?"
"A'a idona biyu"
"Yawwa tashi mu yi magana"
Maman Bilqees ta tashi ta zauna ALAJA ta soma magana
"To mutanen Nigeria sun iso, yanzu haka suna hotel, gobe za su sami Malliman"
Haka kurum ƙirjin Maman Bilqees ya buga, ta kalli ALAJA ta ce
"Wai har yanzu Yaron yana kan bakansa ne?"
"Ah to me za a fasa? Tun da sun iso ai aikin gama ya gama, ka ki ba ki son cire kuɗi kuma biki za ayi"
"Su suka ce miki biki za ayi?"
"Shi ne mana, su taso daga wata ƙasa su zo kuma ki ce haka, to sai ki shirya tarɓan baki"
"ALAJA wannan abun ba mai yiwuwa bane, da an hakura ma shi ya fi"
"Mene ne abin da zai hana shi yiwuwar? Kin ga kada ki kawo mana fitina a ciki"
"To ke ma kin san ba fita nake yi ba, ban san yadda zan tarɓe su ba"
"Duk wannan ki bar min a hannuna gobe ko restaurant ba zan je ba"
"To sai ki yi abin da ya dace"
"Ke cire kuɗi za ki yi, ayi mata kayan arziki, kin san daga ganin yaron nan daga gidan masu kuɗi ya fito"
"Ni ALAJA da kike cewa na fiddo da kuɗi, ina nake da kuɗi abin da suka bada na sadaki da shi za ayi amfani"
"Ke dai kika sani, Allah ya kyauta Bilqees ta shi mu je side nawa"
Ta mik'e jiki a sanyaye ta fito zuwa side na ALAJA ita kaɗai ce babu kowa a bangaren, ta zauna kan kujera, ALAJA ta miƙa ma ta wayar tare da cewa
"Yallaɓai likita zai yi magana da ke"
"To Maa"
Ta kira ya katse kiran sannan ya kira ta, ta ɗauka cikin siririyar muryarta ta yi sallama ya amsa, ta gaishe shi nan ma ya amsa tare da cewa
"Mon Ange gani a Ghana, na so na zo na ganki hakan bai yu ba"
"Sannunku da dawowa"
"Yawwa sannu mata ta"
Murmushi tayi, hawaye suka gangaro mata bata bari ya fahimci damuwar ta ba, ta ce
"Da su Babanka ka zo?"
"Eh da Daddy na, da ƙannensa da yayunsa sai da ɗan'uwana Sa'eed"
"Ayya suna lafiya?"
"Lafiya kalau, gobe zan kai su wajen Malliman"
"Allah ya kai mu"
"Ya na ji muryar ki wata kala haka?"
"Babu komai Uncle"
"Okay gobe zan zo mu ga juna"
"Allah ya kai mu"
"Amin Mon Ange"
Sun ɗan yi hira sannan su ka yi wa juna sai anjima, Bilqees ta iso ɗakin ALAJA ta miƙa mata wayar, ta ce
"Maa sai da safe"
"Yawwa zauna mu yi magana"
"To Maa"
Ta zauna, ALAJA ta ce
"Duk abin da Mamanki za ta ce kada ki yi magana, ki yi shiru har ayi auren kin ji"
"To Maa"
"Kin ga a samu ayi komai cikin tsari, gobe da kai na zan kaisu wajen Malliman"
"To Maa"
Bilqees ta fito ta koma side nasu, ta tadda Mamanta zaune, ta zaune kusa da ita ta ce
"Mamata me yasa ba ki son wannan auren?"
Sauke numfashi Maman Bilqees ta yi, ta kwanta ba tare da ta ce komai ba, Bilqees kamar ta yi kuka, ta kasa gane kan Mamanta tun lokacin da Yallaɓai likita ya ce yana so ya aure ta, ta sauya ba ki ɗaya kamar ba ita ba...
"Kin ce iyayen Yallaɓai likita sun iso?"
"Eh sun iso"
"Daga Nigeria ne suka zo har nan Ghana neman auren ki?"
"Eh Mama"
"Kina so ki yi nesa da ni?"
"A'a Mama"
"Kina so tun da ga shi har farin ciki kike yi"
"Ki yi hakuri Mama, zan ce mu tafi dake Nigeria"
"UHM"
Kawai Mamanta ta yi, shiru bata sake cewa komai ba har Bilqees ta kwanta, nan da nan bacci ya ɗauke ta...
**********************
Ghana International hotel
Tun da ya tashi daga bacci yake jin faɗuwar gaba, jiki a sanyaye ya shirya cikin riga da wando na shadda fari kal ɗinkin half jampa, ya ɗaura hula akai, ya yi kyau sosai ya tsaya gaban mirror yana ɗaura wrist watch nasa, bayan ya ɗaura ya shafa turare, ya dawo ya zauna ba kin bed...
"Likita ka iso mu ci abinci mana"
Cewar Sa'eed yana zaune kan carpet ya zuba musu abincin da aka kawo musu na safe, ya sauke numfashi ya taso ya zauna, a hankali yake iya ci, Sa'eed ya ce
"Menene duk ka yi sanyi?"
"Ban sani ba, kawai yanayi ne"
"Okay mu ci abinci"
Suna ci suna hira har Alhaji ƙarami ya leƙo ɗakinsu ya ce
"Ku fa ake jira ku fito mu tafi"
"To muna kan fitowa"
Cewar Sa'eed, suka fito suka tadda su tsaye a farfajiyar hotel ɗin suna hira, Dr Waahab yana ƙarasowa ya gaishe su cike da girmamawa suka amsa, ya yi musu jagoranci zuwa bakin titi, suka ce su ba za su iya hawan mashin me ƙafa biyu ba, sun manta irinsa, texi ya samu guda biyu suka wuce unguwar Tumbin Giwa, har bakin masallacin unguwar aka sauke su, suka sallame su, Dr Waahab ya shige ciki yana tambayar Malliman, aka ce baya nan, yanzu ya bar wajen amma ba zai jima ba zai dawo, ya dawo ya tadda su Alhaji babba a tsaye ya rasa abin cewa, Daddynsa ya ce
"Ina Liman ɗin?"
"Daddy ya ɗan fita yanzu zai dawo"
"To mu ƙarasa cikin masallacin mana"
Cewar Alhaji babba, Abbie mahaifin Suhaima ya ce
"To mu fara gaisawa da iyayenta mana"
Dr Waahab ya sosa keyarsa ya ce
"Abbie wannan Malliman ɗin shi ne wanda za ayi magana da shi"
Daddy ya ce
"A'a kai mu cikin gidansu mu taso daga wata ƙasa ba mu gaisa da mahaifiyarta ba, ko danginta ba"
Ƙirjin Dr Waahab ya buga, ta yaya zai shigar dasu Tumbin Giwa, kada su ga wani abu su hana auren shi da Angel...
"Mu je mana ya ka yi shiru"
A sanyaye ya ce
"Bari na kira Mamanta"
"To kira ta"
Ya kira layin ALAJA ya sanar da ita suna ƙofar masallacin unguwar amma Malliman baya nan, nan ta ce ya shigo dasu Tumbin Giwa ta main gate ta yi mishi kwatancen bangaren da zai kai su. Dr Waahab bai fahimce ta ba kai tsaye ya shigo dasu cikin gida, sai kalle² su Alhaji babba suke yi, da mamaki da al'ajabi ba ki ɗaya kan su ya kunce a lokacin da suka fahimci in da suke, saboda ganin ƴan wiwi da masu shan kwaya, Daddy ya ce
"Kai ina ne kake kai mu?"
"Daddy wajen mahaifiyar Bilkisu ne"
"Shi ne a cikin wannan gidan?"
Cewar Alhaji babba, Dr Waahab ya sudda kai ƙasa Daddyn sa ya ce
"Ana yi maka magana sai wani sudda kai ƙasa ka ke yi kamar mara gaskiya"
Ya ɗan tsosa keyarsa ya ce
"Daddy mu ƙarasa ciki"
"Wane irin mu ƙarasa ciki, ina ne nan?"
"Daddy za mu haɗu da iyayen Angel ne"
"What? A cikin wannan gidan?"
Dr Waahab ya sauke numfashi kirjinsa na ci gaba da buga wa, Alhaji babba ya ce
"Menene sunan wannan gidan?"
"Tumbin Giwa"
"Eh naga alama, yanzu iyayenta anan suke rayuwa?"
"Eh Alhaji babba"
"To ƙarasa da mu ciki"
Yana gaba suna biye da shi, suna iso inda ake busa wiwi da sigari, Alhaji ƙarami ya ce
"Lahaula fi shi'atillahi, wiwi?!"
"Likita an ya ka san inda kake kai mu kuwa, in dai baka sani ba, to ka tsaya ka yi tambaya"
Jiki a sanyaye ya ce
"Nan ne gidan iyayenta"
"Ah to mu anan za mu dakata"
Cewar Daddy, Dr Waahab ya ce
"Babu nisa saura kaɗan mu ƙarisa"
"Kai ba za ka mai da mu manya banza ba, wannan wane irin iya shege ne, mu za ka kawo wannan gidan"
"Ku yi hakuri mun kusa isowa"
"Sai cewa ka ke yi mun kusa isowa, sai ratsa ƴan iska muke yi muna wucewa, ka tsaya mu yi maganar fahimta"
Suka tsaya, sanya shi a gaba su kayi suna jiran ƙarin bayani, ya sudda kai ƙasa, Alhaji babba ya ce
"Ɗago ka sanya idanunka cikin namu, ina ne ka kawo mu?"
"Gidan su Angel ne"
"Kana nufin a cikin wannan gidan za me nemi aure?"
Cewar Daddynsa, ya sauke numfashi ya ce
"Gidan haya ni, anan suke zaune"
"Kai ba gidan hayaba ko gidan gado ne mu ba za mu amince ba"
Cewar Daddy Dr Waahab kamar ya yi kuka ya ce
"Wannan ɓangaren shi ne na waɗan da basa jin magana, amma ɗayan bangaren ba matsala"
"Cewa za ka yi na ƴan iska, ba wai mara sa jin magana ba, to kuwa in mu ka ƙarasa mu ka ga abin da bai yi mana ba za mu juyo"
Cewar Alhaji babba, Abbie ya ce
"Tun da mun shigo har nan ɗin mu daure mu ƙarisa cikin"
Dr Waahab yana gaba suna biye da shi, har ciki, bangaren su Angel, suna shiga kuma suka tadda ƙamain yaƙi, maza ne zaune suna shan sigari, wasu na busa wiwi, wasu na chasewa, sai kuma ƴan daru, Zee Dollers ce ke faɗa da me bakin sigari kamar yadda suke yi, don ba sa jituwa abu kaɗan faɗa, yau ma tana wanka ya shige bayi ya yi uzurin sa ya fito, shi ne ta ɗaura zani ta fito ayi wacce za a yi, cukume sa ta yi duk da vest ce a jikin sa amma hakan bai hanata ta haɗu hannun vest ɗin waje guda ba ta damke sosai tana zazzare idanu wa waje tana cewa
"Bilahillazi ka yi na farko kuma yau ka yi na ƙarshe, sai na nuna maka ƙarshen iskanci yau"
Ƙoƙarin kwatar kansa yake yi amma ya gagara, yana cewa
"Don uwarki ki cika bi, na rantse kika yaga min vest sai kin saya min"
"Don kutumar durun uwar nan sai naga uban da zai sanya ba biya"
Ta hauka ce, sai tsalle take yi, ta yage masa riga, ta yi wulli da shi ya faɗi nan ƙasa, sai zage zage ta ke yi tana zuba ruwan ashar, me bakin sigari ya taso ya yo kan Zee Dollers yana ƙoƙarin shi ma sai ya rabata da zanin jikinta ya kunyata ta kamar yadda ta yi masa amma ina ta filla a guje ta yo bayan ɓakin da suke tsaye tana cewa
"Ɗan shegiya sai ka kamani mu gani"
Ko a jikin su, sai za gaye bakin su ke yi, daga bisani ta gudu bayan mutanen da suke zaune suna busa wiwi, wani ya tashi a wajen ya tsaya tare da nuna me bakin sigari da hannu ya ce
"Kai zan sauke maka ƙwayar da ka afka yanzun, ba ka da aiki kullum sai faɗa da mata, zo ka taɓata in ka cika ɗan iska"
"Sai na rama, ni, za ta yagawa riga a bainannasi, sai na nuna mata na fita bariki, yarinya ce ita bata sanni ba ne, dubunta ma sun kasa"
Faɗa ya koma sakanin me bakin sigari da wannan mutumin, Sadeebaby ta fito tana
"Kun ishe mu gaba ɗaya kowa ya ci uwarsa, ya za ku ishe mu da hayaniya muna ɗaka muna hutawa"
"An yi ɗin sai a ɗau mataki"
Cewar me bakin sigari, aiko su ka yi masa taron dangi sai zazzaga masa bala'i suke yi...
"Jami'a kuna ganin abin da nake gani kuwa?"
Cewar Alhaji babba, Daddy ya ce
"Muna gani yaro dai yana neman ya zubar mana da mutunci"
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun"
Shi ne abin da Abbie yake faɗi a fili, Alhaji ƙarami ya ce
"Ga dukkan alamu wannan gidan karuwai ne"
Dr Waahab ya runtse idanunsa cikin tashin hankali, shi kenan zai rasa Angel, Alhaji babba ya yi magana cikin ɓacin rai
"Kai in baka da hankali mu muna da shi, wallahi baka isa ba, ka yi kaɗan ka mai da mu shashashashu, gidan karuwa za ka kawo mu?"
A hankali Dr Waahab ya buɗe idanunsa da su ka yi ja, ya kalli Sa'eed, ya kasa cewa komai, riƙe hannun sa Sa'eed ya yi alamun ka nutsu...
"Ba magana ake yi maka ba, me ya sa ka ɓoye mana asalin ta? Me ya sa ba ka faɗa mana komai ba, kasa mu ka taso daga nesa zuwa nan"
"Daddy ku yi hakuri...
"Kai ka ci gidanku da hakurin, mu juya ko zai yi yaya ne ma ya yi, babu me nema masa aure a wannan gidan"
Sun juya cikin ɓacin rai suna ƙoƙarin fitowa ALAJA ta hango su ta iso tana cewa
"Sannunku da zuwa, ya za ku koma?"
Suka tsaya, suna kallon ta, har ta ƙaraso ta ce
"Yallaɓai likita ai ba nan na ce ka kawo su ba, ɗayan bangaren ne"
"Ko saman ɓangaren ne ba za mu je ba"
Cewar Alhaji babba ya ci gaba da cewa
"Da na san nan za a kawo ba abin da zai ɗago ni daga ƙasata"
"Ku yi hakuri woo, gida ne dai me jama'a let's seat and talk"
"Idan ku za ku tsaya ni kun ga tafiya ta"
Cewar Daddy, ya yi gaba suka mara masa baya, ALAJA tana biye dasu har main gate ta sha gaban su ta ce
"You'll not go anywhere"
Suka zuba mata ido ta kalli Alhaji babba ta ce
"Daga gani kai me hankalin ne, za ka fahimce ni"
"Ba abin da zan fahimta, tsayuwa cikin gidan ma ai zunubi ne"
Malliman ya ƙaraso sanye da manya kaya, cikin kamala ya yafa hirami a kafaɗa ya ƙaraso yana cewa
"SA'ADEEY menene yake faruwa?"
"Yawwa Malliman sannunka da zuwa, ƙoƙarin tafiya suke yi"
Cike da kamala ya ce
"Assalamu alaikum sannunku da zuwa"
Ya miƙa musu hannu suka karɓa, sannan ya ce
"Ku yi hakuri mu ƙarisa cikin masallaci"
Alhaji babba ya ce
"A'a tafiya za mu yi, ba abin da za a gaya mana"
Abbie da hankalinsa yana kan Dr Waahab ganin duk ya shiga tashin hankali ya ce
"Yaya mu ƙarasa ciki mu ji abin da zai faɗa mana"
Da ƙyar suka ƙarisa cikin masallaci, ALAJA ta zauna a matakalan masallacin ta kasa ta tsare, Malliman ya ce su zauna, duk suka zauna, ya yi musu sannu da zuwa ya basu ruwa duk da a cikin ɓacin rai suke amma sun ɗan sauƙo Malliman ya ce
"Ku maza ne ba mata ba, bai dace ku yanke hukunci anan take ba, kada ku yi amfani da abin da idanunku suka gani"
"Amma dai kasan muna da hankali da idanu, kuma komai a bayyane yake"
Cewar Alhaji babba, Alhaji ƙarami ya ce
"Yanzu kai Malami da kai me ye haɗin ka da gidan karuwa"
"Wa'iyazibillah kada ka yanke min hukunci bawan Allah, ni da kake gani taimakon su nake yi"
"Kaga malam wannan zaman amfasa shi mu gobe ma za mu koma ƙasar mu"
"Ba ayi haka ba, ku yi hakuri mu tattauna, neman aure ya kawo ku saboda raya sunnar ma'aiki"
"Wannan bai san me yake cewa ba, gidan karuwai fa tumbin Giwa ko Tumbin raƙumi ne kai ku Tumbin kura ce mu babu ruwan mu, shi ne ka ke cewa raya sunna"
Cewar Daddy, ALAJA da take waje tana jin me suke cewa ta leƙo ta ce
"Wa ye yake aibata min gida, wannan gidan na gade shi ne tun kakana, kuma haya nake bayarwa ko ku kuke so zan baku kafin ku tafi"
"Allah ya sawwaƙa ba ki gaji gida ba wallahi, tuff"
Cewar Alhaji ƙarami ta kama ƙofar shiga masallacin tana haƙi ta ce
"Kai tun da na sauke idanuna kan ka na tabbatar baka da kirki"
Ta maƙe salasalan cinyoyinta da hannye biyu, Malliman ya bada izinin a kawo shimfida Alaja ta zauna, aka kawo ta shigo ta mik'e ƙafafunta ta ce
"Mu ba mutanen banza bane, Bilqees yarinya ce wacce muka bata tarbiyya, so, never judge a parson according to the way he or she looks neither the dressing code nor on anything"
"But your dress definitely define who you are"
Cewar Alhaji ƙarami, ta nuna shi da yatsa har damtsinta yana rawa saboda cika ta ce
"Kai ma ba mutumin kirki bane tun da baka da mutunci, kada ka kaini bango"
Alhaji babba ya ce
"Ka yi shiru mu saurari Malam"
ALAJA ta yi murmushi ta kalli Alhaji babba ta ce
"Ai kai kam mutumin kirki ne, baka da matsala, you look gentle"
Alhaji babba ya sauke numfashi ko kallon inda take bai yi ba, ya bai wa Malliman hankalin, Malliman ya ce
"Har ga Allah zan faɗa muku gaskiyar abin da na sani a matsayina na malami, wanda yake shugaban cin wannan unguwar a inda nake zaune na aurar da ƴan mata a Tumbin Giwa sun fi a kirga, kuma Alhamdulillah muna ci gaba da yin haka, wannan baiwar Allah da kuke gani haya take badawa kuma duk waɗan da ke cikin gidan suna biyanta kuɗinta, Bilqees tamkar ƴa ce a wajenta ita ta ɗauki nauyin karatun da tun daga matakin primary har ta yi karatu na gaba da secondary, Bilqees marainiya ce, tun tana ƙarama aka zo da ita saboda rashin mahaifi suka kama gida anan, tabbas ba a cikin gidan nan aka haife ta ba, zuwa da ita aka yi Mamanta mutuniyar kirki ce, kuma haya suke biyan Alaja yaron ku ma shaida ne kwanaki ya biya musu kuɗin haya ma"
Suka kalli Dr Waahab da ya sudda kai ƙasa, Alhaji babba ya ce
"To mun ji bayanin ka Malam, ba mu san me ubangiji yake nufi ba da wannan haɗin, mu gaskiya auren family mu ke yi saboda yaro ya tada hankalinsa ya sa muka taho nan nema masa aure, amma tsarin gidan maganar gaskiya ya ɗaga mana hankali, ko yaro mara gata ba za aso ya nemi aure a wannan gidan ba balantana Waahab, za mu tattauna sakanin mu a ba mu waje"
ALAJA da ƙyar ta mike sabar ƙiba ta ce
"Wallahi na rantse da Allah Bilqees ba ƴar iska ba ce, ko a lahira zan bada shaidar haka, in kuma ƙarya na yi Allah ya tsene min"
"Tsinuwa ta nawa? Wacce kuma kike nema"
Cewar Daddy, Malliman ya ce
"A'a kada ka faɗi haka, baka san ita wacece ba a wajen ubangiji"
Alhaji babba ya ce kada a sake yin magana, Malliman da ALAJA suka fice, aka barsu sun fi minti talatin suna tattaunawa sai goge zufa suke yi da ƙyar suka yanke shawarar za su karɓi Bilqees a matsayin surka, Dr Waahab farin ciki kamar ya yi yaya.
Suka sanar da Malliman sun gama ya shigo, ALAJA ta shigo ita ma ba za ayi babu ita ba, Alhaji babba ya ce
"Shikenan, mun yanke shawarar za ayi auren, amma in zai yu mu ga yarinyar da Mamanta saboda kore shakku"
ALAJA ta wuce ciki Tumbin Giwa saboda kiran Bilqees da Mamanta, su kuma suka zauna zaman jiran fitowar su...
_____________________
Ayi hakuri da typing errors
Na gode sosai fan's da kira da kuma addu'oi kada ku damu labarin yanzu aka fara.
Comments and share fisabilillah