Free chapter · Read without an account
Chapter 25
Boka ya yi wata irin dariya mai sauti, wadda ta cika ɗakin da wani yanayi na ban tsoro. Ya ɗan karkatar da kansa, ya zuba wa matar ido kafin ya ce:
“Na gaya miki tun farko cewa abin da kike nema ba abu ne mai sauƙi ba. Wannan mutumin yana riƙe da ibadarsa, yana kiyaye addu’o’insa da azkar. Saboda haka, yana da kariya sosai. Amma ki sani, ba zan ja da baya a wannan al’amari ba har sai mun cimma burinmu. Dole ne ki kasance cikin shirin fuskantar duk abin da zai biyo baya, domin wannan ba ƙaramin al’amari ba ne.”
Matar ta yi shiru na ɗan lokaci, tana kallon bokan cike da damuwa. Daga bisani ta ce:
“To, yanzu me kake so in yi? Na gaji da jira, kuma ba zan iya barin wannan al’amari ya wuce haka ba tare da na cimma burina ba. Boka, ka san irin matsin da nake ciki a wannan lokaci. Na daɗe ina jiran wannan rana, kuma ba zan iya jure ganin komai ya tafi a banza ba.”
Boka ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ɗaga kansa ya zuba mata ido. Ya yi wani murmushi mai ban tsoro kafin ya ce:
“Na rantse da abin da nake bautawa, wannan karon sai mun cimma burinmu. Ba zan ja da baya ba, kuma ba zan bari duk ƙoƙarinmu ya tafi a banza ba. Ki kwantar da hankalinki, lokaci ne kawai ya rage.”
Matar ta kalli bokan da kakkausar murya, sannan ta ce:
“Boka, na bar maka wuƙa da nama. Ba na son a samu wata tangarɗa a wannan karon. Ina son ganin an kawo ƙarshen wannan al’amari. Kada ka ba ni kunya, domin duk fatana yana kanka ne yanzu.”
Boka ya ɗan sunkuyar da kansa yana kallonta. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauki kuɗin da ta ajiye a gabansa.
“Na fahimci irin ƙuncin da kike ciki. Amma ki sani, akwai abubuwan da ba sa faruwa cikin gaggawa. Ki yi haƙuri, lokaci zai bayyana mana abin da ke ɓoye.”
Matar ta yi shiru, tana nazarin fuskarsa. Ba ta ce komai ba, amma a zuciyarta ta ƙuduri aniyar cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai ta ga burinta ya cika. Sai ta miƙe tsaye, ta gyara mayafinta, sannan ta nufi ƙofar fita.
Kafin ta kai ƙofar, muryar bokan ta dakatar da ita.
Boka ya zuba mata jajayen idanunsa masu ban tsoro, yana kallonta na ɗan lokaci kafin ya ce:
“Ki tuna da abin da na gaya miki. Kada ki bari rashin haƙuri ya sa ki tona asirinki. Ki koma gida, ki ci gaba da harkokinki kamar yadda kika saba. Idan lokaci ya yi, za ki ji daga gare ni.”
Matar ta tsaya, sannan ta juyo ta kalle shi cikin rashin gamsuwa.
“Na ji abin da ka ce, amma ka sani, ba zan iya jure wani jinkiri ba. Na gaji da ganin shi yana ci gaba da rayuwarsa cikin farin ciki, alhali kuwa ni kullum cikin damuwa nake.”
Boka ya gyara zamansa, ya ɗan ɗaga gira kafin ya ce:
“Na fahimce ki. Amma ki bar komai a hannuna.”
Matar ta ɗan zuba masa ido, ba tare da ta ƙara cewa komai ba. Daga nan ta juya ta fita. Duk da kalaman bokan, zuciyarta ba ta samu nutsuwa ba. Tana jin kamar har yanzu akwai wani abu da bai warware ba.
Sai da ta yi tafiya mai nisa kafin ta isa inda aka ajiye motarta. Da isarta, direbanta ya fito ya buɗe mata ƙofar motar. Ta shiga, sannan ya koma mazauninsa ya tada motar. Ba su tsaya ko’ina ba sai da suka isa cikin garin Abuja.
🌸 ƘARAMIN SAƘON TALLA 🌸
Masoya karatu, ga kayayyakinmu da suke nan domin masu buƙata:
🍯 Zumar Kiba
🍯 Zumar Brest
🍯 Zumar 3 in 1
📩 Domin ƙarin bayani ko yin oda, ku tuntube ni.
RUKAYYA SOKOTO ❤️