Free chapter · Read without an account

Chapter 24

by Salis M Reza · MIJIN AMAL

Chapter 24
Har zata buɗe labulen ta fito sai kuma ta fasa. Ta cire Niƙaf ɗin jikinta ta koma da baya tana tunanin to meye amfanin fitar da zata yi, ina ruwanta da zuwansa har zai dame ta. Sosai zuciyoyinta ke ta faman tafka muhawara akan taje ta ci masa mutunci ya bar musu gida. Wata zuciyar kuma na cewa idan kuma ba gurinta yazo bafa. Haka dai ta fasa fita. Amma kuma hankalinta na wajen hirar tasu. Abun mamaki sai ta tsinkayayo muryar Nana na dariya kamar wata mahaukaciya. Hakan yasa ranta ya sake ɓaci. Jikinta har rawa yake tamkar ƙaura yaji kiɗan fita dawa. Gashi bata jin abun da suke cewa. Sai tayi nufin kawai ta fita daga sabgar su. Amma ta kasa. Ta ɗauki wayarta domin ta ɗebe mata kewa. Nan ma dai hankalinta na waje. Sai kawai ta kwanta a kan gadon ko zata samu barci ya ɗauke ta. Tana kwanciya aka buɗe labulen ba tare da anyi sallama ba. Tabbas taji an buɗe, kuma zuciyarta ta sanar da ita waye. Amma wallahi ta ko kasa iya motsawa saboda mamaki da kuma rikicewa da tayi. Ya ƙaraso tsakiyar ɗakin ya ce "Amali" Ya faɗa da sigar da ya saba faɗa. Amal taji wani yarr kamar fitar wani abu daga jikinta. Wasu irin lugudan bala'i ake mata a zuciya. Ko ganinsa bata sonyi, duk da cewa wata daga cikin zuciyar tata na kwaɗayin ganinsa. Ya sake faɗin "Amali ya jiki". Yana rufe baki ta miƙe tsaye. Bata yarda ta kalli cikin idanunsa ba. Ta buɗe baki zatayi magana amma ta kasa saboda maganar ta haɗe da kuka. Ta buga masa wayar hannunta tana fashewa da kuka. Sai yayi yunkurin taɓa ta zai lallasheta. Hakan ya bata wani ƙwarin gwiwa ta ce "Kar ka sake ka taba ni, ka fita min ɗaga ki, tsinanne wawa bututu dabba wanda bai san halarci ba, in sha Allah ba zaka gama lafiya ba, sannan idan ka sake kiran sunana a rayuwarka Allah ya tsine maka albarka. Abu na karshe da nake so ya shiga tsakani na da kai shine ka rubuta min saki ka bani. Idan ba haka ba zan kai ka kotu, kuma zaka biya duk abun da kasan ka aikata min wallahi". Yasir ya ce "Amal ke ce kuw..." Kafin ya ƙarasa ta ɗauke shi da  wani irin mari wanda ake yi daga cen cikin zuciya. Ta ɗora da "Kar ka sake kiran suna na na faɗa maka". Ya riƙe gurin yana kallonta. Ta ce "Zaka fita ko sai na maka ihu?". Ta faɗa tana kallon cikin idanunsa. Ya ce Amal ni..." Ta sake ɗauke shi da marin da yafi na farkon. Daidai lokacin Mama da Nana suka shigo ɗakin suna kallon ikon Allah. Ta ce "Ka fita min daga ɗaki nace tsinanne mara kunyar Ubangijin sa". Ta faɗa tana neman wani abu a ɗakin da zata rafka masa. Sai dai bata ga abin da zai mata daidai ba. Mama ta ce "Amal meye haka, kinyi hauka ne, mijin naki kike wa wannan rashin hankalin harda mari?" "Allah ya tsinewa wanda ya sake cewa mijina ne, kuma mai yasa ma zaki barshi ya shigo min ɗaki, akan me, me na haɗa dashi dan uwarsa". Ta faɗa cikin kuka da rufewar ido wanda yasa ita kanta Mama ta tsorata. Daidai lokacin kuwa ta hango wani dutsen guga wanda basa ma amfani da shi. Ta sungumo shi ta yo kansa. Gaba ɗaya suka kwasa a guje daga shi har Mama da Nana. Yana zuwa tsakar gidan ya tsaya yana binta da kallo ya kasa magana. Yana mamakin wai Amal ce Wanna. Ai kuwa bai nufa ba yaga ta wurgo masa da ƙarfinta. Allah ya bashi sa'a ya matsa. Ta ce "Wallahi tallahi Mama idan har ana barin sa ya shigo gidan nan to ni zan bar muku gidan. Na tsane shi, na tsani ko ganinsa da duk abin da ya shafe shi". Yasir ya juya da baya ya bar gidan ya shiga mota. Bai tsaya ko ina ba sai gidan sa. Ya faka motar ya fito ya shiga. Ya zama a palo yana sauke ajiyar zuciya daidai lokacin kuma wayarsa ke ƙara. Ganin dai wannan number ce da ake yawan kiransa tun ɗazun sai ya ɗaga yana yin shiru. Ya tsinkayayo muryar Mace ta na gaida shi. Ya masa da tambayar wacce. Ta ce "Ina ta kira tun ɗazu baka amsa wa". "Wacece ke? Mai yasa kika kira ni?" "Ina so ka faɗa min dalilin da yasa baka daga ba". Sai kawai ya kashe wayar yana tsaki domin ya gane mai maganar. Ya tashi ya kunna Tv ko zai daina jin sautin muryar Amal na kiransa da wadannan sunayen ƙiyayyar. Afili ya ce "Allah na tuba, kafi kowa sanin cewar ina son mata na". Ganin ana sake kiransa da number ɗazu ne ya kashe wayar gaba ɗaya. Sai kuma ya tuno da wani abu. Ya kunna wayar yana jiran a sake kiransa. Ai kuwa sai ga kiran ya daga yana sallama.

Sosai Mama ta hauta da faɗa kamar zata dake ta. Ta inda ta ke shiga bata fita ta gurin. Amal ko tari bata mata ba. Ita dai a ranta tana jin muddin zai sake zuwa gidan nan idan da wuka a kusa zata iya burma masa wallahi. Haka ta ƙaraci faɗanta ta gama. A cikin faɗan ne har Mama tana cewa ta bashi dama taji mai yazo da shi. Kuma ta fahimci hakan ne ganin ya bata kuɗi. Wato ita dai Mama idan kana da kuɗi shikenan, kaman ba Yasir bane mutumin da ta tsana a baya ba, yau shi take bawa kariya duk da abun da yayi mata, dan kawai yana da kuɗi. Wani sabon salo ma ta fara yabon sa da faɗin ita bata ma san cewar yana son ta har haka ba sai yanzu. Ita ma Nana sai da maganar ta bata dariya. Haka har bayan kwana biyu kullum Mama a maganar Yasir take. A kwana na uku ne tana bayan gida tana wanka taji shi shigowarsa. Abun mamaki kamar ba shi ɗaya bane. Ta gane hakan ne ta yadda Mama take musu maraba da kalmar jam'u. Hakan yasa taƙi fitowa daga bayan gidan duk da babu ko siminti a ciki. Bayan ta gama ta zauna a ciki tana jin Mama na kiran sunanta. Ganin abun yayi yawa yasa maman da kanta ta leƙo toilet ɗin. Ta sameta zaune tana hawaye. Mama ta tafa hannu tana kallonta da salati. Ta ce "Amal bayan gida gurin matattarar aljannu nan kika zauna hankalin ki kwance baki ko tsoron kwasar cuta?" Ta gyra zama bata ce kaomi ba sai share hawaye. "To kinyi baƙi suna jiranki". "Wallahi ba zan fito ba, koma su waye bana son ganinsu, domin ni bani da wasu baƙi". Mama ta ce "Ba ke kika ce saki kike so ba? To sai ki taso ki amshi takardar". Mama ta faɗa tana juyawa. "To Mama ki amsar min wallahi bana son ko ganin sa ne". Ta faɗa da farinciki. "Ashe baki son sakin kenan". Amal ta yi jim kaɗan Kamar gabanta ne ke faɗuwa. Sai kuwa tayo waje. Tana fitowa ta shige ɗaki ta ɗora hijjabi ta fito. Da mamaki take kallon sa tare da Ali. Ɗaya daga cikin mutanen da ta tsana a duniya bayan Yasir. Mutumin da rabon da ta ganshi ma ta manta. Tana daga tsayen ta ce "Ina takardar Ku bani takardata ku bar mana gida". Yasir ya ciro takardar daga aljihu ya miƙa mata jikinsa har rawa ya keyi. Tana amsa suka miƙe suna yiwa Mama sai an jima. Sukayi waje. Suna fita Ali ya ce "Wai meye haka ne Yasir, ya kana abu kamar ba namiji ba, ji yadda kake wani tsoro kamar wanda ya haɗu da abin tsoro". "Ba zaka gane bane". Ali ya ce "To ni na rasa gane dalilin ka na yin hakan. Gaka ga ita ma bata ko iya kallonka ba, sai a wasika ne zata saurareka. Yarinyar nan tana sonka, kuma ka mata laifi, so dole ne ka tunkareta ka jure komai, ba wannan hanyar ba. Jifa ko kallon arziki bamu samu ba, yarinyar da gaisuwa sama da ƙasa. Ga wani girma na da take gani. Yanzu duk ka zubar min da shi a wani banzan dalilin ka da kuma shirmen ka". Daga haka suka bar gurin Yasir na faɗin in sha Allah idan har ta karanta zata saurare ni". 

Tana shiga ɗaki ta fito da takardar ta fara karantawa. Ko nisa batayi ba ta yaga ta nana tsaki da alwashin kai shi kotu. Bama zatayi shawara da kowa ba. Kaman ta kira Hafsa amma har yanzu haushin ta take ji. To wa zata kira ya taimaka mata. Sai ta tuna da maganar da yaya yayi akan cewar idan har ya dawo bai saketa ba shi zai tsaya mata ko kotu ne ya kai domin ya saketa. Hakan yasa washegari ta shirya ta faki idon Mama ta fita. Da yake sanyi take da niƙaf take ba wanda ya ganeta har ta isa gidan. Allah yasa kuwa ta same shi zai fita. Ganin haka yace su shiga cikin gidan amma tace a'a ba sai sun shiga ba. Ta faɗa masa abun da ke tafe da ita. Yaya ya gama sauraron ta. Ya ce "Yanzu kina so a kai shi kotu ne saboda ya sake ki?" Ta ɗaga kai. Ya ce "Tabbas ina tare dake, kuma dama na miki wannan alkawarin. To amma kunyi magana da shi ne yace ba zai sake ki ba?" Ta sake ɗaga kai. Ya ce "To an gama, ina mai tabbatar miki cewar ko yaso ko bai so ba sai ya rabu dake. Ki koma gida zan neme ki". Ta ce "Wannan Monday ɗin nake so na shigar a shigar da ƙarar".  Ya ce "Jibi kenan ko?" Ta ɗaga kai. 

Daga haka ta dawo gida. lokacin Mama ta gaji da nemanta, tayi zaton ma ko ta gudu ne Kamar yadda take cewa, to amma ga kayanta komai da komai harda waya da magungunan ta. Tana ganinta kuwa ta fara tambayar ina taje bata faɗa mata ba, bata da hankali ne, kuma ko ta manta ita mata an hata fita ne, sannan kuma a idda take. Haka ko tari bata mata ba ta shige ɗaki abun ta. Ta cire Niƙaf da hijabin ta zo gaban madubi tana kallon kanta. Ta tuno farkon haɗuwarsu, har da ranar da aka daura musu aure. Da irin rayuwar da suke yi da kuma abun da yayi mata da kuma yanzu da yake nuna yana so su ci gaba da zaman aure. Idan ta auna sai taga to me yasa baiji aransa cewar abun da yayi budulci bane. Mai yasa ba zai mata adalci ya rabu da ita ba. Mai yasa ba zai fahimci yanzu ta tsane shi bane. Haka ta ƙaraci kukanta ita ɗaya a ɗaki. Ganin taki fitowa ne yasa Mama ta shigo ɗakin tana binta da kallo. Ta ce "Kin kuwa gamu da aiki wallahi, ina ce kece kika buƙaci sakin nan, kuma gashi an miki, to kukan na menene?" Ta faɗa tana ƙaraso gurin da take, Kuma ranta a bace domin taji haushin sakin. Amal ta ce "Mama bai sake ni ba, sakon haƙuri kawai ya turo min. Mama na rasa yadda zanyi. Wallahi bana ko son Jin muryar sa". Mama tayi shiru jin babu sakin. Ta ce "Da gaske kin daina sonsa? Da gaske kin tsane sa?" Ta ce "Eh Mama, na tsane komai nasa". "To amma saboda me?" Amal ta ɗago kai da sauri suka haɗa ido. Ta ce "Mama abar maganar". "To an barta. Itama maman ta faɗa. Haka washegari ma ya dawo shi ɗaya. Wannan karan ma ya dinga roƙon ta bashi lokaci suyi magana, bayan taji Komai zai ce sai ya yanke hukunci. Wannan karan harda ruwa ta matsa masa. Da ikirarin kisa. Har lokacin dai Mama bata cewa komai. Kaman yadda kuwa suka shirya da yaya. Ranar Monday ya kirata akan tazo suje. Bata ɓoyewa Mama ba, itama tai mata fatan nasara bata hana ta ba. Domin tayi alkawarin ba zata sake cewa komai ba. Tana fitowa kuwa sai ga motarsa ta faka. Yayi saurin fitowa yana jin dadin ganinta da yayi a waje, ya sha gabanta har yana riƙe mata hannu. Cikin wata murya mai Kama da ta yaudara kuma ta neman afuwa ya ce "Amal da gaske kotu zaki kaini? Ba zaki bani ko minti biyar muyi magana ba, yanzu Yaya yake faɗa min cewar idan ban baki takarda ba zaki kaini kotu, haba mana Amal duk abin da ya faru a baya ya wuce mana, wallahi na miki alƙawarin..." Kafin ya karasa ta ɗauke shi da mari har uku, tana jin wani sabon tsanar tasa. Ta ce "Sau Uku ka kira sunana, kuma dama na faɗa maka idan har bakinka ya sake kiran sunana sai na mare ka. Kuma ba iya ƙara ba. Wallahi duk abun da ka mun sai na faɗa a kotu an bi min kadi tun da kai jahili ne ɗan a ku..." Kafin ya rufe baki ya haɗe bakin nasu guri ɗaya yana matseta a jikinsa. Gaba ɗaya ya manta a waje suke. Amal ta kwaɗa wani irin ihu tana ƙwace jikinta tana kiran korto kuma ñarawo ɗan iska. Lokaci ɗaya yan unguwar suka taso, dama safiya ce, kuma ihun ne ya bawa kowa damar ganin su. Wasu da sanda wasu da itace. Suna zuwa kuwa suka same shi har lokacin bai sake ta ba. Suka raba jikinsu suka fara dukkansa. Suna dukansa wasu na jifan sa harda naushhi ana kiran kwarto. Wasu daga ciki sun gane shi, dama kowa nada labarin abun da ya faru. Sosai suka dinga dukansa har sai da Mama ta fito ta shiga tsakani tana kare shi, itama ta samu rabonta. Ko motsi baya yi, gurin da suka fashe a jikinsa ba zasu irgu ba, kan nan nasa ta ko ta ina jini ya keyi. Motsi mai kyau ma baya iya yi. Ita kanta Amal abun ya bata tsiro domin yadda kasan gawa haka ya koma. Wasu daga ciki suna sake yunƙurin kai masa duka amma wasu na hanawa. Wasu ma na faɗin ai ya riga ya mutu. Wasu manyan unguwar da sai yanzu suka ƙaraso. Sune suka Kama aka saka shi a Mota akayi asibiti da shi. Amal dai tuni ta shige cikin gidan tana kuka...📝


Mijin Amal

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol