Free chapter · Read without an account

010

by SultyWrites · NI DA YA NABIL

NI DA YAYA NABEEL _


  _YOUNG WRITER✍️




* 010 *




Zaune take daga Inda tayi sallar asuba, in banda kuka babu abinda take kamar ranta zai fita, tashi yayi daga kan prayer mat ɗin bayan ya idar da sallar ya koma gefenta ya zauna, hannuwanta ya riqo, a tausashe yace, "Pleaseeee an baby am, ki daina kukan nan haka, ki barni inyi jinyar abu daya kar ki janyo wa kanki wani ciwon".

 "Ni dan Allah ka rabu dani, dama ni nasan ba tsakani da Allah ka taho dani garin nan ba, kawai kazo dani ne dan ka dinga gana min azaba iri iri. To dan Allah ka taimaka ka maidani wurin su Mommy, whl ba zan iya ba, ni kafi karfi na". 

Murmushi yayi kafin ya ɗauke ta ya daura kan cinyar sa ya rungume ta tsam yanajin kamar ya maidata cikin sa, a hankali ya shiga faɗin, "Duk abinda kikace naji, kuma ba zan yi musu dake ba, duk ma nufi na a kanki zai bayyana kansa da kansa ba sai nayi defending ɗin kai na da kalamai ba. Sannan wurin su Mommy ma da kikace in maida ki duk naji amma saikin warware tunda kin ga dai ai da kunya nayi barna na kai musu jinya ko". Ya karashe yana ɗaga mata gira ɗaya.

Wani sabon kukan ta sake fashewa dashi tana faɗin, "Ni whl ba zan warware a wurin ka ba. Mugu kawai". Hannu ya kai ya shiga shafa gyararren gemun sa yana ɗan murmushi, idanunsa a kanta yana watsa mata wani kallo me melting heart.

 Ɗauke kanta tayi tana kumbura fuska, a hankali ya kai fuskarsa gefen wuyanta yana hura mata iskar bakinsa a kunne yace, "Do you know what Assumah?". Ƙasa bashi amsa tayi saboda jikinta da ya fara karbar sakon nasa. Shi kuma ya cigaba, "Nabil loves you. He's so much in love with you. I know yanzu zaki ga kamar dan na samu wani abu me muhimmanci a tare dake ne yasa nake faɗa miki haka. Eh wannan ɗin ma ya ƙara min son ki da kuma qimarki a idanu na, but ina so ki sa a ranki tun kafin yau Nabil yana son ki. You Are so special, ke ɗin ta dabance a rayuwa ta. Kin bani abu mafi tsada da bani da arzikin da zan iya biyan ki sai dai in roqi ubangiji Allah ya miki Albarka, ya faranta miki kamar yadda kika faranta min Assumi am, Allah kuma ya bamu zurriya ta gari, yasa nan da wata tara ki haifa min baby. Ai zaki haifa min yara da yawa ko Assumi? Ina son yara whl, kinga yanzu kin cike rabin zuciyar Nabil, idan kika haifa min Babies kuma shikenan zan mallaka miki zuciyata da makullin gabaɗaya". 

Kallonsa tayi taga yadda yake maganar tsakani da Allah, dan har wasu abubuwa masu wuyar fassarawa take hangowa a cikin kwayar idanunsa. Ba tare da tace komai ba ta kwantar da kanta a kirjin sa tana nazarin Maganganun sa da suke neman dasa mata wasu zarge zarge akan rayuwarsa da Jumayman. Can kuma ta katse tunanin tare da faɗin, "Ai kafi son Jumayma a kai na".

Dan tsuke fuska yayi kafin yace, "Dukkan ku mata na ne, kuma ina son ku sannan kowacce da irin son da nake mata da kuma irin Matsayin da take dashi a zuciyata, dan haka ba ruwanki da Jumayma". Ƙokarin tashi ta fara daga jikinsa amma sai ya ƙara janyota yana kallon face ɗinta cike da so. Juya fuskarta tayi tana cuno baki, kissing din goshinta yayi yana murmushi yace, "Rigimammiya kawai". Ya faɗa yana daukanta suka koma gado. Kwanciya suka yi yana rungume da ita, ba jimawa kuwa bacci me daɗi yayi awun gaba dasu.

Kiran wayarsa da ake ne ya tashe su, janyo wayar yayi yai picking ba tare da ya bude Ido ba, sai da ya gama sauraren mai maganar sannan yace, "Ba zan samu shigowa ba yau amma ku cigaba daga in da na tsaya, ni kuma zan riqa monitoring duk wani moves naku daga nan, sannan zamu riqa communicating daku". Shuru ya sakeyi yana sauraren sa kafin yace, "Ohk hakan ma yayi". Ya fada sannan ya katse kiran yana buɗe idanun nasa, haɗa Ido sukayi da Asum data ƙure shi da ido, da sauri ta datse idanun nata cikin kunyar kamata da yayi tana kallonsa, murmushi yayi yaja hancinta tare da fadin, "Good morning an baby". Sake sunne kai tayi shi kuma ya tashi da ita a jikinsa ya wuce bathroom.

Wanka suka yi suka fito, ya shiryata da kansa sannan ya sa aka kawo musu abinci. A baki ya dinga bata kamar wata baby, har ta koshi sannan shi ma yaci. Wata irin kulawa yake bata ta musamman wadda ta sake sa Asum ɗin mamakinsa, ashe haka ya iya kula da tarairaya lalle dole Jumayma tayi hauka a kansa. Wani takaici taji ya kamata da ta tuna ai Jumayman ma haka yake mata. 

Shi kuwa Nabeel gabadaya ranar komai ajje shi yayi ya bawa Assum dukkan lokacin sa, waya ma dakyar yake amsawa har dare. Tana kwance a kan cinyar sa yana jagwalgwala mata kai shi a lalle kitso yake mata, wayarta ce tayi Kara hakan yasa ya ɗago ya harari wayar sannan ya dauka ya amsa kafin ya sanya ta a handsfree ya miqa mata. Karba tayi suka gaisa da Adda Yusran, kamar abun arziki Adda Yusra ta shiga yiwa Assum faɗa kan ta rage taurin kai da kafiya, sannan ta rage wannan tsiwarta ta indai tana so ta ci ribar zaman aure. 

Nabeel da yaga abun Adda Yusran bana karau bane ya sashi karbar wayar daidai lokacin da Adda yusra ke faɗin, "Wacece ke da zaki ce duk abinda kika faɗa sai kinyi shi? to dan uba......".

"Keeee". Nabeel ɗin ya katseta a kausashe kamar ba shi ba.

"U..ba..naaaa". Ta karashe kalmar data ɗauko a rarrabe kafin tayi saurin faɗin, "Ya.. ya Nabeel ina wuni".

 "Da ban wuni ba zakiji murya ta?". Hamma Adel dake gefe yace, "Tuba muke babban yaya, ai mana afuwa".

"Okay Kai Ka bawa matar Ka waya ta Kira ta zageta Kenan?".

" Ah ah whl ni ba ruwana, dan dana san ma abinda zata yi Kenan ai da ba zan barta ba, itama tsaurin Ido ne irin nata ai, ka san Yusra bata ji Ya Nabeel in kazo dan Allah ka zane min ita d...". Kashe wayar Nabeel yayi yana jan tsaki ya kalli Asum dake dariya. Gira daya ya dage mata, sai kuwa ta tashi zaune tana cigaba da dariyar tace, "Amma whl Hamma Adel ma, wato dan ya zame kansa shi ne harda cewa wai Adda yusra ta cika tsaurin Ido, kuma wai a zane ta". Sai kuma ta sake kwashewa da dariya.

Ɗan murmushi kawai yayi kafin yace, "Tashi muje mu kwanta gobe inason fita da wuri". Nan da nan ta shagwabe tare da faɗin, "Ni whl bana jin bacci yanzu, kuma ni whl goben ma baza ka fita ba". Jin yayi shuru yana kallon ta kawai yasa ta shiga diddira masa kafafu tare da sakar masa kukan shagwaba, "Ni dai whl sai dai mu fita tare dan ba inda zaka fita Ka barni ni kaɗai".

"Ahh lalle yarinyar nan, sai kice mun kin samu lpy, to matso ki faɗa min abinda zaki bani In na zauna din". Kallonsa tayi sai kuma tayi saurin tashi ta koma Kan gadon ta kwanta tana fadin, "Ni na ma janye maganar tawa kayi tafiyar ka kawai, na yafe zaman ma whl". Tashi yayi ya biyota shi ma yana fadin, "Ai ina yarinya baki isa ba kuma, ba dai kince in zauna ba. Zan zauna ɗin muga ya zakiyi dani".




***************




Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, yau satin su uku kenan a Germany, Asum da Nabeel sunyi wani irin dinkewa kamar tube da tyre, dan duk da yanayin aikin sa hakan bai hanashi nuna mata soyayya da kulawa ba, cikin ƙanƙanin lokaci rayuwa ta canja mata, ta koma kamar ba ita ba, tayi kiba ta ƙara wani cika ido dan shi kansa Nabeel ɗin sai da yace mata wai ba rakiya aiki tayi ba honeymoon kawai tazo yi abun ta.

Kamar yanzu da yake zaune yana aiki, Assum ɗin kuma na bacci. Tashi yayi da sauri ya ture system ɗin dake gabansa ya wuce ya shiga canja kaya a gurguje, ya gama ya ɗauki abubuwan da yake da buqata, baya son ya tashe ta dan bata daɗe da kwanciya ba, sai kawai ya ƙarasa wurin gadon yayi kissing din goshin ta, kamar tana jinsa yace ki kulamin da kanki sannan ya juya ya fice a hanzarce. 

Lokacin data tashi bata ganshi ba da mamaki ta ɗau wayarta dan Kiran sa taji ina yaje amma sai ta tarar da message dinsa, murmushi ta saki bayan ta gama karantawa kafin tace, "Allah ya karemun Kai mijina, ya baka nasara da sa'a a dukkan lamuran Ka". Ta ƙarashe tana ajje wayar ta tashi ta wuce bathroom ta wanko fuskarta ta fito ta fice falo, Kira tayi ta saka order abinci sannan ta zauna jira. 

Ba jimawa kuwa aka kawo mata, kamar yadda taga Nabeel ɗin na yi itama haka ta yi, sai da tasa ma'aikaciyar ta dandana kafin ta sallame ta, ta shiga cin abincin, tana gamawa ta koma daki, sallah tayi sannan ta sake wanka ta shirya cikin wata maroon bodycon me V neck, tayi yar kwalliyar ta sannan ta ɗauki wayarta ta kira gida dan su ɗebe mata kewa, sun dade suna waya dasu mommyn kafin suyi sallama. Ajje wayar tayi ta shiga bin ɗakin da kallo, babu abinda yake damunta irin rashin abinyi, dan in baya nan gabaɗaya takura take, saidai tayi ta kai kawo daga falo zuwa daki, kiransa ta shiga yi bai daga sai kawai ta hakura ta koma ta kwanta, bacci ya sake dauketa .

Tana cikin bacci ta jiyo knocking, tashi tayi dakyar tana murza idanunta, ta kalli agogon bangon dake ɗakin, "To waye ne?". Ta yiwa kanta tambayar dan ta san Nabeel na da spare key a wurin sa. Jin ana cigaba da knocking ɗin yasa ta miqe a fusace tana jan tsaki ta wuce tana mitar shikenan kuma mutum ba zai huta ba a dame shi da buge², Allah yasa ba wani important abu bane in ciwa mutum uwa. Tana buɗe ƙofar ta ga wata baturiya tsaye sanye da kakin sojoji, gaisheta tayi ta amsa sannan tace, "Daga office ne, field Marshal Nabeel ya turoni nazo na tayaki zama saboda tafiyar gaggawa ta tasar musu". Harara ta bita dashi kamar za tace ta koma saboda wani irin haushi ta bata da ta ce wai Field Marshal Nabeel ne ya turota,  Amma da ta tuna waye Nabeel ɗin a waje, tasan abokan aikin sa Maza ma ba sake musu fuska yake ba ballantana kuma Mata, saidai kuma ya za'ayi yayi tafiya bai fada Mata ba, sannan ta kira shi bai daga ba?

 Wuri ta bata ta shige sannan ta rufe kofar ta wuce dakinta ta bar ta a falon, alwala ta ɗauro ta yi sallah ganin lokaci yayi, bayan ta idar ta ɗauki wayarta ta shiga kiransa amma kiran baya tafiya, addu'a ta masa sosai kafin ta kwanta nan Kan prayer mat din ta lumshe idanunta, bitar karatun alqur'ani ta fara har bacci ya fara daukanta da sauri ta miqe tunawa da tayi ta bar mutum a falo, tsaki taja tana faɗin Rashin aikin yi ma dai baiyi ba whl, mutum daga bacci sai bacci, shikenan duk inda ka jibge sai bacci kamar wani kasa.

Wayam ta ga falon ba kowa, murza idanunta tayi sai kuma ta dawo ɗakin da sauri ta leqa toilet wai ko tazo ta shiga bata sani ba amma sai ta tarar nan ma ba kowa, ɗan tabe baki tayi ta koma falon dan ta kunna TV, duk da ita kallo ba wani damunta yayi ba amma dai yanzu da bata da abunyi zata kunna ta rage lokaci .

 Wani Kara taji bangon falon ya amsa gabadaya kafin taji tashin hayaniya cikin hotel din, wayarta taji na ruri, a rikice ta koma dakin hannun ta har rawa yake ganin Nabeel ne, tana dagawa ta jiyo muryar sa a rikice yace, "Assum ki fita, duk yadda za'ayi kiyi sauri ki bar hotel ɗin nan yanzu², karki bi ta elevator, dan Allah ki hanzarta, ki taimaki rayuwata assumiiii". Ya karashe muryarsa a raunane kamar zaiyi kuka, tunani ta tsaya yi har bata san ya yanke kiran ba, wani Kiran ne ya sake shigowa, wannan karon a tsawace yace, "Nace ki fita ko .....". Bata tsaya jin karashin maganar ba ta zari hijabin da tayi sallah ta sanya sannan ta nufi kofa amma jin yadda bangon ke kara yana wani irin girgiza kamar ginin zai rufto, ga wani irin ife² mutane, sai tsoro ya sake kamata, dawowa tayi ta bude window dakin, sa'ar ta ɗaya ba can sama suke ba, ta gama yanke hukuncin dira kawai idanunta suka kyallo mata takardun sa da system ɗin da ya bari. Kiran sa ne ya sake shigowa wayarta, bata kula ba ta juya ta koma, takardun ta kwashe ta sanya cikin hijab ɗin sannan ta taho da gudu tayi tsalle ta fice ta window, tun kafin ta dira ƙasa bangon hotel din ya fara tsatsagewa wani irin Kara kawai kakeji, ga wata farar wuta dake fita da wani irin koren hayaqi  .

A tsugunne ta sauka saboda in ta dira a tsaye zata iya jin ciwo haka in a zaune ne ma bayanta zai iya samun matsala. Bata tsaya ba tabi ayarin masu gudu a rikice, kwata ² bata san inda take jefa kafarta ba, bata taba ganin tashin hankali irin na yau ba. Tana cikin gudun wasu mutane suka sha gaban ta tare da bata umarnin shiga mota su wuce, bata yarda dasu ba hakan yasa ta fara neman hanyar gudu amma sai dayan ya sa mata bindiga a ka. Kuka ta fashe dashi tana roqon su kyale ta amma ba wanda ya saurare ta, haka tana ji tana gani suka tisa keyarta zuwa motar, sannan suka ja da mugun gudu suka bar wurin.



Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol