Free chapter · Read without an account

EP___________8️⃣

by SultyWrites · QADDARARREN AURE

🕊️ DESTINED MARRIAGE 🕊️



*HAUSA EDITION*



🕊️ QADDARARREN AURE🕊️



          SWRITES 
              A-K-A 
     YOUNG WRITER✍🏻




بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ

 وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوٓا۟ إِلَّآ إِيَّاهُ وَبِٱلْوَٰلِدَيْنِ إِحْسَـٰنًا ۚ إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِندَكَ ٱلْكِبَرَ أَحَدُهُمَآ أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُل لَّهُمَآ أُفٍّۢ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُل لَّهُمَا قَوْلًۭا كَرِيمًۭا

For your Lord has decreed that you worship none but Him. And honour your parents. If one or both of them reach old age in your care, never say to them even ugh nor yell at them. Rather, address them respectfully.




EP___________8️⃣



Karɓar wayar Faryal tayi ta amsa tana faɗin, "Yanzu nake tunanin kiranka inji ko kun isa gida lafiya".

"Ni kuma kira nayi inji Allah yasa ruwan nan bai saki mura ba".

Murmushi Faryal tayi kafin ta ce, "Na gode da kulawa Fayyad, ina lafiya alhamdulillah babu abin da ya same ni".

"To Alhamdulillah, wannan shi ne abin da nake son ji dama. Amma dan Allah nan gaba ki tabbatar da lafiyar motarki kafin ki fita da ita. Kin san fa mata ba su iya magance matsalolin mota".

"Wlh you are on point Fayyad, mu da ko faci tire tayi bamu iya canza spare, ballatana kuma wata babbar matsala".

"Ke da kika san gaskiya kenan, amma da Manira ce ai da yanzu ta musa".

Yar dariya tayi kafin ta ce, "Ai matsalar Manira daban take".

"Na sani ai". Haka suka cigaba da hira kusan mintuna goma kafin daga bisani ya ce, "To kyakkyawa, zan je in ɗan yi wasu ayyuka yanzu. Kin ba ni izinin tafiya?".

Yar dariya ta yi kafin cikin sigar zolaya ta ce, "Ummm a'a, ban ba ka izini ba".

"To shikenan, barin cigaba da zama har sai kin ba ni izinin tafiya, ranki ya dade".

Kayataccen Murmushi ta sake saki kafin ta ce, "Wace ni. Kaga iyi tafiyarka kawai. Take care Okay".

"Thank you Ma'am. In sha Allah, and you too".

"Okay sir". Ta amsa masa cikin sigar da ya mata maganar kafin suyi Sallama ya kashe.

Ta kalli Hadiyyah tana ɗan murmushi ta ce, "Will I believe your realization Hadiyyah?".

Hadiyyah dake ta faman smiling tana kallonta ta gyara zama tare da faɗin, "Ai dolen ki ma ki yarda, ko ba da hasashena ba, but a lokacin da shi da kansa zai furta miki abin da ke zuciyarsa".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta danna kiran Barr. Hashim dan bin bayan kiran da ya yi mata. Tana yin ringing ɗaya ya amsa, bayan sun gaisa ya ce, "Ai na kira ba ki ɗaga ba, nace to kar na dameki. Maybe kina wani uzurin ne".

"Eh whl, Ina ƙoƙarin amsawa kiran ya katse, ina ƙoƙarin maida ma kiran kuma sai aka kira ni".

"Oh Eyyerh, ba damuwa, na fahimta. So how was today's work? Ya ruwa kuma?"

"So far so good, Barr".

"Masha Allah. May Allah bless you, protect you from all harm and make you among the successors".

"Ameen, Ameen ya Allah Barr, na gode ƙwarai da addu'a, and I wish you the same".

"Ameen Faryal. Ai kin cancanci hakan ne, Wonder woman ba".

Tayi ɗan murmushi kafin ta ce, "To yaya aikin naku ku ma?".

"Normal, Alhamdulillah, we are managing".

"Allah ya taimaka, Ya kuma ba ku ikon yin adalci daidai gwargwado".

"Ameen ya Rabbi. Emm Faryal?".

"Na'am, Barr".

"Nace ba, idan ba zan takura ki ba, send me your address. Ina son in zo mu gaisa, ayi zuminci, fatan ban zaqe da yawa ba?".

"A'a Barr. You don't. Babu matsala, zan tura maka In sha Allah."

"Alryt to nagode sosai".

"Don't mention".

"To, bari na bar ki ki huta haka. Good night, have a sweet dreams".

"Same to you Barr.". Daga haka sukayi sallama ya kashe.

Ajje wayar tayi ta kalli Hadiyyah tare da faɗin, "Yww ke, za ki raka ni birthday party ɗin Walida?".

"Yaushe?"

"Gobe ne around 7 wai".

"Ummm, bari in gani dai. Idan Abubakar bai ce zai zo ba, sai mu je".

"Ikon Allah. To ba za ki iya sanar da shi zaki fita ba ne? Ni dai ki faɗa min tun wuri, dama gate pass ne dani guda daya, in baza kije ba in san wa zan bawa".

"Ehh tou, as long as he's coming, kasancewa tare da shi ya fi mini muhimmanci fiye da rakaki birthday ɗin ƙawar ta ki".

"Ehh lalle, tou gaya min magana kin ji".

Dariya Hadiyyah ta yi ba tare da ta ƙara cewa komai ba.





***           ***          ***




Washegari, bayan ta je Company ta gama abinda zatayi sai kawai ta wuce brand ɗin ta domin duba yadda abubuwan ke tafiya acan ɗin. Sai da ta tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai, kafin ta wuce gidan wata friend ɗin ta data bata order haɗawa Walida birthday gift, ta karɓa sannan ta wuce gida.

Sai da tayi parking ɗin motarta a parking space, sannan ta lura da baquwar motar dake pake a wurin wadda ta kasance mallakin paternal Uncle ɗin ta. Wani gauron numfashi ta ja, dan ta san ba daɗi ke kawo yan uwan Appahn nasu gidansu ba.

Fitowa tayi daga motar ta wuce cikin gidan. A main falon ta tarar da iyayen nata tare da babbar yayar su Appah da kuma ƙaninsa, sai Hadiyyah dake zaune a kan rug kanta a ƙasa.

Sallama tayi, sannan ta ƙarasa shiga falon tana gaishe da yan uwan Mahaifin nata.

Maama ce ta amsa sallamar yayin da yayar baban nasu, wadda ke zaune, cikin yanayi na ɓacin rai ta ce, "Ke wato ubanki ya mara miki baya, kin tsufa a gida sai gantali da sunan aiki ko?".

"Haba Yaya Turai, Faryal fa ita ce babbar yata. Tun da bani da babban ɗa namiji, dole ita ce zata gaje ni. Ita ce za ta taimaka wajen kula da ƙannenta. And moreover shekarun Faryal dududu nawa ne, gabaɗaya fa ko 24 bata kai ba...".

"Rufe min baki Hafiz. Idan kai matarka ce take juya ka, to mu ba ta isa ta juya mu ba. Ta yaya za ka bar yan mata haka zagada zagada a gidanka ba aure? Yanzu ko Hadiyyah da an mata aure da wuri ai da tuni yanzu watakila tana da yara biyu, ballantana kuma Faryal. Amma ka yi shiru ka zuba musu ido kana kallonsu. Basu da masoya ne? Ko kuwa kyawun nasu na yawo daga wancan kwararo zuwa wannan kwararo ne kawai?".

"Ki yi haƙuri Yaya Turai, In sha Allah za a gyara". Maama da bata jin daɗin kalaman da yaya Turai ɗin ke jifan ya'yan nata dasu ta faɗa.

"Ai ke Sharmila, ba ki da abin faɗa. Dan kamar hoto kike a cikin gidan nan. Sam ba ki cancanci zama uwa ba, saboda ba kya sawa yaranki ido yadda ya kamata. Idan shi mijinki ɗan kasuwa ne, ba ya samun isasshen lokacin da zai kula da tarbiyyar yaran, to mene ne amfanin auren macen ta gari? Ba don ta zama uwa ta gari ba ne? ta kula da gidanta da yaranta? To amma ke ba ko ɗaya".

Ta juya ga ƙanin nata, wanda ya kasance qani ga mahaifin su Faryal ɗin Kafin ta ce, "Kamal, me ka ce ka gani jiya?".

Gyara zaman hularsa yayi kafin ya ce, "Faryal na gani tare da wasu samari har biyu, ta shiga motarsu sun tafi".

Yaya Turai ta kalli Faryal ta ce, "Ke! Kalli cikin idona, shin haka akayi?"

"Ai Yaya Turai, ba za ta taɓa faɗar gaskiya ba". Kamal ɗin ya faɗa yana hararar Faryal.

Ita kuwa Faryal bata bi ta kan maganar kawun nata ba, kai tsaye ta ce, "Eh Hajiya, haka ne. Motata ce ta tsaya a hanya, ina neman taimako sai suka zo wucewa shi ne suka tsaya suka rage min hanya kuma dama ɗaya daga cikin su friend ɗi na ne".

"Ka ji ko? ka ji dai da kunnenka. Shin kuna sane da wannan?". Yaya Turai ta tambaya tana kallon Appa da Maama.

"Eh Yaya Turai, ta fada mana. Kuma ai ba wani abu ba ne tun da abokinta ne, ta sanshi". Appa ya faɗa.

"Qalu innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Hafiz, haka ka koma? To, idan kai ba za ka iya shawo kan wannan lamarin ba, ni zan shiga ciki. Ba zai yiwu a dinga zagin mu a dangi ba saboda ya'yanka. Ku!". Ta nuna Faryal da Hadiyyah.

 "Zan ba ku wata ɗaya kacal. Ku fito da mazajen aure, domin idan iyayenku wawaye ne, ni ba zan zauna mu cigaba da sa muku ido ba. Kuna ji na?".Ta ƙarashe tana kama kunnenta.

Faryal da Hadiyyah suka gyada mata kai ba tare da sun ce komai ba, yayin da Yaya Turai ɗin kuma ta juya ga Kamal ta ce, "Kamal, tashi mu tafi".

"Allah ya tsare hanya". Maama ta faɗa a sanyaye.

Appa ya kalle su bayan yaya Turai da Kamal sun fita, ya ce, "Ku tashi ku shiga ciki, kar ku damu".

Da to suka amsa sannan suka tashi suka bar falon, Maama ta kalli Appa kafin ta ce, "Hafiz, kana jin abin da Yaya Turai ta faɗa?".

"Rabu da ita, na san yadda zan magance matsalar. Kamal ne fa yake tunzura ta takeyin duk waɗannan abubuwan".





***          ***          ***




 Riqo hannun Faryal Hadiyyah tayi bayan sun shiga ɗaki, cikin damuwa ta ce, "Faryal, kin san abinda wannan matar za ta iya yi. Yanzu menene mafita?".

"Ban sani ba Hadiyyah. Ke kin ma yi sa'a, Abubakar na tare da ke. Ni kuwa har yanzu ba kama kowa ba".

"Ke kuwa kika kama kowa Faryal. Dan idan akwai wanda ya cancanci samun ki, to Fayyad ne".

"But Hadiyyah, ba na son sake maimaita kuskuren da na yi a baya. Fayyad hasn't proposed yet, sannan..."

"Sannan me Faryal? Ai kawai ki fara canza yanayin mu'amalarku, yadda yake nuna miki kulawar nan, ke ma ki fara nuna masa. I promise you he will propose soon, because he's just waiting for the signal opportunity to do so. And da zarar ya yi hakan, sai ki gaya masa cewa mahaifinki ba zai amince da dogon soyayya ba tare da wani tsayayyar magana ba. Dan haka yaje ya gabatar da kansa ga Appa. Yayin da yayi hakan kuma, na san Appa zai sanar dashi in har da gaske yake to ya sanar da iyayensa, manya su shiga Maganar.

Ni ma kuma kinga zan nemi Abubakar mu tattauna kan Maganar, kinga da zarar magana ta koma hannun iyaye, na tabbata Yaya Turai ba za ta sake takura mana ba har na samu na kammala karatuna. Ke kuma idan Fayyad ya shirya, sai kuyi auren ku kawai, tunda dama a shirye kike".

Wucewa Faryal tayi ta zauna a bakin gadon yayin da Hadiyyah ta ci gaba da yi mata bayanin yadda ya kamata su yi dan magance matsalar tasu, har akayi kiran sallar Magriba.

Sallar sukayi sannan suka shirya dan tafiya wurin birthday ɗin. Fita suka yi inda suka isko mahaifiyarsu a ɗakin Daadee suna magana. Nan Faryal ta shaida mata za su je birthday ɗin Walida ne.

"To amma kar ku daɗe. Kun san fa yanzu idanu sun dawo kanku".

"In sha Allah Maama, ba za mu daɗe ba". Faryal ɗin ta faɗa.

"Shikenan, ku dawo lafiya". Juyawa sukayi zasu fita, Maama ta sake kiran Faryal ɗin.

Tsayawa tayi tare da juyowa tana amsawa da, "Na'am Maama".

"Yaya Hamdan kuwa?".

Faryal ta kalli Hadiyyah kafin ta ce, "Yana lafiya".

"Na lura kwanakin nan duk ba'a mana zancen sa, nace to ko lpy".

"I don't know about him anymore Maama". Kamar Maama zata sake cewa wani abu, sai kuma ta fasa. Ta ce, "To shikenan, ku je kar dare ya muku".

Da "To". Suka amsa sannan suka fice.

Sai da suka fito harabar gidan, Faryal ta sauke nannauyan ajiyar zuciya, tare da furta, "Huhhh!".

 "Hmm, ai Hamdan ya riga da ya yi wasa da damar sa. Ba za ma su yi mamaki ba sai ranar da kika gabatar musu da Fayyad a madadinsa".

"Hmmm". Shi ne kawai abinda Faryal ɗin ta faɗa, sannan ta shige motar Hadiyyah da zasu fita a ciki, suka bar gidan.

Haka suka isa wurin da Alhaji Barau Ido Naira ya shiryawa Walida haɗaɗɗen birthday party.

Babu wani isasshen haske sosai, dan irin disco lights ɗin nan ne kawai, kallon mutanen dake kai komo a wajen sukayi, gabaɗaya babu wanda ke sanye da kayan kirki. Haka dai suka ƙarasa suka nemi wuri suka zauna.

Hadiyyah ta kunna fitilar wayarta, yayin da Faryal kuma ta kira Walidan. Ko da ta ɗaga, akwai hayaniyar mutane sosai a inda take, dan daƙyar ma ta iya jin tambayar da Faryal ɗin ta mata na yaushe zata zo wurin?

"Kin gan mu a harabar wurin, ki fito kawai sai mu shigo tare".

"Okay". Faryal ta faɗa kafin ta katse wayar ta miƙe.

Riqo hannunta Hadiyyah tayi tare da faɗin, "Faryal, gaskiya I'm not comfortable with this environment. Kar ki je, mu jira ta a nan ɗin kawai".

Faryal ta sauke ajiyar zuciya kafin ta koma ta zauna. Daidai lokacin MC ya fara sanar da isowar ta, kafin wani lokaci ta shigo tare da tawagarta maza da mata. Suka raka ta zuwa kujerar da aka tanada mata, sannan kowannensu ya nemi wurin zama.

Sai a lokacin Faryal ta miƙe ta nufi kan stage ɗin, a kusa da walida ta zauna dake kujerarta ta two seater ce.

Cikin sigar zolaya Walida ta ce, "Na ce ki fito mu shigo tare, amma kika ƙi kamar wanda zan sace ki". Ta ƙarashe idanunta akan Faryal ɗin.

"Sorry friendzo. Ina tare da Hadiyyah ne, kuma ba na son in bar ta ita kaɗai shiyasa".

"Oh haba? Ina take?".

"Gata can". Faryal ta faɗa tana nuna mata inda Hadiyyah take zaune. Hira suka shiga yi na wasu yan mintuna kafin Faryal ta ajiye mata gift ɗin, ta bar wurin.

Bayan an yi yan ciye ciye, aka kunna full light saboda me Birthday da zata shigo tsakiyar fili.

Hadiyyah ta kalli kofunan da kwalaben da ake kai wa wasu particular tables ɗin kafin ta kalli Faryal ta ce, "Faryal, ya kamata mu tafi. Wannan fa ba birthday party ba ne, club ne! Alcohol a birthday party? Aaa inaa, tashi mu bar wurin nan".

"Alcohol kuma?" Faryal ta tambaya cikin mamaki.

"Eh, duba can". Ta faɗa tana nuna mata wasu ma'aikata biyu da ke ɗauke da serving tray sun ɗauko tumblers da kwalaben alcohol.

Kafin Faryal ta samu damar Maganar, Hadiyyah ta sake cewa, "Ya kamata mu tafi. Kin san abin da Maama ta gaya mana kafin mu fito ko? Don haka muje kawai".

"Innalillahi, wlh Hadiyyah, ban san abinda Walida ta shirya kenan ba. Da na sani ai da sai dai in bata excuse, yaso washe gari na kai mata gift ɗin a gida". Ta faɗa tana tashi, Hadiyyah ma ta miqe.

"Barin je na mata Sallama in zo mu wuce". Faryal ta faɗa kafin ta nufi tsakiyar filin inda Walida ke rawa, maza na mata watsin naira. A daidai lokacin ne kuma MC ya fara sanar da kyautar GLK ɗin da aka bawa me Birthday.

"Hmmm". Kawai Faryal ta faɗa tana mamakin wannan rayuwar. Ko da ta ƙarasa wurin kamo hannun Walida tayi ta ja ta gefe tana faɗin, "Walida, mu za mu tafi. Maama ta ce kar mu daɗe".

"To Faryal. Na gode sosai, i truly appreciate. Kun ci abinci kuwa?".

"Eh, Alhamdulillah".

"To, shikenan. Sai mun yi magana ko".

"Alryt bye". Faryal ɗin ta fada tana juyawa domin barin wajen.
Sai dai tana ɗaga idanunta, suka sauka kan abun da ya sa ta dafe ƙirjinta cikin tsananin mamaki.

Wani mutum ne yake tafe yana rangaji ya nufo tsakiyar filin, kana ganinsa kasan ya gama buguwa yayi Makil.

Da sauri Faryal ta canza hanya domin kauce masa, ta nufi inda Hadiyyah ke tsaye tana jiranta.

Riqo hannunta tayi a firgice tace, "Hadiyyah! Kin san wa na gani kuwa a bige yanzu?".



TIRKASHI 

READERS, WHO'S THE MAN FARYAL SAW INTOXICATED? 🤔 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol