Free chapter · Read without an account
Chapter 25
by Salis M Reza · MIJIN AMAL
*MIJIN AMAL*
*FREE BOOK*
*Chapter 25*
Sosai take kuka wanda ta rasa gane ko kukan menene. Farinciki da kuma tsoro ne fall cikin ranta. Dama tayi ihun ne domin a masa hakan kuma gashi anyi. Sai dai dukan yayi yawa kar suyi masa illa. Tana cikin wannan halin Mama ta shigo cikin gidan da kuka domin itama an buga mata dutse akai. Sai dai gurin bai fashe ba, amma taki zafi kwarai da gaske. Sannan hankalinta ya tashi da yadda taga Yasir ɗin. Bata ko kalli Amal ba ta ɗauki mayafi ta fita tana kuka. Amal ta bita da kallon mamaki domin dai ta gane cewar asibiti zata je. Hakan ya sake ƙona mata rai. Wai me Mama take nufi ne, da gaske tana son Yasir ne, to wallahi ba za ta saɓu ba bari ma kawai ayi ta ta ƙare. Take ta naimi tausayin da ta fara masa na daukan da ya sha ma ta rasa. Ta share hawaye tana jin ina ma sun masa dukan da ko ya ganta a hanya ba zai iya gane taba. Sai take jin ina ma su bishi har asibitin suyi masa shegen duka wanda yafi na yanzu. Ta ɗauki buta ta wanke idanunta da bakinta. Sannan ta ɗauki waya ta nemo number Yaya ta kira. Tana shiga kuwa ya ɗaga ta ce "Kana gida ne Yaya?". "Eh ke nake jira tun ɗazu". "Tom ka biyo ta gida ka ɗauke ni, ba kowa a gidan namu". "To ina nan zuwa". Tana kashe wayar sai ga kiran Hafsa. Taja tsaki tayi banza da ita. Bayan ta katse ta sake kira. Ta ɗaga tace "Hafsa lafiya dai irin wannan kira?" Hafsah ta ce "Wai Yasir yazo gidan ku?" Amal taji tambayar wani iri. Ta ce "Hafsa ba nace ki daina min maganar sa ba? Wai ina ruwanki da rayuwata ne dan Allah, to daga yanzu bana ma so ki sake ko kiran number na pls". Ta faɗa tana ƙoƙarin kashe wayar. Ta ce "Dan tsaya mana masifaffiyar dole, gaba ɗaya kin mayar da kanki wata bala'i, to ba wai ina nufin wani abu ba. kawai ina mamakin ƙarfin halinsa ne, bayan duk abun da ya faru, kuma har ya samu ƙwarin gwiwar zuwa har gidan ku. Dan Allah idan da gaske ne dama dai kin ci masa mutunci kin zagi babarsa da babansa. Idan ma kina bukatar zagi mai gunna da mai tajwidi duk ki min magana zan turo miki". Ta karasa tana dariya. Amal ta ce "Bana so". Ta kashe wayar tana jin ba dad'i a ranta. Gaba ɗaya bata da riƙo amma har yanzu haushin Hafsa take ji wallahi ta rasa mai yasa. Tashi tayi ta sake kayan jikinta. Ta shirya ta fito tana ƙoƙarin rufe ɗakin nasu sai ga Nana.
"Ina zaki je anty Amal?" Nana ta faɗa tana shigowa gidan.
"Daga ina keke tun ɗazu?". Itama ta tambaye ta ba tare da ta amsa mata ba.
"Asibiti mana, kin manta nace miki zanje awu ne? Sannan mai ya faru tsakanin ki da Yasir, naji ana ta min gulma tun ina kan hanya?".
"Wannan bai shafe ki ba. Ga gidan nan Mama bata nan. Nima zanje wani guri ne dan Allah kar ki fita ko ina".
Bata daɗe ta fitowa ba kuwa sai ga motar Yaya ya buɗe mata ta shiga. Ya kama hanya. Suna tafiya ba mai magana a cikinsu tun bayan gaisuwar da tai masa ya amsa. Ya katse shirun da faɗin "Kina dai shan magani akan lokaci ko?" Ta ɗaga masa kai. Shi dai yana mamakin yadda bata iya masa magana sai ɗaga kai. Ya sake faɗin "Kicigaba da haƙuri, kaomi mai wucewa ne in sha Allah kinji?" Ta sake ɗaga masa kai. Har sai mata wata maganar wayar sa ta hau ƙara. Ya ɗaga da sallama da girmamawa har yana faka motar a gefe. Wanda hakan ya tabbatar da babban mutum ne a gurinsa. Minti ɗaya yayi yana sauraron wayar. Sannan ya ce "Okay Sr, bani minti biyar ɗaki mai lamba 308 ko?". Ya amsa masa da cewar eh. Daga haka ya kashe wayar. Ya kalleta ya tada motar ya ce "Wani uban gida nane da nakewa aiki ya naimi ganina yanzu. So dan Allah zakiyi hakuri muje zan shiga ba zan fi minti goma ba zan fito sai mu karasa". Bata ce komai ba, sai kai da ta sake ɗagawa alamar ba komai. A wani babban hotel ya faka motar. Ya kalleta yace "Minti goma zan dawo, kar ki fita ko ina fa". Ya fito daga cikin motar ya nufi cikin hotel ɗin. Kamar ance ta kalli gurin da ya dosa, idanunta suka sauka akan mutumin dake tsaye yana ganinsa suka rungume juna. Da sauri ta sake kallonsa gabanta na faɗuwa. Da yake mutumin motar tasu yake kallo yasa tai masa kallon tsaf kuma ta tabbatar da shine. Daga haka suka shige ciki. Amal ta ciro wayarta ta kira Nana. Kira ɗaya ta ɗaga ta ce "Nana turo min hoton mijinki yanzu-yanzu please?" Nana ta ce "Mijina kuma, mai zai miki?" "Dalla ki turo min yanzu nace". Ta faɗa da masifa tana kashe wayar, sannan ta kunna data tana jiranta. Shiru-shiru Nana bata hau online ba, har minti biyu. Hakan yasa ta sake kiranta. Tana ɗagawa ta ce "Dan uwar ki Nana ba zaki turo min bane?" Cike da rashin yarda ta ce "Wai me zakiyi da hoton sa ne, to ni dai bani da data ma, mutumin ma da bama tare, har yanzu bai neme ni ba". Amal ta kashe tana tsaki. Sai ta fara tunanin wayar da taji yana yi ɗazu. Tabbas ya fadi number ɗakin da yake ciki. Ta rufe ido tana bubbuga kanta da yatsa ɗaya tana kokarin tunanowa. Amma ina ta kasa. Ta ce "Ya Allah". Ta sake yin shiru tana sake tariyowa tun fitowarta gida da hirar da yayi mata. "Okay Sr, bani minti biyar ɗaki mai lamba 308 ko?". Take maganar ta dawo mata akai kamar yanzu yake faɗa. Afili ta ce "Yes 308" Ta buɗe motar ta fito ta shiga cikin hotel ɗin. Ta ƙarasa gurin masu tarɓar Costormars tana tambayar su ina ne zata bi taje ɗaki mai number 308. Nan take suka nuna mata inda zata bi. Haka ta fara hawa sama gabanta na faɗuwa. Tana irga number har tazo kansa. Ta tsaya tana tunanin mai zatayi. Ga wani irin duka da gabanta keyi na fargaba. Ta dake, tana ji a ranta tabbas shine. Har zata bubbuga kuma tana tsoron kar a tambaya waye. Kuma kar taje ta buɗe ta shiga kuma ba shi bane. To idan ma bashi bane sai ta ce ma Yaya wasu ne suke son saceta a waje shine ta gudo nan. Hakan yasa ta murɗa ƙofar da karfi ta tura ta shiga kanta tsayae.
Take idanunta sukayi ganin da bata taɓa tsammani ba. Hankalinta ya tashi ta rikice, gashi su basu ma kula da Ita. Ta tsaya a gurin ta kasa gaba ko baya kuma ta kasa ihu. Abun ne take ganin sa kamar dai mafarki kuma kamar tunani take yi. Yaya ne da Mijin Nana aihuwar uwarsu suna aikata abun da ba zai faɗu a baki da tunanin ta ba. Surukanta guda biyu a wannan yanayin, astagfurullah. Sai lokacin wani matashin ihu ya zo mata. Wanda suma suka tsorata suna kallonta. Da sauri kowa yaja bargo suna rufe jiki. Amal ta rufe ido da hannu biyu ta juya a guje tana kuka.
Dole sai da aka je aka zo da yan sanda kafin likitoci suka amshi shi. Nan suka fara wanke masa ciwukan. Bayan kusan minti talatin likitan ya fito ya samu Ali da sauran mutanen da suka kawo shi. Yake sanar dasu cewar dole za'ayi masa scainin akai ko jini ya shiga cikin kansa, saboda akwai babban ciwon da sai an masa ɗinki. Bayan an duba kuwa aka tabbatar da hakan ta faru. Ba'a fara aikin ba sai da Ali ya chake kuɗin aikin kafin aka fara masa aiki. Har lokacin da aka gama bai san inda kansa yake ba. Likitan ya naimi Ali wanda tun da za'a shiga akin sauran mutanen suka tafi. Bayan sun zauna likitan ya ce,
"Waye kai a gurinsa?"
"Abokinsa ne?"
"Ko zan iya ganin wani nasa bayan kai?"
"Yanzu dai babu, ni ɗin dai kawai nine ɗan uwansa. Amma mai ya faru?"
"Eh ba wani abu bane, kawai dai wata ƴar matsala ce. Amma bari nai maka bayani. Game da abun da ya samu abokinka ne. Jini ya taɓa ƙwaƙwalwarsa kamar yadda muka yi hasashe. Kuma muddin jini ya shiga wannan sashen dole mutum na iya kamuwa da wasu ciwukan da yanzu zan maka bayani...
"Idan aka ce jini ya taɓa ƙwaƙwalwar mutum, to ana nufin cewa wani jijiyar jini ta fashe ko kuma jini ya shiga cikin ƙwaƙwalwa ko kewaye da ita. Wannan matsala ce mai hatsari da ake kira Brain hemorrhage. Ga wasu abubuwan da za su iya faruwa da mutum idan jini ya shiga cikin gurin. Mutum zai iya fama da ciwon kai mai tsanani akai-akai, wanda zai hana shi sukuni. Ko kuma wani ɓangare na jiki, kamar hannu ko ƙafa, zai iya kasa motsi wato shanyewa. Ko kuma mutum zai iya kasa magana sosai ko kuma ya kasa fahimtar abin da ake gaya masa, wato saurin mantuwa da kuma manta komai da yake yi. Ko kuma ganinsa zai iya disashewa ko ya samu matsala a idanun nasa. Ko kuma zai iya kasa tafiya ko tsayuwa yadda ya kamata. A wasu lokuta kuma mutum zai iya suma ko ya shiga halin rashin sanin abin da ke faruwa. Babban matsalar kuma da ake tsoro itace matsalar ƙwaƙwalwar gaba ɗaya. Zai iya samun matsalar tunani, fahimta ko mantuwa wanda sune dama aikin ƙwaƙwalwa, idan ta samu matsala to ba shi da wannan abun.
Ali ya ce "Innalillahi likita yanzu likita daga ɗan wannan abun ne ya samu wannan ciwon ko ma?" "No bai fa samu ba, ina faɗa maka abun da zai iya faruwa da shi ne idan ya tashi, saboda jini ya taɓa ƙwaƙwalwar sa, wanda cikin ɗaya dole zai faru. A yanzu dai mun gama aikin mu, saboda gurin da jinin ya taɓa ne yasa nake maka wannan bayanin. Idan kuma Allah yaso ma sai ya tashi babu kowanne daga ciki, amma abu ne mai kamar wahala". "To amma likita, idan hakan ya faru ana iya warkewa dai ko?".
"Eh, akwai mutanen da suke samun cikakkiyar lafiya bayan an yi musu magani. Wasu kuma suna iya kasancewa da nakasa ko matsalar tunani na wani lokaci ko na dogon lokaci. Hakan ya danganta da ina jinin ya shiga. Yawan jinin agurin da ya shiga ɗin. Da kuma irin samun kulawar likita da mutum ya zamu. Kamar dai shi wannan kun kawo shi asibiti a kan lokaci, wanda muna sa ran in sha Allah komai zai zo da sauki". "Ina sha Allah ma ba abun da zai faru". Ali ya faɗa yana tashi. "To Allah yasa". Bayan ya fito hankalinsa ya tashi da wannan jawabin. Yana ta tunanin to a ina akai masa wannan dukan domin shi dai number Yasir ya kira aka ce yana asibiti, shine da yazo yaga halin da yake ciki bai tsaya tambaya ba. Yana zama ya hango Mama ta shigo asibitin tana kuka. Ya karasa gurinta yana mata magana.
Suna cikin tsaka da tashin hankali da abun da ya faru. Yayin da mutumin ke tambayar wacece ita. Yaya kuma ba masa ƙarin bayani suka ji ana buga musu ƙofa. Suka kalli juna kowa ya kasa magana. Aka sake bubbugawa nan ma su kayi shiru. Mutumin ya tambaya waye. Yana cigaba da zagin yaya da ɗora masa laifin mai zai sa ya zo da Mace nan, dama ashe bashi da hankali. Daga waje aka ce idan basu buɗe ba za'a fasa kofar a shigo. Hakan yasa suka buɗe suna ɗaga hannu sama ganin Amal tare da yan sanda. Haka aka tattara su izuwa police station mutumin na tambayar mai ya faru mai suka aikata. Dama tun lokacin da ta fito tayi nufin ta gudu saboda ta tsorata, kuma bata san abin da zata iya yi ba. Amma taga police station a kusa da ita shine ta yanke wannan shawarar. Sannan ta kira Nana ta faɗa mata. Suna shiga kuwa itama ta ƙaraso cike da addu'ar Allah yasa shine. Tana ganin sa kuwa tace shine tana kuka. Nan suka faɗi abun da ya faru akan cewar ya auri ƙanwarta ya mata ciki ya gudu. Mutumin ya kalli Nana da mamaki wai ya aureta. Tabbas ya santa, kuma ya nuna yana sonta, amma yaushe ya aure ta, a ina ta yaya. Abun ya ɗaure masa kai. Yace shi wallahi bai aureta ba, ya dai taɓa ganinta yaji yana sonta suka fara soyayya, daga ma shi bai sake gwaninta ba. Yaya dai ya kasa haɗa ido da Amal, kuma yana ta mamakin wannan lamari. Wata irin kunya yake ji, amma ita ko ta kansa ma bata bi. Nana kuwa sai kuka take ganin da gaske ƙaryata wa yake yi wai asu yi aure ba.
Su kansu Police abun ya rikita su, hakan yasa suka ce to wannan kotu za'a kai su domin acen ne za'a tabbatar da gaskiyar kowa. Ai kuwa take aka tattara su gaba ɗaya. Yaya dai aka sake shi domin shi baya cikin maganar. Yana so yayi mata magana amma ya kasa. Ganin zata tafi ne bata ko kalleshi ba, tayi ƙarfin halin faɗin "Dan Allah bana so kowa ya san da wannan abun da kika gani, na roƙe ki dan Allah Amal, ki rufa min asiri, wallahi gaddara ce da ikon Allah?" Ya faɗa cike da matsananciyar kunya mai kashe mutum. Ko lokacin da Yasir ya kama shi bai ji irin wannan kunyar ba. Wani hawaye guda ɗaya mai kauri ya gangaro kumatunta ta ce "Da irin wannan kuɗin aka mun aiki ko?". Ta faɗa tana ɗauke hawayen da hannu ɗaya kuma bata ko iya kallonsa domin kamar ma ta fi shi jin kunyar abun. Ta ɗora da cewar "Ban san yaya nake ji ba, ban ma san mai zance ba. Babu wanda zaiji amma ina so dan Allah a yau kasa ƙaninka ya sake ni, kuma kace masa na gode da zubar min da ciki da yayi da ban haɗa zuri'a da ku ba. Na gode masa, sosai na gode, na gode". Ta cigaba da faɗar kalmar kuka na zuwar mata mai sauti. Take shima wani irin hawayen nadama suka fara zubo masa. Ya ce "Bada irin wannan kuɗin bane aka miki aiki ba, kuma ina so ka bawa..." "Ya isa dan Allah, bana son Jin komai. Kafin yamma na ga takarda ta a gida, idan ba haka ba". Tana faɗa tayi gaba ta barshi a bakin gurin yana hawaye yana binta da kallo. Bai taɓa jin nadama da kunya irin na yau ba. Wani irin tonon asiri ne wannan sai da ya kusa kammala aikin haka zata faru. Ya amshi wayrsa a gurinsu da makullin motarsa ya bar gurin. Yana fita daga motar bayan ya isa gida kiran Ali na sake shigo masa wanda tun ɗazu yaga miss calls din sa. Ya amsa yana ƙoƙarin shiga gida yana danne halin da yake ciki. Sai dai bayanin da Alin yake masa ne yasa ya juyo da baya ya shiga motar ya ɗauki hanyar asibiti yana kiran sunan Allah.
Bangaren Amal kuwa take ta dinga kiran yan uwa akan an samu mijin Nana. Amma har lokacin yana nan akan bakan sa shi bai aureta ba. Alkalin ya jasu ofishin sa domin ayi abun a sirrince amma dai lamari dai babu makama. Ga wanda suka bashi auran harda wasu da aka ɗaura auran dasu a gurin sunce shine amma ya ce bai fa aureta ba. Shi wallahi idan ba da ya ganta bama ya manta da Ita. Karshe ma harda hoton su lokacin suna ƙasashen waje, da wanda suke a hotel-hotel. Kuma shine a ciki amma yace wannan AI ne ba na gaskiya bane. Shi dai yace ya santa, amma bai aure ta ba. Kuma yasan sun fara soyayya amma shi dai bai je kowacce ƙasa da ita ba. Abun ya fara bawa Amal tsoro ganin kamar fa gaskiya yake faɗa. Alƙali ya ce "To wani abu ya shiga tsakaninku da ita ne a lokacin da kuke soyayya, tunda gashi ance harda ciki?" Ya ce "Ranka shi dade, kofa sati bamuyi da haɗuwa ba muka rabu, wallahi ko hannunta ban taɓa riƙewa ba". Nana ta fashe da kuka tana ƙaryata shi. Amal dai ta kalli Nana ta kalle shi domin ita ma sheda ce saboda har gidan ta sun zo harda kuɗi ya bata, kuma lokacin suna da sure. "To kenan cikin ba naka bane?" "To ana samun ciki haka kawai ne Yallaɓai". Alƙali ya juyo ga Nana yace ta faɗi gaskiya kar ta bawa Shari'a wahala. Ta fashe da kuka mai cin rai ganin irin wannan tonon dililn akan cikin da kowa ya san na aure ne, amma ana so a haukata ta. Tana ta fara rantsuwa da Allah akan cewar cikin sa ne kuma da aure. Wanda ya bada auran ya ce "Wallahi tallahi nine nan na bashi auran yarinyar nan da hannuna, ga wannan sune shedu, kawai raina mana wayo yake sonyi". Mutumin shima yayi rantsuwa Kamar yadda Nana take yi yana mamakin wannan ƙarfin halin nasu. Kan alkali ya cika, to amma ai ga hotuna, kuma yace AI ne, to bari a kai a bincika a tabbatar ko na gaske ne. Ya ce "To lokacin da aka yi auran a wacce unguwar kuka tare kuma zaki iya kaimu gidan?...📝
Wai me ke faruwa ne?😅