Free chapter · Read without an account
Riya Chap 10
by Quenneriya · Riya
Meye tsakaninki da Abdul … ina nufin Ustaz dinku….
Riya tayi jimm…. sai ta fara kame kame
tana fadan am … umm.. ba .. bah komai kaway dai Riya tayi shuru dan kuka ya kwace mata cikin tashin hankali da damuwa
tace … Wallahi Allah mallan shi ya fara cewa yana sona….
kuma nidai dama tun fari saida nace za’ayii min fada…indan Abban mu ya sani!!!
ta karasa maganar vikin kara wa wa sawtin kukan da take volume….
mallan ya dan kwalleta yace …Ok ya isa haka na yarda da abinda kika fada amma zan fada miki wata magana…yanzu..
dede nan aka bude kofar office din aka shigo abdul ne!!! sanye yake cikin yadin marron dinki doguwar riga da wando…
yayi gaisar da Mallan din sanan ya kwalli Riya hankalinshi yace ???
kaii lafiya kike wanan kukan haka kamar wanda akayi wa rasuwa ???
koh bakida lafiya ne ???
ya karasa tambayarta yana kwallanta kamar zai riko hanunta dake ran fuskarta …
Mzlkan yace wa Abdul barnan da kayi itace nake gwarawa …..
kaii yanzu kasan komai kasan irin alkawarin da mahaifinka yayiwa yayar lu amma shineh daga zuwa har ka fara soyeya da yar mutaneh…. ni nasan kule kulen mata bah halinka bane amma niyasa kace kana sonta ????
jikin Abdul yayi sanyi yace yace nifah uncle Gaskiya banason Baddiya kuma tub cen saida na fada !!!! yanzu kuma riya nake so
mallan yace wanan kuma mahaifinka zaka fadawa tun kan azo nan bani bah da aka bawa izinin yi maka aure Idan lokacin da muka baka ya cika kuma kah fadawa yarinyar mutane gaskiya kan cewa an Riga da an sa maka Rabar aure da yar uwar jah sanan bah wata wanda zaka kuma aure insha’Allah koh nan da shekaru masu zuwa dan kasan akan me?? nake magana !!!!
Mallan ya kwalli Riya yace mata abinda zan fada miki anan shineh !!! Shi abdul inan da kike gznin an riga da anyi mishi mata tun tunni ah family mu sanan na fada miki Gaskiya ne saboda
mutunci dake tsakanina da Abban ki sanan , kar sai anzo abu yayi nisa kuji haka,
ki jai ki fita daga hanyar sa idan yaci gaba da miki magana ki sanar dani kinji
kuma ba zan fadawa abban ki bah …
tashi ki tafi aji !! !
Riya ta mike dakair , Tayi tangal… tangal kamar zata fadi sannan ta saya sosai akan kafafunta…
cikin mutuwar jiki ta nufi kofar office din ta bude ta huce ajin su
tana shiga aji ta hango Maryama da Amina zawne a kasa dan an cire musu table din aka saka musu Capet masu kyau
sam hankalinta da tunaninta be nuna mata daliban da suke zawne bah kaway burinta ta nufi Maryama ta kwanta akan kafadarta….
taba karasowa kusa da su ta fashe da wani irin kuka da ya jawoo hankalin daya daga cikin yan matan ajin
hankalin kawayen nata in yayi dubu toh ya tashi…
Amina tace Kaii Lafiya waya rasu dan kukan nata yayi kama da na wada akayiwa rashi…
cikin kuka Riya ta fada musu komai har nunfashinta na sarkewa .. ..
Maryama kinji wata saboda Innalilahi tih dama shi yasan da haka koma zece yana sonki..
toh kaway dama yayi niyar yaudarar ki ne kaway
amma kiyi hakuri.. kinji ki bar kukan nan haka kinga sau kwallanki ake sanan banso wani yaji maganar duk da nasan dole za’a fahimta
inda an sabka sai muyi maga …
Riya tace shiyasa n
tun fari banso na yarda dashi bah wallahi…
ta kuma rushewa da kukan me taba zuciya..
dede nan mallan Abdul ya shigo ajin ya zawna rai hade… ya kwallu riya ya kwalli kawayen ya sanan ya kuma kwallen yan matan ajin kamar yana nelan wani abun ne ???
dede ban ya kuma kwallen Riya ta kuma sukayi ido hudu dashi …Nan Riya ta kuma rushewa da wani sabon kukan…
dan komai da komai ya Dinda fado mata ah rai irin Alkwarin da ya dinga mata in sunyi aure insha’Allah nan bah da jimawa bah …
tun tanayin kukan da karfi ah jikinta har ta fara gajiya…
harda karatu akayi kuma layi yaka kansu …
Maryama tace kinyi zamanki kar kije harda nan kinji…kice kanki yake miki ciwoo
Amina … a’a fah barta taje tayi karatunta tunda ai babu abinda zai cenza da tayi da kar tayi kenan kinga gwara tayi karatun ta maybe taji sawsacin abinda ke ranta..
dede nan Maryama ta mike eywa harda dan sune ajan layi tana dawo Riya ta mike ta huce…
kankin ta kai indan Abdul ke zawne sai taji gurin yau yayi mata nisa….
tana fara karutun koh aya 3 bata karanta bah fashe da wani irin kuka mai sawti har saida yan ajin sukayi citt dunan kwallen abun mamakin nan dan wasu tun shigowarta suke kananun magan ganun akan kukan da take…
da sawri ta koma wajen zamanta ta kife kanta akan kafadar Maryama tana kuka ida nowanta sunyi suntum fuskarta tayi jazir . ..
Abdul kasa jurewa yayi ya taho gabanta duk da mutanan ajin na kwallenshi kuma dalibanshi yace
Dan Allah Riya kiyi hakuri ban fara sonki dan na daina bah , sanan mallan tamkar mahaifi yake a gareni doke nabi umarninshi
kiyi hakuri zan neman mana mafita..
Riya ta kwalleshi tace dan Allah rabu dani kaii ni koh ganinka ma banso yi balle fuskarka kaji daii Abinda mallan baba yace indan baka daina yimin magana bah ze dawki mataki….
so please ka rabo dani ta karashe maganar cikin haoushi da kaunar dan ta lura tsaf abdul mayaudari ne waii harda sa rana akanshi….
Riya tace !!! Uhum