Free chapter · Read without an account

Chapter 5

by Meemi Bashir · HABIBULLAH

HABIBULLA

BY

Meemi Basheer

5

Gyara zama Ado sauk'i yayi tare da sakin numfashi! ya ce "inajin ka"

Idanuwan Habib ne saukai jajawur! ta shi zaune yayi, da yake ana zafi ya d'au mifici yana firfita ,sannan ya cigaba da ce wa:

"Lokacin da mahaifiyata tabar gidan, sai ya zamana na dawo marayan k'arfi da yaji, domin in banda ganamin azaba ba abinda yakumbo keyi,idan na tashi da safe ba mai kulani, hakan zan fito tsakar gida na zauna sai nai Awa biyu azaune ba wanda zai kulani,haka za tai ta aikace -aikacenta, ban iya magana ba balle nai magana sai dai nai fitsari a zaune anan, wataran in ta b'aci har kashi zanyi,tana ganin hakan zata zo tai ta jibgata kamar wani babba ina kuka, babana ko kallona ba zai ba.

Sai ta gama jibgata nayi kuka na gaji anan bacci zai kwasheni,sai na kai sha-biyu na rana a nan, sai ta ga dama sannan za ta ta so babana tace yazo ya wanke min ya yi mun wanka,to asan nan ne zata ban koko rabin ka'aramun kofi wanda ban ma iya sha da kaina ba, hakan duk zai tsiyaye,kai! intak'ai ce maka labari hakan nai ta rayuwa cikin izaya har na kai shekara biyar, wanda kafin na kai shekara biyar d'in nan bana wata d'aya ban yi ciwo ba duk na rame .

Alokacin ne ta tsiri d'oran tallan cin-cin, hakan zan je tun safe sai na sai da shi,in ban sai da ba banda abinci,kuma aranar a kitchen zan kwana ,wataran innai cinikin ma da yake ba wayo gareni ba, hakan zai sa wasu b'ata gari za su k'wace kud'in ,akwai sanda su ka k'wacen kud'in, sai na biya ta gun sana'ar mahaifina na ce ya ban kud'i na kai mata an sace.

Da ya gama jin hakan zai hau jibgata har dasu ball dani, sai dai nai ta yawo,abokaina duk suna makaranta amma banda ni, sai dai suyi ta tsokanata ko makarantar Allo bana zuwa balle islamiya,sai da ta kai ta kawo duk wani wanke -wanke da shara ni nake yi ga ni namiji,akwai wani lokaci da na tafi tallan cin-cin ba wanda ya siya, sai na bi ta wani kududdufi wasu yara suna wasa da yake su za su kai shekara goma sha, suka kirani za su siya,duk suka cinye suka k'i ban kud'in, da na sa musu kuka, d'ayan ya fara duka na, yana tura ni baya, cikin tsautsayi sai ji nai na fad'a cikin kududdufin nan, take yaran suka dare da ragowar cin -cin d'in.

Haka nai ta ihu, cikin ikon Allah wani mutum yazo wucewa ya cironi, lokacin ma har na suma, ganin halin da nake ciki yasa ya tafi dani gidansa.


Yakumbo sam! bata bibiyi b'atan da nai ba, babana yana son fita nemana amma tak'i bari, duk da rashin sona da baya yi amma yaji d'acin daba a ganni ba,sai da nai kwana biyu agidan mutumin da ya tsince ni,har na d'an dawo hayyacina.

Ranar da na cika kwana biyu ya tasani agaba muka tawo gidan mu,ganin babana ak'ofar gida yasa suka gaisa yayi mai bayani,babana yayi ta yi mai godiya.

Shigata gidan ta hau masifa, ai bawani bata da nai, wai salon yawo na ko ya, haka ta hau jibgata akan sai na biyata kud'in cin -cin d'inta, dole tasa na tafi cikin kasuwa ina ta cewa abani sadaka.

Wani Alhaji yaji tausayi na yaban d'ari biyar, da murna na dawo na mik'a mata tasa dariya, ba tambayar inda na samo, tsugunnawa nai nace ta ban abinci, ball tai dani tare da zagina .

Cikin rauni na fita k'ofar gida ina kuka, sai gidansu habule abokina na shiga muka ci abinci ,idan na ce zan tsaya baka labarin halin dana shiga daki-daki to sai mu kwana anan."

Shuru yayi, san nan ya d'ago idonsa yayi jajawur! ya kallo Ado ya ce "har yau inna tuno da wannan rana sai na zubda hawaye."

Bubbuga bayansa Ado yayi "Mahak'urici mawadaci ci gaba kawai."

"Lokacin da na shiga shekara shida aduniya mahaifiyata ta kawon ziyara, a mak'otanmu ta zauna, maman habule tasa aka kirani, kuka mamana ta saka ganin yanda nai bak'i na rame sai rank'walelen kai da dogon hanci kuka sosai take yi, musamman yanda maman habule ta bata labarin duk irin halin dana shiga bayan rabuwa,sai da maman habule tai ta bata hak'uri Alokacin taci Alwashin tafiya dani.

Haka ta yi ta bani abubuwan da ta kawon tana yi tana hawaye,har nai kwanta ajikinta, wanda alokacin duk na ji labarin nan da nake baka awajenta, da kuma wanda maman habule ta bata, su ne na kwafe akaina.

Bayan mahaifina ya dawo, ta je ta same shi yana Alwala ak'ofar gida, nan ta gayamai za ta tafi dani, ko kallonta bai ba ya ce;
"da akaina ya ke? Idan ma za ki bar duniyar da shi ma baya gaba na."

Wasu hawayene suka zubo mata, za tai magana, yakumbo talek'o tana sababi ta na tambayarsa da wa yake magana,ganin mahaifiyata yasa ta had'e rai mahaifina ya ce.

"Tafiya za tai da d'anta fa."

A fusace ta fito "a ina? kai yanzu kai da d'an naka sai ka bari ta tafi da shi? to wa zai na mun aiki da tallah, to wallahi ban yarda ba."

Jin hakan mahaifina ya ce, dole mahaifiyata ta hak'ura da tafiya dani, nan mamana ta k'ek'ashe k'asa ta ce sai ta tafi da ni, fad'a sosai sukai akaina, don mahaifina har marin mamana yayi, tamkar ba 'yar uwar saba,don adalilin rabuwar da sukai ma har yanzu mahaifiyarsa na fishi da shi.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol