Free chapter · Read without an account

Chapter 3

by Meemi Bashir · HABIBULLAH

HABIBULLAH
By


 Meemi Basheer
*3*

Kafin safiya zazzabi ya rufe shi, ko kuɗin Panadol ba shi da shi. Hakan ya rarrafa da ƙyar ya je gun ADO SAUƘI.

Ado na ganinsa ya ce, “Subhanallah!” Da sauri ya taro shi.

“Habib me ya same ka?”

Kuka ya fara tamkar ƙaramin yaro, jikinsa in banda rawa ba abin da ya ke yi. Ganin ya kasa magana ya sa ya ɗauko Maltina ɗaya da wani ƙaramin bread. Duk da shi ma ba wani cika ke da kantin ba, amma tsananin tausayin HABIB ya cika shi, a hankali ya juya ya share kwalla.

Cikin mintuna Habib ya cinye, sannan ya dauko masa Panadol  ya ba shi ya sha, ƙanƙanin lokaci jikinsa ya yi ɗan ƙarfi. Godiya ya hau yi wa Ado, shi kuwa ya ce, “Ai ba komai yi wa kai ne, wallahi jinka na ke tamkar ƙanina.”

Murmushi Habib ya yi, ya koma gefe da ke cikin kantin ya ɗan zauna, ya ɗau Al-Qur'ani yana karantawa. Haka Ado yaci gaba da siye da sayarwarsa.

Wajen kamar rabin awa Ado ya ce, “Habib.”

Ɗagowa ya yi ya kafe Ado da kallo, yana jiran ya ji me zai ce. Nan Ado ya ja benci gabansa ya ce:

“Habib idan ba zan takura maka ba, ina son sanin kai ɗin waye? Ina ne mahaifarka? Su waye iyayenka? A dunkule dai ina son sanin labarin ka.”

Take jikin Habib ya yi sanyi, hawaye suka zubo masa ya ce, “Ado haƙiƙa kai masoyi na ne, mai ƙaunata da taimakona a duk faɗin unguwar nan. Duk da Allah ne mai rayawa, amma kai ne gatana a nan. In sha Allahu zan sanar da kai ko ni waye, amma ka ba ni awanni zan yi Sallar Walaha, idan na idar zan ɗan je kasuwa ɗaukar dako, idan na dawo zan gaya maka. Amma sai dai mu je ɗakina, saboda masu sayayya kar su zo shagonka su ga hankalinka ba ya gare su.”

“Babu komai Habib, duk yadda ya wanzu, ni a waje na shi ne dai-dai. Allah ya kaimu.”

Wajen huɗu HABIB ya koma dakinsa, wanda da ƙyar ya samo ɗari biyu. A hakan ma murna ya ke. Ado Haske ne ya zo, bayan sun zauna a ɗakin habib din gefen katifa inda ya ke kallon ko ina, cike da tausayawa.

“Yaro har yaro, amma ba gata. Allah kawo mana mai kyau, ya fada a zuciyarsa.

Bayan sun zauna Habib ya ɗan kwanta don a gajiye ya ke, ya fara ba shi labari kamar haka:

*HABIBULLAH*

“Asalina ni ɗan garin Gombe ne, a ƙaramar hukumar Dukku. Na kasance ɗa na farko a gun mahaifina da mahaifiyata. Sunan mahaifina Malam Bukar, mahaifiya ta kuma Mama Kubra. Dukkansu Fulani ne na Gombe ɗin. Tun kan mahaifina ya auri mahaifiyata, yana da mata, Yagumbo Hassana, wadda ta kasance ita ce matarsa ta auren saurayi da budurwa.

Tunda suka yi aure shekara uku ba su samu haihuwa ba. Duk sai suka tashi hankalinsu, sabili da ita mahaifiyar mahaifina sun damu kan rashin haihuwarsa, hakan ya sa dangi suka sako ta a gaba.

Da yake masifaffiya ce kuma ba ta da kunya, babu ragayya a rayuwarta, hakan ya sa suka sama mata lafiya, domin Yagumbo ba ta da kirki ko kaɗan. Akwai ta da son zuciya, ga bun bokaye. Shi kanshi haƙuri ya ke da ita. Idan mahaifina ya samu amfanin gonarsa, haka za ta yi ta ɗiba a ɓoye tana sai dawa, haka za ta yi ta cin kuɗin tana fankamaa.

Mahaifina ba shi da ikon magana, ranar ko da zai tanka, haka za ta hayayyako masa. Kai a ƙarshe ma sai da duk ta raba shi da iyayensa da ‘yan uwansa.

Akwai lokacin da Kakata ta je gidan, da yake shi ba zuwa ya ke ba, ta daɗe ba ta gan shi ba, hakan ya sa ta je, har da su ƙullinta. Tunda ta je ko ruwa ba ta ba ta ba, ga rana, kuma Babana yana ɗaki ta hana shi fitowa. Hakan ya zauna yana kuka, ita kuma ta kafe dauri a bakin ɗakin tana shan rake. Hakan Kakata ta gaji da zama, ga yunwa da kishirwa na damunta, amma ta ƙi ba ta.

Kakata da ta ga hakan ta sa kuka ta ce, ‘Yanzu kai Bukar kana ji na amma kai shiru?!’ Jinjina kai ta yi ta kalli Yagumbo ta ƙara da cewa, ‘Abinda ki kai min Allah ya yi miki fin shi!’ Tana faɗa ta miƙe ta yi hanyar waje.

Mahaifina na cikin ɗaki yana ta kuka cike da takaici, wanda ji ya ke kamar an ɗaɗɗaure shi. Kakata kuwa tunda ta koma gida ciwo ya kwantar da ita saboda baƙin cikin da ta kunsa.

Sauran ‘ya’yanta ne ke kula da ita. Umartarsu ta yi da su taimaka su tsamo wansu daga halaka, da yake shi ne babba.
Ba shiri suka ba  zama, sai da suka samo ma mahaifina maganin karya duk asirin da ta mai, ya karye. Ganin hakan ya sa Kakata ta mahaifina ya ƙara aure.
Take ta haɗa shi da mahaifiyata, wadda ta ke ‘yar ƙanwarta ce.”

Muje zuwa

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol