Free chapter · Read without an account
BABI NA ARBA'IN DA SHIDA
by Zainab · Zaren Rayuwar Mu
Zaren Rayuwar Mu
AUREN SHAHIDA ne ya tashi ana ta shirye-shiryen biki an fitar da invitation card. An fidda ashoebi tun ba yanzu ba. Yaya Hauwa ce ta siya mana ashoebi nida Zainab kuma itace ta kai mana ɗinki aka mana iri ɗaya ta biya kuɗin ɗinki. Ganin haka yasa na siya mana mayafi iri ɗaya da high heels half cover shoes.
Kayan Shahida na biki ɗinkin su yayi kyau fashion designer ce anan Abuja ta mata design. Za'a yi ƙunshi da dinner se buɗar kai da za'a yi.
Zaid ya ƙara min kuɗi yace nayi biki dasu. A cikin kuɗin nasa man mota nayi full tank saboda zuwa gidansu.
Ranar ƙunshi mun tafi gidansu a chan za'a yi event ɗin amma bama ciki, kawayen Shahida kawai ne a wurin. Anyi decoration me kyau me ƙayatarwa dama ga gidansu babba ne yana da girma da faɗi. An jera pillows na sarauta an aza flower vases na gargajiya wanda ya ƙara sa yayi kyau.
Mu muna ciki ana yiwa Yaya Hauwa lalle idan aka gama za'a yi wa Zainab nidai nace bana so saboda ba zan iya zama a min lalle ba. Har kitso ma sun yi amma ni ban yi ba nafi son ganin sumar kaina haka babu kitso.
Ni na fara wucewa gida da dare saboda yadda nake jin kwanciya kawai nake so nayi duk na gaji kuma ba wani aiki nayi ba.
Washegari ranar dinner har wurin kwalliyya muka tafi. Yaya Hauwa ce ta matsa min tace idan ba'a yi kwalliya ba aka sa irin wannan ashoebi ba'a yin kyau shiyasa na tafi muka je wurin kwalliya. Bayan an gama muna kwalliya harda hotona muka wuce wurin dinner.
A waje na tsaya a cikin mota nayi hoto me kyau na tura wa Zaid ta Instagram. Ban fito daga motar ba ina jiran koda reply ne na samu a wurin shi. Kamar yasan jira nake naga ya turo saƙo “My God, Diza!. My Diza is beautiful. I love you”
Murmushi nayi ina ƙara jin ƙarfi a jikina na fito motar na shiga ciki. Mutane ne a ciki an cika moderately. Decoration yayi kyau iya kyau har wani kamar crystals nake gani. Da akwai flowers a kowane table na baƙi wanda ya ƙara fito da kyawun wurin. Waƙar Beyond by Leon Bridges ce take tashi ahankali in slow rhythm.
MC ya bada announcement ga amarya nan za'a shigo da ita. Ita da bridesmaids nata suka shigo kawayen ta kyawawa masu kyau sun fito abin su daga gani sun waye ƴan gayu.
Ba'a wani jima da fara bikin ba naji duk na gaji ina ma so naje gida amma nasan babu inda zan tafi.
Duba hall ɗin nake da idanuna ina duban ko Zaid ya shigo ina tsammanin ganin shi amma ban gan shi ba. Waya ta na jawo daidai lokacin da kiran shi ya shigo se na tashi daga inda nake na koma inda ba'a jin hayaniya.
“Ban gan ka ba. Ba zaka zo bane?”
“Yanzu muka zo tare da Muhammad. Shi ya shiga ciki yanzun nan”
“Kaifa? Ba zaka shigo ba?”
“Ina so na shigo ciki, hayaniya ce bana so”
“No, please ka shigo. Kiɗa kawai ne babu hayaniya”
“Alright” Zaid yace
Tsaye nayi ina jiran shigowar shi se gashi ya shigo. Yana sanye da blue kaftan harda babbar riga ban taɓa ganin Zaid da irin wannan shigar ba. Kanshi babu hula ga sumar ta taru gyaran ta kawai yake.
“Kinyi kyau” ya faɗa min yana kallo na kamar be taɓa ganina ba “Amma kin fi min kyau ba da wannan kwalliyar ba amma kuma kinyi kyau”
Murmushi nayi ina kallon shi cikin idanu “Ina hular ka?”
“Har nasa na cire. Da kina gida da na tambaye ki nasa ko na cire”
“Da ka sa kayan ka. Ka ga da ka fito daidai”
“Yanzu ban fito daidai ba?”
“This is 8/10”
“Akan rashin hula?” Zaid yace tare da jawo ni a jikin shi “You look beautiful, Diza”
“Thank you” na faɗa mishi murya ƙasa-ƙasa “Kaima kayi kyau” na ƙara faɗa ƙasa-ƙasa sosai
“I heard you. Kika ce nima nayi kyau. Baki so naji ne?”
Murmushi nayi ban ce komai ba.
“Bari naje naga ƙanwata” yace tare da riƙe hannuna muka tafi wurin Shahida tare. Gaban ta ya tsaya yana mata magana tana mishi murmushi tana bada amsa. Mijinta na gefe shima yana murmushi ga abinda Zaid ke faɗa. Bayan ya gama magana dasu ya aje kuɗi a cikin basket yanzu ba'a kari se de a ajiye nima na aje nawa ɗazu.
Hannuna ya riƙa kafin mu matsa ko ina cousins ɗin su suka zo wurin Zaid suna magana dashi. Cire hannuna naso nayi a cikin nashi naji ya riƙe sosai se ban ƙara ƙoƙarin cirewa ba.
Ya gama magana dasu muka dawo wurin sauran ƴan uwanmu. A tare dasu muke har aka gama shagalin da ake. Da yake a motoci daban daban muka taho yasa ko yanzu ba tare da Zaid muka wuce ba.
Washegari da safe, ƙarfe goma sha ɗaya aka ɗaura auren Shahida da Mubarak. Tunda safen muke gidansu Zaid tare dashi muka zo ya maimaita min da safe ze zo gida kuma tare zamu fito ya kuma tabbatar min baya son rasa daurin auren Shahida kuma baya son lateness. Ni kuma duk abinda Zaid yake nuna min yana da muhimmanci a rayuwar shi, ina taya shi nuna yana da muhimmanci. Da ya riga ni fitowa shiga mota ma na tsaya sa kayan da zanyi biki dasu na buɗar kai a cikin jaka, koda na fito na same shi ran shi duk ya ɓaci. Ko motsi bana so nayi na shiga motar nan. Dama a kunne motar take ya fara tuƙi. Tun kafin mu fito gida yace “Me ya hana ki gama packing naki tun jiya da na dinga maimaita miki bana son ɓata lokaci? Sau nawa na maimaita miki ina son zuwa gida da wuri? I think it was uncountable but you wasted my time. And if you think you can count it, then go on”
Shiru nayi ban ce mishi komai ba yana faɗan shi. “Next time kika ƙara min irin haka zan tafi na bar ki ne se de ki fito baki ganni ba”
Nan ma shiru nayi ban ce mishi komai ba. “Okay ga wanda bayi da aikin yi yana magana ko? Nuna min you're a barrister”
“To me kake so nace maka? Yanzu fa tara da rabi tayi amma kana yi kamar an ɗaura aure an kai amarya”
“Laifin nawa ne kenan? Nawa ne nida ke son nayi sauri”
Shiru nayi ban ce komai ba saboda bana son faɗa na dashi yana yin tsawo. Bana son Zaid yace nima nace. Idan faɗa ze min nafi so yayi magana shi kaɗai ni kuma na saurara. Idan akwai inda zan gyara se na ɗauki gyaran shi amma bana son ya faɗi na faɗi.
“An faɗa wa mutum magana amma baya ji” Zaid yace. Titi nake kallo ina jin duk abinda yake faɗa ban ce mishi komai ba
“A yi maimaita magana times without number amma ga banza. You're not trying that with me anytime from today, Hadiza. Bana son irin haka. Na faɗa miki na maimaita yafi a kirga amma da yake kina so na makara jiya baki yi packing ba se yau ban san abinda ya hana ba. Kawai son ranki saboda nace ina so na fito da wuri”
Yanzu haushi nake ji akan maganganun da Zaid yake yi. Ban san ya akayi na haɗe kukan da nake ji ba saboda bana so ya ɓata min rai na tafi da fuska wani iri cikin mutane. Kuma da na buɗe baki na maida mishi magana nasan yau faɗan da yake min se yafi wanda zamu yi. Shiyasa nayi shiru ban ce komai ba har muka isa gidansu Zaid faɗa yake min akan na ɗan spending wasu minutes ban fito muka zo gidansu ba.
Ina shiga cikin gidan, a ɗakin da na san zan samu Yaya Hauwa kukan da na tare ya dawo min ashe be tafi ba. Yaya Hauwa ita kaɗai ce a ɗakin tayi tsaye tana kallona ina kuka. Ganin na kasa yin shiru tasa jikina a nata tayi hugging ɗina.
“To menene kuma, Hadiza? Ba dai Zaid ba?”
Cikin kuka nace “Faɗa fa yake min. Tunda na shiga motar shi zamu zo nan yake min faɗa har muka iso”
Kaina take shafawa ahankali alamar rarrashi. “Ya isa. Kiyi haƙuri”
“Ban fa mishi komai ba. I was a little late wurin shiryawa shine ya dinga faɗa inda yake shiga ba nan yake fita ba”
“Amma kuma gashi kun iso cikin lokaci. Kai Zaid! Menene na faɗa kuma? Yi haƙuri kinji ya isa” tace tana cigaba da rarrashi na.
Kukan da nake yi na daina na zauna gefen gado. “Ki sake fuskar ki kinga muna cikin mutane. Halin mazan nan se ahankali wani lokaci. Abinda ma be kamata suyi faɗa ba akan shi suke faɗa”
Gyaɗa kai nayi saboda nasan da gaske ne. Yanzu menene na faɗa a cikin abinda ya faru da har ze sa Zaid ya dinga faɗa daga gidanmu har zuwa gidansu?
Ƙarfe biyu na ƙara gyara kaina nasa kayan da Zaid ya dinga masifa na tsaya ɗauka. Ko hoto banyi ba bana ma son ya ganni dasu da ina da wasu kaya a gidan ma ba zan sa wannan ba.
Ƙarfe huɗu aka fara buɗar kai na Shahida a gidansu anyi wani decoration wurin an sa mishi duhu yayi kyau sosai yana bada wannan rich culture.
Kwalliyar da aka yiwa Shahida light makeup ce ta mata kyau skin nata se glowing yake akan fuskar ta da sauran jikinta.
Dangin ango sun zo a gida se zuba kuɗi suke yi a cikin basket ana kwashewa to give way for other money.
Ƙawayen amarya ake magana dasu akan kuɗin da za'a bada na buɗar kai na amarya. Ina zaune a gefe ƙafafuwana sun so su haɗe wuri ɗaya amma basu haɗe ba ina sauraren su ina danna waya ta.
Reasonable amount aka yi fixing in dollars dangin ango suka bada aka buɗar kan Shahida. They went awnn for Shahida ina kallon su ina murmushi ina jin faɗan da Zaid yayi min yana wankewa a cikin zuciya ta.
Kiɗa aka sa wanda bashi da hayaniya to make the event lively ana rawa sama-sama har lokacin gama event ɗin yayi.
Da dare bayan Shahida ta shirya an gama mata nasiha aka kai ta parlourn Abba. Shima nasiha ya mata sosai tare da faɗa mata ta kula da kanta. Anan ne naga Zaid nayi kamar ban san shi ba. Naga ya kalle ni sau ɗaya da tired eyes ɗin shi ya rufe kaɗan ya kuma buɗe ko murmushi bayi da akan fuska bale ma dariya.
Bayan Abba ya gama yiwa Shahida nasihar zamantakewar aure, da kukan ta, ya damƙa wa Yayun ta ita yace ya basu amana su kaita ɗakin ta.
Babu mace da aka je da ita kai Shahida. Muhammad ne da Zaid da Khalil suka kaita. Ina gidan ina jiran ya dawo mu tafi har ƙarfe goma. Se sha ɗaya na dare ya dawo muka wuce. A cikin motar ba wanda yace wani abu har muka isa gida.
Bayan na gama shirin bacci na wuce ɗakin Zaid tunda shine ɗakinmu dama dani dashi tun farko tare muke bacci a ɗakin. Bana son idan wani abu ya shiga tsakanina dashi na ɓacin rai ya kasance ina kauracewa zuwa ɗakinmu. Nafi so ko faɗa ne tsakanina dashi, ya kasance a tare muke bacci a ɗaki ɗaya ba mabanbantan ɗakuna ba.
Juya mishi baya nayi bayan na kwanta. Presence nashi naji a kusa dani nayi sauri na rufe idanuna.
“Kina iya bacci idan muna fushi da juna?”
Rolling idanuna nayi ban ce mishi komai ba.
“Kina iya bacci idan muna fushi da juna?” Zaid ya ƙara faɗa babu alaman wasa a tattare dashi. Shiru nayi ban amsa ba.
“Kinyi girman da zan miki magana amma ba zaki amsa ba?”
Yanzu Zaid so yake ya nuna min shi mijina ne.
“Ina magana kinyi min banza, Hadiza”
“Wani faɗan zaka sake min? Faɗan gaske kake so muyi ne? Ko wani ya gama ɓata maka rai kana so ka zubar da fushin a kaina”
“Drop it, okay? Ba wanda ze ɓata min rai nazo na saukar miki. I'm not stupid”
“Then why Zaid?” nace tare da tashi daga kwancen da nake ina kallon shi “Why were you blowing things out of proportion earlier on? Because I took some few minutes? Did you attend the wedding Fatiha or didn't you?”
Rufe idanun shi yayi ya buɗe cikin gajiya. “I'm sorry” ya faɗa. Akan jin haushi da takaici yasa hawaye suka fara fito min daga idanu.
“Me yasa kike kuka? Ba za'a miki faɗa ba idan kinyi ba daidai ba se ki fara kuka?” yace tare da hugging ɗina. “I'm sorry”
“I'm sorry too. Forgive me”
“Zanyi hakuri idan kika dena kuka”
Fuska ta nasa a chest ɗin shi ina son kukan da nake ya tsaya yayi pecking sumar kaina.