Free chapter 路 Read without an account
Chapter 23
*Idan kana son ka gane adalcin kanka to ka karbi shugabanci, Idan kana son sanin waye kai? Ka dubi abokin ka, duk yadda abokin ka ya kasance to haka kake, mutum na rayuwa ne bisa doron zuciyar sa, dukkan abinda yake rayawa akan mutane ko zuciyar sa take kallon mutawa to haka zai kasance, al'amarin wannan rayuwar a bayyane yake, kar ka wahalar da bakin ka wurin yiwa mutane bayanin Lanka, wani tun kafin ka bude baki kayi magana ya gama karantar abinda zaka fada,*
_Akwai completed na littafin nan akan 1k ***_
*Haj kin kuwa karanta littafin _KISHIYA TARA na MARYAM LITEE MALUMFASHI_ ko kuwa kina nan Baki San duniyar da aka zuba cikin littafin ba?*
..........Wata zuciyar ta sanar Dani har abada ba Zan taba nadamar abinda nayi ba musamman na SHIGA musulunci sai dai har ga Allah zuciya ta batayi min Dadi ba akan halin da najefa Amaka na damuwa bare Kuma mahaifina Maazi Nkem na Aman jinin da yake har ya Kai shi gadon Asibiti
Sai naji Babu abinda na ke bukata irin in kwara ihu ko zanji dadin damuwar da tayiwa zuciya ta zobe sai kawai na kwala uban ihu da duka muryata kafin na zube kasa Ina birgima don hakan NE Kawai zanyi naji Dadin zuciya ta dake gana min azaba saboda damuwa
Ina cikin kwala ihun ne yayana Sony ya shigo ya sameni Ina ihu sai kawai ya Rufe Ni da duka Wai nayi kukan Mai Dalili dama Wai Yana Jin haushi na Wai Zan kashe mishi iyayen shi da Bakin ciki na
"Shegiya kukan Dadi kikeyi kin Kai baba gadon Asibiti ke shegiya? Shine Kuma Kika dawo Nan kina ihu babu Wanda ya taba ki saboda kin maida mutane Yan iska? To Bari nayi Miki abinda Zakiyi kukan da Dalili shegiya marar tausayi
Yana dukana Yana fadin hakan jibgata Kuma yakeyi da iyakar karfin shi . Duk da dukan da Yake min na Rashin imani banji inajin zafin shi ba don nasan duk wannan zai zamo shafar Mai matukar sukaji Ni din yanzu ba cikin Ahalin su nake ba bana ko shakka sai Sony ya kashe Ni don yafi kowa tsanar akidar musulunci shine Kuma ya biyo Amaka sak wurin akida
Shigowar Emmanuel ne ya kwace Ni hannun Sony Yana bashi hakuri
Sai kawai Sony ya fashe da kuka Yana fadin da sun Rasa Maazi Nkem sai ya kasheni Yana can Yana kusa mutuwa
Gabana yayi masifar faduwa Jin abinda Sony Yake fada Wai Maazi Nkem ya kusa mutuwa Ni Kam Ina Zan saka kaina idan wannan bakin cikin ya kashe Maazi Nkem ? Da kuwa nasan Haka wannan Al amarin zai zamo da na bawa Gibson kaina yayi min cikin da suka kwallafa Rai akai da ba akai wannan jallin ba na Amaka da take gaba Dani da Kuma Maazi Nkem dake Shirin mutuwa
Sony ya koma Asibiti Ni Kuma nayi ta kuka Emmanuel Yana bani hakuri Yana Rarrashi na don hakika Ni da Emmanuel tamu tafi zuwa Daya don ko da muke ciki daya dasu nafi aminta da Emmanuel Akan Sony Kuma shi din idan ya ganni cikin damuwa Yana kokarin Rarrashi na ya Kuma kwantar min da hankali don Haka yanzu ma Rarrashi na yake Yana fadin nayi hakuri Maazi Nkem ba zai mutu ba sai dai nayi kokarin gyara kuskure na. Haka Emmanuel ya kwantar min da hankali kafin ya koma Asibitin inda naji lallai Nima ya kamata naje Asibitin Nan ko don Naga halin da Maazi Nkem Yake ciki to Amma Kuma a wannan yanayin da Amaka tace min babu Ruwa na da ita zanje ? Idan fa naje komai zata iya yimin don Haka Dole na hakura da Zuwan
Sai dai ban sani ba Ashe Rashin zuwan nawa ma matsala ya haifar don Sony ya shigo Yana kunzuga min Ashar Wai dama nayi hakan don Maazi Nkem ya mutu shiyasa banje na ganshi ba? Na Soma Bashi hakuri Ina Fadin Ina tsoron gamuwa da Amaka ne........
"Kin Gama zuwa inda Amaka take Kenan? Ya fada yana zaro min ido. Da sauri na SHIGA daki na dauko makullin mota ta na nufi Asibitin inda na SHIGA dakin na hango Maazi Nkem an sakala mishi naurar zuko numfashi wato oxygen Kuma idon shi lumshe kirjin shi na harbawa sama sama inda na SHIGA Ina nufar gadon Maazi Nkem kallo daya nayi mishi naji tausayin shi ya kamani na Riko hannun shi Ina HAWAYE inda kuma Amaka ta fito daga bandaki ta ganni Ina Rike da hannun Maazi Nkem ta kwatso min tsawa
"Sake mishi hannu kinzo ne ki karasa kashe min shi ko? To fice ki bani wuri ban fada Miki babu Ruwa na dake ba? Kar ki kuskura Kika sake zuwa kusa Dani don sai na shake ki saura kadan ma na la ance ki tunda dai Kika yi min Haka Kika tozarta Ni a gaban igwai Kika Kuma yiwa mijina sanadin zuwa gadon Asibiti Kuma Bari in Gaya Miki mijina Yana mutuwa Allah sai na kashe ki na gutsutsureki na zubawa karnuka......
Na zube a kasa Ina bawa Amaka hakuri ina kuka Amma Bata saurare Ni ba saima ingizo Ni da tayi daga dakin ta fiddoni waje ta maida kofar kyauren ta Rufe har tana datse min hannu
Na Kuma zubewa a kasa a kofar dakin Ina kuka ga Kuma hannu na Yana digar jini ya Kuma Soma kumbura inajin tausayin Maazi Nkem ban San hakan zata faru ba da na Rufe idona yarima Gibson yayi yadda yaso Dani in yaso sai na Roki Allah ya yafe min Amma ban zaci Haka ba
Ina zube Anan Ina kuka Sony yazo SHIGA dakin ya ganni yasa ka Kara Yana kwallo Dani ya kwankwasa Amaka tazo ta bude mishi ya shigo ta maido kyauren ta Rufe
Emmanuel ne ya kamo Ni Yana tada Ni Yana share min HAWAYE Yana bani hakuri Yana fadin na koma gida tunda Amaka zata hakura shi Kuma Maazi Nkem nayi mishi ADDU A Allah zai Bashi lafiya
Naji Dadi sodai da kulawar Emmanuel sai kawai na koma gida na daura Alwala nayi salla na Kuma Roki Allah ya bawa Maazi Nkem lafiya ya Kuma daidaita mu da Amaka
Munyi waya da Umar na fada mishi baba na Yana Asibiti bashi da lafiya inda yace zaije ya duba shi Amma nayi maza nace A a Kar kaje ka Bari ya dawo gida sai nayi maka magana Ashe ban sani ba Umar yayi shiri ya nufi Asibiti abinda Kuma ya kuma jawo min matsala...................
Kar ku Bari ayi tafiyar nan Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran
Hadiza Bara'u Gidan iko ne sunana ke cewa saduwar ALHERI馃グ馃枻馃崚
_Masu Neman labarin daga farko su duba cikin channel din mu zasu samu labarin daga farko_