Free chapter · Read without an account
LOKACI CHAPTER 30
***
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU FULANI
YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's.
FULANI ❣️
***
PAGE 3️⃣0️⃣
Cikin sauri Mahmah ta shige ɗakinta, sosai kukan da Zahra take ya taɓa mata zuciya, gaba ɗaya hankalinta yana can ɗakin da ta baro, zama ta yi a gefen gadonta, hannunta ta ɗora a goshinta, tare da sauke doguwar ajiyar zuciya, kalaman da Zahra ta yi mata na ta maimaita kansu a cikin kunnuwanta.
"Mahmah yaushe rabon da ki kalleni a matsayin ƴarki?"
Lumshe idonta ta yi, ta na jin yanda damuwa ta fara lulluɓeta, ba da son ranta ta yi mata kalaman da tayi mata ba, sai dai ta rasa abin da ya kamata ta yi, saboda ta san duk wani abu da za ta yi mata shi a yanzu, Zahra ba za ta taɓa karɓarsa da zuciya ɗaya ba, ta san ta gina wata iriyar katanga a tsakaninta da ƴarta, ta yanda har ta kai ga Zahra a wasu lokutan tana tantama akan anya itaɗin mahaifiyarta ce.
A karon farko ta fara jin wata iriyar nadama da ba ta taɓa tsammanin za ta ji ta ba, a hankali ta fara tunanin tsayin shekarun da suka wuce da yanda dangantakarsu take kafin komai ya lalace.
Yanzu ta ina zata fara gyara abin da itace da kanta ta lalata sa, ta yaya zata dawo da Zahra ta dawo sakewa da ita kamar dai can baya, ta ina zata fara, hannunta ta ɗora a ƙirjinta, ta na jin yanda yanda zuciyarta ta yi mata nauyi sosai.
Sai dai duk wannan abin da take ji, ba ta jin zata bari auren Zahra ya rushe, ba ta shirya Zahra ta lalata aurenta akan shirme ba, saboda duk da ba ta san wane Muhammad ba, ta na ganin shine mijin da ya dace da ita, kuma ba za ta taɓa barin ta ta rasa wannan damar ba, koda kuwa hakan zai ƙara nesanta ta da Zahran.
Idanunta ta buɗe a hankali ta sauke wata ajiyar zuciyar, sannan ta miƙe ta fito daga ɗakin...
★
Zahrah na zaune a gefen gado ta na kallon Salmah da ke tsaye a gaban mudubi tana ɗaurin ɗan kwali.
"Big Sister dan Allah ki ta shi ki shirya sun zo fa, nama san yanzu suna ƙofar gida, gama ƙarar mota nan" ta yi maganar tana ɗora mayafinta a kafaɗa.
Ɗagowa ta yi ta kalleta, sosai ta yi mata kyau, kanta ta mayar ƙasa.
"Autah baƙin ai naki ne"
Da sauri Salmah ta juyo "baƙina kuma?"
Murmushi ta yi mata bata ce mata komai ba. Kusa da ita Salmah ta ƙarasa ta riƙe hannunta, ta na shirin magana wayarta ta fara ringing.
"Kin bar su a waje kije ki shigo da su cikin ɗakin Mahmah"
"Assalamu alaikum"
Princess ta yi sallama ta na shigowa, dai_dai lokacin da Salmah ta fito daga ɗaki.
"Wa'alaikumus..." Sauran maganar ta maƙale mata a maƙogwaro ta fara nuna Teemah idonta duka a waje cike da mamaki.
"Autah!"
"Princess!"
Suka haɗa baki wajen kiran junansu, cike da mamakin ganin junansu, Teemah ta ƙarasa shigowa cikin gidan.
"Kar kice min wai Big Sister ce matar da Yah Zay'd zai aura?"
"Wallahi ita ce" Ta bata amsa suna riƙe hannun juna. Salmah da iya ƙarfinta ta fasa ihun murna itama Teemah ta biye mata, dan sunyi wata iriyar shaƙuwa a online, kuma sosai suke maganar bikin yayyan nasu, sai dai tunaninsu bai taɓa basu haka ba.
Mahmah ce ta fito daga ɗakinta.
"Salmah yaushe zaki hankali ne?" Ta yi maganar ta na kallon baƙuwar dake tsakar gidan, daga kallo ɗaya da mata ta fahimci duk inda yarinyar ta fito, dukiya ta gama ratsata.
"Mahmah ga Fatima ƙanwar mijin Big Sister, kuma ƙawata"
"A'a Mahmah ni sunana Princess ƙanwar Big Sister ba mijinta ba"
Murmushi Mahmah ta yi lokaci ɗaya taji yarinyar ta kwanta mata a rai, ganin yanda take abu kamar Autah.
"Lah na manta Autah suna waje fa suna jirana ashe" ta yi maganar ta na jan hannun Salmah suka fita daga gidan.
Suna jikin mota a tsaye cikin manyan kaya. "Yahhh ashe ƙawata da na ke baka labari ƙanwar Aunty Zahra ce bansaniba"
Sameer ne ya ce "wai Salmah Autah?"
Ƙifta masa ido ta yi ganin yanda ya yi suɓutul kalam a gaban Yah Khaleel, murmushi kawai ya yi bai kuma magana ba.
"Salamatu kullum sai an bani labarin ki, muna ta cewa zamu zo kawo miki ziyara ashe ma ƙanwar muce" cike da barkwanci ya yi mata maganar.
"Fisabilillahi me ye wani Salamatu" ta yi maganar cikin gunguni ƙasa_ƙasa.
"Idan ba iyayi ba kowa yasan ainayin sunanki Salamatu ko salame, amman wai Salmah"
Ta gefen ido ta hararesa, sannan ta gaishesu, Sameer da Teemah sai dariya suke ganin yanda duk ta ɓata rai tabbacin dai ba ta ji daɗin yanda ya ɓata mata suna ba, iso tayi musu zuwa cikin gidan, har parlown Mahmah, bayan sun gaisa, suka gabatar mata da kansu, a matsayin ƙannan mijin Zahrah, daga nan kuma suka koma ɗakin baƙi inda a can ne Salmah ta shirya musu abinci.
"Wai ina amayar ne?" Sameer ya tambayi Salmah ganin tun da ta ajiye musu abinci da ruwa, ta koma kusa da Princess suna ta shirme a waya.
"Lah ba ra na kirata"
miƙewa ta yi ta nufi ɗakin Zahran, lokacin da ta shiga ta na tsaye gaban mudubi ta na rolling na mayafinta, wani irin ƙamshine yake fita daga jikinta, ba wata kwalliya ta yi ba amman sosai ta yi wani irin kyau, kwallin da ta saka kuma sai ya ɓoye jan da idonta ya yi da kumburi.
"Wow big sister kin ga yanda ki ka yi kyau, wallahi kinyi mugu mugun kyau"
Ba ta san sanda murmushi ya kubce mata ba.
"Autah Allah ya shirya min ke"
"A shirye na ke kamar carbi ai, baƙin sun ƙaraso har da ƙawata a cikinsu"
"Na ji ku ai muje" ta yi gaba tana saka flat takalmi, fita sukayi daga ɗakin, da sallama a bakinsu suka shiga cikin ɗakin. Gaba ɗayansu suka haɗa baki wajen amsawa, tare da ɗago kai suka kalleta gaba ɗaya. Sameer a zuciyarsa ya furta "ma sha Allah banga laifin ka ba dude dan ka ruɗe a wajen nan"
Ƙarasowa ta yi ciki ta samu waje ta zauna, gaisawa sukayi sannan suka gabatar mata da kansu. Cikin sakin fuska itama ta gabatar musu da kanta. Teemah ce ta dawo kusa da ita ta zauna, sai ya zamana sun sakata a tsakiya da Salmah.
"Daman muna son sanin shirinki ne na biki da kuma abin da kika tsara" Sameer ya tambayeta ya na kallonta.
Murmushi ta yi kawai ba tare da ta ce komai ba, toh ita me take shiryawa, idan son samunta ne ma ta yafe duk wani abu da za'a yi.
"Duk abin da kuka shirya ya yi min"
"Kar ki ce min shi kaɗai yake ta shirye-shiryen bikin nan, ko kuma dai kin riga da kun gama tsara komai ke da shi?"
Shiru ta yi ta rasa abin da za ta ce, sai faman juya zoben hannunta da take, Salmah da ta kula da yanayin da ta shiga sai ta yi saurin shiga maganar.
"Yau fa muke shirin tsara komai da daddare nan"
Teemah ta ɗaga hannunta ta na dariya "Ni dai ina team ɗin amarya gaskiya"
Harararta Khaleel ya yi "gaba ɗayanmu team ɗaya ne ni da Salamatu, ke da Sameer, mu muna ɓangaren amarya, ke kuma ango"
Rama hararar ta yi "Big sister nidai ina tare da ke" cike da shagwaɓa ta yi maganar ta na riƙe hannun Zahra.
"Kar ki damu namesake duk in da kike so anan zaki zauna" sai ta juya wajen Khaleel " a bar min ita a tare dani tun da ta na so"
"Yanda kika ce haka za'ayi babbar yaya"
Murmushi tayi, ringing ɗin wayar Sameer ce ta katse hirar da suke. Duba mai kiran ya yi ganin sunan Zay'd ne ya sa shi murmushi, ɗaga wayar ya yi ya kai kunnensa.
"Hello dude"
Daga can ɓangaren Zay'd ya ce "ya ne fatan kunje lafiya?" Ya tambayesa zuciyarsa cike da fargabar kar ta yi wani abu da zai sa su fahimci babu jituwa a tsakaninsu.
"Alhamdullah mun je lafiya ga mu ga amarya, a gefe ɗaya kuma a za'a jiƙa maka aiki dan Princess da Autah sun haɗe kai, kuma dai kasan abin da hakan yake nufi ko?"
Murmushi ya yi "bar su dude duk zan iya dasu, bata wayar"
"Gashi Madam" ya taso ya miƙa mata wayar.
Dasauri ta kallesa, sannan ta kalli wayar "waye?"
Murmushi ya yi kaɗan "me girma ango"
Karɓar wayar ta yi ta kai kunnenta "Hello" ta ce ƙasa_ƙasa.
Ajiyar zuciya ya sauke daga can ɓangaren.
"Falmata"
Dum! Zuciyarta ta buga da ƙarfi babu shiri ta kira sunansa "Muhan"
"Na'am kina lafiya, ya kuma baƙin?"
Ɗagowa ta yi ta kallesu, sannan ta ce "Alhamdullah"
"Na yi kewarki Besty"
Shiru ta yi masa "Zan zo na ganki, kiyi min kwalliya kinji" da wata iriyar murya yayi mata magana kamar ba ta sa ba.
"Muhaan" ta ja sunan nasa, dan ta na jin yanda duk suka zuba mata ido. Miƙawa Sameer wayar ta yi. Salmah sai taɓo Princess ta ke, suna dariya dan ba ƙarya yana yin da akayi wayar ya tafi da su, duk da ba su san abin da yake ce mata ba, amman yanda take kiran sunansa "Muhan" abin ya mugun burgesu, watakam ba zata ce Muhammad ko Zay'd ba, sai Muhan.
"Autah an kashe min zuciya" Teemah ta faɗa tana dafa zuciyarta.
"Ni ai kullum sai anyi min raga_raga da tawa" ta bata amsa tana dariya.
Daga haka suka maida hankalinsu kan abin da ya kawo su, Teemah ce ta yi wa Salmah bayanin duk abin da suka shirya, wanda sosai hakan yayi mugun tafiya da Salmah, dan an shirya harka cikin girma da mutunci, event huɗu suka shirya, duk ciki kuma babu wanda bai burge Salmah ba, exchange sukayi na number's, bayan sun gama suka ce za su tafi, sallama suka yi Zahra ta miƙe ta ce su jirata, hannun Salmah da Teemah ta ja suka shiga cikin gidan.
Wata jaka ta ɗakko me kyau ta na da girma ta bawa Teemah "ki kawai Ammie" sannan ta bata ƙarama wadda ba ta kai wannan ba ta ce ta "Abhie"
"Autah ki kai musu saƙonsu yana kitchen" daga kallon da tawa Autah ta fahimci me take nufi, Hannun Teemah ta ja ta ce ta rakata. Bayan sun fita wardrobe ɗinta ta buɗe sababbin abaya guda biyu ta ɗaukarwa Teemah ta haɗa mata da kayan kwalliya, a cikin jaka ta haɗa mata itama sannan ta fita, lokacin da ta fito sun shigo yiwa Mahmah sallama, bayan sun gama har ƙofar gida suka raka su, bayan sun tafi suka dawo cikin gidan.
★★★
Lokacin da suka koma ya na zaune a part ɗin Ammie ya na jiransu, daga yanayin da suka shigo ya sauke ajiyar zuciya dan ya tabbatar da babu wata matsala da ta faru, kayan hannunsu suka ajiye kowa ya nemi waje ya zauna. Teemah ce ta bata saƙonta da Abhie, sannan ta bata nata, sai kuma kayan snacks ɗin da Salmah ta ɗakko musu a kitchen, sosai Ammie ta ji daɗin aiken, ta kuma yi godiya. Shi kuwa gogan ya fi kowa farin ciki dan ba su ta yiwa ba shi ta yi wa, a take yaji wata iriyar ƙimarta ta ƙaru a cikin zuciyarsa.
Washe gari Ammie suka tafi haɗo lefe, kwanansu uku a can suka dawo, duk wani abu da amarya zata buƙata sai da suka haɗo mata, Itama Teemah anan tayo musu siyayya da Salmah na duk abin da za su buƙata a bikin, kusan duk abin da suka siya sai da ta turawa da Salmah, suna dawowa kuma aka saka ranar kai lefe, a take ɓangarori biyun suka fara shiri.
★★★
Wani irin gyaran jiki a ke wa Zahra, takanas Mahmah ta ɗakkota da ga Maiduguri, haka kuma kullum sai Inna ta zo tunda gidanta, ta yi mata nasu na tsofaffi, ko tsakar gida bata fitowa, duk abin da zata yi a cikin ɗakinta take, gaba ɗaya gidan ya baɗe da wani irin ƙamshi da ake turara mata jiki da shi.
Ta na zaune tana duba wayarta, har wajen massage sai da ta duba, gaba ɗaya babu wani saƙo daga Muhan, ajiye wayar ta yi sannan ta kalli zoben hannunta, fara juyasa ta yi a hankali, bata taɓa tunanin cewar da ya yi ya ƙyaleta ta yi duk abin da ta gama zai dameta ba, sai yanzu tana jinsa yana waya da Salmah, amman ita ba zai neme ta ba, duk da cewar ita ce ta nemi hakan gashi kuma abin yanzu ya zo ya na damunta, gaba ɗaya sai ta ji auren ya ƙara fita daga ranta.
"Big sister" Salmah ta katse mata tunanin da ta ke yi.
"Yah Zay'd ne ya turo min wasu hotuna yace na zo na nuna miki"
Ɗagowa ta yi ta kalleta, a take idonta ya cika da hawaye, watakam ita bata isa ya tura mata ba, sai dai ya turawa Salmah, gashinan tun ba'a je ko ina ba, rainin da take jin tsoro ya fara a tsakaninsu. A take Salmah ta kula da yanda fuskarta ta sauya, ajiye wayar ta yi ta riƙe hannunta.
"Big sister har yanzu dai damuwar ce ba za ki cirewa ranki ba?"
Ajiyar zuciya ta sauke "ba za ki gane ba Autah" daga haka ta ja bakinta ta tsuke.
"Gobe za'a shiga satin biki kuma gobe za'a kawo lefe"
"Nasani" ta bata amsa kai tsaye.
Mahmah ce ta shigo ɗakin da sallama, kallon Zahra ta yi yanda fatarta take ɗaukar ido saboda gyaran da ake mata, ga wani irin ƙamshi da ya ke tashi a jikinta.
"Zahrah za ki tafi gidan Innah da daddare ki kwana a can, idan ya so bayan an kawo lefe sai ki dawo ko bayan magriba ne"
Sunkuyar da kanta ta yi ba tare da tace mata komai ba.
Ita dai Salmah ƴar aike ce, dan haka a take ta aikawa yayanta da saƙo, suna a haka sauran yayanta suka shigo, tun ɗazu ta ji zuwan su, amman bata fita ba, dan taga wannan zuwan na su ya canza salo, akan yanda suka saba, babu rashin kunya ko wani abu duka suka gaisheta, sannan kowaccen su da akwai abin da ta bayar nata gudunmawar da za su bawa ƴan kawo lefe, zama suka yi suka zagaye ta, kowa na ƙoƙarin ya ja ta da hira, sai dai ta kasa sakin jiki ayi hirar...
★★
Bayan sallar magriba ta shirya ta yi wa Mahmah sallama akan zata tafi, ta ce Salmah ta rakata ta ce ba za ta je ba, dan haka ta fito da niyyar tafiyarta ita kaɗai.
Turus ta tsaya ganinsa a tsaye a jikin motarsa, hannayensa a ƙirjinsa, idonsa kuma a ƙofar gidan, dan haka tana fitowa idonta ya faɗa cikin nasa, ɗauke kanta ta yi kamar ba ta gansa ba ta wuce, a take yanayin fuskarta ya sauya.
"Besty!" Ya kira sunanta ya na bin bayanta.
Lumshe idonta ta yi a hankali ta na jin wani yanayi mai kama da kewa da ya kira sunanta, dan sun kusa sati bai kulata ba, ita daman ba kulasa take ba, juyowa ta yi ta kallesa, ba tare da ta amsa ba.
"Shi ne kina kallona zaki wuce?"
"Yaushe na ganka na zata ai wajen Salmah ka zo"
Murmushi ya yi, amman gudun kar ya ja ta da rigima, sai ya ce "wajenki nazo ba wajenta ba"
Harararsa ta yi ba ta ce masa komai ba, wajen motarsa ya koma, buɗe mata wajen me zaman banza ya yi.
"Zo ki shiga"
Kallonsa ta tsaya yi ba tare da ta motsa ba.
"Please mana"
Ƙarasawa ta yi ta shiga, rufe mata ƙofar ya yi, sannan ya zagaya driver seat ya zauna, ya na rufe ƙofar wani irin ƙamshi ya daki hancinsa, ɗan dakatawa ya yi yana kallonta, a hankali ya ja numfashi dan ya na son tabbatar da ga ina ƙamshin ya ke, a take ya fahimci daga jikinta ne, kallonta ya ke ta na zaune cikin nutsuwa kanta a sunkuye, ji yayi wani irin abu ya tsaya masa a ƙirji.
"Me yasa za ki shafa turare me ƙarfi haka ki fita bayan kinsan fita za ki yi, da kenan a haka za ki shiga cikin napep wani ya shaƙi ƙamshin da yake fitowa daga jikinki?"
Ya yi maganar cikin wata iriyar murya mai ɗauke da zallar kishi, ya na kallonta kai tsaye.
Ɗagowa ta yi da sauri ta kallesa cikin mamaki.
"Wai me ya sa kake min magana cike da ba da umarni ne? Ka dena bana son Muhan, sai kace wani yayana haba dan Allah ka bari"
Ƙara matsowa kusa da ita ya yi.
Ko me ta tuna koma sai ta rufe bakinta da hannunta ta ja da baya, ganin yanda tsoro ya bayyana a fuskarta, duk da yanda ta ɗaure fuskar, sai ya ja baya ya koma kan kujerarsa ya zauna daidai.
"Kar ki kuma saka turare ki fita na gaya miki, daga yanzu ma idan zaki fita kiyi min waya, ko bananan zan aiko Khaleel ya kai ki"
Buɗe baki ta yi za ta ba sa amsa, sai ta fasa, gyaran jikin da a ke mata ne yasa turaren ya zauna a jikinta, ita kanta ƙamshin yana damunta, saboda ko ya ta motsa sai ya tashi, ita kanta ya ishe ta, mayar da kanta tayi ƙasa ta fara wasa da zoben hannunta...
FULANI
***