Free chapter · Read without an account

Page 25

by khadijah danasabe · TASWIRAR KADDARA

*TASWIRAR KADDARA*



   DijahAM(Oum Amani)




Page 25






BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM





  Duk mutanen palourn zuba masa ido sukai, ganin haka yasa shi mikewa a hankali ya durkusa a kusa da Abba yace "don Allah ku yafe min kuskure ne da sharrin zuciya so daya na taba yi ashe hadda rabo"



Baffa ne yace "meye haka kuma"



Juyo wa yai ya kalli Baffa yace "lokacin nima kuruciya ce ke damuna, amma na gane kuskure na tun daga lokacin ban sake ba, ku yafe mun don Allah”



Kallon Abba yai yace "don Allah ku yafe min, Allah ya jikan Khadija ya gafarta mata."



Wani murmushi Abba yai tun daga lokacin da yaron ya fara magana yake karantar sa tabbas wani abu ya darsu a zuciyar sa amma ya gyada kai yace "bkm nidai na yafe ma kuma itama Khadijan tace ta yafe, zan yiwa mamanta magana itama nasan zata yafe din insha Allah."



Baffa ne yace "Alhamdulillah, dama haka muke so amma tabbas Ka cika mahaifi na kwarai ba ko waye bane za'a ma diyar sa wannan abun amma ya yafe lokaci daya da alama itama Khadijan tana da kyaun Hali, Allah y jikanta"



Sai da aka Kara godewa su Abba akan yafiyar da sukai sannan Baffa yace "in ba damuwa ina nemawa Azlan auren babar Mimin Batul"



Da sauri Abba ya kalli Baffa sai kuma ya kalli su kawu Nasiru.



Azlan ma dagowa yai ya bude baki zai magana Baffa ya zare masa ido dole yai shiru.



Kawu Nasiru ne yace "zamu yi magana akai insha Allah Baffa, duk yadda muka ce zamu Kira ku".



Murmushi Baffa yai yace "Allah yasa muji alkhairi".



Mikewa Azlan yai ya fita yana sakin wani makirin murmushi ransa fess....





Bayan tafiyar su Baffa kallon Kawu Nasiru Kawu Kabiru yai yace "Yaya ya kuke gani ynxu nidai bansan Mai zance ba"



Murmushi kawu Nasiru yai yace "da alama gidan dattako ne, kuma a yadda yaron ya bada hakuri yana da hankali kamar, sannan bayan wannan hakan da za'a yi shine rufin asirin Mimin kaga zata tashi cikin dangin mahaifin ko dan sbd gaba, sannan kaga da alama baza a iya raba batul da Mimi ba don haka duk lokacin da ita Batul din tai aure ta tafi da Mimi gidan aurenta ko shi mijin bai goranta ba a cikin dangin sa sai an samu wani yayi".



Gyada kai Kawu Kabiru yai yace "tabbas haka ne Yaya kuma kaga ita Mimin ko auren ta aka tashi sai an samu Wanda ya ce ba mijin Batul ne mijin taba kaga dole a binciko dangin Mahaifin ta, amma in suna tare da Mahaifin nata komai zai tafi lafia insha Allah"



Kallon Abba sukai da tunda suka fara magana baice komai ba amma fuskar sa dauke da murmushi sannan Kawu Nasiru yace "bakai magana ba kai ya kagani"



Yalwataccen murmushi Abba yai yace “hakan shine daidai Yaya amma zan same su na fada musu tukun aji ta bakin yarinyar, sannan kaga sai na fadawa Yusuf shima tunda ya nuna yana son Batul din da aure"



Sai da suka kara tattauna wa sosai sannan kowa ya shige gida don fada ma iyalin shi bayyanar mahaifin Mimi.



Lokacin da Abba ya shiga gida tuni Aisha ta soma fesawa Umma duk abinda ya faru a gidan baffa, Sawa Abba yai aka Kira masa Batul sannan yafada musu komai har ma da auren da suke so a basu na Batul



Da sauri Batul ta kalli Abba tana hawaye tace "Abba aure na kuma?"



Daga kai Abba yai yace "hakan shine rufin asirin mu da na Mimi, zata tashi tare da mahaifin ta kema baki da fargabar komai akan dangin mijin ki wata ran zasu iya miki gori"



Kuka na fashe dashi nace Abba "don Allah kayi hakuri wallahi na tsane sa"



Shiru Abba yai yana tunani kafin ya kalli Umma data ke kallon Batul kamar ta make ta murmushi kawai yai yace "tunda baxa ki iya ba Batul, Aisha ke zaki aure sa?"



Da wani irin sauri Batul ta dago ta kalli Abba kirjin ta na wani irin bugawa tace "Aisha kuma Abba sai ta auri Mr Wicked?"



Gyada kai Abba yai yace "tunda ke baxa ki iya auren sa ba Batul ina jin kunyar nace ma tsohon baxan iya basa jinina ba sai na bawa Aisha kawai"



Mikewa nai ina kuma fashewa da kuka na shige daki, dukkan su da kallo suka bini sannan Abba ya kalli Umma, ciro wayar sa yai yace ma Yusuf yana son ganin sa, mikewa yai yace ina zuwa ku jira ni anan Zan dawo na muku bayani.



Yusuf bai dau lokaci ba ya iso, tare da Abba suka tafi babban gida sun dade suna tattauna wa kafin Abba yace "zan fada ma lokacin da za'a tsayar da ranar bikin sai Ka fadawa magaba tan Ka, tunda so nake a hade bikin gaba daya kuma Aisha bata gama secondary school ba wannan shekarar dai zata gama"



Sunkuyar da kai Yusuf yai cikin kunya yace "ngd sosai Allah ya kara girman"



Mikewa yai ya fita fuskar sa dauke da murmushi, sai da suka kara tattauna wa sannan Kawu Nasir ya Kira ya fada ma Baffa sun yadda sai dai kuma ga abinda Batul din tace shima dai sun dade suna magana kafin ya kashe.



Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace "Alhamdulillah"



Da ya koma gida har lokacin Umma da Aisha suna zaune sai maida maganar suke, Zama yai ya musu bayani gwari gwari sannan ya umarci Umma ta same sa a daki da kwai maganar da zasu karasa.



Ran Umma fess ta bi bayan Abba Jin ta take cikin farin ciki auren Yaya Mata biyu lokaci daya ba tare data kawo ba, gasu tana aurar dasu ba wata a gabanta ai abin a mata murna ne.



Ina kwance sai dai na daina kukan sai tunanin wai Abba zai bawa Mr Wicked Aisha ne kawai yake damuna a raina”



Dagowa nai jin shigowar Aisha, kallon ta nai naga sai murmushi take da sauri na mike nace “Aisha wallahi kar ki yadda mutumin nan ba na kirki bane mai zaki yi da shi Allah kar ki soma yadda, shine fa yayi wa Khadijata fyade”



Zama Aisha tai t tace "Ya Batul me yasa, kuma ai Ya Khadija ta yafe masa su Umma ma duk sun yafe masa. yana kama da Mimi fah sosai baki gansa ba mai kyau in na same sa matsayin miji ai na haye wallahi."



Tsaki nai nace "baki da hankali ke ana maganar hankali kina wani hauka meye kyau kuma, dallah ki nutsu ki gane mana bashi da hali mai kyau Dan iska ne"



Da Sauri Aisha tace "nidai Ya Batul ki daina iskanta min shi, kuma Abba har sun Kira Baffa sun fada masa cewa ke kince a'a amma ni sun bashi ni"



Da sauri nace "Mai Baffan yace"



Murmushi tai tana janyo dankwalin ta tace "murna sukai sukai godia, Abba ya fada musu dai kema dama da wanda kike so sai a hada bikin lokaci daya"



Zaro ido nai nace "ni kuma waye Wanda nake so din?"



Kallona tai da mamaki tace "Ya Yusuf mana, Abba ma ya fada masa shima ya shirya ina gama secondary school za'a yi biki ynxu dai zasu tsayar da rana kinga saura wata 5 mu fara WAEC lokacin kema kin gama second semester dinki kawai sai musha biki"



Kasa magana nai sai binta da kallo kawai nake sai iyayi take tana yafa mayafi a saman kai irin matan auren nan..









********

Kallon Azlan Mami tai da kansa yake kasa, gaba daya ta kasa yarda cewar Azlan ne zai aikata wannan abun sai dai kuma hujjojun da suka bayyana da kuma yadda ya amsa da kansa yasa bata da yadda zatai.



Mama kuwa ba karamin farin ciki tai ba ko bakomai wani tabo ya shafi Mami jikarta ta farko shegia ce.



Cikin nutsuwa Uncle Mustapha yace "har aure Baffa ya karbo masa na maman yarinyar, duk da an samu matsala amma sun mana bayani yace duk lokacin da muka shirya asa rana."



Cikin fushi Mummy da tunda aka fara maganar take tunanin halin da yar ta zata shiga tace "amma kawai sai a nema masa auren ta, bayan bama ita ce ta haifi yarinyar ba"



Baffa dake kallon ta yace ko "banyi daidai bane uwata"



Da sauri Mummy tace "ba haka nake nufi ba Baffa amma a duba, shi baya ra'ayin auren yarinya kuma tun tuni ake binsa da zancen Zainab yana botsarewa ynxu ya zata ji Baffa don Allah" ta karashe cikin rawar murya.



Shiru Baffa yai yayinda Abie yace "Baffa a duba lamarin gaskia kodan sbd Zainab din kowa yasan tana son Azlan"



Da sauri Azlan yace "Abie don Allah kuyi hakuri wallahi horon ya min yawa taya za'a bani mitsilar yarinya kuma azo ace za'a hada ni da Zainab wallahi hauka zan fara inaga, gurin wa zanje na sauke budurcina....."



Make masa baki Abie yai yace "kar na sake jin Ka ambaci budurci ko ranka ya baci"



Murmushi Baffa yai ya kalli Azlan ya ce "Allah ya baka ikon yin adalci a tsakanin matan naka da Zainab za'a hada ayi auren rana daya zaka angwance da Mata biyu Insha Allah nan da Wata bakwai"





***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol