Free chapter 路 Read without an account
Chapter 24
*Labarin zuciya a tambayi fuska, wani labarin ba kowa yake fahimtar sa, wani labarin bai cancanci bayarwa ba, wani labarin fuska bata isa fahimtar da ainihin sa ba, wata kil dai baki n zai iya fadar yadda zuciyar ta kasance*
_Complete din littafin GARWASHI 1k ne_
_***_
GARWASHI
.............Washe gari na shirya abin break na nufi Asibiti don na kaiwa mahaifina Kuma na samu ko kallo na Amaka tayi don gaskiya banajin Dadi inda na tuno da nice silar bacin Ranta Kuma sanadin ciwon Maazi don Haka sai nakejin babu Dadi Amma Kuma naki yarda nayi nadamar kasancewa ta acikin musulunci wannan Kam nasan akwai wata manufa da Ubangiji Yake nufi Dani Akan hakan Wanda nake kyautata zaton ALHERI gareni
Na iso Asibitin Ina kwaso kayan break din daga cikin motata na nufi cikin Asibitin inda na iske Amaka tana bawa Maazi Nkem Ruwan shayi a Baki ga Kuma wainar kwai a cikin flat tana gutsurowa tana bashi a Baki Yana ci da gani kasan babu lafiya a tare dashi ga Kuma jug Nan na Ruwan zafi har da katon bredi da wata kula wadda na Gane daga gidan Sony aka kawo musu wannan kayan Karin . Turo kyauren da nayi shi yasa Amaka juyowa Tana ganin nice ta dauke kanta Bata Kuma kallo inda nake ba ta maida kanta akan mijinta tana bashi abincin sai ma shine ya tsura Min ido Yana kallo na tamkar Bai taba gani na inda Kuma na hakikance wa kaina kallon mamakin abinda nayi mishi yakeyi Wanda Bai zata ba
Na sulale a kasa Ina gaishe da Amaka Amma tamkar da Dutsi nake magana Bata ma nuna ta San Ina wurin ba bare ta kalli inda nake ko ta amsa gaisuwar da nake Mata
Na maida kallo na ga Maazi Nkem na gaishe shi Ina tambayar halin jikin shi shi Kam ya amsa Amma ahankali Wanda na tabbatar da ciwo ne yaci karfin shi sai kuma muka ga ya Soma fitar da numfashi da sauri da sauri Yana dafe kirji Alamar dai ciwon shi ne ke kokarin tashi inda Naga hankalin Amaka yayi masifar tashi ta fita aguje sai gasu ita da likita Wanda ya SHIGA kokarin daidaita mishi numfashi ta hanyar tsira mishi allura ya Kuma mayar mishi da oxgen a hancin sa inda Yake tambayar Amaka me akayi mishi Wanda ya fusata shi har Yake neman mayar dashi Ruwa Akan Yar lafiyar da ya Soma samu?
Ta waigo ta kalleni wani kallo me cike da tsana da tsangwama har da harara
Kafin tacewa likitan nice ya gani har hakan ta faru inda shi Kuma likitan yace a kiyaye da dukkan abinda zai motsa mishi Rai har ya Kai ga baci don zuciyar shi ta kumbure Kuma idan Yana fusata a irin wannan yanayin to zuciyar shi zata iya fashewa idan Kuma ta fashe to zai mutu ne Kawai don Haka a kiyaye
Fitar likitan ya bawa Amaka damar fasa kukanta tana Rike hannun Maazi Nkem tamkar Ranta zai fita
Ina tsaye Ina kallon Amaka da kukanta ke raurawa zuciya ta domin ko ta bani tausayi na Kuma yarda da ganina ya tadowa Maazi Nkem ciwon shi don Haka ya Zama Dole na hakura da zuwa Asibiti na Kuma saurari sakamakon hukuncin da zasu yanke min. Ina shirin juyowa in fito naga Amaka a kaina tamkar sako min ita akayi daga sama don Banga ta inda ta karaso gareni ba sai kawai gani nayi ta daga jug Ruwan zafin Nan ta kyaraya min su ajiki kafin ta dauko kular da na zubo musu dankalin turawa da kwai da agada shima ta kife min shi a kaina idonta fall masifa ta Soma nuna Ni da yatsan ta
"Mun Gaya Miki muna da bukatar abin da ya shafe ki ne da Zaki nufo mu da wannan? Ta Fadi wannan din tana nuna kayan da jue min ajikina
"Idan har Kika Kuma zuwa Asibitin Nan har kikayi min sanadin da ciwon mijina ya Kuma tashi kema Zaki Budi naki idon a Kan gadon Asibitin fice min daga Nan tun ban murde Miki wuya ba Yar iska kawai
Jikina da ya kone da Ruwan zafin Bai dameni ba kamar yadda kalaman Amaka zuka damu zuciya ta lallai ya Zama Dole gareni na bigi hanya na koma jihar imo wurin yarima Gibson don yayi min cikin Nan na dawo cikin su Amaka ko na samu Zama lafiya da su
Na juyo jikina a sanyaye na fito da Shirin komawa gida fuskata duk man da ya wanke min ita ga Kuma jikina da ke radadi da dankon sukarin shayin amma duk ba ta su nake ba ta yadda Zan gyara kuskure na da iyayena nake
Ina fitowa nayi kicibus da Umar ya shigo Asibitin Yana tunkaro dakin inda Kuma naji gabana Yana Kara fasuwa don nasan wani tashin hankalin ne zai Kuma samu na Amma Dole Kuma Zan jure don komai Yana da mafari kafin Kuma ya Kare
Ya karaso Yana haskeni da murmushi Yana fadin yazo a sa a kenan don Haka muje nayi mishi Rakiya Dole na na koma cikin dakin Amma Yana gaba Ina bayan shi inda bude kofar yasa Amaka juyowa sai Kuma tayi Arba da Umar da Kuma Ni sai ta Kara mutuwa a zaune
Umar ya zube Agaban Amaka Yana gaisheta ta amsa a hankali kamar Bata so ba Kuma don komai ba sai don ganin mu tare kuma ba haushen da Bata kaunar taga Ina mu Amala dasu
Ya kuma tambaye ta me jiki ta amsa cikin sikewa tana watsa mishi harara ya aje lader da ya shigo da ita a gaban ta Yana Shirin mikewa ta dakatar dashi tana tambayar shi daga ina? Kuma Bata Gane shi ba?
Yayi murmushi Yana fadin shi abokina ne da sauri ta Kuma hade fuska tana kallo na daga Haka Bata sake kallon Umar ba ta maida hankalin ta Kan mijinta ta watsar damu inda nayi mishi nunin muje kawai
Yayiwa Amaka bankwana Amma Kai da ke can in ka amsa to Amaka ta amsa Bata ma kalle shi ba bare yasan ta San da wanzuwar shi don Haka muka fito Ina mishi godiya Yana kallo na Yana fadin me ya samu fuska ta haka da maiko? Nashafa fuskar Ina Fadin Babu komai HAWAYE na biyowa fuska ta inda yace na SHIGA mota zai kirani don muyi magana da Haka muka Rabu na taho gida Ina yanke shawarar kulle kayana na nufi jihar imo wurin yarima Gibson don nayi mishi abinda na kasa yi mishi a farko Wanda ya Kara lalata min komai na dangantakar mu da iyaye ne
Ina kuwa zuwa gida na Soma shiri Ina kuka Dan uwana Emmanuel ya shigo ya same Ni Ina kuka ya ke tambayar abinda ya faru
Ban boye mishi komai ba na sanar dashi shima ya Kara karfafa min gwiwa da yin hakan ko don na samu dajdaito da su Maazi Nkem Amaka. Shi ya bani kudi Wai nayi kudin mota duk da nace mishi Akwai kudi a wurina Amma sai da ya aje min ya fita Yana min fatan in Isa lafiya
Nayi wanka nayi shiri na fito na fadawa Rutu cewa na tafi
Na fito na samu Napep na hau ya kaini Tasha don na hau mota............
Kar ku Bari ayi tafiyar Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran
Gidan iko nake nake cewa saduwar ALHERI馃枻馃グ