Free chapter · Read without an account

Chapter 46

by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI

***

***

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐.
Chapter 46

 Da sauri ta ɗago kanta daga duƙen da tayi, tana zare idanuwanta cike da tsoro, jikinta ya hau rawa.
    Jin shiru babu sauti yasaka Junaid  shiga cikin ɗakin, yana raba idanuwan shi, can ya hangota ƙasan gado, ta firfito da duka idanuwanta waje tana kallon shi da yanayin tsoro.
     Tausayinta ne ya lulluɓe Junaid, yacigaba da takawa    zuwa inda take zaune, yana karantar yanda take sake takurewa jikin gado kamar zata shige ciki ta ɓoye.

   Tsuhunnawa ya yi kusa da ita, yana ƙarewa firgitacciyar fuskarta kallo, zuciyar shi na dokawa da kamar da ke yi ma shi gizo akan fuskarta.
     Hannunta ya kama ya riƙe, cikin taushin murya yave da ita.
   "Ki nutsu bazan cutar da ke ba kinji, tambayarki kawai zan yi."
   Ya faɗa cikin kwantar da murya.
    Ƙare ware idanuwanta ta yi akansa, tana kallon shi har lokacin jikinta bai daina rawa ba.
    "Mu...mu..Muhammad!." Ta faɗa da raunaniyar murya, sai kuma kuka ya kubce mata me ƙarfi, da ƙarfi ta faɗa jikin Junaid ta ruƙunƙume shi da ƙarfi tana sambatun daya kasa gane me takr faɗi.

    Rasa abin yi Junaid ya yi, domin kuwa ta shammace shi, jin kukanta ya ke yana hawar ma shi kai, ga tsananin tausayinta daya lulluɓe shi.
    Ta ɗauki lokaci a haka yana shafa bayanta da sigar rarrashi, har ya samu ta daina surutan tayi shiru tana shehseka.
   Da  ita ya tashi a jikin shi ya nufi wajen fredge ya ɗauki ruwa, da dabara ya zameta a jikin shi ya zaunar da ita akan sofa, ya kafa mata goran ruwar kamar yarinya ƙarama.
    Tas ta shanye ruwan tana sauke ajiyar zuciya, imbanda kallonta babu abin da Junaid ke yi.
   Lallaɓawa ya yi zai zare hannunta daga na shi, karaf idon shi ya sauka akan zoben da ke cikin yatsarta ta tsakiyya.
   Ba iya idanuwan shi kyallin zoben ya haska ba harda can cikin zuciya da kwanyar shi.
    Da sauri ya kama hannun nata, ya raba yatsunta biyu yana ƙarewa zoben kallon hantar cikin shi na kaɗawa.
    Cike da tuhuma ya ke kallon fuskarta zuciyar shi na sauya salon bugun da take a ƙirjin shi, cikin sauƙaƙiyar hausar shi ya ce da ita.
    "Zobe, Muhammad, a hanunki kuma to tayaya?."
   Ya jefa mata  tambayar yanayin shi na sauyawa lokaci ɗaya.
 
   Fizge hannunta ta yi tare da ɓoye shi a ƙirjinta ta ƙanƙame.
    Zaman daɓas Junaid ya yi, kan shi na sarawa da ƙarfi, cikin rawar murya kamar me shirin fashewa da kuka yace da ita.

   "Muhammad, wannan zoben na  Muhammad ɗina ne, tayaya, tayaya ya zo hannunki bayan daga ni sai shi muke da wannan samfari?."
  Junaid ya faɗa cikin tsumayin amsar da zata bashi, ta kasance tana da dangane da Muhammad ɗinsa.

    Wani tunani ne ya Haska a kanta, kamar an fizgo kalmar daga bakinta ta ce. "Junaid?." kamar me tambaya kamar meson tabbatarwa, zuciyarna ta soma harbawa da tsananin ƙarfi, kewa  gami da raɗaɗin azabar rabuwa da masoyinta ya soma dawo mata nan take a lokacin.
    Da hanzari Junaid ya sake tashi ya riƙe hannunta da ƙarfi ya soma faɗin.
   "Junaid, yes ni ne Junaid abokin Muhammad, faɗa min ina Muhammad ɗina ya ke?." ya tambayeta kamar me magiya.

Rayuwarta ita kanta, zuwa haɗuwarta da Muhammad, zamansu aurensu shaƙuwa da soyayyarsu sune suka soma dawo mata tiryan-tiryan kamar yanzu komi ke faruwa.
    "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, Muhammad sun raba ni da shi, ya tafi bansaniba Muhammad ɗina yana ina to???".
Ta shiga sambatu haɗe da kuka me ƙarfin, a kuma lokacin ne wani babban lamari ya soma faruwa da ita, jini, jini ne me gauraye da baƙi ya soma ɗisa daga hancinta ɗis-ɗis, da farko a hankali ya fara kamar ba wani babban abu bane zai iya tsayawa.

Amma daga baya, bayan Junaid ya tarba hannayensa ya riƙe fuskarta, sai jinin ya soma zubowa da yawa, wani ta hancinta wani ta bakinta.

    Cak tunanin Junaid ya tsaya na wani ɗan lokaci, ya ƙure jinin da ke taruwa a hannunshi da kallo, yana bincike da nazartar wani abu, wani tunani daya nemi bugar da kwanyar shi nan take a lokacin.
    Nan take tunanin ranar da aka ƙera zoben ta faɗo ma shi, da kuma yana  yin da suka kasance.

     ***    ***   ***   **
"Wow wannan kyawawan Rings ɗin fa, nawa ne price nasu gaskiya sun burge ni."
Muhammad ya faɗa muryar shi aɗan sake shi ba dariya ba haka kuma shi ba murmushi ba.

    "Nasan dai baka da wanda zaka siyawa Ring, ko kayi girlfriend ne bani da masaniya?."
   Junaid ya faɗa yana amsar zoben ya jujjuya shi, sannan ya mayar a a mazaunin shi.
    Muhammad na kallon ɗan ƙarin Ring box ɗin ya ce.

   "Banida kowa sai Allah, amma kuma ai ina da aboki me son farinciki na, haka kawai nike maka sha'awar shi imbaka a matsayin gift." 
    Cak Junaid ya tsaya daga takon da yake yi ya waiwayo gaba ɗayan shi, da harshen larabci ya ce da Muhamma.

«أحقًّا تقول ذلك؟ أحقًّا يا محمد أنك معجب بي وتريد أن تهديني خاتمًا؟»

(Dagaske ka ke? da gaske kake Muhammad ni kake sha'awar bama kyautar zobe?.)

Sai Muhammad ya gyaɗa kai ya bashi sauƙaƙƙiyar amsa ta hanyar faɗin.
«هل هناك شخصٌ آخر يمكن أن يكون مهمًّا بالنسبة لي بعدك؟»
("Ina da wani ne da zai zama me muhimmanci a gare ni bayan kai?)

   Da wani irin ƙarfi Junaid ɗin ya janyo Muhammad ya rungume shi tare da sumbatar gefen fuska zuwa kafaɗar shi yana faɗin cikin maɗaukakin fatinciki.

«أحبك كثيرًا يا حبيبي ويا سندي.»
(Ina sonka da yawa masoyina kuma ɗan uwana.)

Daga nan sai Junaid yaja shi zuka zaga can ciki ta hanyar tambayar ma'aikatan wajen inda ake ƙirar zobba nan take.
    Kuma koda suka je wajen bai cire hannun shi daga cikin na Muhammad ba yana nan riƙe da shi tamau kamar zai gudu ya barshi.
    Ya bada samfari ya kuma bada harafin da yake so tagwayen zobban su kasance da su.

Koda aka ƙera zoban, da wannan bayyanannar fara'ar a kan fuskar shi, ya miƙawa Muhammad yace ya ɗauka.
    A tsamanin shi Muhammadi zai ɗauki me harafin sunan shi Junaid, sai yaga ya ɗauki me harafin M, sai ya yi murmushi yana tuna yanda wasu abubuwan na Muhammad suke kasancewa daban da tunanin shi dama saura  mutane.
 
  Kuma har zuwa ranar da ta kasance ranar rabuwarsu, zobban suna tare da su, kusan koda yaushe Muhammad na yawan tambayar shi ina na shi zobe, idan ya manta bai mayar ba daya tashi barci, Muhammad ɗin ya dinga mita kenan yana ƙarawa, daga ƙarshedai Junaid ya gaji da mitar Muhammad ɗin ya haƙura ya daina yawan cire zoben, sai idan yaji ya takura ma shi da yawa.

***   ***
A yanzun kuma da yaga zoben a wani wajen, a wajen wani na daban ba Muhammad ɗin shi ba, sai ya ƙagautu da jin labarin ta yanda aka yi zoben ya zo hannunta,yasan ba ƙaramin daliki zai saka Muhammad ɗin bayar da zoben ba nan take ga wani waninma mace, wacce babu ita a tsarin rayuwar Muhammad.

Rarrashi da tausasawa sune abubuwanda ya saka cikin kalamanshi daya nace da yi mata tambaya har saida ta buɗe baki, duda cikin kuka me tsanani ta fayyace ma shi komi, ta fara bashi guntun labarinta daya fahimta a baibai, sannan ta ɗora da bashi labarin haɗuwarta da Muhammad, zuwa aurensu zuwa gwagwarmayar da suka yi ita da Muhammad, daga barowarta gida har zuwa taimakonsu da Malam ya yi, da kuma zamansu a hannun Makafa da taimakon da Aljani Kanzul ke yi musu.

Tashin hankali yayi kaɗan akan abin da Junaid ke ji na baibaye ƙirjin shi, ya  kasa magana ya kasa motsi ya kafe waje ɗaya yana fizgar numfashi, haɗi da kallon uban jinin da ya zuba daga baki da hancinta.

    Ya ɗauki lokaci me tsayi yana jin zafin shesheƙar kukanta na ratsa zuciyar shi, a labarin data bashi ya tabbatar da gaskiyarta, yasan Muhammad yasan waye shi kuma yasan abin da zai yi da wanda ba zai aikata ba, babban abin da ya idasa saka shi yarda da ita 100% bai wuce yanda ta bashi labarin Makafa da alaƙar shi da Muhammad ba tiryan-tiryan da kuma irin rayuwar da suka yi, yasan kaf duniya a yanzun dai daga ita sai shi kaɗai suka san waye Muhammad ciki da bai, suka kuma san abin da ke lulluɓe cikin rayuwar shi.

    Rintse idanuwan shi da suka kaɗa suka yi jazur ya yi, sai kuma ya buɗe su da tsananin ƙarfi tare da tsaida su daidai saitin lafafen ciki Zunaina, ya haɗiyi yahu busashe me ɗaci sannan ya yi maganar da baisan ya yita a fili ba.

   "A cikin nan ajiyar Muhammad ce a ciki ko? jinin Muhammad ne kwance a ciki." Ya yi maganar maganganu da farar peppar da Doctor ya miƙa ma shi me ɗauke da bayanan bincike da aka yi mata har aka gano tana ɗauke da ciki ɗan ƙarami sosai wanda bai wuce kwanaki kaɗan ba.  
  Dalilinda ya saka ya sake tausaya mata kenan ya kara rabuwa da ita ganin bata cikin cikakkiyae nutsuwa da tunaninta, dalilin da yasa ya bawa Uncle shawarar su taho da ita gida taɗan kwana biyu daga baya sai a nemi dangi ko ƴan uwanta, yasan a lokacin shima Uncle yaji tausayinta matuƙa shiya sa baija zancen ba ya amince suka taho da ita. Ko bayan da suka isa gidan baya jin ƙarfi a jikin shi, hasalima Doctor ya bashi shawarar ya samu cikakken hutu, da fari Falo yace ta zauna, amma kuma sai yayi tunanin wataƙila ya jima idan ya shiga duba jinin Saminaka, sai ya kira ɗaya daga cikin ma'aikata matan yabata umarni ta gyara ɗakin da ke can lungu kaɗan, idan ta gama takai baƙuwar ta bata dukanin abib buƙata, idan akwai wata damuwa ko matsala ta sanar musu.
   Sosai ya yi mamaki lokacin da Uncle ya ƙara da faɗin.
   "Kuma ki kula da shan maganinta akai-akai batada wadatacciyar lafiya, idan kinga wata matsala a tare da ita ki nemi ko ni ko Jay."
   Daga ranar basu sake bi takanta ba hasalima ya manta da ita shaf, saboda abin da ya faru tsakanin Mommy da basu gani ba da kuma birkicewar da Fahad ya yi, da kuma samun sauƙin da Saminaka ya yi a ƴan kwanakin sosai suka duƙufa wajen bashi cikakkiyar kulawa suna kuma kasancewa tare da shi.
    A ranar daya tuna da ita ranar da komi ya fara saituwa ne, bayan ya amso maganin Saminaka ya sameta tsaye tana leƙen shi daga ƙofar ɗakinta, da ace tasan zai juyo lokacin zata iya saurin shigewa  amma daya mameta ya juyo suka haɗa ita sai taja da baya da sauri tana ɓarin jiki ta shige ciki, daga ranar ya soma ƙoƙarin duba lafiyarta koda sau ɗaya ne a rana duda ya lura babu wani sauyi a lamarin nata....✍🏻
Karku manta da danna min like share and comment.

AMANAR BILYN ABDUL CE

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol