Free chapter 路 Read without an account

Chapter 22

by Gidan Iko 路 GARWASHI

*Idan baka San gari ba saurari daka, in baka San Abu ba kar kaji kunyar cewa ban sani ba, don itama ban sani ba din rabin ilimi ce, idan kaga kunyi kama a fuska, to baya nufin kunyi kama a hali da zuciya, wani mutum din mutum ne, wani mutum din ba mutum bane, ba zaka iya shaidar mutum ba sai wani Abu ya ratsa tsakanin Ku, mutum? Bar mutum da mutum taka*



Complete din littafin 1k ne,
***


_Gaishe da makaranta littafin nan, tare da masu share godiyar ma ta gods_

........... Na dubi yarima Gibson na kuma dubi mutumin da ke amsa sunan Mai magani. Wanda Sam banji ya kwanta min a Raina ba, hasali ma kyamar sa nakeji a raina Amma Dole na kawar da komai saboda igwai ya turo shi 

Mai magani ya aje jakar shi wadda kallo Daya nayi Mata naji kyamar ta saboda fatar ta biri ce akayi jakar da ita Kuma daga cikin ta ne Yake kokarin fito fa magungunan da zaiyi amfani dasu Kuma gaba Daya dakin ya dauki wani zarni Wanda jikin shi ne ke fitar da hakan

Saukin da na samu Daya ne Gibson Bai matsa daga kusa Dani ba Alamar komai Akan idon shi za ayi shi

Mai magani ya gama fito da magungunan da zaiyi amfani dasu kafin ya nemi garwashi wuta aka kawo ya banka min hayaki Wanda ya Rufe Ni Ruf a cikin mayafi nayi ta tari Ina atishawa Amma ba a bude Ni ba sai da nafita hayyaci na ba don Ina fahimtar komai ba sai kuma ji nayi ana ta lafta min bulaliya wadda tasa na ida fita hayyacina ban Kuma sanin abinda ya biyo baya ba sai farkowa nayi na ganni kwance a jikin yarima Gibson Yana tallabe Dani a kirjin shi muna hada ido yayi min murmushi Yana fadin sannu nayi barka dai aljanun Nan sun fita inda suka sanar da Mai maganin ba zasu Kuma dawowa ba
Inajin shi ban wani tanka mishi ba don nasan wahalar kawai Nasha ba Wai don aljanun sun fita ba 

Sai da nayi sati guda kafin na girgije na koma daidai inda Amaka ta kirani take tambaya ta Yaya nayi batan wata kuwa? Naji haushin wannan tambayar ta Amaka Amma da na tuna har kudi ta bayar don ayi min ADDU A na samu cikin sai na Daina Jin haushin ta na Kuma fada Mata ma bani da lafiya inda ta Rude ta Rikice Wai kwance nake Koko dai na kwanta da yarima ne ya sani ciwon? Na fada mats nifa ban wani kwanta da shi ba sai Kuma ta SHIGA Rarrashi na tana fadin Wai na taimake ta Kar na Bata kunya ta gama fadawa mutane inada ciki don Allah nayi kokarin samu. Nace Mata ko tayi ta saka min Albarka muka Rabu ina mamakin Amaka da irin yadda take son na Auri yarima Gibson duk da irin tarin kudin Maazi Nkem itama da nata kudin Amma sun Dora Rayuwar su akan sarauta sai Kuma na Gane ita sarauta wata giya ce da duk  kudin mutum da shaharar sa baya kin ta shiya sa su Amaka da Maazi Nkem ke burin nayi Aure acan don su mamyi Duniya ace komai sun hada ga kudi ga mulki

Cikar sati da zuwan Mai magani sai ga Yan Aiken mah sun Kuma dawowa da fararen shimfidun su suka Kuma baza inda yarima Gibson ke cike da dokin wannan Rana don yasan aljanun da zasu kawo mishi matsala dai anyi maganin su 

Sai dai me? Bayan duk mun Gama komai har mun kure a turaka komai na Shirin faruwa Amma sai na Kuma tuburewa Ina kakari abinda Kuma ya fusata yarima Gibson don ya Soma gano akwai iya shege cikin lamarin nawa don Haka ya kyale Ni Bai Kuma bi ta kaina ba inda da gari ya waye mah ta Aiko Akan kwasar mata kayan shimfidar gado ta Kuma ganin babu komai bare wata Alama sai ta Kuma sanar da igwai Wanda shima a take ya Soma gano lamarin nawa iya shege ne don haka ya nemi ganawa da yarima Gibson Wanda Bai boye mishi komai ba Akan yadda nake furje furjen inda igwai yayiwa Gibson tambayar da ta nuna shi din namiji ne Mai hankali akasin tunani irin na Mata musamman mah da take ta fada da hayaniya

Tambayar da yayi mishi kuwa itace ya taba tambaya ta Ina son shi ? Idan kuwa ya taba wace amsa na bashi?
Gibson ya kada kanshi Yana fadin gaskiya Bai taba tuntuba ta yaji yadda nake son shi ba ko Akasin hakan inda Kuma igwai yake bashi hakuri da cewa

"To my son sai dai kayi hakuri Amma yarinyar Nan Bata son ka Babu wani aljani akanta don Haka Zan shirya Mata komawa gida a yau 
Kaduwar da Gibson yayi ba kadan bane don shi Kam ba da wasa Yake sona ba Sona Bai kamashi don ya saki ba shiyasa yakejin zai iya Zama Dani ahakan

Sai ya Soma Rokon igwai Wai abari na cika wata ukun in yaso sai a mayar Dani wata Kil kafin lokacin ya shawo kaina Amma igwai yace ya gama magana in kuwa zai barni to sai yaji ta bakina don Haka yasa shi yayi kirana da nazo Kuma sai yace ba ma zai tambaye Ni anan ba sai a gaban su Amaka da Maazi Nkem don akawo karshen tuka tuka Tik

Haka kuwa akayi muka taho tare da igwai da yarima Gibson sai ganin mu Amaka da Maazi Nkem sukayi babu sanarwa Kuma gashi wata uku Bai cika ba bare ace goyon cikin aka maido Ni

Amaka da Maazi Nkem suka tarbi igwai da yarima Gibson da duka abinda suke ganin shine karshen karramawa kafin su natsa igwai ya korowa Maazi Nkem bayani akaina da Rashin yardar da banyi da Gibson ba Wanda na fake da aljanun Amma da aka dauko Mai magani ya fitar min da aljanun ma ban daddara ba na koma halina inda shi igwai ya Gane bana son Gibson don Haka zai tambaye Ni a gaban su Maazi da Amaka amsar da na bayar itace zata wakilci Auren mu Mai yuwa ne ko A a

Su Maazi Nkem da Amaka sun kadu ba kadan ba don Haka aka kirani igwai ya Soma da Rarrashi na da kalamai masu Dadi da sauki inda yace zai tambaye Ni Amma na fada mishi gaskiya Kar nayi mishi karya na Kuma yi alkawarin fada mishi gaskiya inda ya tambaye Ni ko Ina son yarima Gibson? Ganin yace Kar nayi mishi karya na fada mishi gaskiya yasa banji shayin komai ba nace mishi gaskiya bana son Gibson don ko Bai bani damata ba bare na fada mishi yadda nakejin shi 

Ya Kuma tambaya ta maganar aljanu da nake tadawa shin da gaske ne ko kuwa karya nake ? Nan ma na fada mishi gaskiya karya nake don bana son yarima Gibson ya taba Ni ne yasa nake hakan

Igwai ya dubi Maazi Nkem ya Kuma dubi Amaka ya Rufe su da fada Yana fadin don me sun San bana son Gibson suke kokarin matsa min Auren shi? To tunda bana so abar maganar Gibson ya nemi wata matar a gaba ya Kuma kashe maganar daga yau Kuma daga yanzu

Gibson Wanda ya ke cikin matsanancin tashin hankali Bai so wannan hukuncin da igwai ya yanke ba Kuma ya San bashi da wata magana Dole ya dauki hakuri don Haka igwai ya taso ya taho inda su Amaka suka SHIGA matukar tashin hankali saboda ganin igwai ya fusata 

Tafiyar su Gibson ya bawa Amaka damar fasa kukanta na bakin ciki Wai haihuwa ta batayi Mata Rana ba tunda na tozartata na muzantata Haka tayi ta kururuwa ana Bata Baki sai da kyar tayi shiru Amma ko inda take tace Kar na sake na kalla babu ita babu Ni don ma dai gidan ubana ne da gidan tane Kora ta zatayi 

Washe gari kuwa muka tashi da wani tashin hankalin don Maazi Nkem ne Yake ta Aman jini har Yana fadin zai hadiye zuciyar shi ya mutu ne da Bakin cikin da nake ja mishi  su Sony da Amaka suka kwashe shi Zuwa Asibiti aka bashi gado


Idan nace ina cikin tashin hankali naso Bata yawun bakina ne kawai Amaka tayi fushi Dani ga Maazi Nkem agadon Asibiti Yana kwara Aman jini har Yana fadin zai hadiye zuciyar shi ya mutu saboda bakin cikin da najawo mishi na kuma tabbata duk wannan shafar Mai ne akan suji na karbi musulunci Bala in sai ya wuce wannan Anya kuwa ban jawo abinda ya Fi karfina ba kuwa? ............
.


Labarin GARWASHI daban yake da sauran Kar ku Bari ayi tafiyar nan Babu ku


Gidan iko shine sunana kecewa saduwar ALHERI馃グ馃崚


_Masu Neman labarin daga farko su shiga cikin channel din mu zasu samu farkon labarin_

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol