Free chapter · Read without an account

Chapter 46

by Sayyada barrister · BIYU A ƊAYA

BIYU A ƊAYA 
   (Don't judge a book by its cover)



Page 46
Sayyada barrister 
***
YOTA 13 
The five ink legends 



Shiru ne ya ratsa a sakaninsu, kowa da abin da yake tunani cikin ransa, jiran fitowar Bilqees da Mamanta suke yi, Dr Waahab sai addu'a yake yi cikin ransa Allah ya sa ayi komai cikin sauƙi, ba zai iya jure rasa Angel ba, ji yake yi ana hana masa ita zai rasa ransa, Alhaji babba ne ya numfasa ya dubi Malliman tare da cewa 

"Menene ma'anar wannan gidan na Tumbin Giwa?"

Malliman ya sauke numfashi tare da cewa 

"Gidan haya ne, sannan kuma wasu abubuwa da suka shafi taroa ana zuwa ana yi anan ɗin, yawancin matasa dake cikin Tumbin Giwa ba ƴan nan ƙasar bane, da nesa suka zo yin aikin hannu"

"Ikon Allah, to su da suka zo neman abin yi shi ne suka fake da shanye shaye"

"Ai matasan yanzu sai dai Allah ya shirya, wasu ma da matansu barin su suke yi su taho, su yi aikin hannu kuma su tura musu kuɗi su riƙe kansu da ƴaƴansu"

Abbie ya ce

"Gaskiya basu kyauta wa kansu ba, sun lalata rayuwar su, ni akwai wani wanda na gani aka yage masa vest tausayi ya bani, ya cuci rayuwarsa"

"Su ai ba sa tausayin kansu, kada ka sha mamaki kai yake tausaya wa"

Cewar Alhaji ƙarami, Malliman ya ce

"Shi yasa duk wacce za ta yi aure nake shige mata gaba, kuma suna yi fa"

"Ni wacce ta kafa gidan ce ta fi bani haushi, mutum saboda kuɗi shikenan duk wata shara bola a ɗauka a ba shi gida, club fa suka maida gidan"

Cewar Daddy, Dr Waahab ya runtse idanunsa yana ci gaba da addu'a Sa'eed ya dafe sa ya ce

"Ɗan'uwa amma me ya burge ka da wannan yarinyar yasa kake son aurenta, jahadi za ka yi?"

Ya juyo sosai yana kallon Sa'eed sannan ya ce

"Yarinyar tana da hankali, dabi'unta ne suka jani"

"Ok Allah yasa su Daddy su amince"

Bilqees ce ta iso ita da Alaja sanye da ɓakar Abaya ta sake fitowa da haskenta, da sallama ta shigo ta zauna daga bakin kofa tare da cewa 

"Ina wunin ku, sannunku da zuwa"

Cikin sanyayyen muryarta, kanta a ƙasa, tana wasa da siraran yatsun hannunta, jikinta duk ya yi sanyi, tun da aka ce ta taho ta kamu da fargaba Allah ya sa lafiya...

"Lafiya kalau" 

Suka amsa mata, suna kare mata kallo sai kuma suka ga yarinya ce ga nutsuwa ba irin matan da suka gani a Tumbin Giwa ba, da bambanci sosai, Malliman ya ce

"Bilqees"

"Na'am Malliman"

Ta faɗa kamar ta yi kuka don ganin manyan mutane zaune sun cikata da kwarjini, ya ci gaba da cewa 

"Waɗan nan sune surkayenki, yaronsu ne yake neman auren ki, mun kira ki ne ki gaishe su"


"To"

Ta faɗa, Dr Waahab yana ɗaura idanu a kanta yaji wani sanyi cikin ransa, yaye kewar rashin ganinta, sai yaga ta sake yi masa kyau duk da ta ɗan faɗa, a lokacin Alaja ta ƙaraso ta shigo ta zauna tare da cewa 

"Mamanta bata jin dadi, ba zata iya fitowa ba"

"Subhanallah jikin ne?"

Cewar Malliman, ALAJA ta ce

"Eh fah a kwance take"

"To Allah ya sauwaƙa"

Cewar Malliman amma Alhaji ƙarami ya ce

"Ai sai ki ce ta fito tun da batun aure ake yi, duk rashin lafiyarta ba zai hana ta tako zuwa nan ba"

Hararar shi ALAJA ta yi sannan ta ce

"Mutum yana fama da rashin lafiya yana kwance amma ka ce sai ta fito"

Ya ce da ita

"To yaushe za mu sake haɗuwa in bata zo nan mun gaisa ba?"

"Menene damuwar ka da haka?"

Alhaji babba ya ce

"Shikenan zuwan yarinyar ma ya wadatar, sai ta tashi ta koma cikin"

Bilqees ta tashi ta fito, Dr Waahab kamar ya biyota amma ba hali, Alhaji babba ya sake cewa 

"Shikenan sai kuma zancen ɗaurin auren yaushe za ayi?"

Malliman ya ce

"Ko yanzu ma ina dai da sadaki za a ɗaura"

Alhaji babba ya ce

"A yau?"

"Eh muna sallah azahar sai a ɗaura tun da lokacin ma ya gabato"

"Ok ba damuwa, sai mu jira lokacin"

ALAJA ta ce

"Sadaki in ba 200k ba ba zamu karɓa ba"

Alhaji ƙarami dariya ta kuɓu ce masa ya ce

"Wai 200k kai kina da abin dariya, yo ke ce za ki yanke sadaki"

"Ina ruwanka mara mutunci kawai, ai yarinya ta ce"

Malliman ya ce 

"SA'ADEEY ta shi ki koma ciki, duk yadda mu ka yi za ki ji mu"

Abbie ya ce

"Ni zan bada sadaki 1m"

ALAJA tafiya ta gagare ta, what? 1m! Abban Ashfat ya ce

"Kada asha wahalar cewa za ayi mata kayan ɗaki, duk zan yi in mun koma Nigeria na ɗauki nauyi"

ALAJA kamar ta taka rawa don murna amma sanin a cikin masallaci take yasa ta nutsu ta ce

"Heh Angel was different than others, sadaka 1m kuma ba za mu saya kayan ɗaki ba, we thank God"

Babu wanda ya kulata Malliman ya ce ta koma cikin Tumbin Giwa, ta fito sai sauri take yi tana haƙi ta iso cikin gida bangaren su Angel...

Tana shiga ta ƙwala wa Maman Bilqees kira har ta shigo cikin palour tana cewa 

"Ke tashi ki ji, kin wani kwanta a ɗaki ana abin arziki"

Maman Bilqees dake kwance ta tashi zauna ta ce

"An ɗaura ne?"

"Ana sallah azahar za a ɗaura akan sadaki 1m"

Maman Bilqees ta waro idanuwa waje, ta ce

"Million ɗaya sadakin Bilqees!"

"Ke bari na ƙaƙare miki, bugu da ƙari har kayan ɗaki za ayi mata, ba a buƙatar ko sisi daga wajen mu"

Bilqees ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta lumshe idanunta, tana jin farin ciki sosai cikin ranta, shikenan za ta zama matar Yallaɓai likita kuma zai tafi da ita Nigeria...

"Da gaske?"

"Ah ƙarya nake yi miki tun da na saba ai"

"Allah ya huci zuciyar ki ALAJA, abin ne ya zo min ba zata"

"To sai ki shirya nan da zuwa anjima kaɗan za a ɗaura auren"

ALAJA ta fice, kamar wasa zance ya karaɗa ko'ina cikin Tumbin Giwa, za a ɗaura auren Bilqees akan sadaki 1m, yawanci 50k ake badawa wajen biyan sadaki amma na Bilqees ya ninka haka sosai...

Ana idar da sallah azahar aka ɗaura auren Dr Waahab da Bilqees Angel, bayan sun sayi goro da minti nan aka hau rabawa Dr Waahab ya washe hakura yake yi kamar me tallan maclean, ya dubi gabas ya yi sujudusshuqur yana yi wa ubangiji godiya da ya nuna masa wannan ranar ya mallaka masa Angel, dariya iyayensa su ka yi ya ɗan sosa keyarsa yana murmushi, suka fito daga cikin masallaci, ALAJA tana tsaye daga bakin ƙofar Tumbin Giwa, Alhaji babba ya ƙaro inda take tsaye, Maman Bilqees tana tsaye daga nesa tana kallon su, tana jinjina kai, hawaye suka gangaro mata a hankali ta furta 

"Allah kai ne Allah"

Alhaji ƙarami su ma suka ƙararo Alhaji babba ya ce 

"To an ɗaura auren mu za mu koma hotel mu huta, amma mun yanke shawarar gobe kawai za mu tafi da amaryar mu Nigeria, babu ɓata lokaci"

ALAJA ta ce 

"Mun gode Allah shi kenan Angel ta zama ƴar ku, to amma batun tafiya gobe da ita bai taso ba, ko dai ku tafi daga baya a kaita"

Abbie ya ce

"A'a duk wahala ne, da ita za mu tafi tun da an ɗaura auren"

Alhaji ƙarami ya ce

"To me ku yi mata har kike neman a ƙara muku lokaci"

"Trouble maker za mu shirya ta"

Abban Ashfat ya ce 

"To shikenan za mu baku zuwa jibi ko babban Yaya?"

"Eh sai ku gama shirye shiryen ku, to ma menene na wani shiri?"

"Za mu yi biki, aɗan shana kowa ya san ana auren Angel, da fatan za ku zo dinner party gobe da daddare za a yi"

"A'a mu ba ma yin haka, ku yi abin ku, amma kada ya wuce kwanaki da aka bada"

"To ba damuwa amma Ango zai zo fa"

"Ga ki ga shi ku yi magana, amma ban da mu"

ALAJA ta kalli Alhaji ƙarami ta ce

"I invited you Alaji"

"Ke cen ki yi abin ki kada ki saka ni a ciki"

Dariya ta yi ta ce

"Za ka bani number ka muna gaisawa abokina"

"Tirr"

Dariya ta yi, suka yi gaba, Dr Waahab ya tsaya tare da cewa 

"Sannu ALAJA na gode da ƙoƙari"

"Yallaɓai likita ba komai ai komai zan yi maka"

"To me da me kuke buƙata"

"Za a yi mata gyaran jiki, sannan za a yi renting kayan da za ta saka a dinner party gobe, amma kuɗin sadaki ma ya wadatar"

"A'a kada ki yi hidimar biki da kuɗin sadaki, bari na tura miki kuɗaɗen da za su isheku daga yau zuwa gobe"

Ya fiddo wayarsa ta ba shi account details nata a take ya tura mata 1.500m Alaja tana ganin Alart kaɗan ta ruga a guje sabar kaɗuwa, ya ce

"Kada matata ta nemi komai ta rasa, ki faranta mata"

"Ai dole ma, wai chab bayan aikin likita kana wani aiki ne?"

Murmushi kawai ya yi ya ce

"Zayyu na zo na ganta anjima?"

"Ƙofa a buɗe take ai matarka ce"

"Okay"

Ya yi sauri ya iso wajen iyayensa suka wuce HOTEL...

ALAJA ta karɓi kuɗin sadakin a wajen Malliman ta ba shi 200k yaki karɓa ya ce sun yi masa goma ta arziki musamman ma Angon, ta dawo ciki ta tadda Maman Bilqees tana ƙoƙarin komawa ciki ta ce

"Tsaya mu shiga tare"

Suka shigo ciki, bata ɓoye mata ba duk abin da suka bada ta faɗa mata, ta damƙa mata kuɗin sadakin cub amma ta ce kuɗin da yake account nata da shi za ta yi uzurin bikin.

Maman Bilqees ba ta ce komai ba, ta kurawa kuɗaɗen idanu, tana jinjina al'amarin, ALAJA ba zama an ɗaurawa kare aure, na ta sanya Bilqees a gaba suka wuce shagon saloon da gyaran jiki ta ce a yi mata gyaran da ba a taɓa yi ba, har yamma suna cen Bilqees ta yi kyau kamar ba ita ba, darajar aure da kimarta suka bayyana a tare da ita, Alaja ma sai kallonta take har suka dawo gida ta sha gyaran gashi, Bilqees ta shigo bangaren su, Mamanta tana kallonta, taga duk ta sauya...

Dr Waahab ya kasa tsaye ya kasa zaune, sai tunanin Angel yake yi, ya yi wa Sa'eed magana ya yi masa rakiya zuwa Tumbin Giwa ya kalli fuskar matarsa, Sa'eed yana sokanarsa har suka iso kasancewar dare ne gidan cike yake da mutane, Sa'eed ya ce zai zauna a waje ya yi waya da Suhaima Dr Waahab ya kira ALAJA akan ya iso ta ce ai ya zama ɗan Ahalin Tumbin Giwa kawai ya shigo, ta tura Abeedah ta yi masa isowa ciki, a wani madaidaicin palour aka yi masa masauƙi ya zauna yana jiran isowarsa princess nasa.

ALAJA da kanta ta shirya ta, ita cewa take yi ba sai ta yi kwalliya ba, Alaja ta ce

"Ke sanya idanunki cikin nawa yanzu kin zama matar aure tashi za ki yi ki riƙe mijin ki da gidan, mace sai da gyara, namiji sai da kwarkwasa, ba wai za ki je ki tsaya kamar wani namiji ba, to ki zage wajen sanya shi farin ciki"

Ita dai bata ce komai ba, har ALAJA ta shirya ta cikin doguwar rigar lace tayi matukar kyau sai ƙamshi take yi, ta ce

"Yawwa ki je yana palourn baya, sai kuma ki yi ƙauyancin da kika saba"

Jiki a sanyaye Bilqees ta fito, ta shigo palourn tare da sallama yana zaune ya yi kyau sosai cikin riga da wando na shadda fari kal ya sanya hula, sai ƙamshi yake yi, yana ganin shigowar ya sauke numfashi yaga ta ƙara kyau.

Ta kasa ƙarasowa ta tsaya daga bakin kofa, ya mik'e suna kallon junansu kowanne da abin da yake tunani cikin zuciyarsa, a hankali ya buɗe mata hannayensa alamar ta ƙaraso ya rungume ta, amma ta yi sauri ta sudda kai ƙasa zuciyarta ta soma bugawa, ta kasa motsa wa.

A hankali ya tako zuwa inda take tsaye, sosai ya matso kusa da ita, ya sanya hannu ya riƙe nata hannun, wani sanyi yaji cikin ransa, ya ɗago da haɓarta yana kallon fuskarta ta sauke idanunta hannunta ya soma rawa, ya ɗan yi murmushi ya ce

"Barka da zuwa Mon Ange"

Jikinta yana rawa, da ƙyar ta ce

"Ina wuni"

Ya janyota kusa da shi yana kallon fuskar ta, ta kalle shi ya sakar mata murmushi ya ce

"Ki saki jikin ki yanzu mun kasance ma'aurata, babu hijabi a sakanin mu, kin zama halak malak nawa, ni ma haka na zama mallakin ki"

Ta sauke numfashi, a hankali ya kwantar da ita a ƙirjinsa ya lumshe idanunsa, hawayen farin ciki ya gangaro maza tabbas babu abin da ya fi farin ciki mutum ya kasance da abin da musulunci ya mallaka masa, tabbas babu abin da ya fi aure, babu abin da ya fi mutum ya kasance da farin cikinsa da ya rasa Angel shi kansa bai san irin halin da zai shiga ba, yana ji ta sauƙi numfashi ya furta 

"Alhamdulillah"

Ya share hawansa ba tare da ta fahimta ba, ya ɗago da haɓarta suna kallon junansu ya ce

"Matata"

Ta yi murmushi dimple nata ya lotsa, ya sanya yatsansa kan ramin ya ce

"I really miss you Mon Ange"

Ta lumshe idanunta tana ci gaba da murmushi, ya riƙe hannunta suka zauna kan 2 seater, yana jujjuya hannunta ya ce

"Yaushe za ki yi min siffa/ ko lalle ake cewa?"

"Sai gobe"

"A yi miki ya yi kyau sosai"

"To"

"Za ku yi shagali gobe ko?"

"Eh"

Ya shafi gefen fuskarta yana lumshe idanunsa a hankali ya ce

"Gobe a hotel za ki zo mu kwana, sai jibi mu tafi Nigeria"

A hankali ta kurawa sajensa idanu, ta ce

"Mamata ba za ta bari na kwana a hotel ba"

Ya kama hannunta ya ɗaura su ka sajensa yana shafa sajen a hankali ya ce

"Ki taɓa mana ai na ki ne, ke za ki dinga gyara min a gidan mu"

Kunya ta lulluɓe ta, tana ƙoƙarin sudda kai ƙasa ya ce

"Yanzu kina matsayin matata Mama ba za ta hanaki bin mijin ki ba"

Tana ƙoƙarin janye hannunta taji saukan hot kiss kan ramin dimple nata...

______________________

To fa yara suna so su maidani tsohuwar banza😃 tsimi tsimi na tattara Alƙalamina da takardata na fito farfajiyar Tumbin Giwa😁

Best couples of the year ko kunyata ba su ji😁


Ayi hakuri da typing errors.




Comments and share fisabilillah

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol