Free chapter · Read without an account

Page 1

by A'ISHATU OUMBHANAT · HAƊUWAR ƘADDARA

          💦HAƊUWAR ƘADDARA💦
                    (Hatsari da Rai)

✍️Story and writing by✍️ 
             Aisha Sufyan (Oumbhanat)❤️‍🔥


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W\.A)*
*Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi*.✏️


Follow my WhatsApp channel 👇
***


                ♡~~~~~~~~~~~~~~♡
   💞Ina rokon Allah ya bani ikon faɗakar da Al’umma,Yahana ni gurɓata tunanin, Al'umma, kura-kuren dake ciki Allah ya yafe mana yanda nafara lafiya Allah yasa mu gama Lafiya Ameen🙏 

Wannan shine Littafina Na farko dan haka sabuwar marubuciya ce, idan An ga kuskure A ciki to A yi min Uzuri. 

      💝Sadaukar wa ga dukkan Ahalina💝

TSOKACI: Ƙagaggen labarine banyi shi dan cin zarafin wani/wata ba idan yayi kama da labarin wata/wani To Arashi ne.

FREE BOOK 

   BISSMILLAHIR RAHMANUR RAHEEM 


PAGE 1

KANO, GWALE L.G
Ɗorayi,babba
Layin gidan me unguwa.
Gidan Alhaji Umar Sabo.
                         

                  ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Banko ƙofar gidan tayi, A guje ta faɗa ɗaki haɗi da mako kofar da ƙarfi ta na garƙama sakata, Jingina tai a jikin ƙofar ta na sauke numfashi saboda mugun gudun da tayi.

 Hmmm ta yi wani huci cikin Ran ta ta na faɗin “wai yau nasha daƙyar Gaskiya Allah yana so na, yau da'ace su Duna sun kamani ai na kaɗe har buzu na wallahi”

     A fili kuma tace “yau na shiga uku shikenan babu ni babu yawo a gari sai an kwana biyu idan sun manta” gwaraamm aka Buga ƙofar da ƙarfi ta zabura ta na ihuu a zaton ta sune suka biyo ta har cikin gidan.

Sai kuma ta ji muryar ƙanwarta tana cewa “Dallah Malama ki buɗe min ƙofa aikin banza kawai kullum Mutum baida aiki sai neman masifa ke ba ƙarfi ba Ga shegen tsoro mtssww ta ƙarashe da jan tsaki”.
    
     Daga cikin ɗakin Nanah (KHADIJA) ta buɗe muryar ta tana cewa “ina ruwan ki munafuka wallahi idan na fi to jikin ki Ne zai faɗa miki na rantse” Heeeh ƙanwar ta Amira tayi shewa tana Faɗin “ to kibuɗe mana a gwada a gani aikin banza kaw…

    Kafin ta kai ƙarshen maganar ta ji ƙarar buɗe ƙofar kamar an jefo ta, ta cakume ta suka kasa dambe ba ji ba gani, Matar baban su Amarya da su ke kira da Anty ta miƙe ta nufe su dan ta raba su aikuwa ta na isa ta samu rabon na ta dukan a fuska saurin matsawa baya ta yi. 

Mama hajara Ita ce uwar gidan Baba ta na kofar kitchen ta na tankaɗen garin tuwo ta ce “ke waye ya aike ki raba su faɗa” 

  Yaran gidan Da suke a gefe su ka fashe da dariya su na waƙar a casu arna a casu suna tsalle da ihu, Da ya ke Nanah Ba ƙarfi ne da ita ba kuma irin Mutanen Nan ne ma su ƙaramin jiki. 

Saɓanin ƙanwar ta, data kasance me garin jiki,Sai ko ga shi ta ɗagata ta buga Da ƙasa ihuu tayi Tana faɗin “ ke Amera ni fa yayar ki ce Haba ki ɗaga ni mana dan Allah ke bakisan Wasa ba ne”?

  Haka tai ta roƙonta Daƙyar ta samu ta ɗaga ta suna haki duk su biyun suna harar juna,Sai lokacin suka lura da yanda gidan ya cika da yara ƴan kallon faɗa wata uwar tsawa ta daka musu kamar fari haka suka watse a guje.

 Wuce wa tai bakin rijiyar dake gidan ta zura guga ta ɗebo ruwa a bokiti ta shiga banɗaki dan tayi wanka kasancewar ta me mai son tsafta dan sam ba tason ta ga datti a jikinta, Bayan ta fi to ta ɗaura Alwala ta shiga ɗakin su.

Ta nufi wardrobe ta ɗauko wata riga me laushi ta saka ta feshe jikin ta da turare, sannan ta nufi gaban mirror ta na ƙarewa kan ta kallo

     Baƙa ce amma ba irin me dubun nan ba, irin me ƙyallin ta nada ɗan haske kaɗan, doguwar fuska gare ta da dara daran idanu masu haske, bakin ta ƙarami ne amma ta na da tudun laɓɓa, ba tada wani tsawo amma ta na da cikar halitta don murjejjen jikine da ita ba ta da rama sam Aƙallah shekarun ta zasu kai 22.

Nanah tanada tsiwa amma akwai Haƙuri, barta da gani ba ƙyalewa, matsoraciya ce ta gaske,sai dai Akwai Ƙarfin Hali.

 Juyawa tayi ta ɗauki hijabin ta tahau kan darduma a nutse ta kabbara sallahr magriba da a keyi a lokacin, Bayan ta idar tayi azkar da addu’o’inta ta miƙe ta cire hijabin ta ajiye.
  
 Fita tai tsakar gidan nasu dan tun ɗazu ta kejin hayaniyar yara, Bin su da kallo ta ke fuska a tsuke ta na harar su ji dan Allah yara kamar kiyashi.

 Matan Baban su uku ne, Hajara wadda suke kira da Mama ita ce Uwar gidan Alhaji Umar Sabo wadda sukai auren samartaka kuma ƴar Uwar sa ce, da Baban ta da mahaifiyar sa Uwa ɗaya Uba ɗaya suke, dukkan su ƴan Asalin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu ne.

Mama Mace ce yar ba ruwana idan abu bai shafe ta da ƴayanta ba to baza ka ji bakin ta ba sam a gidan, Sannan mace ce wadda ta ƙware a kisan mummuƙe sai dai duk ƴan gidan babu wanda ya gane hakan.

     Tana da ƴaya shida uku Maza uku Mata 
Yaya Jamilu ne Babba sai Anty Binta da Anty Uwani (taci sunan kakar su ne Karima) sai yaya Ibrahim da kuma Anty Amina sai Habiba Autar ta, Dukkan sunyi aure banda Habiba.

     Sai mahaifiyar su Nanah,Sunan ta Zainabu ( Ita ƴar nan cikin gari ce Gadon ƙaya),da suke kira Umma, su Biyar ta haifa Amma ɗaya ya rasu, Nanah wadda Sunan ta Khadija Ita ce Babba sai Amira, Wanda yake bin Amira ne ya rasu tun ya na ƙarami, Sai Amir sai kuma Auta Maher.

Bayan Umma, Baba yayi Aure-Aure har mata uku biyu sun haihu da shi ɗaya daga ciki yaranta uku, Aliyu da Sadam da shafa’atu.

Ɗayar kuma yaran ta biyu duka mata, Firdausi da Saleema ta ukun kuma bata jima ba tabar gidan.

 Sannan ya Auro Rabi wato Anty Ita kuma ba ta haihu ba a gidan amma ta na da wasu yaran wanda ta haifa da mijinta nafarko, bayan ya rasu ta auri baba. 

Wannan kenan.(Mun Dawo cikin Labari).

    Kallon Amira Nanah tayi tana tambayar ta yaushe Umma za ta dawo kasancewar ba ta gidan san da ummar ta fita unguwa.

 Harar da ta ɓalla ma ta ne ya sa ta tuna da sunyi faɗa ɗazu, kasan cewar ta Mutum ma ra ruƙo da saurin yafiya amma idan ba'a ƙure ta ba.

      Sallamar Ummar ce ya sa ta maida duban ta ga ƙofar shigowa gidan.

Ƙannen ta maza biyu su ka ruga su na yiwa Umman oyoyo. 

    Waje ta samu ta zauna ta na mai gaisawa dasu Mama, Amsawa Maman tayi Tana tambayar ya Hanya.

Amsawa Umman tana ta na ma ta sannu da Aiki.

  Juyawa Umma tayi wajan yaran tana amsa sannu da zuwan da ake mata, tabuɗe Jakar ta ta fito da Alewa ta fara raba musu wanda hakan kamar ya zame ma ta jiki ba ta fita bata siyo mu su ɗan abin taɓawa ba.

    Baba ne ya shigo gidan da gyaran murya mesa yaro nutsuwa, sallama ya yi yana shigowa cikin gidan duk suka amsa suna ƙara gyara zamansu….✍️


Oumbhanat✍️❤️‍🔥.
*** chat only.

Ya ku ka ji tafiyar? 😃

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol