Free chapter · Read without an account

BABI NA HAMSIN

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu 

AN: so we're at babi na hamsin? wow. it really deserves a wow if you knew the amount of writers block I got!!!! Hmmmm! Ban taɓa kawo zan ma kawo babi na arba'in amma har mun taho na hamsin. wani lokaci ƙwaƙwalwata shut down take gabadai na rasa abinda zan rubuta se kuma chan ta dawo daidai 😅. Shi labarin Zaid da Hadiza ba, dama nasan yana son ta irin ƙauna me ƙarfi amma ita bata damu ba. Labarin su Ibrahim da Maryam kuma...hmmm. su nasan Ibrahim will cheat. But I wanted to dive into Ahmads character I didn't know how it changed to Baffa maybe because of the introduction of Temi and I fell in love with Baffa's character. Yanzu dai gamu a babi na hamsin. it's a win win o.



ƘARFE GOMA na dare kiran Zaid ya tada ni daga bacci. Lazily na ɗauki waya na ɗaura akan chest ɗina. A cikin muryar bacci nace mishi “Bacci fa nake ka tada ni”
   “I'm sorry” ya faɗa.
Idanuna na rufe naji yace “Na katse zaki koma bacci?”
  “A'a. Amma idan kana magana ka ji anyi shiru ka katse”
    “Kina da sleeping sickness ne?”
   “Eh, ina dashi” na amsa shi 
Ganin bak'ar magana ce Hadiza tayi yasa Zaid yace “I'm sorry Diza”
   “Na gaji fa” na faɗa kamar zanyi kuka “Allah na gaji. Jikina kaman ba nawa ba. Na gaji Zaid”
Shiru Zaid yayi ya kasa cewa wani abu saboda be san da wace kalma ze amfani wurin mata magana ba. 
   “Kar ka damu kanka. Zan samu lafiya in sha Allah”
    “I'm sorry you're feeling that way”
Murmushi nayi na dole wanda ba'a ji.
    “Me kike yi yanzu?”
    “Laying on the bed, listening to you as you disturb me”
Dariya Zaid yayi “Se da nace na katse kika ce a'a”
    “Eh, ina son damuwar ne”
Wani murmushi yayi yace “Menene a cikin bakin ki?”
    “Uhmm, wannan...me ake ce mishi? Na manta idan na tuna zan faɗa maka”
    “You don't know the name of saliva again?”
    “Ka sani kake tambaya kenan?”
     “Hadiza dai yanzu mijinta take faɗa wa magana son ranta”
  “Mijin Hadiza kuma ya tafi ya bar ta ita kaɗai a cikin gida gashi tana shan wahalar juna biyun da ya mata”                      
Dariya Zaid ya fara yi kafin yace “What? I'm sorry”
Rolling idanu nayi ban ce mishi komai ba. 
   “So kike na dawo? Nima inaso na dawo na ganni a kusa dake a wannan lokacin kiyi haƙuri i have to do this work”
     “Ni dai ka dawo. So kake na maka gori nace first trimester na baka ma nan kayi tafiya you don't know what I went through?”
   “Diza na” Zaid ya faɗa, muryar shi ƙasa-ƙasa amma hoarse “I'm sorry”
Dariya Hadiza tayi tace “Wasa nake maka. Da gaske kuma nake wasa nake maka. Ka tsaya kayi aikin ka kar ka tada hankalin ka. I'm okay. Ɗazun ka turo Yaya Hauwa” na faɗa na tashi na shiga banɗaki. Bakina nayi rinsing a sink tukunna na dawo na kwanta a gado. Rufe jikina nayi da duvet nace “Yaya Hauwa ta jima anan. She made me took my bath. She made my bed. She made oats and tea and made me took the oats and she stayed with me till nine. She's so kind and my heart is still full of gratitude ”
   “She's like a mother to me”
Gyaɗa kai nayi nasan gaskiya ne. 
     “Inaso na gan ki”
“Video call?”
 “Yes” yace tare da kashe waya se ga kiran shi a video call. Ɗauka nayi ba'a ma gani na sosai saboda bedside lamp kaɗai ce a kunne. 
“Are you feeling cold?”
Girgiza kai nayi. “Ba zafi a Abuja?”
     “Ban sani ba. Ban fita yau ba”
         “What do you feel?”
Shiru nayi ina kallon shi.
       “What is it?”
“Jikina ne gabaɗaya bana jin daɗin shi. Kila gobe zan yi reporting sick a ministry”
      “Yes, you need rest”
     “So, I'll send an email to my supervisor”
Gyaɗa kai Zaid yayi yana kallona. “For two days?” yace
    “Zan sa rana ɗaya naga”
      “Alright, at your own phase”
     “Yes, thank you”
Shiru muka yi dukan mu ya ma ajiye wayar ya amso abu a ƙofa ya dawo.
     “Me ka amsa?”
          “Eyedrop”
 “Idanun ka ke maka ciwo?”
   “Kamar ina jin ƙasa a ciki”
   “Akwai iska a garin ne?”
    “A'a, babu iska. A offshore na samu”
   “Wa ze sama ka eyedrop ɗin?”
   “Ko zaki zo ki saka min?”
Murmushi nayi ina kallon shi “Eh”
    “Are you here already?”
  “Eh. Gashi har zan sama ka, ka buɗe idanun ka da kyau. Kasan ba'a so tip nashi ya taba idon ka”
   “Okay, you have my eyes wide open” Zaid yace tare da buɗe idanun shi.
Murmushi nayi shima yayi murmushi yace “I wish I can have you here”
        “Really?”
         “Yes”
 “What would you do if I was with you?”
    “I'll stare at you more and take care of you”
Wani murmushi na ƙara na tashi na shiga bathroom nayi rinsing baki na saboda yawun da na tara. 
   “Ba zaki iya haɗiye yawu bane?”
    “A'a yanzu ne ya fara”    
Shiru Zaid yayi chan kuma yace “Okay”                                            
   “Tell me a story”
          “A story?”                                       
        “Yes, a story”
   “Do I know any story? Well, let's see. Back in the days when Yaya Hauwa gave birth to Zara. She was home. Mummy was the one taking care of her and the baby. Yaya Hauwa's husband called her in the morning and told her he'll be coming to see his little girl......” Zaid yake faɗa min ina kallon shi da murmushi akan fuska ta ina uhmm bacci na son rufe ni ina kokari ina barin idanuna a buɗe “That was 8am..the time he called to inform her” daga wannan abun ban san abinda Zaid ya ƙara faɗa ba bacci ya rinjaye ni. 

Zaid shiru yayi yana kallon Hadiza tana bacci se kace ba ita yake ba labari ba. Eyelashes din ta sun kwanta ƙasan idanun ta. Fuskar ta tayi haske sumar kanta a buɗe. Daga kallon ta tana bacci kasan bata da isasshen lafiya. Wayar dake riƙe a hannun ta ta faɗi ya dena ganin fuskar ta. Numfashin ta yake ji yana fita ahankali yayi minti biyar yana sauraren ta kafin ya kashe waya. 

Washegari tun ƙarfe takwas Zaid ya kira waya ta mu gaisa amma ban ɗauka ba saboda lokacin ina bacci. Se ƙarfe goma sha ɗaya na safe na tashi. Koda nayi returning kiran shi be ɗauka ba nayi tunanin yana kan aiki ne. 
Ƙarfe biyu ya tura min saƙo yana tambaya ya jikina ko da sauki. Replying mishi saƙo nayi ina sanin yana kan aiki ne shiyasa ya turo saƙo da kira ze yi. 

Ƙarfe uku Yaya Hauwa tazo inda nake. Irin aikin da ta min jiya shi tayi yau amma abinci ta dafa min dankalin turawa plain bata sa komai ba. Na samu naci shi lafiya ban harar ba amma ina fara shan ruwa na fara jin amai. Ajiye ruwan nayi nasa kaina a jikin kujera. 
     “Jikin da sauƙi ko aman ne?”
    “Naji kamar ya koma”
              “Okay to”
Yau ganin yadda jikina yake da chanji yasa ƙarfe biyar ta wuce gida. Bacci na koma ban tashi ba se ƙarfe bakwai. Sallah nayi na kwanta akan carpet ina jiran Isha. Ban san lokacin da wani bacci ya ɗauke ni ba ban tashi ba se ƙarfe tara da rabi. Tashin da nayi na ɗauro alwala nayi Sallah. Bayan na gama Sallah na koma kan gado na kwanta. Waya ta na jawo koda Zaid ya kira amma be kira ni ba. Haushi naji sosai na ajiye waya ta na ɗaura hannuna akan cikina. 

Zaid be kira ni ba se ƙarfe goma na dare. Yi nayi kamar ba zan ɗauka ba amma haka nayi haƙuri na ɗauki kiran shi saboda nasan aiki yake. Video call ne so ina ɗauka na samu aiki ma yake a laptop. 
   “I'm sorry I didn't call again but i sent a message. I'm sorry” 
Shiru na mishi ban ce komai ba se kallon shi da nake. 
     “Why are you staring at me?”
    “Ya idanun ka?”
          “All good”
  “Aiki kake? Kayi aikin ka maybe gobe se muyi waya”
    “Wait first. Ya jikin ki?” yace yana kallona da jikina 
    “Da sauƙi, naji sauƙi”
          “Yau me kike ji?”
         “Komai ma ina ji”
              “Komai?”
  “Yaya Hauwa tazo yau. She made Irish porridge for me. She's so warm and kind”
Gyaɗa kai yayi yana me cigaba da kallona. “Wannan irin kallo. Ka dena kallona irin haka”
  “Idan ban dena ba, me zaki yi?” yace cikin wasa
    “Zan cire idanun ka duka naje na siyar”
   “Yau gaskiya ta fito. Dama Hadiza so kike ki siyar da idanuna?”
Dariya nayi nace “Eh. Kana da abinda zaka yi ne?”
     “Eh, zan sa ƙara a kotu. Zan ce wata tayi threatening nawa da cire idanuna. Idan aka ga wani abu ya fara da idanuna, itace ta farkon tambaya”
Murmushi nayi ina kallon shi nace “I'll draft a sheet for you. But you have to pay me”
   “Nope. You don't have to worry about that. I'll find me a barrister”
Rolling idanu nayi ina kallon shi. 
  “Ke ce zan cirewa idanu idan na dawo”
Wani rolling na ƙara yi Zaid yayi murmushi yace “I have to go, Diza”
  “Aiki ba? Se da safe”
  “Goodnight. I love you”
   “I love you too” na faɗa mishi tare da blowing a kiss for him
  “Wait, do that again” Zaid yace. Murmushi kawai na mishi na kashe waya ta.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol