Free chapter · Read without an account

Chapter7

by Meemi Bashir · HABIBULLAH

HABIBULLAH

By

Meemi Basheer


7

Wata sabuwa muna zaune k'alau a lokacin shekarata goma sha-uku ,lokacin na kammala primary ina jiran Result, domin har na sauke alqur'ani da ma wasu littafan duk a shekara biyar da nai a maiduguri, abubuwa duk sun shud'e. Bani da kowa sai mutanen da Allah ha had'ani da su. 

k'addarace ta afku, yayinda aka fara fa'da a maidugurin, dalilin hakan yasa baba Tahir Mama laurat su ka fara shirin hijira komawa kano, da yake dama ita 'yar kano ce aure ne yakaita maidugurin.

Alokacin zaman maiduguri ya fara gagarar jama' a da dama.Dalilin da ya sa kenan wasu ke yin hijra.

Hakan kuwa akai suka tafi dani, domin malam ma sun bar nan hakan tasa suka tawo dani nan kano,cikin ikon Allah ga 'ya'yansu hakan yasa suka kuma rik'e ni, bamu dad'e da dawowa ba na shiga aji d'aya na secondry, domin Allah ya d'oran son karatu, nan su ka kuma sani a islamiyya, gasky ba abinda zance musu sai fatan Alheri.

Shigata aji biyu ne muka shirya dan su kaini gun iyayena, da yake na sanar musu sunan garin wanda ban manta ba yana rik'e akaina, hakan kuwa akai munje, amma wani ikon Allah basa nan, ba inda ba mu jeba Allah yaso ban manta sunan unguwar ba, munje har gun maigari amma ance da dad'ewa sun tashi ba a san ina suka koma ba, gashi ni ban san dangin mahaifiyata ba ko d'aya, haka na mahaifina,na yi kuka har na gode Allah, haka nad'au dangana da Allah, mundawo kano duk na damu wanda har rashin lafiya nayi ,daga baya na ware, haka lokuta saukai ta ja.

"Abinda ba zan tab'a mantawa da shi ba Har k'arshen rayuwa ta, lokacin da na shiga aji uku na sakandire har munyi third time munyi exam, ina zaune gida kafin exams tafito na shiga ss1.

Ina islamiya dan har lokacin ban daina zuwa ba,wajen 6 oclock na dawo na biyo unguwar da muke, ganin mutane na yi suna ta gudu da jarkokin ruwa a hannunsu, take na d'an bi su da sauri nima naga abinda ke faruwa.

Gabana ne ya fad'i ganin wuta nacin gidanmu, da gudu naje ba inda baya ci aciki, kuka na fara ina iyayena na ciki, amma ba wanda ya kulani, haka na kutsa ana rirrik'eni na shiga ciki, har can ciki ba inda wuta bata ci, ni ma da k'yar aka fito da ni, don na suma,bud'e ido nai na ga duk gidan ya k'one har lokacin hayaki na tashi.

'Yan uwan Mama laurat na gani, da gudu na je gare su ina kuka, da yake na san wasu, tambayar su nake ina su mama da baba .

Kallona tai tace "Sai hak'uri habib Allah yai musu rasuwa, duk sun k'one da lauratun da baba tahir d'in har haris da sadiya da kabir,duk sun k'one duka, kuma ba' a san ta inda wutar ta taso ba, daga kawo nepa kawai abun ya faru.Alamarin Allah babu wanda ya tsira."

Kallonta nai na ce "ina RAUDAT auta?."

ta kuma kallona wanda da k'yar take magana, ai Auta na wajen k'anwar mama laurat ,ikon Allah da safe ta zo suka tafi gidan ta A kaduna tai mata hutu, ashe! Ajalin babu ita."

Alokacin suma na kuma yi na farfad'o,hakan akai ta jimamin rasuwarsu, wanda ni aguna gani nake ni akaiwa mutuwar, domin ni sune gatana, banda kowa sai su ,duk da gatan kowa Allah.

Bayan gama zaman makoki wani k'anin baba tahir yace na kama gabana, daama ba mu da had'i tsakanina da su ,dama can! ya tsaneni,ina kuka na rasa inda zani ,hakan yasa na koma kwana cikin masallaci, kullum ni ke sharewa na yi komi, a hakan kuma ina zuwa islamiyyar,ba zan manta ba, wani ne ya takuran a masallacin, saboda ya ga ina samu inde na share a kwai wani mutum da ke zuwa sallah in ya zo zai ban kud'i, hakan yasa sai da yayi yanda aka koreni daga nan, ba yanda na iya na bar wajen.

Wani abokina da muke islamiyya tare, shi ya ja ni gidansu inda nake kwana d'akinsa,babansa na da maimutunci k'warai da gaske, tun da ya ganni yake sona, hankalina ne ya kwanta, sam! duk wata damuwa ta ta k'are a ganina na samu uban gida, sai dai duk lokacin da na tuno da su baba tahir na kan yi kuka na godewa Allah.

Maman nasir wato mahaifiyar abokina ce ta takuramin, sam! Ba ta san taimako, musamman ganin irin yanda Alhaji ya maidani tamkar d'ansa, domin shi yayi mun hanyar da na cigaba da makaranta inda na shiga SS1, domin wanda mukai jinior da su duk lokacin suna ss 2, hakan ya sa na samu damar ci gaba, matar nan kuwa sai da tai sanadiyar bari na gidan.

Tamin sharrri wai ina koyawa d'anta shan sigari kuma inai musu sata,har maigadi sai da Ya bada shedar k'arya,  ganin hakan yasa na tattara kayana nai tafiya ta, na bar unguwar na'ibawa ,bansan inda zani ba, nan na yi ta gararanba, hakan ya sa na tafi kasuwa nake kwana acikin runfar shago, to anan ne na had'u da Aleb'una, shi irin jinin mu ya had'u da shi duk da ba halinmu d'aya ba ,ganin halin da na ke ciki ,yasa ya jani yace na koma shagonsa, wanda shine asalin zamana a unguwar fagge,muna zaune a d'akin Aleb'una wanda har zuk'e-zuk'e yana yi,mu wajen biyar ne ad'aki d'aya, dukkansu na shan sigari, bayanda ba suyi su jani ba, amma nak'i, duk kayana sun d'auke, da d'ai da d'ai.

Duk a hakan nake zuwa makaranta, wata mata mai saida abinci za ni makaranta da safe naga ta kasa tsallaka titi, taimakonta na yi na d'aukar mata kaya har gunta na kai mata, ganin hakan ya sa tace ko zan na zuwa ina taimaketa wajen wanke tukunyoyi, da yake nanne shagonta komi na girkin anan take hakan kuwa akai kullum kafin na tafi makaranta ma sai na wanke mata kwanuka,haka bayan na dawo, wannan dalilin ne yasa ban fiya zama d'akin aleb'una ba sai dare, kud'in da nake samu shi nake biya wa kaina kud'iin makaranta da siyan littattafai, a hakan har na shiga ss2 inawa matar nan aiki.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol