Free chapter · Read without an account

Chapter 6

by Meemi Bashir · HABIBULLAH

HABIBULLAH

By

Meemi Basheer.


6

Sai da baban habule ya bawa mamana hak'uri sannan ta hak'ura ta k'ara da ce wa; komai daren dad'ewa sai ta d'auke ni, da fad'ar hakan ta tako har gabana da na ke ta kuka ta ce "Habib d'ana ka yi hak'uri, na so tafiya da kai, amma Allah bai ba, ka sani Allah ne gatan kowa, kuma Allah baya bacci yana tare da kai, duk inda kake ka rik'e Alk'awari karkaci amana, san nan ka dogara da kanka," ta fad'a tare da shafa kaina tana zubar hawaye.

Zan turo umar ya zo ya kai ka gunsu kaka,taban Alawa tana hawaye ta tafi.

Ni kuwa tunda naga hakan sai zazzab'i ya rufe ni, saboda Alhinin rashin bin mahaifiyata, hakan ina ciwo nake mata aiki,wata k'awarta ce tazo suna hira take bata shawara ta kaini Almajirci ta huta da jarabar rik'onsa, hakan ya sa ta amince, dawowar mahaifina yasa ta i mai maganar, be ce uffan ba! 
Sai daga bisani ya ce duk yanda za tai tayi.

Sati d'aya da maganar ta had'ani da wani hamisu, don ya kaini maiduguri Almajirci.

K'wayoyin kayana ta had'ani da su a bakko,lokacin da zan tafi na rungume mahaifina ina kuka, duk da rashin kulawa dani da ba ya yi,amma ina sonsa, rana d'aya kenan da ya tausayamin har da hawayensa ya ce "habib Allah yai maka Albarka, ya kyautata rayuwar ka, ka yi karatu sosai kaji, zanzo idan kai wata d'aya, dad'ine ya isheni har kud'i yabani.

Yakumbo ta janyo ni ta rank'washen i.
"Saura kai tunanin dawowa, domin kai da gidan nan kunyi ban kwana,harda d'a kan dundu a baya, ta ce tafi can! ka shiga duniya ja'irin yaro kawai, kake wani kallona da shegun idonka, to ko ubanka me zai iya? ai na gama da shi, ta kuma rank'washina ta hankad'ani, kuka hardasu majina nake yi, hakan ina waiwayen gidanmu hamisu ya tafi da ni maiduguri.

"Wannan shine barina gida", ya fad'a tare da share hawaye.

ADO sauk'i harda d'an hawayensa ya ce Yi hak'uri habib, Be A Man mana dai na kuka, ina son ka k'arasa bani ka san an kusa kiran sallah" 

kallonsa yai yace" Ado ka bari muyi sallar sai na k'arasa maka ko? Ko kuma mu bari sai gobe?, kar iyalan ka na gida su ga ka dad'e."

" E! da wannan kuma, abarshin sai goben HABIBULLAH."

Kud'i ya d'auko ya bashi ya ta shi su kai Sallama ya tafi
........Ni ma to zan da kata anan nai sallar.


Washegari!

Saboda zumud'in son jin k'arashen labarin HABIBULLAH. Ado sauk'i ko bud'e kantinsa ma bai ba.

Haka ya tafi shagon habib harda break fast, wanda ya sa aka had'a mai ya tawo mai da shi. Habib ya ji dad'in hakan yayi ta godewa Allah, bayan kammala karyawar ya cigaba da bashi.

"Bayan mun tafi nida hamisu m cikin ikon Allah mukaje maiduguri, kwanan mu biyu a wani gida da muka sauka, sannan hamisu ya kaini makarantar Allon ta Almajirai, bayan kamar kwana biyu, hamis ya tafi tare da Alk'awarin zai zo dubani idan an kwana biyu.

Tun bayan tafiyarsa kullum bani da aiki sai kuka,ga kuma rashin sabo, so biyu aka bani abinci a gidan malam akace na fara bara, haka zamu tafi ayari, kuma duk nine k'arami acikinsu, wataran inna samo abincin ma Manyanne ke k'wacewa su cinye, duk kayan da nazo da su duk an d'ebe, kullum ka ganni da riga d'aya ,malamin myana yawan tausayamun, hakan ta sa yace kar wanda ya kuma dukana har abinci yake ban, ta ke na fara hak'ura ina karatu sosai, kullum sai na wanke Allo, dalilin da ya sa na kuma samun karb'uwa a gun malam kenan.

Watana uku duk an sanni, saboda son karatuna da kuma k'ok'arina, hakan ya sa malam ke k'aramun da littafai saboda ganin ko me aka karantan ya zauna kenan.

A wannan lokacin sai na ce ma zamana a maiduguri ya min amfani,watana biyar kowa ya fara tafiya garinsu da wanda suke garin ma, ni kam ko kare ba wanda ya zo,tun ina kuka har na hak'ura, shi kanshi malam abun ya dame shi,har d'alibai suka dawo nikam ina nan, ganin hakan ya sa na nemi aiki awani gida ina zubda musu da shara, da su aike- aike suna ban abinci, da kaya.

Matar gidan mai kirki, ta jawo ni tamkar d'anta ko banyi aiki ba zata ban abinci ,maigidanta ma akwai kirki, tun ina damuwa akan rashin komawa ta gida har na hak'ura na saba,da yake matar 'ya'yanta na kano suna karatu bata da k'aramun yaro sai ta rok'i malam ya barni ina kwana gunta, hakan kuwa akai, na dawo gunta, saboda karamcin mutanen nan suka sani a makarantar boko a primary 2 aka sani tunda ina da k'wazo, da yamma na tafi ta Allo, lokuta na shud'ewa haka watanni sai gani nayi shekara d'aya amaiduguri wanda malam har ya fidda ran sake gani wani nawa, nikam da yake yaro ne, sai ban damu ba, saboda kome nake so ina samu gidan baba tahir da mama laurat da yake hakan nake kiran su.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol