Free chapter · Read without an account

BABI NA ARBA'IN DA HUƊU

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu 

A KWANA A TASHI Baffa ya gama jarabawar shi ta ƙarshe a jami'ar Nijeriya, Nsukka, a gefen Law. A lokacin gamawar su ne akayi convocation a makarantar. Daddy da Umma harda Farida da Ahmad duk sun tafi convocation na Baffa. Sunyi hotona masu kyau na zuri'a. Tun chan Daddy ke faɗi wa Umma ze sa a wanko mishi hoton ayi enlargement su aje a parlourn su. 
Farin cikinsu marar misaltawa ne saboda sun san inda suka fito. Yanzu Farida ce kawai ta rage musu tayi nata karatu. Sun san sunyi ƙoƙari a ƴaƴan su da taimakon Ubangijin su. 

Nigerian Law School dake Lagos Baffa ya tafi for his one year programme. Ya ma jima yana tunanin wace Law School din ze tafi tsakanin Abuja da Lagos, kafin dai ya yanke shawarar zuwa Lagos duk da da Abuja da Lagos duk akwai opportunities. 
Bayan one year programme nashi, yayi Bar Finals nashi se kuma Call to Bar. Bayan Call to Bar na Baffa yaje one year service inda ya samu direct posting a Lagos. 
Bayan bautar ƙasar Baffa ne ya fara aiki a corporate legal department. Yana lokacin aikin shi ne yaga wani scholarship kamar wasa Ahmad ya turo mishi. 
     “Why don't you try this one, Baffa? This corporate thing get mad money o. Abeg fill am up and do your masters abroad”
“You think I go get am?” Baffa yace waya na wurin kunnen shi yana sauraron ɗan uwan shi. 
   “Wetin go stop you from getting am? You can do it man”
       “Okay lemme try my luck”
        “Please do”
Kashe wayar suka yi Baffa ya tsaya yana kallon link da Ahmad ya turo mishi ta Whatsapp yana nazarin cikawa. 
 “Bismillah” ya faɗa tare da clicking link ya shiga ya cika shi for his LL.M. Yana gama cikawa ya kira mahaifiyar su. Gaisawa suka yi tana tambayar shi ya garin Lagos. 
“Umma garin nan bashi da dad'i. Da nasan haka yake Allah da Abuja zan tafi Law School ɗina. Mutum fa bashi da hutu tun ƙarfe biyar na safe ka fito kana biyar Bus kullum. Ni ina tunanin zan je naga likitan ƙwaƙwalwa kar su fasa min kai a garin nan”
Murmushi Umma tayi “Wannan raki Baffa? Shekarar ka nawa chan to?”
   “Umma se idan kina garin nan tukuna zaki gane. Nothing feels right in this Lagos. We've so many mad people here”
     “Dont forget you be barrack boy oo”
Dariya Baffa yayi “Amma kin san Umma ni bana cikin yara marar ji”
   “A'a yanzu dai ka girma kayi hankali. Ma sha Allah”
    “Umma, na kira Farida jiya naji ko ta isa Sokoto lafiya bata ɗauka ba. Kunyi magana?”
      “Eh, lafiya ƙalau. Nayi waya da ita a wayar Yaya”
     “Nata wayar fa?”
 “Tace min bata gani ba an ɗauke”
   “Bata gani ba kuma?”
    “Sacewa akayi Baffa”
     “Idan kunyi waya kice ta kira ni da wayar Yaya” 
     “To yayi zan faɗa mata. Amma dai dan Allah idan kasan zaka takura kanka kar kuyi maganar siye mata sabuwar waya yanzu. Kaga mahaifin ku ma cikin watannan ze yi retire nasan kuɗin shi zasu fito da wuri se ya saya mata. Kar ku wahalar da kanku bana son ku yi ta ɗawainiyya baku tsaya kun gina kanku ba”
     “Umma me ya kawo wannan maganar kuma? Farida ba ƙanwar mu bace? Idan bamu mata ba, wa ze mata? Dan Allah ki dena magana irin haka”
   “Na dai faɗa maka”
Shiru Baffa yayi. Chan kuma yace “Dama na kira na faɗa miki scholarship na cika a UK Umma”
           “Europe?”
 “Yes, part of Europe”
      “Baffa tafiya zaka yi ka bar mu?”
Da sauri Baffa yace “Umma baki so? To an dena maganar”
Murmushi Maryam tayi tace “Wasa nake maka Baffa. Masters ka cika ne?”
       “A'a Umma idan baki so an fasa. Ko na samu ma ba zan tafi ba”
  “Wasa nake maka fa Baffa. Ai cigaban ku shine nake dubawa a kodayaushe. Allah yasa albarka yasa a dace Baffa”
   “Amin Umma, nagode”
     “Karatu zaka cigaba a chan ko aiki ne?”
         "A'a, Master's ne nake so nayi, karatu”
             “Allah yasa a dace Baffa”
     “Amin Umma”
“Yanzu yaushe zaka taho gida? Ka jima baka shigo ba”
   “In sha Allah idan na samu lokaci zan zo. Tare da Ahmad nake so mu zo”
        “To yayi Allah ya kawo ku lafiya”
              “Amin Umma”
    “Nace kin gama shawarar inda zaku zauna bayan retire'n Daddy?”
Ajiyar zuciya Umma ta sauke. “Har yanzu ina tunani Baffa. Bana tunanin ina iya sake zama Arewa bayan kwashe shekaru kusan talatin bana chan. Kuma ina tambayar kaina ko zama kudu ze yi a gare mu. Ga kuma Farida chan mun tura wurin Yaya domin jami'ar ta”
“Ba zan sa miki tunani a cikin kai ba Umma. Kiyi tunani da kyau kika ga abinda yafi”
      “Ina kan yi. Allah yasa mu dace”
     “Amin. Shi Daddy be ce komai ba?”
    “Yace nayi shawara nagani amma ina ga zamu yi shawarar tare saboda kaina ya ƙulle da tunani”
Gyaɗa kai Baffa yayi kamar Umma na ganin shi. 
   “Kai Baffa kana ma sa aure a rayuwar ka?”
Shiru Baffa yayi se chan yace “Baya a cikin raina yanzu. Idan na samu scholarship nayi Master's, maybe I'll go for it”
Fuska Maryam ta takure tace “Maybe kenan? Baka son companionship ko akwai me cire maka shi a Lagos ɗin?”
   “Umma ba haka ne ba. Ina so na ƙara tsayawa ne shiyasa”
       “To yayi shikenan. Ko Ahmad da ya gama tsayawa ana mishi maganar aure amma har yanzu yaƙi cewa wani abu. Haka ze zauna a Abujan ba aure? Ka bashi shawara fa”
“Umma kar ki damu. Ze yi auren in sha Allah”
   “To Allah yasa amma ga yara manya manya ba wanda ya tashi aure, haba!”
       “Tun ina secondary nace ku min aure kika ce ba za'a yi ba” Baffa ya zolaye Ummansu
          “Tunda a secondary kana da kuɗin kula da ita ba”
Dariya Baffa yayi Maryam na tuna wannan lokacin domin kawai yaga wata yarinya wacce suke da bambanci addini da al'ada da yaji ta kwanta mishi a rai.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol