Free chapter · Read without an account
Chapter 2
by Meemi Bashir · HABIBULLAH
HABIBULLAH
By
Queen Meemi bashir
2
Sauri -sauri yake don ya k'arasa school da sauri, yana son ya bada kud'in waec na shi don tun watan baya aka gama biya, shikad'aine bai biya ba,inda 'yan ajinsu nasu suke mai dariya da tsokanarsa, suna ce mai baban 'yan aji 6 sai dai kawai yayi murmushi, tabbas! rashin gata ne yasa bai shiga school da wuri ba.
Ak'alla mate nasa na level 2 a yanzu, amma shikam ba abinda ya dame shi ba ne domin ba a girma da neman ilmi,gate d'in makarantar ya bude ya shiga.
Ya riga kowa zuwa school d'in, hakan ya zame mai jiki, a kullum saiya share ko ina, malamai na sonsa saboda K'ok'arinsa da son addininsa, ga mutunci da girma ma nagaba.
Bashi da girman kai ko kad'an!komai k'ank'antar yaro yayi mai
abu to zai bashi hak'uri ne kawai a wuce wajen saboda babu abinda ya sanya a gaba sai ya inganta kansa. Office d'in principal ya shiga ya
gaida shi ya dosana ya zauna kan kujera, zancen kud'in waec yayi ma sa take principal yace ai an rufe karb'a .
D'agowa yai da sauri kirjinsa na dukan uku ya ce;
"Ataimaka min dan Allah wallahi dak'yar na had'a wannan kud'in ma."
"Wani malami ne ne ya shigo office din ya ji zancen da ake nan ya zauna a kan kujera habib ya gaishe shi.
"Aa Malam Habib."
Jinjina kai yayi cikin sakin fuska ya junyar da kansa ga principal ya cigaba dan Allah sir ataimakamini."
Ganin haka malamin ya ce ; "Ataimaka mai principal,don yaron yana da k'wazo sosai rashin ba shi dama kamar dakusar da shi ne."
Kwalla ce ta taru a idanuwan habib saboda tsoron rasa wannan dama da zai yi yana jin inta wuce shi kuma kamar ba zai sake samu ba su ka zubowa Habib din ido ya ci gaba da roko. Ataimake ni wallahi dak'yar na samu wannan ma bashi na karb'a, da yake principal d'in ba mutunci ya cika ba, ya k'ank'ance ido yace "dole ya bayar in yana san zana waec."
Mik'ewa yai zai fita teacher nasu ya zaro dubu d'aya ya bayar, ba kunya principal ya karb'e, godiya Habib yayi ta yi ma malamin.
Fita yayi yana mai farin-ciki ya je bayan class nasu ya zauna ys runtse ido yana maida numfashi amkar yayi gudun famfalaki, hakan ya zame mai d'abia inde Suka fita break nan yake tahowa yai zaman sa yana karatu,domin ba shi da ku'din siyan Abinci.
Wasu 'yan class nasu ne suka biyo ta nan suna hirar ball in da za a gabatar Ayau.
Ganinsa sukai cikin had'a baki suka ce "Aa! baban kana nan ashe."
D'ayan ya ce "ka manta ba shi da kud'in siyan Abinci."
"Hakane fa," inji d'ayan ya zira hannnunsa a aljihu ya zaro meat pie
ya yar a kasa ya sanya takalmi ya taka ya ja meatpie din har kusa da habibi.
"Gashi ka ci ko ka d'an kashe yunwar dake sasuk'arka."
Kansa a sunkuye ko d'agowa bai ya kalle su ba, wulla mai yai ajikinsa, "dalla banza poor da kai sai ji da kai, to kar Allah yasa kaci Useless kawai".
D'ago ido habib yai ya kallesu d'aya bayan d'aya.
"Me nai muku? ko kunji na ce ina
buk'atar taimakonku ne,idan ma zanci abinda ya fito daga hannunku ai kasan nafi karfin naci abincin karkarlshin kafarka da ko kare ba zai ci ba, to Allah ya baku hak'uri ba na bukatar taimakonku ina jin dadin rayuwata a haka.
D'ayan ya ce "lallema guy d'in nan wuyanka yai k'wari." Dayan ya ce da alama ya biya kudin waec fa shi yasa ka ga yana takawa da karfi Ya fad'a tare da kaiwa k'afarsa hauri,take
takalmun k'afartasa yaji mai ciwo.
Tashi yayi a fusace ya ce, ya kade rigarta ya ce "banda time d'inku."
Dariya suka fasa, "dallah mara
gata kawai, ai ba ma asan suwaye iyayenka ba." Dayan ya fada yana tare gabansa.
Juyowa yayi, ya ce "wannan
bai shafeka ba.
Ganin za su raina mai hankali ya damk'o d'ayan wanda ya wullo
mai meat pie, bai aune ba ya kaimi mari tare da shak'e mai wuya ya shiga naushinsa a ciki yana fidsa hucin fushi a saman fuskarsa take
d'ayan yayi baya da gudu dan ya tsorata ganin habib yanda ya haukace.
Sai da Habib yai ma yaron nan lilis ya yasar a kasa a tsaya akansa yana huci.
Dayan yaronne tare da Principal ya tawo wajen a fusace ya tsaya, ganin Habib ne yace "da ma kaine?
Ina ganinka salihi ashe ba ka da kirki? kashe musu yaro za kai, habib zai magana principal ya zuba masa maruka masu zafi!
Ganin yanda yaron ke murk'ususu ya sanya ya zaro waya ya sanar
da uban yaron.
Da yake d'an kansila ne,sai gashi nan da d'an sanda guda d'aya,take yasa aka tafi da habib aka tsare shi,kansila ya ce kar a sake shi sai idan d'ansa ya warke,wajen kwanansa uku a tsare yana shan azaba.
Yaron na can yawonsa ko ina, domin a ranar ya sha magani ya warware, sai yayi lamfa dan a cigaba da tsare habib, sai dai ya saci jiki ya fita yawonsa.
***
Aleb'una ne yaje kantin Ado sauk'i, domin kan ya tambayeshi ina HABIB yake nan ya ke sanar dashi wai ai an tsare shi kan sunyi fad'a da d'an kansila."
Jinjina kai aleb'una yayi Ya ce "kai duniya idan ba ka da gata kai ba komai bane"
"Wallahi fa sai addua, ado ya fad'a yana mai yak'inin zuwa yayi belin habib.
Bayan tafiyar aleb'una ado ya tashi ya rufe shagonsa ya tafi police station,ko da yaje da kyar aka ba da belin habib tare da yi masa mai kashedi.
Sun tawo hanya ado yake dad'a nusarda habibi akan hakuri da ja baya ga hadari, Fad'a sosai yayi masa shi kuma yayi tai masa godiya har suka karasa gida ya karasa dakinsa, tunda ya shiga bai fiti ba sai sallah ke fito da shi.
Kwanansa d'aya baici abinci ba alokacin, duk bincike da yayi a dakinsa bai samu komai ba sai wata tsohuwar naira Ashirin ya
gani d'akinnasa take farin-ciki ya wanzu a fuskrsa. Da ita ya sai biskit haka yaci ba yanda iya ba wai dan ya k'oshi ba.
Washegari!!
Ya yi shirin school ya tafi,ana cikin yi musu lesson principal ya shigo yayi kiransa, nan ya mik'e ya bishi har zuwa ofishinsa bayan ya zauna, principal ya mik'a mai takarda tare da kud'insa ya ce "mun koreka daga school d'in nan."
Diriricewa habib yayi, ya kasa karbar takardar jikinsa ya shiga rawa ya kasa magana, sir nayi wani laifin ne?
Ya fada hawaye na zubo masa, principal bai ko kalleshi ba ya cigaba da rubutu, cikin tsoro ya ce principal mai nayi?"
"Au ka manta ko? to tashi kabar mun offfice ina, ko na sanya afitar da kai stupid kawqi
A hankali habib ya mik'e ya fita, yana kukan zuci, ya ci buri akan karatu ba kadan ba, kuka ya tsaya yana yi tamkar mace. Ya dad'e a wani dan loko a tsaye daga k'arshe ya mik'e cike da gajiya ya bar wajen. Tafiya ya ke a k'asa cikin halin ha'ula'i ga yunwa sai jiri ke d'ibansa.
Kuuuuuu! yaji mota ta ja birki, take wani saurayi yafito cikin masifa ya ce da habib "Dallah kai matsa, ku irinku sai masifa tai muku yawa sai
ku zo bakin titi kuna tafiya hala shaye shaye kayo shi yasa kake layi akan titi, matsa ko na kwashe maka kauri"
Ba shiri habib ya matsa ya na bashi hak'uri ya bar wajen da sauri Al'amuran rayuwa sun taru sun mai yawa tun yana yaronsa gashi har ya girma,da k'yar ya k'arasa d'akinsa, ga jiri na d'ibansa, akwai sarkakiya da fagamniya a cikin novel din.
"Waye HABIBULLAH NE??? ku biyoni dan jin waye HABIB.
***